Ticker

6/recent/ticker-posts

Neman Addu'ar Samun Mijin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum da ftn malam Yana lfy. Dan Allah malam ina so a taimaka min da wata addu'a Wanda Zan dinga yi dan na samu mijin aure. Allah ya jarabceni da jinkirin aure shi ne nake neman taimako na addu'a ko Zan samu mafita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Abu na farko da zanyi miki wasici dashi shi ne ki Ƙara haƙuri da juriya bisa wannan jarrabawar da Allah ya dora miki. Ki sani cewa akwai wasu da dama waɗanda musibar da suke ciki ta ninninka taki. Kuma ki sani cewa Allah bai manta dake ba. Yana sane dake da kuma halin da kike ciki. Kuma da sannu zai yaye miki damuwarki cikin falalarsa.

Ga wasu daga Sahihan addu'o'i nan ki rikesu ki rikayi. In Shã Allahu zaki ga biyan bukata cikin sauki:

1. Ayah ta 3-4 a cikin suratut Talaƙ:

وَمَن يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَل لَّهُ مَخْرَجاً -وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْراً

Yazo a cikin Musnad na Imamu Ahmad bn Hanbal, Hadisi daga Sayyiduna Abu Dharrin Al Gifariy (Allah ya yarda dashi) yace "Manzon Allah ﷺ bai gushe ba, yana karanta mun wannan ayar, sannan yace "YA ABA DHARRIN, DA ACHE DUKKAN MUTANE ZA SUYI RUKO DA WANNAN AYAR DA TA ISHESU".

(Aduba Musnadu Ahmad juzu'i na 5 shafi na 178).

Don haka ki rike wannan ayar ki rika yin wuridinta da kyakkyawar niyyah. In Shã Allahu zaki samu biyan bukata cikin sauki.

Bayan wannan akwai yawaita istighfari. Hadisi ya inganta daga Muhammad dan Aliyu dan Abbas ya karbo daga babansa, daga Ka kansa Sayyiduna Abdullahi dan Abbas (Allah ya yarda dasu) yace Manzon Allah ﷺ ya ce:

"DUK WANDA YA YAWAITA ISTIGHFARI, ALLAH ZAI SANYA MASA YAYEWA DAGA KOWACCE DAMUWA, DA MAFITA DAGA KOWANNE TSANANI, KUMA ZAI AZURTASHI TA INDA DUK BA YA TSAMMANI".

(Musnadu Ahmad juzu'i na 1 shafi na 248).

Ki yawaita sadaƙah domin itama hanya ce ta samun yayewar tsanani da kuma biyan bukatu. Sannan shima istighfarin ki rika yin daruruwa ko dubunnai a kullum.

Hakanan ki yawaita salati bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu ﷺ. Shima babbar hanya ce ta samun biyan bukatu da yayewar damuwa in Shã Allahu.

Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki ya biya miki bukatunki ya yaye miki damuwarki, kuma ya azurtaki da samun miji nagari wanda zai rikeki cikin mutunci.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments