Gudanar da rayuwar mai inganci tana buƙatar jagorancin mutane masu amana da sanin yakamata. Wannan takarda mai taken salon “ Kambamawa a cikin wasu waƙoƙin kassu zurmi” Takarda ce wadda take ƙoƙarin bayyana irin rawar da salon kambamawa take takawa ga rayuwar jaruman mutane, mutane suna son a riƙa zuga su, su yi wani aiki na mazantaka, wanda idan ba a kambamasu ba, ba za su iya aiwatar da shi ba saboda haka wannan takarda za ta mayar da hankali ga salon kambamawar kassu zurmi da yake amfani da ita cikin waƙoƙinsa na maza, domin ya ƙara ingiza wanda yake yi wa waƙa, su aikata abin bajinta.
Salon Kambamawa A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu
Zurmi
RABI S. ZAMFARA
GODIYA
Ina godiya ga Allah subhanahu
wata’ala da ya ba ni damar gudanar da wannan binciken bisa ga ikonsa da
taimakonsa. Haka kuma ina ƙara godiya ta ga shugaban halitta Annabi Muhammad
(S.A.W).
Haka kuma wannan aiki na da
matuƙar wahala a aikatashi ba tare da an samu mataimaka ba. Don haka ya zama
dole in miƙa godiyata ga malammaina waɗanda suka taimakamani musamman malamar
da ta duba ni Malama Halima Mansur Kurawa Allah ya saka mata da mafificin
alhairi Amin.
Bugu da ƙari ina godewa iyayena da
kuma musamman maigidana Alhaji Labaran Abubakar Zurmi wanda ya taimaka mani
matuƙa wajen gudanar da wannan karatu har kawowa yanzu.
Haka zalika ina miƙa godiya ta ga
duk wanda ya taimaka mani wajen ganin na kammala wannan karatu kamar Aliyu S/
Zamfara, Shehu S/ Zamfara da kuma ƙaunata Binta Sani Nakwada, Asma’u S/ Zamfara
da sauransu. Daga ƙarshe ina ƙara godewa Allah da ya gwada mani na kawo ƙarshen
wannan binciken.
SADAUKARWA
Na
sadaukar da wannan bincike ga mahaifina Alhaji Muhammadu Mainasara (Sarkin
Zamfaran Zurmi) Allah ya jiƙansa da rahama Amin.
BABI NA
ƊAYA
1.0
SHIMFIƊA
Hausawa na cewa “Tushiya mafarin dawa" Duk
abin da za ka yi a duniya ya kamata ka gabatar da shi kafin ka fara bayani a
kansa saboda haka dukkan lokacin da aka yi maganar kambamawa ga al'ummar Hausa
sai ace abu ne bayyananne musamman idan aka yi magana a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Kassu Zurmi.
A bisa ƙashin gaskiya makaɗa da mawaƙan Hausa
na kambama ko zuga wanda ya basu kyauta da kuma wanda ya nuna bajinta ko ƙwazo
domin ya yi wani abu da bai ta shi yi ba.
Saboda haka aka gabatar da wannan bincike mai
taken salon kambamawa a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi. An kasa wannan bincike akan
babi-babi har zuwa babi biyar.
Babi na farko an yi gabatarwa, da manufar
bincike, hasashen bincike farfajiyar gudanar da bincike, matsalolin bincike,
muhimmancin bincike, hanyoyin bincike, sai kuma naɗewa.
A babi na biyu za’a yi bayani akan bitar
ayyukan da suka gabata, wato abin da ake kira waiwaye ga wasu ayyuka da suka
gabata wanda ya ƙunshi bugaggun littattafai, da kundaye, da kuma maƙalu.
A babi na uku za a dubi tarihin rayuwar Kassu
Zurmi, wanda ya haɗa da gabatar da tarihin rayuwarsa, iliminsa, koyo da fara
waƙarsa, gadon kiɗansa, abin kiɗansa, da kawo bayani a kan yaransa, nau’o’in
waƙoƙinsa da iyalansa, ƙarshe da rasuwarsa.
A babi na huɗu an yi gabatarwa da kawo salon
kambamawa a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, kambamar zulaƙe, da kambamar yabo.
A babi na biyar wanda shi ne na ƙarshe a wannan
bincike, an yi bayani akan sakamakon bincike, sai shawarwari, manazarta, da
kuma ratayen wasu waƙoƙin da aka gabatar.
1.1 MANUFAR
BINCIKE
Akwai manufar da ta sa aka gudanar da wannan
bincike ga su kamar haka.
Dalili na farko shi ne, ina da matuƙar
sha'awar sauraron waƙoƙin makaɗan Hausa musamman waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi,
saboda haka nayi sha'awar gabatar da bincike a wasu daga cikin waƙoƙin. Dalili
kuma daya sa aka gudanar da wannan bincike akan wannan makaɗi, shi ne domin a
ƙara fito da wannan makaɗi a fili, duniya ta ƙara saninsa ta kuma ji irin
fasaha da hikima da Allah (S.W.T) ya ba shi ta fuskar harkar, kiɗa da waƙa.
Maƙasudin wannan bincike shi ne don zaƙulo
wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi don ayi nazarin salon kambamawa da
ya yi amfani da shi a cikin wasu waƙoƙin nasa. Ta haka ne za'a zaƙulo salailan
da mawaƙin ya yi amfani dasu domin nuna fasaha da Allah ya ba shi.
Haka zalika ya na daga cikin manufar wannan
bincike a samar da wani kundin karatu wanda zai zama abin karantawa ga ɗalibai
da manazarta.
1.2
HASASHEN BINCIKE
Hausawa na cewa “ Maiki mai hange ne sa” A bisa
nawa hasashen da kuma tsinkaya da nayi ko kuma a bisa nawa kudirin da nayi
domin bunƙasa ko haɓaka harshen Hausa naga ya da ce da nayi wannan bincike
domin nazari da ni kaina da kuma raya matasa masu tasowa, ma’ana waɗanda zasu
taso nan gaba.
Bugu da ƙari kuma na yi wannan bincike domin
ganin cewa da na karanci littafai na Hausa musamman na adabi wanda ya shafi
irin waɗannan shahararru mawaƙan namu na Hausa. To shi yasa nayi tunanin da
hangen nesa na ganin cewa bari inyi bincike ko nazari a kan wannan shahararren
mawaƙin wato Alhaji Kasu Zurmi domin bunƙasa adabin Hausawa.
Abu nagaba kuma duk a bisa wannan hasashen shi
ne ina ganin cewa idan wannan bincike zai zama abin dubawa a makarantu na gaba
da kuma na gaba da sakandare. Domin a saka shi a cikin ɗakin karatu don na baya
su karanta kuma su karu wannan shi ne hasashe na dangane da wannan bincike da
na gudanar.
1.3
FARFAJIYAR BINCIKE
Wannan bincike zai taƙaita ne kawai a wasu daga
cikin waƙoƙin makaɗa Kassu zurmi, kuma binciken zai dubi ko zai zaƙulo salon
kambamawa ne da mawaƙin ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙinsa. Don haka duk
wani abin da bai shafi salon kambamawa ba, ba za a kawo shi ba.
1.4
MATSALOLIN BINCIKE
Na
yi tattaki har garin kadawa domin in samu tabbataccen tarihin mawaƙin Kassu
Zurmi, amma matarsa guda kawai na iske tare da ‘ya ‘yanta guda biyu, wadda tace
min lallai ba ta da tabbacin shekarar da aka haife shi, amma tace ya rasu a
lokacin da aka yi (idoji) sunan matar “Abu” wadda take zaune a gidan nasa a
yanzu tare da ‘ya ‘yanta, watau Tunau, da Namakka waɗanda diyan nan nashi waɗanda
suka zama malamai wanda a yanzu suna nan suna jagorantar Hizba a garin kadawa.
Tattaunawa da na yi da matarsa ‘ABU’ a garin
kadawa a ranar littanin (07/02/2021) inda ta tabbatar mini bata da masaniyar
shekara da aka haifeshi,Amma tace mini ya rasu a lokacin da ake yi idoji watau
(1983).
Tattaunawa da na yi da matarsa ‘ABU’ a garin kadawa
a ranar littanin (07/02/2021) inda ta tabbatar mini bata da masaniyar shekara
da aka haifeshi,Amma tace mini ya rasu a lokacin da ake yi idoji watau (1983).
1.5
MUHIMMANCIN BINCIKE
Binciken zai taimaka wajen killace tarihin
rayuwar Kassu Zurmi da salon kambamawa a cikin waƙoƙinsa domin amfanin masu
nazari, da kuma adana wani ɓangare na adabin baka.
1.6
HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Wannan bincike ya dogara ne a kan wasu hanyoyin
gudanar da bincike, wato ziyarar ɗakunan karatu don nazartar waƙoƙin baka na
Hausa, ta hanyar duba bugaggun littattafai, da kundayen digiri na ɗaya, da na
biyu, har zuwa na uku, da aka gudanar a fannin adabin Hausa. Sannan da duba takardu da maƙalu waɗanda aka
gabatar a wurare daban-daban na ilimi.
Sannan an tattauna da masana na wannan fanni
na waƙoƙin baka da neman shawarwari tare da jagorancin mai duba wannan bincike
na ciki,duk dai don samun gamsassun bayanai. Haka kuma za a bi wata hanya ta
yin amfani da rediyo domin sauraron kaset na waƙoƙin da aka yi nazari da kuma
duk wata hanya makamanciyar wannan da zata taimaka wajen gudanar da wannan
aikin.
1.7 NAƊEWA
A wannan babi an yi bayanin gabatarwa, ainahin
manufar bincike, hasashen bincike, farfajiyar bincike, matsalolin bincike, haɗi
da kawo mahimmancin bincike, duk a cikin wannan babi na ɗaya.
BABI NA BIYU
2.0 SHIMFIƊA: A
wannan babi na biyu za a yi bitar ayyukan da suke gabata, haɗi da hujjar ci
gaba da bincike, sannan da naɗewa duk a cikin wannan babi na biyu.
2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
Babu shakka wajibi ne ga dukkan wanda ke son
aiwatar da wani bincike ya waiwaya baya don ganin ayyukan da suka gabata, domin
ya san inda aka kwana kuma ya san inda zai tashi. Saboda Hausawa na cewa
“waiwaye adon tafiya". Shi wannan irin waiwaye ya zama tilas domin ta haka
ne mutum zai nuna ya san inda ya dosa, wato yana da masaniya game da aikin
binciken da zai gudanar, don haka sai ya ɗora a kansa ko ya rushesu ya gina
nashi tsarin, ko ya ɗauki waɗansu abubuwa ya watsar da wasu gwargwadon yadda ya
fahimta.
Akwai rubuce-rubuce da waɗansu manazarta suka
gudanar wanda ya ƙunshi bayanai wanda yake kuma idan muka duba waka tana ciki.
Saboda haka ire-iren waɗannan nazarce-nazarce da aka gudanar akwai bugaggun
littafai, da muƙalu da kuma kundayen bincike.
2.1.1 BUGAGGUN LITTATTAFAI
Masana da dama da kuma manazarta sun rubuta
littafai da yawa da suka shafi adabin Hausa, musamman na baka.
Ɗangambo, (2007) a cikin littafinsa mai suna
Ɗaurayar Gadon feɗe waƙa, ya bayyana yadda ake nazarin rubutattun waƙoƙi a ciki
ya yi bayanin salo da sarrafawa harshe da abin da ya ƙunsa da kuma bayanin
waƙar baka, (zubi da tsari) da sauran su.
Aikin nasa ya yi kama da wannan sai dai inda
suka bambanta shi ne wannan yana magana ne akan salon kambamawa a wasu daga
cikin waƙoƙin Kassu zurmi.
Yahaya (2001) a cikin littafinsa mai taken
Salo Asirin waƙa, marubucin ya yi bayanin ma'anar salo da ire-iren salo, da
muhimmancin salo, haɗi da kawo nau'o’in salo. Saboda haka wannan aiki yana da
alaƙa da na shi sai dai inda suka bambanta shi ne, wannan aikin yana magana ne a kan salon kambamawa a
wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Kassu zurmi.
Aikin ya yi kama da wannan saboda duk suna
magana ne a kan mawaƙan baka na Hausa. Sai dai inda suka bambamta shi ne wannan
aikin ya taƙaita ne a kan mawaƙi ɗaya ne kawai na yi nazarin salon kanbamawa a
cikin waƙoƙinsa Kassu zurmi.
Gusau (2005) a cikin wannan littafi nasa mai
suna maƙada da mawaƙan Hausa ya yi bayani yadda mawaƙan Hausa suka rabu, ya
kasa littafin har kashi hudu. Kashi na daya maƙaɗan yaƙi, kashi na biyu makadan
sarakuna , Kashi na , Kashi na uku makadan jama’a, kashi na hudu makadan
sana’a.
Aikin nasa ya yi kama da wannan saboda duk suna
magana ne a kan mawaƙan baka na Hausa sai dai inda suka banbamta shi ne wanga
aiki ya takaita ne a kan mawaki daya ne kawai na yi nazarin salon kambamawa a
cikin waƙoƙin sa.
2.1.2
KUNDAYEN BINCIKE
Masana da manazarta da dama sun rubuta kundayen
bincike masu alaka da wannan bincike.
Bunguɗu. (1990) A cikin aikin binciken da ya
gabatar don neman digiri na ɗaya a sashen koyar da Harsunan Najeriya, Jami'ar
Usmanu Ɗan Fodiyo Sakkwato, mai suna Muhammadu Auwalu Isa Bunguɗu, da waƙoƙinsa,
ya kawo gabatarwa da tarihin rayuwar Muhammadu Auwalu Isa Bunguɗu sannan ya
kawo sharhin wasu waƙoƙinsa. Haka kuma ya nuna waƙoƙinsa a kan adabin Hausa, ya
kuma kawo salo da zubi tsarin waƙoƙin.
Wannan aiki yana da alaƙa da wannan sai dai
inda suka bambanta shi ne wannan aiki yana magana ne akan salon kambamawa a
wasu waƙoƙin Kassu zurmi.
Ammani, (2009) ya gabatar da bincikensa don
neman digiri na biyu a sashen koyar da harsunan Najeriya jami’ar Bayaro, Kano,
mai suna “Nazarin maganganun Hikima a waƙoƙin Aliyu Ɗandawo” A cikin wannan
aiki ya fara yin shimfiɗa da gabatarwa da ma’anar waƙar baka ta Hausa da
ra'ayoyin masana dangane da ma’anarta. Sannan ya kawo ma’anar hikima da
matsayinta a waƙa.Haka kuma ya bibiyi tarihin rayuwar makaɗa, Aliyu Ɗandawo a
taƙaice.
Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aikin, sai
dai inda suka bambanta shi ne wanga aiki yana Magana ne akan salon kambamawa a
wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa kassu zurmi.
A wannan babi an yi bayani ne game da ayyukan
da masana da sauran manazarta da suka gabatar a matakan ilimi daban-daban
kundayen bincike da buggagun littatafai da muƙalu da aka gabatar, sannan aka yi
bitarsu tare da bayyana dangantakarsu da wannan aiki.
2.1.3
MAƘALU
Masana da dama sun gabatar da maƙalu akan
adabin baka wanda ya shafi waƙar baka.
Wannan aiki ya yi kama da wannan sai dai aikin
yana magana ne akan salon kambamawa a cikin wasu waƙoƙin Kassu zurmi.
Gusau (2013) ya gabatar da maƙala mai taken
"Dangantakar waƙoƙin baka da al’adun Hausawa; Bunƙasa ko koma baya"
Wannan takarda cike take da ɗimbin bayanai akan al’adun Hausawa da matsayin
waƙoƙin baka a wajensu, tare da misalan kaɗe-kaɗen Hausawa haka kuma, ya nuna
irin bunƙasa da waɗannan waƙoƙi suka samu tun daga wancan lokaci har kawo
yanzu, sannan kuma ya rufe takardar da kawo halaye da ɗabi’un waƙoƙi masu
hikima da armashi waɗanda al’ummar Hausawa zasu amince.
Wannan aiki ya na da alaƙa da wannan sai dai
inda suka bambanta shi ne wannan aiki yana Magana ne akan salon kambamawa a
wasu daga cikin waƙoƙin Kassu zurmi.
Dunfawa (2005) A cikin takardarsa mai taken “
Zambo da Haibaici a cikin rubutattun wakokin addini” A cikin wannan mukala ya
gabatar da kawo ma’anar zambo da ma’anar habaici, da halayen dan Adam,
Wannan aiki ya yi kama da wannan aikin domin
duk muna Magana ne a kan adabi bangaren waka.Sai dai inda aikin ya sha banban
shi ne shi yana Magana a kan rubutatcin adabi ni kuma ina Magana a kan adabin
baka.
2.1.4 HUJJA CI GABA DA BINCIKE
Daga bitar ayyukan da aka yi a kundayen
bincike, da buggaggun littafai, da maƙalu, babu wani aiki mai kama da wannan
aiki kai tsaye, ta fuskar fito da salou kambamawa a waƙoƙin Kassu Zurmi, don
haka binciken ya samu hujjar da za a
gudanar da shi.
2. 2 NAƊEWA
A wannan babi an yi ƙoƙarin kawo bitar ayukan
da suka gabata, Bugaggun littattafai, kundayen bincike, maƙalu, Hujjar ci gaba
da bincike duk a cikin babi na biyu.
BABI NA UKU
3.0
SHIMFIƊA
Wannan babi zai yi magana ne akan taƙaitaccen
tarihin rayuwa Alhaji Kassu Zurmi. Wanda ya haɗa da bayani akan haihuwarsa da
ƙurciyarsa, haɗi da neman iliminsa, da koyo da fara waƙarsa, da kuma gadon kiɗa
da bayani akan abin kiɗansa, haɗi da
yaransa da salon kambama a cikin wasu wakoki Kassu zurmi.
3.1
TAƘAITACCEN TARIHIN RAYUWAR KASSU ZURMI
Magaji
(2016) Ya ce Alhaji Kassu Zurmi sunan sa na yanka Abubakar an haife shi a wani
gari da ake kira magarya ta ƙasar zurmi karamar hukumar Zurmi a jahar Zamfara ta
yanzu nisan wannan gari lilo mita ashirin da hudu ne daga Zurmi, Kassu Zurmi ya
zauna a kadawa Garin da nisan kamar kilo mita biyu kafin karasawa zuwa magarya
wato mahaifarsa. Shi wannan garin wanda ake cema kwata kamar sabon gari ne,
sunan mahaifin Kasu Zurmi Muhammadu mahaifiyarsa maimuna.
(Kassu Zurmi)
Mahaifin Kassu Zurmi Muhammadu Ganga gadon farauta yayi, saboda haka
Kassu zurmi gadon kiɗa ya yi bada rana tsaka ya fara ba ko da ya ke bai yi
karatun zamani ba, amma Kassu Zurmi ya ɗan taɓa na alkur’ani tun kuwa lokacin
da ya isa misalin mutum ne ya fara bin tsohonsa wurin kiɗin farauta. Allah maɗaukaki
ya yi ma Kassu baiwa ta ya ya masu yawa a cikin manyan ‘ya’yansa akwai waɗanda
suke tafiya tare shi wurin kiɗa. A ciki akwai Ummaru wanda a da ya yi kiɗin
tauri wannan ya nuna a yanzu kassu Zurmi baya da mai gadonsa.
3.1.1.
HAIHUWARSA DA KURUCIYARSA
Kamar yadda tarihi ya nuna Alhaji Kassu Zurmi
dai mutumin garin Magarya ne kuma a nan ya yi har ya buɗe idanunsa. Sai daga
baya ne da yai wayo ya koma a garin kadawa watau Kassu dai ko da ya tashi yana
yaro hatsabibi ne a cikin tsaransa, domin ba da tsoro, kuma shi Kassu Zurmi mai
kuzari ne kuma mai ƙarfi, saboda duk warinsa ba a samun mai buge shi a wajen faɗa.
Bugu da ƙari kuma Alhaji Kassu Zurmi lokacin da
yake akan ƙuruciyarsa yaro ne mai kwarjini ga jama'ah tun daga yara abokanansa
har zuwa manya. Saboda zaman Kassu Zurmi hatsabibi tun yana yaro yakan haɗa
abokansa yara kokowa, yana zuga su. Kuma har takakka yake kaiwa abokansa a
gidajensu (Dodo hari: juma'a 2021).
3.1.2 ILIMINSA
Kassu Zurmi bai samu yin karatun boko ba na
zamani amma ya taɓa karatun Alƙur'ani. Kassu Zurmi ya yi karatunsa a wajen wani malami mai suna
Ladan. Kuma a nan hannun malamin ya sauke alƙur'ani mai Girma sannan ya fara
yin karatun littafai sai dai bai yi nisa ba, sai sha'anin kiɗa ya dauke masa
hankali, inda yake tara yara samari yana yi masu kiɗa suna yin kokawa da
junansu (Gusau 2005:225).
3.1.3 KOYO DA FARA WAƘARSA
Kassu Zurmi ya fara bin mahaifinsa wajen kiɗin
farauta tun yana yaro ƙarami. Bayan koyon kiɗan farauta da yake yi daga wajen
mahaifinsa, ya taɓa kiɗan noma, amma bai mayar da hankali sosai a kansa ba. Shi
dai kiɗan farauta ya gada, ya tarar ubansa yana yi. Don haka ya himmatu a kansa, har Allah ya ba shi rabo mai yawa a
ciki.
A matsayinsa na makaɗin farauta da yan tauri,
bawai gidajensu kawai yake bi idan suna taron suna, ko biki ya kama ba, a'a
tare da shi ake zuwa dajin farauta, duk abin da ake yi a farauta a gabansa ba
wani mai bashi labari. Shi kansa a wasu ɗiyan
waƙoƙinsa ya nuna cewa da shi ake farauta dubi abin da yake cewa.
Tahiya madoka ko dajin kuna,
Ko waji yan kalangana na tashi an nan,
Sai da kai ake neman daji
(wakar garu-garu na maga),
(Gusau 2O05:225-226),
3.1.4 GADON KIƊANSA
Hausawa na cewa "Gado mala" Kassu
Zurmi ya gaji kiɗin fawa a wajen mahaifinsa Amadu. Amadu makaɗin fawa ne, kuma
yana kiɗan ‘yan bori. Daga baya sai ya koma yana yi wa mafarauta kiɗa. Saboda
haka Kassu Zurmi ya gaji kiɗa ne a wajen mahaifinsa don haka waƙa a wajen Kassu
gado ya yi ba haye ba, domin mahaifinsa ya yi.
3.1.5 ABIN KIƊANSA
Kamar yadda kowane makaɗi yake da abin kiɗansa
haka shi ma Kassu Zurmi ba a bar shi a baya ba, yana da nasa abin kiɗan. Kayan
kiɗan Kassu Zurmi su ne kalangu, kamar yadda muka sani, kalangu wani abin kiɗa
ne da ake amfani da shi a wajen kiɗa. Kuma shi kalangu yana da baki biyu kuma
ana buga shi da (kurya Maladi).
Shi dai kalangu wani ice ne da ake sassaƙawa
masassaƙa kan sarrafashi a daji su kuma maidashi kalangu, kashi biyu ne akwai
mazan kalangu, sune dake da sauti mai tsauri-tsauri kuma ƙanana ne basu yi
girman wasu ba. Irin waɗannan kalangun ne Alhaji Kassu Zurmi, da sani Sabulu,
da Ɗanba'u buwai suke amfani dasu.
3.1.6 YARAN KASSU ZURMI
Bayan yaransa na tsatso yana da waɗansu yara
waɗanda yake tare da su wajen gudanar da sana'arsa ta kiɗa da waƙa. Yaran Kassu
Zurm na sana’ar kiɗa, sune kamar :
i.
Dodo
ii.
Tunau
iii.
Shata
iv.
Namakka
v.
Ummaru ƙaho
Shi Shata dai yaron sa ne ta fuskar kiɗa, amma
shi Dodo taubashin sa ne kuma abokinsa ne. Shi kuma Tunau zaman da yake ga
Kassu Zurmi saboda kawunsa ne. Su kuma sauran ya'yansa ne na tsotso shi ya
haife su.
3.1.7 NAU'O’IN WAƘOƘINSA
Kassu Zurmi ya yi nau'o’in kaɗe-kaɗe a
matsayinsa na makaɗin kalangu. Daga cikinsu akwai.
1. Kiɗan Noma
2. Kiɗan Farauta Na'yan Tauri
3. Kiɗan Yan Caca
4. Kiɗan Barayi
5. Kiɗan Fawa.
3.1.8 IYALAN KASSU ZURMI
Kassu Zurmi ya yi aure kuma Allah ya
arzurtashi da ‘ya’ya da yawa. Daga cikin ‘ya ‘yansa ne Ummaru ya zama makaɗin
tauri kusan shi ne mai gadonsa.
Amma shi
Usman, ya zaɓi hanyar almajiranci inda ya yi karatun allo mai zurfi har
ya zama malamin makarantar allo yana koyar da yara karatu (Gusau 2005:229).
Kassu yana da "yaya goma sha biyu (12) da matan aure huɗu :
1. ‘Yar jari
2. Auta
3. Abu
4. Karɓa
3.1.9
RASUWAR KASSU ZURMI
Kassu Zurmi ya rasu bayan yayi fama da wata
gajeruwar rashin lafiya wadda har ta sa kwantawa a asibitin Gwaji na Gusau a shekara 1987
(Gusau,2005:229)
3.2 MA'ANAR SALO
Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu game
da ma’anar salo. (Yahaya 2001). Ya ce salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya
ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana.
Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a
cikin waka wadda aka bi domin isar da sako. Ita wannan dabara ko hanya ta yiwa
waka kwalliya ta yadda sakon wakar zai isa ga mai sauraro ko mai karanta waƙar
(Sarbi, 2007) cewa ya yi salo na nufin zaɓi cikin gudanar da wani abu ko
alƙawari amma a fagen waƙa, salo hanya ce da marubuci ke bi wajen isar da
saƙonsa ga jama’a.
Salo wata dabara ce ko hanya da marubuci ke bi
wajen isar da saƙonsa ga makaranta cikin hikima da gwanintar harshe wajen isar
da saƙo ga makaranci cikin hikima da azanci da nuna gwanintar harshe.
Salo dabara ce mai wahalar bayyanawa saboda
salo ya bambanta tsakanin marubuta, ma'anar kowane mawaƙi da irin salon sa,
haka kuma marubuci ɗaya na iya amfani da salo daban-daban dangane da
sha’awarsa, lokaci ko yanayin daya samu kasan a ciki da kuma irin saƙon da yake
son sadarwa ga jama’a.
(Ɗangambo, 2008) kamar yadda na nuna yana da
wuyar a gane shi a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa. Bisa
jimla, muna iya cewa salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo.
A tawa fahimtar salo tamkar jini ne da tsokar
kowane lamari saboda haka salo wani babban abu ne da mawaƙi zai bi domin ya
nuna manufarsa zuwa ga masu saurare ko masu karantawa. Salo tamkar gishiri ne a
cikin zance ko jawabi ko kuma waƙa, wanda idan babu shi zai sa abin ya zama
bambarakwai kamar miyar da ba gishiri.
3.2. 1
IRE-IREN SALO
To zan kawo masanan da suka yi bayani akan
iren-iren salo. Kamar yahaya (2001. 95)
3.2.2 MA'ANAR SALON KAMBAMAWA
Masana da manazarta da dama sun bada ma'anar salon
kambamawa.
A ƙamusun Hausa (2006) .
Kambamawa ita ce idan mawaƙi ya yi zuƙu cikin
magana ko ya ƙara mata gishiri a taƙaice ya bayyana abu fiye da yadda yake, a
nan zamu ce wannan mawaƙi ya yi amfani
da salon kambamawa. (Yahaya, 2001:95). Idan muka tattara waƙoƙin soyayya zamu
ga cewa mawallafa waɗannan waƙoƙin suna amfani da salon kambamawa ne. misali
Muhammad Rabi'u saulawa ya ce da masoyiyarsa.
Wannan mata mai ƙyan sifa,
Kin mamaye matan duniya.
(R.M Saulawa labarin zuciya)
Wannan mawaƙi ya yi kambamar zulaƙe,don ya
bayyana masoyiyarsa ta fi dukkan matan duniya. Don haka ya yi kambamar zulaƙi.
3.2.3 IRE-IREN SALON KAMBAMAWA
Salon kambamawa hanya ce ta kambama abu fiye
da yadda hankali zai amince akan yi amfani da wannan dabara domin waɗannan abubuwa
kamar haka:
1. Kambamawar zulaƙe
2. Kambamawar yabo
3.3 NAƊEWA
A wannan babi an gabatar da taƙaitaccen
tarihin rayuwar Kassu Zurmi tun daga haihuwarsa da kurciyarsa da neman iliminsa
da fara waƙoƙinsa, wanda muke ce gado ya yi da abin kiɗansa da nau’oin
waƙoƙinsa.Haka kuma an kawo yawon iyayensa da lokacin rasuwarsa. A dai wannan babi an ga ma’anar Salo da
ire-irensa, har da Salon kambamawa wanda a kansa ake gudanar da wannan bincike.
BABI NA
HUƊU
4.0
SHIMFIƊA
A wannan babi na huɗu za'a duba salon kambamawa
a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi. Sai kuma a kowa ma'anar salon kambamawa, hadi da
kawo bayani akan ire-iren salon kambamawa, duk a cikin wannan babi na huɗu.
4.1 SALON
KAMBAMAWA A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kassu Zurmi mawaƙan farauta ne da "yan
tauri da kuma barayi, kamar yadda tarihi ya nuna. A cikin wasu wakokinsa yakan
yi amfani da wannan salon na kambamawa domin ya zuga ko ya kambama gwarzayen
sa, saboda su yi abin da ba su tashi yi ba. Ga misali ire-iren kambamawa kamar haka.
4.1.1
KAMBAMAR ZULAƘE
Ita ce idan mawaƙa ya yi zuƙu cikin magana wato
ya ƙara mata gishiri, a taƙaice ya bayyana abu fiye da yadda yake a haƙiƙani,
za mu ce wannan mawaƙin ya yi amfani da kambamawa zulaƙi (Yahaya, 2001:95).
Kassu zurmi ya yi amfani da wannan salon a
kambamar zulaƙe a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa.
Bisa ga ƙa'ida bahaushe Allah kaɗai yake cewa
maiduka, maibisa, maikomi, maikowa, idan aka yi amfani da ita ga wani bawa daga
cikin bayinsa an yi kambamawa zulaƙi (Bunza, 2009).
4.1.1.1
waƙar Musa na ƙasar ɗan Ali mai Tauri.
Jagora
: Manyan hwaɗa,
: Musa na kasar Dan Ali wan Karhi
Wannan
kalma ta wanƙarhi kambamawa zulaƙe
ce, saboda karhi bai da wa.
4.1.1.2 Waƙar Ummaru Sabon Birni.
Jagora :Daɗi
na da Gobirawa,
:Du in da kunka zo ba ku hukuntuwa.
A nan
ana nuna isa ga gobirawa, amma kalma hukunci ba bu wanda ya wuce hukunci, A nan
an yi kambamar zulaƙe.
4.1.1.3
Waƙar Ɗanjijji.
Jagora : Mazan
jiran maza Ɗanjijji ɗanguru,
:Shiriritad duniya na bayan tanda,
:Ibilishim masussuki Ɗanjijji,
:Da kai ne mai koda nag gani tar rude.
An yi
amfani da wannan salon a kambamar zulaƙe wajen shiriritad duniya na bayan
tanda. Wannan kowa yasan bayan tanda baki ne kawai a nan an yi kambamar zulaƙe.
Kalmar
ibilishi masussukin Danjimma wannan kalma ta nuna cewa shaidan ko aljani a nan
an yi kambamar zulaƙe.
4.1.2
KAMBAMAR YABO
Dabara ce ta jawo hankali fiye da kima. Hanya ce ta kambamawa abu fiye da yadda
hankali zai amince. A kan ya amfani da wannan dabara, musamman domin yin yabo.
Ana nuna cewa mutum ya yi wani abu, wanda a zahiri ba zai yiwu ba, ko ya
mallaki wani abu da zai iya mallaka ba. (Sarbi, 2007).
4.1.2.1
Waƙar Baƙo Na Ɗanƙaya
Jagora : Buwai mai
raba gardama ga mazaje,
: Anne baƙo na
malam mai takobi
Wannan kalma ta ‘Anne’ tana nufin Taurarewar zuciya a
nan Kassu ya Kambamashi da wannan kalma ta mai taurin zuciya mai ƙwazo a nan an
yi kambamar yabo.
Jagora : :Baƙo
na danƙaya na Buwai,
: Damusheren Gandau na Buwai,
: Daji Baƙo na Mallam mai takobi
: Anne gidan ku babu Muhammad,
: Gidan su ba mai suna ragoranci.
Wannan kalma ta ‘Damushere’ tana nufin gawurtatce an yi
kambamar yabo.
Ma’anar kalmar Damushere
I.
Mutum mai aiki tuƙuru
II.
Mafaɗacin mutum
III.
Mutumin da yake son abi umurnin da ya bayar nan take ba da inda-inda ba
IV.
Daidai da damisa
Ƙamus Hausa,2006 :92-93
4.1.2.2 Waƙar Nomau na Magarya
Jagora: Dan kalgo
bani kar na ƙarye,
: Wa ka sai mani doki magarya?
: Nomau ne ko abin tuwo ba ya
dashi,
: Kahiri karen bunu Baƙo,
: Yanzu kau karen Alhaji ne.
A cikin wani ɗan waƙar ana nuna cewa Kassu Zurmi
ya yi amfani da kambamar yabo inda yake yabon gurzunsa da kalmar kahiri.
Ma’ana
kalmar ‘kahiri’ a addinance tana nufin wanda bai da addini, A kuma wani ƙauli
tana nufin mai ƙarfin zuciya, anan Kassu Zurmi ya yi amfani da kambar yabo.
4.1.2.3 Waƙar Shaye Ɗan gida Labbo
Jagora: Kata koro Lado Iro na Ummaru,
: Kura mai guzurin kunye.
A wannan ɗan waƙar ana nuna cewa anyi kambamar yabo,
Ma’anar ‘katakoro’ yana nufin mai ƙarfin gaske / ƙaton
mutum.
4.1.2.4 Waƙar Rabi’u Ɗan Manyan Matcata
Jagora: A’a Rabi’u
ka kyauta ma Kassu,
: Rabi’u ka kyauta ma Kassu,
: Mai dala’ilu ɗan manyan matcata.
A cikin wannan ɗan
waƙa anyi amfani da kambamar yabo idan aka gwarzanta shi da kalmar ‘Dala’ilu’, ma’anar wannan kalma wato mai dala’ilu yana nufin mai tsananin wuridi ga
ubangijin halittu.
Jagora: Ya san mu
tare da tsoho nai,
: Ko da ya yam mutu shidai bai saki
ba,
: Rabi’u dan manya makata,
: Dan manyan kasake
: Rabe dutsin hwashin tama,
: Rabi’u zakka a won maza ɗan maidamma
na kande.
A cikin wannan jigon anyi amfani da kambamawar
yabo, inda ake kambama shi da kalmar Dutcin hwashin tama, anan ana
nufin gwarzon jarumi a wajen faɗa.
Sai
kuma a waje ɗaya inda ake kambama shi da kalmar zakka awon maza, wannan kalma
na nufin wato shi Rabi’u, Rabiu
sikeli na auna mazaje, wato shi ne abin ƙwatance saboda jaruntaka.
4.1.2.5 Waƙar Mai Barbara Shehu Guraguri
In da yake cewa a cikin dan waƙarsa.
Jagora: Tauri
wuya garai sai a yi ƙoƙari,
: A sha malammai a bi
sayyu a yi kariya,
: In an ƙiya ana cim ma
sanin wani,
: Sai ya gamu in yi wai,
: Da ni da wane sai mun
gamu kassuwa,
: Amma ina gida ina tad
da zuge-zugi,
: Kun yi kalan goni suna
hwaɗin wani ya kashe wani.
Kalmar taurin wuya tana nufin gwarzo
mai jarumta.A nan an yi kambamar yabo in da ake kambama shi da ‘Taurin wuya’, wato jarumi, mai gwarzantaka.
Kalmar taurin wuya tana nufin gwarzo
mai jarumta.
4.1.2.6 Waƙar Musa na Ƙasar Ɗan
Ali mai Tauri
Jagora:
Ɗan Mande ban ga jinin ka ba,
: Ɗan Mande mai taurin jiki,
: Ɗan Mande na gode,
: Ka bani kuɗi,
: Kuma ka bani dawaki,
: Ka koma ka sa man riguna,
: Na gode baura,
: ka sun kuɗa mani kuɗɗi ɗan maliki,
: Kassu kuma riguna sai na gaji
: ka sai mani doki,
: ka koma ka sa man riguna,
: Allah dai shi
ƙara maka arziki,
: Baura Allah dai shi ƙara ka amin don Kassu,
: Allah dai shi ƙara maka arziki,
: Baura Allah dai
shi ƙara ka amin don Kassu.
Wannan ɗiyan waƙa an nuna anyi kambamar yabo, in da aka ce ‘Taurin jiki’ na nuna ƙarfin hali, ko jauriya.
Ya ci gaba da cewa:
Jagora: Gagare daga
karen ido,
: Karen ido mai karhin gaba.
Wannan kalma ta ‘Gagare’kalma ce ta
laƙabi da ake yi wa mai suna Abubakar tana kuma nufin jarumi. Don haka kambamar
yabo ce.
4.1.2.7 Waƙar Ummaru Sabon Birni
Jagora: Ko
can in kaji gatari sai buzu,
: Yara ko can don hwaɗa
aka tsoron zuwa gidan
jangwarzo,
: Don hwaɗa aka tsoron
zuwa gidan jangwarzo.
Anan an nuna anyi kambamar yabo domin kalmar ‘Jangwarzo’ tana nufin majiyin ƙarfi,
jarumi.
Duk a cikin wannan waƙar an cigaba da kambamar yabo a
dubi wannan ɗan waƙa na gaba.
Jagora: Hana noma
na hanƙurau,
: Sa’adu mai hana noma na
hanƙurau,
: Sa’adu barkakka da yamutsi,
: Sarkin karman Gobir arnan Sabon
birni.
A cikin wannan ɗan an yi amfani da kambamar yabo, inda ake kawo
kalaman hanƙurau, wannan kalma ta na nufin mai tsananin hanƙuri ne.
Jagora: Sabon
birni gidan Bawa jangwarzo,
: In da masu yaƙi suke gurzuwa,
Kalmar gurzuwa tana nufin haɗuwar mazaje a wurin yaƙi yadda kowa zai ji jiki.
4.1.2.8 Waƙar Mani Na Maƙera.
Jagora: Ya
gagari gaba Mani,
: Ya gagari gaba Mani,
: Kai ne maƙera gudu sai
mata,
: Kai ne maƙera gudu sai
mata.
A cikin wannan baiti an nuna kambamawar yabo
domin kalmar gagara tana nufin buwaye wato wanda yafi ƙarfin kowa ke nan.
Jagora: Wo
jikan zaki,
: A jan zaki ba a haye ma
barde,
: Im ba maganab banza ba,
: Mani bay yi idon tsoro
ba,
: ko kusa ba shi da
tsoron kowa,
: Halin gidan jimfi kay
yi jikan zaki,
Ma’anar wannan kalma ta “Jikan Zaki” zaki dabbar daji ce, yafi
kowace dabba karfi, Kassu yana yabon gwarzonsa da wannan kalma don ya nuna gadon ƙarfi ya yi don haka ya ce masa
“Jikan zaki” barewa kuwa ba ta yin gudu danta yay i rarrafe kamar yadda
Dankwairo yake cewa.
Jagora :Danbajimi, bajime ne,
:Dan giwa, giwa ne,
:Dan
giwa, giwa ne,
Kai tsaye Jikan zaaki ya nuna shi ma zaki ne
Jagora : Barkaka da gaba mani,
:Toho jikan zaki bari tsoron arna,
:Hude-Huda na makera ina ban kwana,
:Bari dai rena ma kiran mani ba,
:Da niz zo wadda akai dayayyi mai,
:Zaman ɗaki da kaho to yai man.
Huda-Huda tsuntsu ne kyawawa mai kama da hazbiya da ɗan tukku a kan sa.
Wasu na kiran sa alhuda-huda an bayar da labarinsa a ƙissar Annabi Suleiman a
matsayin mai ilimi wanda ya kawo masa labarin sarauniya Balkisu da gadon mulkinta.
A kasar Hausa idan a na son a nuna mutum mai son karatu sai a dan gan ta shi da
wannan tsuntsun.
Kassu
Zurmi yasan haka wanda ya kira da sunan ko yana nufin mai ilimi ne ko kuma
saboda kyawonsa da kyawon shigar sa.
4.2 NAƊEWA
A Wannan babi na huɗu an yi ƙoƙarin bayyana waɗansu
abubuwa waɗanda suka shafi wannan babi. Sun haɗa da shimfiɗa, salon kambamawa a
wasu waƙoƙin kassu zurmi kambamar zulaƙe, kambamar yabo.Duk a cikin wannan
babi.
BABI NA
BIYAR
5.0
SHIMFIƊA
A cikin wannan babi an kawo bayanai a taƙaice
dangane da wannan bincike da aka gabatar, sai kuma sakamakon da binciken ya
gano.
5.1
SAKAMAKON BINCIKE
Sakamakon wannan bincike ko nazari dangane da
abubuwan da ake yi kiciƃis dasu, an fahimci cewa makaɗin Kassu Zurmi mutum ne
mai hazaƙa da basira da kuma hikima da azanci wajen ƙulla ɗiyan waƙa.
Haka kuma wannan bincike ya gano Kassu Zurmi
mutumin Magarya ne ta ƙasar Zurmi ta Jahar Zamfara. Har illa yau kuma wannan
nazari ya gano cewa Kassu Zurmi makaɗi ne mai amfani da kalmomin kambamawa, da
kururutawa,da kuma yabo, da zuga.
5.2 SHAWARWARI
Hausawa na cewa “shawara ɗaukar daƙi. Ina bada shawara ga duk wanda zai karanta
wannan bincike don wani nazari ko don wani abu daban ya lura da aikin da aka yi
a kan salo, musamman salon kambamawa a cikin wasu waƙoƙin shahararre mawaƙin
nan watau Alhaji Kassu Zurmi. Domin ya gano abin da mawaƙin ke nufi.
Ina kuma bada shawara ga dalibbai masu nazarin
harshen Hausa da cewa su ɗauka in da na aje. Musamman dangane da aiki irin
wannan, wanda ya shafi adabin baka.
Wata shawara kuma da nake son in bayar a nan
shi ne ɗalibai da sauran al'umma su karanta wannan kundin bincike domin gano
fasahar da mawaƙin ya yi amfani da ita a
cikin waƙoƙin nasa.
Daga ƙarshe ina bada shawara da cewa a ci gaba
da rubuce-rubuce a kan nazari waƙoƙin baka na makaɗa saboda kada su salwanta,
domin sun kamo hanyar ɓacewa.
5.3 NAƊEWA
Wannan bincike ko nazari gaba ɗaya tun daga
farko har ƙarshe an gabatar da shi ne a kan salon kambamawa a cikin wasu
waƙoƙin Kassu Zurmi.
A babi na farko an kawo shimfiɗa da manufar
bincike, da farfajiyar gudanar da bincike, da hanyoyin bincike, matsalolin da
suka shafi gudanar da binciken, da kuma hassashen bincike.
Sai babi na biyu, an yi waywaye ga wasu ayukan
da suka gabata makamantan wannan aiki da suka haɗa da bugaggun littattafai, da
kundayen bincike da muƙalu. An kuma yi bayani hujar ci gaba da wannan bincike.
A babi na uku na kawo bayani kan tarihin Kassu
Zurmi, da kuma ma’anar salo, ire-iren salo da ma’anar salo kambamawa haɗi da
kawo ire-iren salon kambamawa.
Sai babi na huɗu wanda shi ne ƙashin bayan
binciken in da nayi bayanin salon kambamawa a ciki wasu waƙoƙin kassu zurmi, haɗi
da bayanai akan kambamar zulaƙe, da kambamar yabo.
Daga ƙarshe a babi na biyar wanda kuma shi ne
na ƙarshe na kawo shimfiɗa, da sakamakon bincike da shawarwari haɗi da kawo
manazarta duk a cikin wannan babi na biyar, wanda shi ne na ƙarshe a cikin
wannan kundin binciken. Sannan da ratayen waɗansu waƙoƙin Kassu Zurmi.
MANAZARTA
Ammani, M. (2009) “ Nazarin Maganganun Hikima a
Waƙoƙin Aliyu Ɗan
Dawo” Kundin digiri na biyu.
Sashen Koyar da Harsunan Najeriya.
Kano. Jami’ar Bayero.
Bunguɗu,I. (1990), “Muhammad Auwal, Isah Bunguɗu,
da waƙoƙinsa”
Kundin digiri na ɗaya. Sashe
koyar da Harsunan Najeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A.M (2009) Narambaɗa Lagos: Ibrash
Islamic Publication center
Limited.
Dangambo, A
(2007) Daurayar Gadon Fede Waƙa. Kano Amana Publishers.
Dumfawa,A.A (2005)
Zambo da Habaici A cikin rubutattun waƙoƙin Addini. Sokoto.Sashen Harsunan
Nijeria.Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Gusau, S.M (2005) Makaɗa da Mawaƙan Hausa,
Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S.M (2013) Dangantakar Waƙoƙin Baka da Al’adun
Hausawa:
Bunƙasa Ko Koma-Baya sashen koyar da harsunan
Najeriya.
Kano.
Magaji,A. (2016) Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa.
Publish By Spectrum Books
Limited Spectrum House Ring Road Ibadan.
Sarbi, S.A (2007) Nazarin Waƙa Hausa. Kano: Samarib Publisher Limited.
Yahaya, A.B (2021) Salo Asirin Waƙa Kaduna
Media Service.
Rataye Na Daya
Wasu Wakokin Kassu Zurmi Na Tauri
Shayi dan
Gidan Labbo
Jagora: Mai kwana ya tashi,
: Mai tahiya ko ya dakata shi kau:
: Ku tashi kun ji kidin Shayi dan gidan Labbo.
Jagora: Ku hwalka na Kai ga masu dongashi,
: Lalle Shaya ad da ɗangashi
: Ya yi bida amre bara sai da yas samu,
: lro ya kar ta gidan niaigidansu yah hwaɗi,
: Yam mutu yab bas shi ba abin amren.
: Kana ba hatcin diba.
Jagora : Da an game da Labbo yana tattalin
diyan dangi.
: To
dada ya amren Sha, Labbo ya wahala,
: Ra amren Sha, Labbo yai yawo,Yai yawo,
: Amren shaya, Labbo ya yi jidaɗi.
Jagora : Garin biɗad bashi.
: Ya sha raba kamak Karch dajl.
: Ya sha rana kamat tukin daki,
: Labbo ya tawaiwaye walki shina ginah hanya,
: Maidabo dan aula za ya ba shi yah hwasa.
Jagora : Irin gidan Bawa dan Galadima,
: Sai da Bawa yab ba shi sai ladar takkwace,
: Tac ce sabilin Shaya ba a bashe su,
: Dan nema bai raganma kowa ba,
: Wata yag gona garai cikin tabki,
: Bara yat tashi yana Kashin awakinmu,
: Tac ce masalin mai kato gudan awa Shayi,
: An nan ka bidab bashi.
Jagora : Labbo yac ce katon gidan na-banza ne.
: Komi yab bida na mata ne
: Dum mata sun bi Iro sun kode,
: Yakkamnatai tana yi mar wazu,
: Yakkamnatai tana yi mai wazu,
: La anannen ba ya jin batun kamnai.
: La'anannen ba ya jin ba
: Tana hwadin,
: Tana hwadShayi ga ka dai da karhin, Shayi ga
ka dai danka,
: Na Abu hak ka lalace tsohuwa ta cishe ka.
: Na Abu hak ka lalace ts
Jagora : ta Dangiwa Hauwa na yi mai bida
: Ba ta da karhi ba ta biyak kuyya,
: ‘yat tahwasa taka diba a ba ta sadare,
: Ta kau ci hat ta cishe shi,
: Taro kun san ko hauwa uba naice.
Jagora : Katakoron Lando, Iro na ummaru
: kura mai guzurin kunya
: Sha-yaya Magarya ta yi ma doro
: Tana nan ta bar ka, Atu ta tsere.
: Dauri an bar ma ka tsohuwa ta cishe ka,
: Tsohuwag ga ta fuzge
: To dada Sha wa ka cishe ka?
Jagora : Kakab bana tai kyawo
: Ko ta bara mun gode,
: Sai dai Shaya bai yi komi ba.
: Na ga yan tantabaru cikin rihewassu,
: Tantabara goma,
: Amma yanzu ba su sun kare,
: Yanzu kam saura nai guda baki namiji,
: Ko shi kam dan yana yi mai waka,
: Inda sahiya taw waye ya dora mabanci.
Jagora: Tantabari na rigan ka tasowa,
: Kai ga
Ka da ranak Kwana sai luhwa ta shuɗe,
: Sai tsuntsu ya hiko yana sijan hantci,
: Yana gashin keya,
: Shina dubin inda za ka hudowa,
: Shi kau yana cikin dakı,
: Tantabari na gyaran jiki nai.
Jagora : Sai da Shaya yaɗɗago daki,
: Dam mazan tantabaringa na yi mai guda,
: Shina kudunguru Shayi dan gidan Labbo,
: Kudunguru Shayi dan gidan Labbo,
: Kudunguru Shayi dan gjdan Labbo,
: Shi ko kokirzon
: Shi ko kokirzonsai ya watsa ‘yas tsaba sai ya
watsa yas tsaba,
: Kai ko tsuntsu teintce tciyakku ta bi ku.
: Kai ko tsuntsu tcentce tciyaku tabi ku
Jagora : Ya'ya an nan dubu kamas Shayi,
: Babu kayan turawa ruhewakku
: Tai kyawo
: Rannan Shaya yas Shigo sa'a
: Ga ya da dogon baki da yaw wutab bota,
: Na Abu yankan bakinka ya yi ma kyawo,
: Ya samu gama aron zanen saki,
: Had da tsamiya yaddauro da yab bakas shadda.
Jagora : ‘Yammata sun gane shi sun je mai.
: Anka dora wasoso,
: Ni wanin Shayi ni ka jide shi,
: A a kina karya na riga ki zado shi.
: Kamas su buga gasu nan cikin gebe
: Na ce kak ku buga ya ishe ku jidawwa.
Jagora: Daukash Sha-yaya munka sha daula,
: Mun sha damnalutsa mun sha mai,
: Mun sha zabbi ga dan gidan Labbo,
: Nicce ma yan yarana, ku sha ahaha ce,
: Tunda ba ya maishe ta.
Jagora : Katakoron Lando, Iro na Ummaru,
: Kura mai guzurin kunya
Jagora: Sai da za mu watcikkewa,
: Kana uwayen matanga sunka jawo ni,
: ga ni ga yammatanga ga uwayensu
: Mu kadai cikin zaure
: Kassu amana Allah ka ba mu labari,
: Nic ce, Wane labari.
:
Labarin Shayı dan gidan Labbo,
: Yammata sun walwale baikonsu,
: Sun ce Shaya Shi Ka rankonsu,
: Shi muka son ka ba mu labari,
: in akwai gidan Kirki
: Nic ce yau kam dattijo kunka maishe ni,
: Ya yi, ku koma ku shaida na Abu dan uwana ne,
: Mutum kau ba ya shidaddan 'uwanshi ko hwada
Jagora: Kassu amana Allah ka ba mu labari,
: Ni kau amana Allah kadai ka sha min kai,
: In na bi amana Allanga na yi batanci,
: Kuma in tuna ba ni Cin amana Allah sabadda
tantiri.
: Amma hwa ku ba shi in kuna bashi,
: Na-Abu Shayidai da ne,
: Sunka ce "Ba haka munka so ba dan yaro,
: Aimun san da ne tunda anka haihe shi,
: Ba mu labari in akwai gidan kirki?
Jagora: Ni ce, I gaskiyakka dattijo
: Mutum kau ba za ya kai diya tai ba
: Gidan da ba abin kirki
;Amma hwa ku ba shi in kuna ba shi
: Sai diyad dattijai kadai ka amren
: Sha-yaya dan gidan Labbo, na Abu
: Tunda kowa amre shi ita ka cishe shi
: Ta biya kudin garin karen kyasko
: Sannan ta yi mai abin ruhwa
: Kana ta koma ta yi dabbalin abin damri.
Jagora: Dattiyo yat tashi : Yab buge riga yai
cikin zaure.
Nomau na
Magarya
Jagora : Nomau tushen hwada karem masu gari,
: Toronkawan tciya uban Mairogo,
: ko hwatara tai yawa takan zam iko,
: Nomau ko ba ka jin batun masu gari.
Jagora : Na Magaji kankari ba ka jika,
: gaude ba ka matanki,
: Baba kade ba ka baka,
: Nomau tushen hwada karem masu gari
Jagora: Gagarabadau ubangidan yaj Jimmau,
: Da Kassu barka da tciya,
: Banawa kyawon hwada a yo accakwama,
: Baba a wo ta bakikkirin ta kare maku can,
Na Magaji in ga ham magabata, Suna hawa za a
bida.
Jagora : Nai tambaya cikin ‘yan tauri
: Taro na tambaya ga manyam makada
: Wa anka ba doki da gangami ba ni ba?
Jagora: Doki da gangami sai Nomau na Magarya
: Uban Balindo shi ya she ni hak Kadawa
: Yac ce "Kassu ana bidak kada doki
: Ga ka
kana alhwarma.
Jagora: Dan kalgo ba ni kamnak karya
: Wa ka sai mani doki Magarya
: Nomau ne ko abin tuwo ba ya da shi,
: Kahiri karen Bunu Bako,
: Yanzu kau karen Alhaji ne.
Jagora: Yac ce da tarbace Za a saye.
: Niko ga ni da son doki,
: Sai nij ja turayena,
: Nit tasam ma Magarya,
: Niddora"Magarya shin ina alkawali?
: Magarya shin ina alkawali?
: Jama a ashe ba wanda yaj ji yag gani,
: Karya ce.
: Ta shani waka banza.
Jagora : Nizzo nic ce Saraki doki nika so,
: Ku Kau nac ce da tarbace za Ku saye,
: Yac ce la-la-la babu ruwana,
: Kassu in dan ni ko anini nau ba ya shiga,
: Nomau dai ba ya rage ma kowa Magarya,
: Sannan wani ba ya sa shi aiki shi tahi.
Jagora :Nic ce Allah waddan karhin Nomau,
: Mi karhinka yad dada na Magarya?
Jagora: Ni na baz zuwa gida ba ka yi shi ba.
: Baba in da sata ka kai, yi satak ka saye,
: In kau ka ga ba ka sata yi hwashe,
: Amma na baz zuwa gida ba ni da shi,
: In kau na isa gidan, bilai ya kasan,
: Sai La'ilaha illa lahu,
: Dada Kassu ya yi rantsuwak kahhwara.
Jagora : Nomau yaz zo yac ce,
: Saraki ka ga shi doki,
: Sabad da shi za ni hwashe,
: Shegen dai ya shige gida, ya ki hita,
: To hak kajuya yi rantsuwa ka ta kasa
: Saraki yac ce, "Mis sha muna kai,
: In dom mu ka tashi ko yanzu ka je.
Jagora: Sai ga Nomau ana ta gyaran layu,
: Da kambuna za a hwashe,
: Nic ce "In da sabad da ni,
: Ba ka hwashe na Magarya,
: Bari in ba ka shawara,
: Inkab bi ta gobe dokin aka yi
: Magarya, ko ba a da shi".
Jagora: Ba mai gina Magarya sai ta ruhewa,
: Dug gidan kara na,
:Amsad doki gidan kara mina na ga matcaci.
: Jagora Bari sai gobe da swahe,
: Iskan nan ta taso,
: Wanga na shikag gujiya,
: Mai kwasas sansami yana gamawa da Kasa,
: Ya faffako kar-kar-kar,
: sannan ebo wula ga ragga ka hita,: Sannan ebo
wuta ga ragga ka
hita
: koma daz zuwa gidan Dan-Aljanna, Koma daz
Zuwa gidan Da
: Hwalka yab bura uba-sai daji,
: Na Magaji rantsuwa ka ta kasan,
: Gama da yan kashin wuta, za ni hita
: Yac ce Kassu shawarakka ita za hi biya,
: Baba in kau kab bi ta,
: Gobe dokin aka yi Magarya ko ba ada shi.
: Dakanta ka jiya Nomau,
: Yac ce Kai ba in Jiya Da,
: Jab bura uba,
: Ba ni kamnak kowa Magarya,
: Duk ku rabu da ni.
: Ina biye ni kau ina y mai mabanci,
: Ina hwadin in dai ba a sonka,
: Tungak ka hita,
: In dai ba Su sonka,
: Tungak ka hita.
Jagora : Yac ce, Ina hita Mai-Kassuwa,
: Amma hwa ba da alheri ba,
: Bari ko an hana ni yanzu dd rana,
: Sai iskan sha diyun dare ya taso,
: Sannan za ni kunna yab bura uba,
: Magarya Sannan wada ko diyansu wasu ba su
hita.
Jagora: Gaude ba ka matanki,
: Baba kade ba ka baka,
: Na Magaji kankari, Ko Allahu na ruwa ba ka
jika,
: Dakokiso ko ba ka jin batun masu gar?
: Ba ka ya da cukurhwa ba,
: Ba ka ya da taimakon yaki da,
: Bunu ko Kudin gari a shahwa su hita,
: Nomau in am matce ka ce ba ka da su,
: Ban ga abin da za su diba ba garai
Jagora: Sannan Magaji yac ce,
: Assha Saraki dattijo da kai,
: Shin kaka kwabo guda ka lalata gart,
: Kwabo guda mina ne Magarya
Jagora: Ba dai doki ba na tauri,
: Ko mota munka so saye ba mu saye?
: To iyakan Nomau hwa an nan.
Jagora: In yak kau mu yab baro,
: Ban ga abin da za ka diba ba garai
: Wandara sai dai a koshi damri a sakat
: Nomau sai a koshi dibaw.wa adi,
Jagora: Torankawan teiya uban Mairogo
: Ko hwatara tai yawa takan zam iko
:A'a Nomau ko ba ka jin batun masu gari?
: Rabi'u dan Manyan Matcata
Jagora: Ba lahiya Rabi'u ka saba da yaya
: Rabe dutcin hwashin tama lam Majdamma
matcaci,
: Wadda kai mani ka kyaula mia Kassu.
Jagora: Na gode ma Rabe zaki dan Musa mai
takobi,
: Im ma Rabi'u kidi ya tashi ya karo
kau-da-bara,
: Wadda ubanai nah hwada ma1.
Jagora Mutuwa na da magani dan Musa,
: Rabe gidanka ka ga abina bal bace ba.
Jagora :Rawaiya ba ta ratsuwa ai stina,
: Maidamma bai sake ba,
: Rabi'u da nai ka ka yadda,
: Doki ukku kay yi man dan Musa,
: Take-take kowane sau nai bai bace ba,
: Doki ukku kay yi man dan Musa,
: Nomau take-take kowane sau nai bai bace ba.
Jagora : A a Rabi'u ka kyauta ma Kassu,
: Rabi'u ka kyauta ma kassu,
: Mai dala'ilu dân manyan matcata.
Jagora :Sannu da hwama na Rakkiya nal Ha'u,
: Na Rakiya na Ba'u,
: Kahiri na yab bulala,
: Koway yi gum da Rabi'u banza na kashi nai.
Jagora : Na san hwada ga rai dan Musa,
: Bana kowai karo da Rabi'u ya kaskanta kai bai.
Jagora : Na gode ma Rabe,
: Alhaji Mahammadu na gode da kyaula,
: Sarkin Tasha Mahammadu na gode da Kyauta,
: Abdu na mai doki wadda kai mant ka kyauta
makassu
: Sabadda Rabi'u dan manyan matcata.
Jagora :Doki ukku kay yi man dan Musa,
: Duk dore-dore kowane sau nai bai bace ba.
Jagora : Kyautaddan Maidamma mai ganin kwanji
dub baya yin ta,
: A ba ka ka amso fan talatin,
: Kuma gobe shi baka ka ka hwai sai fan
talatin,
: Kuma jibi shi ba ka hwai sai fan talatin,
: Rabi'u ya kyauta ma Kassu,
: Mai da Yas Sababai Allah ka so nai.
Jagora :Na san in Allah ya saukawa ma Rabi'u
mota.
Jagora: Ya sam mu tare da tsoho nai,
: Ko da yam mutu shi dai bai saki ba,
: Rabi'u dan manyam matcata
: Dan manyan kasake,
: Rabi'u dan manyan matcata,
: Rabe dutcin hwashin tama,
: Rabi u zakka awon maza dan Maidamma matcaci.
Jagora : Dutcin hwashin tama dan Musa,Saoues
StA a Dung
:Rabi'u zakka awon maza dan Maidamma na Kande.
Jagora : Maibabarbara Shehu Guraguri,
:A'a kluna bargazak kalangui ku rage wuta,
: Ku kashe wuta,
: Kuna hwa Jin kidin lad da hayaniya,
: Banawa ko ba ku Jin kalangan karayyaw wuka,
: Kuna jin batutuwan tad da hayaniya.
Jagora : Tauri wuya ga rai sai ayi kokari.
: A sha malammai a ebi sayyu a yi kariya,
: in an kiya a cinma sanin wani,
: ina ruwanmu ba ni Ka gama ku ba,
: Tunda Kuna wurin hwada goma ina gidanmu,
: Sai ya gamu in ji wai,
: Da ni da wane sai mun gamu kassuwa,
: Amma ina gida ina tad da zuga-zugi,
: Kun ji kalangai suna hwadin wani ya kashe
wani
Jagora: Bimin Magaji ba su furguria Kassu ba,
: Aa ba su rena kidinga ba,
: inna zo arinsu sai Sui mani kokari,
: Im mun gamu kassuwa suna ba ni na shan hura,
: Sule uku sule hudu,
: Kana su ce sabka lahiya suna gai da wadan
gida,
: Mai babarbara Shehu Guraguri,
: Kun ji kidin shehu masu banna da ido wuri.
Jagora :Rat tariyat Firimiya an bidi yamutci
K.aura,
: Ranat taryat Firmiya an piat anc,
: sai ga magaji ya dora gadauniya
Jagora :Mai babarbara Shehu Guraguri na Musa,
: Ka biya ni ba ka shanye kidin ga ba,
: Dada mahaukaci ya tsare unguwa,
: Amma dai ka na hwakewa da hayaniya ta, -
: Wa bai san kai ne ba ne Musa,
: Shehu masu banna da ido wuri
Jagora :Ba a san kai ne ba na Musa,
: Kassu abin da za a yi dufa yi in gani,
: Kassu abin da za a yi du'a yi in gani,
: Amma kuma ba ni Son ana tad da hwada gida,
: Don kada mu tara wasu ku yi yamutci,
: Ku dai sassabta: Ku dai sassabomu samu jallin tahiya gid mu samu
jallin
tahiya gida.
: Mai babarb: Mai babarbara
Shehu guraguri na Mra Shehu guraguri na
Musa.
: Ka biya ni ba ka shanye kidin ga ba,
: Ka ji kidin Shehu masu banna da ido wuri.
Jagora : Wasa an yi an gama sai tahiya gida,
: Barau na Bawa yas so tahiya gida,
: Niy yi rakkiya nik Koma ciki,
: Yan Gangare sun zo tahiya gida,
: Kassu ni yi rakkiya nik koma ciki,
: Ina dao Birnim Magaji ban tashi barin ta ba,
: Mani na garinmu yas so tahiya gida,
: Kuma niy yi rakkiya nik koma ciki,
: Ina nan Bimim Magaji ban tashi barin ta ba,
: In kun zo ku ce muna gai da wadan gida,
: Sai mun biya mu dan nan mu yi kan wani,
: Daga Gidam Kaso, Kassu ya yi Cgama,
: In dan dai shamusalli ban tashi zuwanta ba,
: Na wuce Sai dai badi in tano,
: Ina gidan Shehu mata tai na tuwo tana ba my
kare- kari,
: Saura a y kassuwa,
: In dai don ubangidan ba a daka ciki.
Jagora : Ba a san kai ne ba na Musa
: Shehu masu banna da ido wuri.
: Yara kuna jin ina hwadin Shehu Guragur
: Yara kuna jin irin kidin Shehu Guraguri.
Alhaji Isa Nakatuka
Jagora : katuka karhwandamin kare mai kashe
kura,
: Mahaukaci na kohur hana noma na Mairo,
: Taho da shirin gaba dan Haruna dan mai hana
nonma.
Jagora : Kai mutane in dai mutum Huntuwa yaz
zo,
: In dai Huntuwa kaz zo,
: In dai ba ka bidi gidan masu gari ba,
: Ba 'yan maza kama Alhaji Isa,
: Wadanda Sunka hali aka zo su ne Delu,
: Na Katuka karhwandamin kare mai kashe kura,
: Mahaukaci na Kofur nana noma,
: Taho da Shirin gabl dan Haruna,
: Dam mai hana noma na Kande
Jagora : Kai ubangidan shanu da Gaybu
: Na Delu albarkacinka nis sabu da Ciambu
: Kuma niss Sabu da Snata nay yay yi man
kujerah Hajiniz zo
: Doki ba a san ka hwasa daukal lihidi ba
: Arziki bu nga na da Ko a zwage ma mutun shi
: Ba ka gudun gaba dan Huruna dam mai hana noma
na Delu
: Ba ka gudun gaba dan haruna dam mai hana
noma.
Jagora : Na Katuka,
: Na Katuka karhwandamin kare mai kashe kura na
Delu,
: Da munka zo gidan Alhaji lsa,
: Yac ce kidi in yi ma Gambu shi alhaji ne shi,
: Nac ce to ban kau rarrabad da waka haka nan
ba,
: Yarana ku dora tausa mashi taki,
: Sai an ga hankalin alhaji ya kau,
: Sai ga alhaji an hilo da gora da barandami
Jagora : Da kau wakakkashi runtce ga hannu,
: Dada hwa hankalin alhaji ya kau na Kande
: Na Katuka karhwandamin kare mai kashe kura
: Na Katuka mai jan hali na Gambu hana noma,
: Na Katuka mai jan hali na Gambu,
: Mahaukaci na kofur hana noma,
: Doki ba a san ka whasa daukal lihidi ba,
: Ban san huntuwa ba sai dai in shiga garin in
yi Kaduna,
: Kuma in biyi ciki in kashe sauna,
: Kuma in shigo garin in yi Kaduna,
: Sai yanzu da dan Haruna yas sa mani hannu,
: Ban dai son in kwan cikin gari ba ni da kowa,
: Kwan da shirin gaba dan Haruna dam mai hana
noma,
: Mahaukaci na Kohur hana noma na Kande.
Musa na Kasar Dan 'ali Mai Tauri
Jagora : Ya san hanyah hwada,
: Musa na kasad Dan AR-mai tauri.
Jagora : Kai mutane tauri ya koma ga gadajje,
: Manyan hwada Musa,
: Na kasad Dan'Ali wan karhi.
Jagora : Na so zuwa gidam Mani a kaye ina
sauna,
: ba yan yara warina,
: Sai yac ce diya nai ba su son tauri,
: Tsohon kau ya yi yayi nal,
: Nic ce sai nai kidi,
: In dai hanyak kidi ta taho.
Jagora : Jama'a na so Zuwa gidam Mani,
: Ba hanyak kidin tauri.
Jagora : Dan yaro ne Musa,
: Ashe ya ci magani,
: Bai samu wunn gwaji nai ba,
: Rannan sai yaddauki kwashe nai,
: Yat tasam ma gona tai,
: Ya ishe Sulllubawa,
: Yab bi yana bugun shanu,
: Yab bi yana kashin shanu,
: Yab bi yana kashin shanu.
Jagora : Ashe Musa ya ci magani,
: Bai samu wurin gwaji nai ba,
: Suna ta bugu suna sara,
: Dud dai ba a huda kainai ba,
: Ku am manyan hwada,
: Musa na kasad Dan Ali mai tauri.
Jagora : Yak kai kurwah hwada,
: Mata kuma sun sheka suna kuka,
: Ku yo gudummawa Hillani sun kashe Musa,
: Ku yo gudummawa Hillani sun sabafta shi.
Jagora : Had Dan'Ali zai wo hawa,
Nac ce: Ko ba ka ji Mani,
: Hillani sun kashe ma da.
Jagora : Tsoho bai bata rai nai ba,
: Bai kai ko ga kai nai ba,
: Sai yai ta jikon karera nai,
: Ya san ya shiryi yara nai.
Jagora : Nac ce ko ba ka ji tsoho,
: Hillani sun sabatta ka.
Yac ce "Dan'Ali koma gida,
: Ja dan nan ba ni son Karya,
: Ba ta biyu ba ba sara,
: Ba kau yakin takbi ba,
: Dan su Musa na tahowa gida.
Jagora : Manyan hwada,
: Musa na Rasad Dan'Ali wan karhi
Dammande
Jagora : Gagari daga karen Iro ba a ga jininka
ba,
: Dammande mai taurin jiki,
Jagora : Na gidan alasan mutanen Zamani,
: Ga ka da karhi Alasan ka hukadkudaku,
: Ko
gewaya sat ran gina dan Musa,
: Ko gewaya sai ran gina,
: Dammande mai tarin jiki,
: Dammande maij tàrin jiki,
Jagora : An yi hwada da Baura ana kuddin gari,
: Ni ce Ku ne zurn'ar rashin dadin batu,
: To an yi hwada da Baura ana kuddin gari,
: Ni ce "Ku ne zuri'ad da ba dadin batu,
: In ka ji an tad da ba, Dansanda ne,
: Kanan ga a dunkuli wuski,
: Bana ba biya sai sai lamuni dan ldi.
Jagora : Dammande ban ga jininka ba,
: Dammande mai taurinjiki
: Dammande na gode,
: Na gode na Gidan oga na gode,
: Ka ba ni kuddi,
: Kuma ka ba ni dawaki,
: Ka koma ka sa man riguna,
: Na gode Baura,
: Ka sunkuda mani kuddi Dammaliki,
: Kassu kuma riguna sai na gaji,
: Ka sai mani doki,
: Ka koma ka sa man riguna,
: Allah dai shi kara maka arziki,
: Baura Allah dai shi kara ka amin don Kassu,
: Allah dai shi kara maka arzikinka,
: Baura Allah dai shi kara ka amin don Kassu.
Jagora : Na gode Alasan mutanen zamani,
: Ga ka da karhi Alasan ka hudak kudaku shi
kadai,
: Ko gewaya sai ran gina,
: Dammande mai taurin jiki,
: A Dammande ba a ga jininka ba,
: Dammande mai taurin jiki.
Jagora : Gagari daga karen ldo;
: Karen ldo mai karhin gaba.
: Ummaru Sabon Birni .
Jagora : Wannan abun mu né dangin Bawa
Gobirawa,
: Amma ko da Bawa yam mutu ba inda bai baro
suna nai ba.
Jagora : Ko can in ka ji gatari sai buzu,
: Yara ko can don hwada aka tsoronuwa gidan
Jangwarzo.
: Don hwada aka tsoron zuwa gidan Jangwarzo
Jagora : Haba abimmu ne dangin Bawa Gobirawan
asali,
: Ko da bawa yam mutu ba inda bai baro suna nai
ba,
: A'a ba inda bai baro hwansa ba,
: Ko gobe dan hwada aka isoron zuwa gidan Jangwarzo.
Jagora : Rad da Allah yay yo ni
: Kassu rad da Maisama yay yo ni,
: Ka ganan nan ban zo kidi ba Sabon Bimi,
: Sai da Ummaru yay Kirammu sabon Birmi,
: Sanda jikan Shawai,
: Ummaru jikan Shawai, :Zuriyag gidan Jari
Kada.
Jagora : Sai da Ummaru yay kirammu sarki naz
zo,
: Amma im baicin rashin sani,
: Ba bako ba ne gida nid dawo,
: Dan hwada aka isoron zuwa gidan Jangwarzo
: ko gobe dan hwada aka tsorgn zuwa gidan
Jangwarzo.
Jagora : Wo dam maki gudu
: Mai sulken jiran maza dan Isa
: Da kai amza suka tsoron hwada na Sabon Bimi
: Dan hwada aka tsoron 2uwa gldan Jangwarzo.
: Bagobiri Sabon Birni
Jagora : A baude ma Bagobiri,
: Koma shirin duniyag ga hay yau ba ta gyaru
ba,
: Ku shirya ba ta kimtsu ba,
: Koma shiri duniyag ga hay yanzu da yamutci,
: To bari wani yai izgilki a debe mashi doriya,
: Kada wani yai zigili a gabce mashi kan hwari,
: Saji da Bagobir.
Jagora : Dadi na da Gobirawa,.
: Du inda kunka zo ba ku hukuntuwa.
Jagora : Baban Lawwali uban fnai saje.
: Sa adu barkak ka da yaute
: Barkak ka da yamutci
: Sa'adu barkak ka da yamutci.
Jagora : Baude ma Bagobiri,
: Sabon Birni Sa adu barkak da ka yamutci.
Jagora : Ga sako wanda za ni kai ma,
: Ka lura da wakad da yay yi ma,
: Sai ka yi kokari ka šho mani rakumi,
: Kahin in taho mu iske ka da rakumi,
: Caman in na zo Arewa sai na rike rakumi,
Kulum niz zo Arewa sai na rika rakumi.
Jagora : Sarkin Rahi Haruna ya kai mani rakumi,
: Sarkin Rahi na Haruna ya kai mani rakumi,
: Dandawaki na mai lalle ya kai imani rakumi,
: Dandawaki na Mai'lalle bara ya kai mani
rakumi.
Jagora : In na zo arewa sai' na rike rakumi,
: Ina son ka yi kokari,
: Ina son ka yi hamzari, ka yi cinaki ka damre
mani in taho.
Jagora : Sa adu ina son ka y cinaki ka damre
mani in tano,
: Baude na Bagobiri.
Jagora : Baban lawwal uban mai saje,
: Sa'adu barak ka da yamutci,
: Nabara so nikai
: Nabara so nikai ku damre mani rakumi
: Ku damre mani rakumi,
: Ku aika mani in taho,
: Kai Nabara so nikai ku damre mani rakumi,
: Ku aika mani in taho.
Jagora : Hana noma na Hankurau,
: Sa’adu mai hana noma na Hankurau,
: Sa'adu barkak ka da yamutci,
: Sarkin Karman Gobir an nan Sabon Birni.
Jagora :Yara ku san dadina da Gobirawa,
: Du inda Sunka zam ba su hukuntuwa,
: Ina wani mai gardama a debo mashi doriya,
: Ina wani mai son hwada a jirge mashi kan
kwari.
Jagora : A koma shiri duniyag ga hay yau ba ta
gyaru ba,
: Yara ku koma shiri duniyag ga hay yau ba ta
kimtsu ba.
: Madalle Bagobiri,
: Madalle Bagobiri,
: zuma na yawo,
: Yaro kada ka yi izgili ta hwada maka
kakkarai.
Jagora : Sabon Birni gidan Bawa Jangwarzo,
: Inda masu yaki suke gurzuwa.
Jagora : Gidan bawa Jangwarzo
: Ka gane su hay yau ba su milku ba,
Sa’adu hay yau ba ku gyaru ba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.