𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, malam don Allah ina da tambaya, shin akwai wata addu'a da ake ma
jaririya a farji idan an haife ta, namiji ba zai taɓa kusantar ta ba in dai ba
mijinta ba ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Ni dai a iya
ɗan ƙaramin sanin da Allah ya ba ni ban san wannan addu'a ba, kuma ban taɓa jin
ko labarinta a wajen malamai ba, sai dai kawai abin da na san ya tabbata daga
Annabi ﷺ shi ne abin da Imamul Bukhariy ya ruwaito, wato hadisin Abdullahi ɗan
Abbas cewa Annabi ﷺ yana nema wa jikokinsa Alhasan da Alhusain tsari da wannan
addu'a kamar haka:
"أُعِيْذُكُمَا
بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ
لَامَّةٍ".
Ma'ana:
Ina neman
maku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaiɗani, da dukkan wata dabba
mai dafi, da kuma dukkan wani kambin ido mai cutarwa.
Bukhariy a
hadisi mai lamba 3371.
Wanda ba zai
iya yi da Larabci ba yana iya yi da Hausa, ko da duk harshen da mutum ya fi
iyawa, idan da Larabci za a yi, kuma ya kasance yaro ne namiji shi kaɗai, wajen
"أُعِيْذُكُمَا" sai a ce 'أُعِيذُكَ', idan kuma yarinya ce sai a ce 'أُعِيذُكِ',
idan kuma yaran sun wuce biyu sai a ce 'أُعِيْذُكُمْ'.
Wannan ita
ce addu'ar da ake yi wa yara, wadda ta tabbata daga Manzon Allah ﷺ Kuma in
Allah ya so duk wanda yake yawan yi wa 'ya'yansa wannan addu'a Allah zai tsare
su daga dukkan cutarwar mai cutarwa mutum ko aljan. Allah ya sa mu dace.
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.