Tarbiyyar Yara A Musulunci [ 19 ]

     MATAKAN SAMAR DA YARA NAGARI

    Addinin musulunci ya koyar damu hanyoyi na samar da yara nagari tun daga matakin neman aure har izuwa haihuwa dama girmansu.

     Matakin farko shi ne hanyar da aka gina neman aure, idan aka sami ma'aurantan da suka yi aure don neman yardar ALLAH tare da niyyar mai kyau, kuma suka kiyaye kansu daga afkawa zina a cikin soyayyarsu kafin aure, to ALLAH zai taimakesu da yara nagari, saboda mahaifar uwar ba a zuba mata haram ba.

     Sannan kuma idan aka sami uwa da uban basu aikata zinace-zinace a wasu gurare can daban ba, kafin su san juna, domin zinar uba tana jawowa a yi ramuwa akan yaran da za su haifa, mutuƙar wannan uban bai tuba ya nisanci zinar ba tunda samar takarsa ba.

     Sannan bayan aure kafin samun ciki, mu'amula mai kyau da kuma kiyaye hakkokin juna tare da samarwa da juna farin ciki a cikin zamantakewa yana sawa a sami yara nagari, domin sai iyaye suna da nutsuwa da ƙaunar junane suke samun damar bawa yaransu tarbiyyar data dace.

     Sannan kuma a duk lokacin da namiji zai kusanci matarsa ya yi addu'ar da sunnah ta koyar, ko kuma yace BISMILLAH kafin ya fara jima'i da matarsa, saboda Annabi {s.a.w} Ya ce:

     Idan mutum ya zo zai sadu da matarsa shaiɗan yakan matso kusa, duk abin da ka aikata da matarka shima sai ya aikata mutuƙar baka ambaci sunan ALLAH ba, idan aka sami ciki a wannan saduwar, to sai a sami yaro ko yarinya mara tarbiyya, fitinanne a cikin al'umma.

     Mutuƙar baka ambaci sunan ALLAH ba to sai ya zama shaiɗan yana da nasa rabon ajikin wannan yaron, shi ne zaku ga yaro ya zama wani iri, kodai ya zo mara lafiya ayita shan wahala, ko kuma ya zama ɗan iska ya fitini kowa a unguwa, ko kuma ta zama ‘yar iska a gari, don haka a kiyaye ambaton ALLAH kafin a fara saduwar aure, sannan kuma namiji ne zai yi addu'ar ba mace ba.

     Sannan kuma idan an haifi yara a rinƙa kula da yanayin cin abinsu da shan abin shansu, domin zaku ga yara suna fara cin abune da hannun hagu, to shaiɗan ne yake sasu ci da hagu, don haka sai ku rinƙa cin abinci tare da yaranku, domin koya musu cin abinci da hannun dama, saboda kaucewa koyarwar shaiɗan.

     Sannan kuma idan yamma ta yi sosai kafin magriba ku rinƙa killace yaranku guri ɗaya, kudaina barinsu suna guje-guje suna wasanni, a tsakar gida, saboda faɗin Annabi {s.a.w} cewa shaiɗanun Aljanu sukanyi wasanni a daidai wannan lokacin, idan suka sami yaran mutane suna iya cutar dasu, daga nan sai yara su zama lalatattu, su gagari iyayensu.

     Sannan kuma iyaye su kiyaye aikata wasanni ko taɓe-taɓen juna, koma saduwa agaban yaransu komai ƙanƙantarsu, domin yaro duk abin da ya gani yana ƙarami baya taɓa mantashi kuma yana tasiri a cikin rayuwarsa.

     Sannan kuma ku rinƙa ƙoƙari wajen bibiyar da suwa suke abota domin ana iya samun masu koyar dasu ɗabi'un banza irinsu neman mata ko neman maza, ko maɗigo ko wanin haka.

     Sannan dole ne uwa ta zama mai kamun kai domin yaranta suna koyine da ɗabi'unta, idan uwa tana ashar suma za su koyi ashar daga bakinta, idan uwa tana yawon shiga maƙobta, suma za su koyi yawon maƙobta, idan uwa tana yiwa mijinta sata suma za su koyi sata, idan uwa ta zama mai kwaɗayi suma yaranta za su zama masu kwaɗayi,

     Idan uwa ta zama mai tausayin mijinta da sauran al'umma, to suma yaranta za su zama masu tausaya mata tare da sauran al'umma, amma idan uwa ta zama tagari, to yaranta za su zama nagari masu tausaya mata.

     Sannan kuma idan kunada yara mata manya, a rinƙa kula da irin saurayin da take kulawa, ko da kuwa yakawo kuɗin aurenta, bai kamata ku saki jiki dashi sosai ba, domin wasu samarin nada haɗari sosai.

     Sannan yana daga cikin abin da ke jawo lalacewar tarbiyyar ‘yan mata a yau da sun yi saurayi musamman wanda yake son aurensu dagaske sai a ɗakko nauyin yarinyar kusan kaso 50 cikin 100 a ɗora masa, ta yaya wani ba zai yi zina da ita ba, wannan bai dace ba, bata zama matarsa ba, bai dace a ɗora masa nauyinta ba, wanda kafin zuwansa ai iyayenta ke ɗaukar nauyinta.

     Sannan wasu iyayen babu ruwansu da irin kyautuka da yaransu ke shigowa gida dasu, basa bincike, basusan cewa samari na amfani da kyautuka su lalata ‘yan mata ba, haka kuma masu lesbian na amfani da kyautuka su lalata ‘yan mata.

     Haka kuma iyaye basu damu da bibiyar wayoyin da yaransu ke riƙewa ba, lallai wannan kuskure ne babba, sai kuga yarinya ta raba dare tana online, tanata chat na banza da samari, ko kuma da ƙawayenta ‘yan lesbian, sunata turawa juna hotunan banza, wannan babbar masifa ce.

     Haka kuma zaka ga yara ƙananu suna shige-shige a wayoyin iyayensu harma sunsan yadda za suyi searching na Blue films su laɓe suna kalla, wannan ba ƙaramin kuskure bane gareku yaku iyaye, ku rinƙa kula da yaranku sosai.

     Sannan idan yara sunkai shekara 10 ku raba musu makwanci inji Manzon ALLAH {s.a.w} inba hakaba, fitina zata afku, shaiɗan zaizo ya raya musu wani abu na saɓon ALLAH, ko da kuwa duk su biyun mata ne, ko kuma duk su biyun maza ne.

     Sannan kuma ku yawaita yi musu addu'a a cikin sujudunku a cikin sallolinku domin nema musu tsarin ALLAH daga shaiɗanun mutane da kuma shaiɗanun abokai da kawaye, domin ku iyaye zaku bawa yaranku tarbiyya na tsahon shekaru amma wani zaizo a cikin minti 10 zai rushe wannan tarbiyyar gaba ɗayanta.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.