Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Hallata Saurayi Da Budurwa Su Yi Aure Ba Tare Da Sanin Iyayensu Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Shin Ya Halatta Saurayi Da Budurwa Suyi Aure Babu Wanda Ya Sani A cikin Dangin Budurwar Da Dangin Saurayin, Kuma Suna Garinda Iyayensu Suke.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد والصلاة والسلام على رسول الله.

Shidai aure baya inganta saida Abubuwa guda uku:

1. Sadaki

2. Shaidu biyu

3. Waliyyi (bangaren mace)

Namiji yana iya neman aure sannan ya biya sadaki harma ya karɓi auren ba tare da ya fadawa kowaba.

Sa'eedu bin musayyib_ ya aurawa dalibinsa 'yarsa ba tare da dalibin ya zoda kowa daga danginsaba.

Sannan Abdurrahman bin Auf ya yi aure azamanin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam kuma bai sanadda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ba, sai daga baya Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yaji labari sai ya ce: masa ka yi WALIMA ko da DA AKUYAC NE ashe namiji zai iya aure ba tare da ya sanadda danginsaba.

Amma mace bata Auradda kanta a shari'ance. Dole ta Samu wani wanda zai zama waliyyinta awajen bayarda aurenta.

Wanda sukafi can-cantar subada auren mace sune:

1. Uba, Kaka, Yayanta.

2. Ɗah, ɗan Ɗah, ko kanin Ɗah, ko yayan Ɗah.

3. Makusantanta cikin dangin uba Yayan mahaifinta ko kanin mahaifinta.

4. Sarki ko wakilinsa, idan babu ɗaya cikin wadancan ko auren yakai gaban alkali.

Induka mace ta rasa wayannan akan dawo aduba a cikin dangin mahaifiyarta awakilta wani ya bada aurenta.

In ba a samuba, to sai tasamu wani namiji ya wakilci bada aurenta.

Malaman fikhu sukace: Idan mahafin mace yana raye sai taje wani daban ya daura aurenta kuma ba mahaifinne yabada damaba, to Aure ya ɓaci.~fathul jauwaad-1-150.

Dan haka sunan wannan aure da sukayi auren mutu'ah auren jin daɗi daholewa kawai zina kenan ma'ana karuwanci.

Shi ne akeyinshi ba shaidu, ba waliyyai, ba sadaki, saidai ladan aiki.

Shikuma auren mutu'a Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya haramtashi alokacin da akadawo daga yakin khaibara.

Dan haka wajibi ne suraba auren tsakaninsu su samu waliyyai da shaidu asake daura musu aure, idan sun samu Ɗah ko ciki to ɗansune.

WALLAHU A'ALAMU

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Nakwarai.

Hukuncin Auren Da Saurayi Da Budurwa Suka Yi Atsakaninsu:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Slm malam ygd . Malam tambayata ita ce miye matsayin Auren da saurayi da budurwa suka yi atsakaninsu alhalin iyayensu na raye sunyi ne dan kada su aikata alfasha sukayi siga tsakaninsu yanemi Aurenta Akan wani Sadaki itakuma ta bashi auren ta bisa amincewarta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Aure baya zama Aure Tsakanin mace da Namiji har sai da Abubuwa guda Huɗu.

1. Na farko Shi ne ya zama Akwai Sigar Aure a Tsakanin Waliyyan Waɗannan Ma'auratan. Ma'ana Waliyyin Namiji Yace Ina Nemawa Ɗana ko Kane na Ko Jika na ko Abokina Wane Auren ɗiyarka Wance ko Kanwarki Wance Ko Mahaifiyarka Wance. Domin Da zai iya Yiwa Mahaifiyarsa Alwalanaci. Kamar Yadda Anas ɗan Malik ya yiwa Mahaifiyar sa Ummu Sulaimin Alwalanci a Lokacin da Abu Dalhatal Ansariy ya zo Aurenta. Sannan shi Alwalalin wannan Macen Yace Na Baka. Sai Alwalin Wannan Namijin Ko Wakilin wannan Namijin Yace Na Karɓa Masa.

2. Abu Na Biyu Kuma Shi ne Alwalanci. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace MACE BA TA AURAR DA MACE, SANNAN MACE BA TA AURAR DA KANTA. Sabida haka Kenan. Wajibi ne a sami wanda zai Aurar da ita, Kuma Wajibi ne ya Wannan da zai Aurar da ita ɗin ya zama Namiji. Mutumin da ya fi kowa Chanchanta wajen Aurar da ita, Yimata Alwalanci shi ne Mahaifinta. Idan babu Mahaifi Sai a Sami wani daga Cikin Dangin Mahaifinta Ya Aurar da Ita. Idan babu daga dangin Mahaifin ta, sai a sami wani daga dangin Mahaifiyar ta. Idan babu dangin Uwa sai Shugaba Kamar Sarki ko Hakimi ko Dakaci ko Bulama ko Mai Unguwa. ya yi Mata Alwalanci.

3. Aure Baya Yiwuwa sai da Sadaki. Wajibi ne ya zama an san sadakin wannan Matar tin kafin A zo Maganar Ɗaura Wannan Auren. Sannan Waliyyanta Za a dankawa Wannan Sadakin Ba Ita ba. Daga baya ne kuma zasu bata kayanta. Amma mace bata karɓar sadaki da hannunta. Ko da Kuma ta Karɓa da hannunta. za ta kawowa Waliyyanta su gani su sanya Masa Albarka. Sai Kuma ita wannan Bata Nemi Albarkar iyayenta akan Wannann sadakin Nata ba. Hatta a Auren Nata ma bata Nemi Iyayenta su Sanya Mata Albarka ba.

4. Wajibi ne a sami Shedun da Zasu Bayar da Shaidar Cewar a Gabansu Aka Ɗaura wannan Auren, kuma duk Wani Sharadi na Wannan Auren an cika Shi. Sannan Ne zasu Ba da Shaida. Wajibi ne Wadannan Shaidun Akalla Su Zama kamar Mutum Ukku, da zasu tabbatar da Dauruwar Wannan Aure. Idan babu Shedu Aure bai yiwu ba. Sannan ya zama Wajibi Waɗannan Shedun su zama Masu Hankali, Adalai.

Sabida haka kenan. Ta Kowanne Fuska wannan Auren bai yiwu ba. Domin bai Cika Duk wani Sharadi na Aure ba. Wannan Wasan yara ne. In banda ma Rashin Tarbiyya. Ta yaya Mace Budurwa za ta Aurar da kanta ga wani Namiji. Ba tare da sanin Iyayenta ba. Allah ya gyara mana wannan zamanin da Muke Cikinsa.

Allah Shi ne Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments