𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Akwai Addu'ar Da Mutum Zai
yi Yashawo Kan Budurwa Tasoshi Saboda Allah Suyi Aure?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله
Babu wata addu'a keɓantacciya
cikin abun da muka sani wacce mutum zai lazimci yinta idan yana neman aure,
wacce ta tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, Saidai wajibi ne ka
roki Allah ya azurtaka da mace tagari.
Hakika Annabi Sallallahu Alaihi
wasallam yakoyar damu Addu'ar "Istikara" Ma'anarta shi ne kanemi
Allah ya zaɓa maka abun da yake shi ne alkhairi agareka, cikin al'amura gaba ɗaya
duniya da lahira, wannan addu'a ita ce wacce jabir bin Abdullahi Allah yakara
masu yarda yaruwaito ya ce: Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance yana
koyar damu "istikara" a cikin dukkan al'amura gaba ɗaya, kamar yanda
yake koya mana sura daka alƙur'ani, Ya ce: Idan dayanku yai niyyaci wani
al'amari, ya yi sallah raka'a biyu, bata farillah ba, sai ya ce:
اللَّهُمَّ
إِنِّي أَسْتَخِيـرُكَ بِعِلْمَكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ
فَضْلِكَ الْعَظِيمِ، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ،
وَأَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ، اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الَأمْرَ
(وَيُسَمِّي حَاجَتَه) خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ
لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا
الأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عَنِّي
وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ
(Allahumma
Inni astakiruka bi'ilmika, Wa'astaƙadiruka biƙudiratika, wa'as'aluka min
fazlikal Azeem, Fa'innaka taƙdir wala aƙdir, wata'alamu wala A'alamu, Wa'anta
Allamul guyub, Allahumma inkunta ta'alamu hazal amru (Saika Ambaci bukatarka)
khairan li fidini wama'ashi, wa'aƙibatu Amri faƙdurhul li, wayassarhulli, summa
barikly fihi, Wa'inkunta ta'alam annah hazal amru (saika ambaci al'amrin )
Sharran li, fi diny wama'ashi wa'aƙibatu amri, fasri-fhu anni, wa'asrif-ni
anhu, waƙdirly khairan haisu kana, Summa Arzhini bihi,)
Bukhari (1109).
Dangane da miji Annabi sallallahu
Alaihi wasallam ya ce: (idan wanda kuka yarda da addininsa da halayensa ya zo neman
auren 'yarku ku aurar masa, idan ba hakaba fitina zata auku aban ƙasa da fasadi
mabayyani,) Turmuzi (1084) da ibnu majah (1967).
dangane da Mace: Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Ana auren mace saboda abubuwa huɗu, kyawunta
nasabarta, dukiyarta,addininta, kanemi ma'abociyar addinin zata hutar da
hannuwanka ) Bukhari (4802) da Muslim (1466).
Alhafiz ibnu hajar rahimahullah ya
ce: Ma'anar mace takasance mai addini, addini yakasance shi ne abun da mutum
yake dubawa akan komai, musamman akan abun da zaka dade kana zama dashi, Sai
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceshi da ma'abociyar addini, wanda shi
ne kololuwar abun nema, fat-hul bari (9/135).
Wannan shi ne abun da zaka maida
hankali a kansa wajan dacewa dasamun mace tagari maisonka don Allah kuyi aure
WALLAHU A'ALAM.
Tambaya da Amsa Abisa fahimtar
Magabata Nakwarai.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.