𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, Allah ya gafarta malam, wata rana ina bacci sai na yi mafalki, a cikin
mafalkin sai na ji an ce min kullum in safiya ta waye kafin na ci komi, na
dinga karanta bisimillah sau 7 ina tofawa a ruwa in sha, to ni kuma da na tashi
sai na dinga yin hakan, to malam ya halatta na ci gaba ko na daina.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam, ‘yar uwa karanta Bisimillah abu ne mai kyau kamar yadda duk Musulmi ya
sani, amma inda matsalar take shi ne: Idan aka buɗe kofar naƙalto ayyukan
addini ko ibada ta hanyar mafarki, to hakan zai iya kawo ma addini rikicewar
al'amura, saboda ai ba a san wane ne yake ba da wannan umurnin ba, wata ƙila
Shaiɗan ne yake neman da haka ya kai ki zuwa aikata abubuwan da ba su dace ba
da sunan addini, saboda ba ta inda Shaiɗan ba ya ɓullowa mutum don ya ga ya halaƙar
da shi, wani lokacin ta hanyar wata ibada yake ɓullowa mutum.
Saboda haka
kawai ki daina yin wannan aikin da ba ki san wane ne ya ba ki umurni ba, ki
dage da riƙon zikirin da Annabi ﷺ yake yi safiya da yammaci, da sauran
zikirorinsa, lallai idan kika riƙe wannan na Manzon Allah ﷺ ɗin muna da yaƙinin
za ki sami dacewa fiye da wanda ba a san haƙiƙanin wane ne ya ba da umurnin ba.
Sannan kuma
yana da muhimmanci a riƙa karyawa da dabino guda bakwai kafin a ci komai a
kowace safiya idan an sami dama, kamar yadda Annabi ﷺ ya tabbatar cewa duk
wanda ya yi hakan wata cuta ta dafi ko sihiri ba za ta same shi ba. Amma a
ruwayar hadisin Muslim an ce dabinon Madina ne, kawai dai idan ba a sami ta
Madinan ba a yi amfani da wadda ake da ita.
Bukhariy
5445. Muslim 2047.
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.