Ticker

6/recent/ticker-posts

Yaya Matsayin Ganin Allah A Mafarki?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam na kwanta bacci da daddare sai na yi mafarkin ubangiji yana tambayata wa'yan ne diya nika son ya ba ni? Sai na ce masu yawa masu albarka, amman fa bangan shi da idona ba, kawai dai na yi mafarki ne, shin da gaske ne ko aikin sheɗan ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, daga cikin malamai akwai waɗanda suka ce mutum zai iya yin mafarki ya ga Ubangiji Subhaanahu Wata'ala a cikin barci, amma fa abin da ya gani ɗin nan ba shi ne haƙiƙanin zatin Allah ba, saboda shi Allah babu wani abu da ya yi kama da shi kwata-kwata. Har ma Imam Albagwiy ya hakaito daga wani malaminsa cewa:

Ganin Allah a cikin barci (mafarki) halas ne, idan mutum ya yi mafarkin Allah har ya yi masa alƙawarin Aljannah, ko alƙawarin gafara, ko alƙawarin samun tsira, to wannan maganar tasa gaskiya ce, alƙawarin Allah gaskiya ce, idan kuma ya yi mafarkin Allah yana kallon sa, to rahamar Allah ne ya gani, idan kuma ya yi mafarkin Allah ya kawar da kai daga gare shi, to gargaɗi ne game da zunubansa, idan kuma mutum ya yi mafarkin Ubangiji ya ba shi wani abun duniya, har kuma ya karɓi wannan abu, to wannan zai gamu da jarabawa da rashin lafiyar da za ta taɓa jikinsa, kuma hakan zai girmama ladan bawa, har ya kai ga samun rahamar Allah...

Duba Sharhus Sunnah (12/227, 228) na Imam Albagwiy.

Haka shi ma Imamun Nawawiy ya hakaito daga Alƙadhiy Iyadh ya ce: "Malamai sun yi ittifaƙi a kan halascin yin mafarkin Allah a cikin barci, ko da kuwa mutum ya gan Shi ne a cikin wata siffa da ba ta dace da halinSa ba na daga cikin abubuwa masu jiki, to lallai wannan abin da aka gani a mafarki ba shi ne zatin Allah Maɗaukakin Sarki ba..."

Duba Alminhaaj (10/25), na Imam Annawawiy.

Wannan ya nuna cewa zai iya yiwuwa mutum ya yi mafarkin Ubangiji, amma ba zai ga Ubangijin a zatinsa ba, ko da ma ya ga wani abu ne, to wannan abin ba shi ne Allah ba, saboda ba wani abu da yake kama da Allah, kuma ba ya yiwuwa mutum ya ga Allah a haƙiƙanin zatinSa a wannan duniya kamar yadda nassoshi da dama suka tabbatar, amma za a iya yin mafarkinSa kamar yadda bayani ya gabata daga waɗancan malamai.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments