𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum ɗan'uwa kuma malamina ga tambaya na ji wata fatawa wacce ba ni da ilimi
a kanta, wai idan mutun ya yi sallah babu Alwala wai hukuncinsa sai ya sake
kalmar shahada ta shiga musulunci, mene ne ingancin wannan maganar? Allah ya
taimaka Amiin.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum
Assalam To malam wannan maganar ta shahara a wajan mutane, saidai a wajan
malamai yin sallah babu alwala ya kasu kashi biyu:
1. Idan ya
aikata, amma bai halatta hakan ba, ya san ba daidai ba ne, kamar ya aikata
saboda kasala, wannan kam bai kafirta ba, saidai ya aikata babban zunubi.
2. idan ya
aikata yana mai halatta hakan, ko kuma saboda izgilanci ga addini, sannan ba
jahili ba ne, ba shi kuma da wani ta'awili, tabbas wannan aikin kafirci ne, har
ma malamai da yawa sun hakaito ijma'i akan kafircin wanda ya yi hakan, saboda
akwai karyata shari'a a ciki, da kuma wula kantata
Allah ne
mafi sani
Duba:
Almajmu'u na Nawawi 2\84 da Minhajussunah 5\204.
DR. JAMILU
YUSUF ZAREWA
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.