Abstract: The aim of this study focuses on the traditional titles of slaves in Katagum. It is based on this aim that the research was presented in five chapters. The first two chapters focussed on general overview of the work and relevant literatures related to this research. Chapter three has taken broader look at the historical background of slevary in Hausaland. After the historical survey, the research narrowed to the slave-only traditional titles in Katagum. This has seen the research scrutinising indepthly all the issues surrounding slave- only traditional titles in Hausaland even before the emergence of Katagum. Similarly, the research has scrupulously found out the findings of the work. The research found out that some traditional titles have become extinct. Against this backdrop, traditional instutition have been recommended to establish a special traditional titles office that will handle the historical facts of the kingdom/emirate and other traditional title holders.
Tsakure
Ƙudirin wannan aiki tunkarar Sarautun
Bayi a ƙasar
Katagum. Bisa ga wannan ƙudirin an kasa binciken zuwa babuka
biyar. Goshin aikin ya tunkari gabatarwa da bitar ayyukan da suka gabace shi.
Kashi na uku na aikin ya yi dogon share fage a kan tarihin bauta a ƙasar
Hausa. Bayan an yi wa tarihi turke mai ma’ana sai aka dubi masarautar Katagum
da sarautun bayi da ke ciki. Wannan ya nuna an ƙoƙarin
kakkeɓe
duk wata ƙura a tarihi da al’ada da bautar take
ciki a ƙasar
Hausa gabanin a yi ƙasar Katagum dubi na nutsuwa. Binciken
ya yi kwakkwara da kammalawa wadda ta fito da ɗan sakamakon bincike da aka yi. Tabbas an
gano cewa wasu sarautun gargajiya a fada sun soma ɓata. Don haka, tilas a farfaɗo ko ƙirƙiro
wata sarauta cikin kowace masarauta a ƙasar Hausa da za ta kiyaye da tarihin
sarautun masarautarta.
Sarautun Bayi A Ƙasar Katagum (1814- 2016) – KASHI NA 3
Muhammad
Abubakar Zabi
muhammadabubakarzabi@gmail.com
08136844199
SADAUKARWA
Na
sadaukar da wannan aiki ga mahaifana, Malam Abubakar Wazirin Zabi da Malama
Hauwa’u Ahmad. Allah Ya ƙara
musu lafiya tare da imani, amin. Allah Ya saka musu da tarbiyar da suka yi
mana. Mun gode, Allah Ya biya.
GODIYA
Godiya mafificiya
ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki,
mamallakin sammai da ƙasai,
wanda Ya raya mu Ya kuma ba mu ikon kawowa wannan mataki. Tsira da amincin
Allah su ƙara
tabbata ga manzon tsira, Annabi Muhammadu (Sallahu Alaihi Wasalam).
Babu shakka, mutane da dama sun ba da gudummawa wajen ganin wannan aiki ya
kammala cikin nasara. Sai dai ambaton sunayensu duka ba zai yi wuya ba, ko da
kuma an ambata godiyar fatar baki ba za ta gamsar ba. Sai dai addu‘ar Allah Ya saka
wa dukkan wanɗanda suka taimaka da alheri.
Godiya ta musamman wadda ba za ta misaltu ba ga Malamina kuma jagoran duba
wannan aiki Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza, wanda duk da ayyuka masu dama da suke
gabansa, amma ya kula ya kuma yi ta taimakawa wajen duba aikin da kuma
gyare-gyare ga wannan bincike. Kazalika, ya yi ta ba da shawarwari masu dama tun
daga farkon aikin har zuwa ƙarshensa. Ina roƙon Allah Ya saka wa Malam da gidan Aljanna Fiddausi, amin.
Haka kuma, godiya marar misaltuwa ga Malamina kuma jagoran duba wannan aiki
na biyu wato Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi shi ma ya yi namijin ƙoƙari wajen ganin wannan aiki ya yi nasarar kammaluwa. Ba don haɗin kan da ya bayar ba, da wannan aiki bai tsayu da ƙafafunsa ba. Da fatar Allah Ya saka wa Malam da gidan Aljanna
fiddausi, amin.
Ina miƙa godiyata ta musamman ga malamina jagoran duba aikin na uku, Farfesa Y. Y
Ibrahim na Sashen Nazarin Addinin Musulunci (Islamic Studies Department), wanda
da taimakonsa aikin nan ya samu kai wannan mataki. Ina fatar Allah Ya saka wa Malam
da gidan Aljanna Fiddausi, amin.
Bayan haka, ina mai matuƙar bayyana jin daɗina da godiyata ga shugaban Sashen Nazarin Harsunan
Najeriya, Jami´ar Usmanu Ɗanfodiyo, Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa, ina yi wa Malam fatar Allah Ya saka
masa da alheri. Ina godiya ga dukannin Malamaina na Sashen Nazarin Harsunan
Najeriya na Jami`ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Waɗanda suka haɗa da: Farfesa Ibrahim Makoshy, da Farfesa Abdullahi
Bayero Yahya, da Farfesa Haruna Abdullahi Birniwa, da Farfesa Ahmad Halliru
Amfani, da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, da Farfesa Abdulhamid Ɗantumbishi, da Dr. Bello Bala Usman, da Dr. Ibrahim
Sarkin Sudan, da Dr. Yakubu Aliyu Gobir, da Dr. Abdulbasir Ahmad Atuwo, da Dr.Yahya
Idris, da Dr. Umar Aliyu Bunza, da Dr. Nasiru Aminu Kalgo, da Malam Naziru Ibrahim
Abbas da Malam Sama’ila Umar da Malam Dano Balarabe Bunza da Malam Mustafa Muhammad
da Malam Musa Shehu. Abokanin karatuna ma sun taimaka da shawarwari da addu’a
na gode Allah Ya biya. Waɗanda ta hanyar basira da ilmi da kyakkyawar fahimtarsu na
samu nasarar kammala wannan karatu.
Ba zan manta da Hakiman ƙasar Katagum ba, musamman Hakimin Itas da Hakimin Gamawa da Hakimin Sakuwa
da Hakimin Gaɗau da kuma Hakimin Azare, da iyayen ƙasa na masarautar Katagum da kuma, Majalisar Masarautar
Katagum wajen ba ni lokaci na musamman domin tattaunawa da su. Na gode Allah Ya
saka da alheri, Amin. Gadiya ta musamman ga Sarkin Garinmu Alhaji Muhammadu
Abdulkadir Madakin Zabi wanda ya taimaka wajen ba ni shawarwari da ƙarfafa mun guiwa wajen ganin kammaluwar wannan bincike,
shi ma Allah Ya saka masa da alheri. Ina miƙa godiya ga Ma`aikatar ilimin Firamare ta Giyaɗe, Jihar Bauchi da ta taimaka mun wajen ba ni damar tafiya wannan karatu.
Allah Ya saka da alheri.
Ba zan manta da abokaina ba, waɗanda suka ba ni shawarwari tare da taimako na ƙara ƙarfin guiwa kan wannan karatu. Musamman irin su Malam Abdullahi Zabi da
Muhammad Abubakar (Khalifa) da Umar Barde da Alhaji Muhmood Abba da Abduƙadir Namangi da Ibrahim Ɗanbaba da Ja’afar Bello da sauran Malaman da suke
Makarantar Firamare ta Baduware. Duk ina musu fatar Allah Ya saka da alheri.
Bayan haka, godiya ta musamman ga abokan karatuna na wannan jami`a ta
Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Irin su Ahmad Garba Aliyu da Jibrin Yusuf da Alhaji Musa
Abdulrahaman da Malam Imam Abdullahi da Hajiya Zara‘u da Shamsudeen Isma’il da ma
sauran waɗanda ban ambaci sunayensu ba. Duk ina musu fatar Allah Ya
sa mu haɗa wannan karatu lafiya, Ya sanya mana albarka a cikinsa.
Daga ƙarshe, ina miƙa godiyata ga mahaifana Malam Abubakar Wazirin Zabi da Hauwa’u Ahmad.
Sannan da matata Maijidda Bello da ‘Yayana Khadiji Muhammad Jaɓɓello. da Salmanu Muhammad Jaɓɓello da Al’amin Muhammad Jaɓɓello da Ibrahim Muhammad Jaɓɓello duk ina musu fatar Allah Ya saka musu da alheri
amin.
BABI
NA UKU
BAUTA
A ƘASAR HAUSA
3.1 Shimfiɗa
Wannan
babin za a kalli bauta a ƙasar
Hausa ta yadda za a duba muhimman abubuwa da dama. Masana da manazarta sun yi
ta faɗi tashi
wajen kawo mene ne ake nufi da bauta. Da kuma ra’ayoyinsu dangane da ma’anar bauta.
Maradun
(1992:52). Bauta wata hanya ce da
sarakunan ƙasar
Hausa suke kamo mutane daga makwabtansu domin su yi musu wata hidima ta daban.
Ita
kuma Waya, (2000:27). Cewa ta yi “kalmar
Bauta ta samo asali ne daga dalilin kai hari ko kuma ganimar yaƙi, wasusnsu kuma a
kan baiwa sarki gaisuwa”.
C.N.H.N
(2006:42). Bauta kamar yadda ƙamus na Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya ya kawo, yana nufin hidimar da Bawa ke yi wa ubangidansa.
Khalil
(2006:18). Bauta aba ce da Musulunci ya
zo ya tarar ana yi bai hana ba. To amma ya yi mata gyare- gyare ya kuma ƙara tsara ta domin ta dace da
rayuwar jama’a. Ko da yake sauran addinai su ma suna da bauta, to amma
Musulunci ya fayyace hanyar da za a samu bayi da yadda za a ‘yanta su da kuma
matsayinsu.
(
Http://wiktionary.org )
Kalmar Bauta, cewa mutum ne wanda wani yake mallake da shi yake gudanar masa da
hidimomin yau da kullum[1].
Wani
lokaci akan danganta bauta da rashin ci gaban ƙasa ko al’umma tare
da danne hakki. Kamar yadda Abubakar Ladan ya faɗa
a cikin waƙar
Afirikiya , ya nuna cewa saboda rashin ‘yanci shi ya hana Afirka bunƙasa, ga yadda ya
ce:
Niyyar ‘yanci ya ta koka
A kudanci nan na Afirka.
Mai barci yau ka farka
Don karɓan
‘yanci ba shakka
Komai ɗauri
komai duka
Afirka, Afirka, Afirkanmu
Da ƙasa
da ƙasa komai namu
Fetur
zinari darmammu
Ga gwal, ƙarfe
da kuzarmu
Da azurfa dudda tagullarmu
Muke iko da ma’adanmu
A
Dauloli kowa na murna
Kyakkyawa mulki ya zauna
Bisa
ga yadda masana da manazarta suka ce, za a iya cewa, bauta na nufin wata hanya
ce, da mai Sarauta, ko mai ƙarfi
a zamanin da, zai je wani gari ko cikin wata al’ummar da ba ta sa ba, ya ɗauko
wani, ya mayar da shi bawa. Ko ya mallaki mutum kacokan ta hanyar saye ko
kyauta ko yaƙi
ko hari domin ya dinga yi masa hidimar yau da kullum; shi kuma ya ɗauke
masa ɗawainiyarsa
ta duniya baki ɗaya.
3.2 Zuwan Musulunci Ƙasar Hausa
Zuwan
Musulunci ƙasar
Hausa wani dogon tarihi ne wanda ya samu kulawar masana da manazarta na ciki da
wajen ƙasar
Hausa. Kasacewar bautar gargajiya ta sami gindin zama a wasu sassan na ƙasar Hausa har zuwa
ƙarni
na 14, bai hana addinin Musulunci ya sami kutsa kansa a cikin wannan yanki tun
da jimawa ba. Tun daga kafuwar addinin Musulunci a ƙarni na bakwai, Musulunci
ya ci gaba da yaɗuwa
har lokacin da a wajejen ƙarshen
ƙarni
na sha ɗaya zuwa
farkon ƙarni
na sha biyu ya iso wasu daga cikin ƙasashen
Afirka ta Arewa irin su Algeria, da Tripoli da dai sauransu. ‘Yan kasuwa waɗanda
aka fi sani da Wangarawa ne suka shigo da Musulunci yammacin Afirka har zuwa
daular Saifawa a Borno lokacin sarki Mai Humai. Musulunci ya zauna a wannan
daula sama da shekara ɗari
kafin daga bisani a ƙarni
na sha uku da sha huɗu
ya kutsa ƙasar
Hausa a zamanin Sarkin Kano Yaji Ɗantsamiya
(1349-1385), sun iske akwai ɓirɓishin
addinin Musulunci a wannan nahiya. Yahaya, (1988:33)
Kafin
addinin Musulunci ya shigo ƙasar
Hausa sai da aka ƙaddamar
da shi a nahiyar Hijaz, sannan ya watsu zuwa sassa daban-daban na duniya, gami
da ƙasar
Hausa. Daga gabas ta tsakiya addinin Musulunci ya ratso zuwa nahiyar Afirka da
Turai, musamman sassan Magrib da Andalusiya. Addinin Musulunci ya barbazu a
ko’ina, inda sannu a hankali ya zama addinin duniya. Daga Afirka ta arewa ne,
Musulunci ya kutso kai zuwa yammacin Afirka ta amfani da aƙalla hanyoyin guda
biyu muhimmai. Waɗannan
hanyoyi sun amfanar ne ta hanyar hada-hadar ciniki da saye da sayarwa. A irin
waɗannan tafiye-
tafiyen ne Musulunci ya biyo ‘yan kasuwa zuwa wararen mazauna yammacin Afirka. Kuma
duk da cewa ba Musuluntar da jama’a aka zo yi kai tsaye ba, amma sai da Musulunci
ya sami wurin zama.
A
lokacin da dakarun Al’murabid suka fatattaki Daular Ghana a shekarar (1076) ya
jawo faɗuwar Daular
aka maye ta da daular Mali. A wani zangon na mulkin Daular Mali, a zamanin
hawan karagar Mansa Musa a (1240) ake jin cewa Musulunci ya bazu a kusan duk faɗin
yankin Afirka ta yamma, ciki har da yankin da ake kira Nijeriya a yau. Malumfashi
(2009:33)
Shigowar
Wangarawa daga Mali (Malle) a zamanin Sarkni Kano Yaji (1339-1385) kamar yadda
Malumfashi (2009) ya bayyana, cewa Musulunci ya ƙara samun gindin
zama a ƙasar
Hausa. Wangarawa sun sa hannu cikin harƙoƙin gudanar da mulki
ka’in da na’in da kuma inganta ayyukan Musulunci ta fuskar Limanci da Ladanci
da Alkalanci da rubuce-rubuce dangane da masallatai don bunƙasa Musulunci a
wannan yanki. Malumfashi (2009:33)
A
zamanin Sarkin Kano Yakubu (1452-1463) wasu gungun Fulani ɗauke
da littattafai suka shigo ƙasar
Hausa daga Mali (Malle). Shigowar waɗannan
Fulani ya ƙara
wa addinin Musulunci martaba da ɗaukaka
a idon jama’a. A wannan lokaci ne aka inganta zuwa aikin Hajji, kuma ƙasar Hausa ta sake
jaddada dangantakarta da sauran ƙasashen
Musulumi da ke a gabas ta tsakiya. Haka abin ya dinga gudana har zamanin zuwan
mashahuran Malamai masu wa’azi kamar al’Maghili.
Daga
wannan zamani ne Musulunci ya bar fada, ya warwatsu cikin garuruwa da ƙauyuka na ƙasar Hausa. Ta haka
ne ko da malamai irin su Al’maghili suka ziyarci garuruwan Katsina da Kano, sun
iske ilimin addinin Musulunci ya ginu. Abin da kawai suka yi shi ne, ƙara rubuta
littattafan addini, kamar waɗanda
suka danganci sha’anin shari’a. Sannu a hankali Musulunci ya zaunu sosai a ƙasar Hausa Malumfashi(2009:34)
3.3 Zuwan Turawa Ƙasar Hausa
Kasancewar
Turawa ba su shiga ƙasar
Hausa a jahilci ba, domin suna da wata masaniya a kan mutanen wurin da kuma
yanayin ƙasar.
Tun a ƙarni
na goma sha ɗaya ƙungiyoyi daga
jinsin Turawa, sun aiko da masana don su binciki yadda ƙasashen Afirka suke
da yadda al’adunsu ke gudana da yanayin harshensu da kuma addininsu. Sa’annan
kuma su binciko hanyoyin sadarwarsu ta ruwa da ƙasa da kuma matakan
da suke amfani da su ta fuskar ciniki da saye da sayarwa. Wannan ƙoƙarin sanin yanayi
da al’ummar nahiyar Afirka da Turawa suka yi, ya kawo kakkafa ƙungiyoyin Turawa
masu manufofi daban-daban. A Ingila an samar da ƙungiyar Afirka (Malumfashi
2009:36). Wannan ƙungiya
ita ta turo da Mungo Park da Clapperton da Barth da Denham da ‘Yanuwa nan guda
biyu, wato Landers Brothers, waɗanda
suka ziyarci yankunan ƙasar
Hausa.
Baya
ga waɗannan ƙungiyoyin na neman
sanin halayen da ƙasashen
Afirka suke ciki, akwai kuma ƙungiyoyin
Mishan da Turawa suka turo don bincike, musamman kan al’adu da harsuna da
addinan ƙasashen
Afirka a tsakanin ƙarni
na 18-19 Shahararru daga cikin waɗannan
‘yan Mishan su ne: G.P Bargery, da J.F Schon da C.H. Robinson da Han Vischer da
wasu da dama. Miller (1947:18-19). Ta fuskar ayyukan ‘yan leƙan asiri da Mishan
ne daga cikin Turawa, labaran ƙasar
Hausa da jama’arta suka isa Turai kai tsaye. Su kuwa ‘yan Mishan irin su
Robinson da Miller da Richardson da Ryder da Burgin, sun sami isowa ƙasar Hausa kai
tsaye bayan sun koyi harshen Hausa a Tripoli Miller (1947:17). Wasunsu sun
zauna a sassan ƙasar
na wani lokaci, daga baya suka koma gida suka bayyana abubuwa da suka gano,
wasu kuma sun ci gaba da rayuwa a ƙasar
suna ayyukan yaɗa
addini.
A
lokacin da Turawan Mulki suka zo ƙasar
nan, sun karɓi mulki a
tsakanin (1900-03). Turawa sun kafa mulkinsu, amma ba su kashe tsarin Sarauta
da suka tarar ana gudunarwa ba. Ko da yake sun ɗan
yi waɗansu sauye-
sauye. Domin kasancewarsu ba ‘yan ƙasa
ba; kuma mutane masu dabara don jin daɗin
tafiyar da mulkinsu sai suka dinga gudanar da mulkin mutane ta amfani da
sarakunansu, domin gudun tawaye da ƙoƙarin tafiyar da
manufofinsu a cikin lumana.
A
tsarin mulkin Turawa, bayan daular Usmaniyya an karkasa wannan ƙasa zuwa mulkin ɓangare-
ɓangare da lardi-
lardi wanda yake a ƙarƙashin gwamna Lord
Lugard ne yake shugabancin gwamnonin ɓangare.
Shi ne babban wakilin Ingila wanda yake sanar da Ingila yadda al’amurran mulki
ke wakana a wannan ƙasar.
Gwamnan ɓangare shi
yake da alhakin tsara kasafin kuɗin
shekara-shekara. A cikin kowane ɓangare
a kan sami larduna da yawa. Bayan gwamnan ɓangare
ya tsara kasafin kuɗin
shekara-shekara yakan kai wa gwamna tarayya domin neman amincewarsa.
Zuwan
Turawa ƙasar
Hausa ya hana sarakuna gudanar da wasu hukunce- hukunce, misali kamar hukuncin
kisa ko yanke hannu, amma bai hana su gudanar da wasu ba, kamar jangali da karɓar
haraji da daidaita tsakanin mutane ko al’umma baki ɗaya.
Zuwan Turawa mulki ya kawo wa sarakunan ƙasar Hausa wani
sabon tsarin mulki. Koma bayan na da da ake amfani da hukuncin Allah da Manzo
sallahu alaihi wasalam (Wato Shari’ar Musulunci). A lokacin kuma Turawa suka
fara hana yin cinikin bayi da kuma bautar da mutane.
3.4 Asalin Bauta A Ƙasar Hausa
Bauta
a ƙasar
Hausa ta samo asali ne tun lokacin da ake yaƙe-yaƙe, tare da kai hari
daga wannan gari zuwa wancan. Idan wannan gari ya samu galaba a kan wani sai a
kama mutanen garin domin a mayar da su bayi. Sannan a kwashe dukiyarsu domin a
kai wa sarkin gari.
Sarakunan
ƙasar
Hausa kan yi amfani da bayi maza da aka kamo musu a matsayin bayin gidan
sarauta da kan yi aikace-aikace da dama a gidan sarki da fada. A wasu lokutan
kuwa, sukan yi amfani da musamman bayi maza wajen musaya a lokacin da suke buƙatar sayen waɗansu
abubuwa. Misali an yi wani lokaci da sarkin Kano ya taɓa
aikawa da bayi Bida domin a kawo masa kayan doki. (Maradun 1992)
A
wasu masarautun ƙasar
Hausa, bayi na da matsayi na musamman wanda kowa yake da irin aikin da yake
gudanarwa a fada ko gidan sarki. Wani lokacin ma a kan ba su muƙamai a mafi yawan
masarautun ƙasar
Hausa, domin amincewa da su da irin ƙoƙari da suke nuna wa
idan an saka su wani aikin. Mafi yawan muƙamin da ake ba wa
bayi za ka tarar wanda ya shafi tsaron ƙasa ne ko kuma kula
da lafiyar sarki ko kuma iyalansa.
Akasarin
bayi mata kuma a kan kai su ga sarakuna a wancan lokaci, wasu su aura; wasu
kuma a tura su gidan ‘ya’yansa mata domin su dinga yi musu hidima, ko cikin
gidan sarki domin yi wa iyalan sarki hidima ta yau da kullum.
3.5 Hanyoyin Mallakar Bawa
Hanyoyin
mallakar bayi suna da yawa. Akwai waɗansu
Shari’a ta amince da su. da kuma waɗanda
gargajiyar Bahaushe ta amince da su. Waɗanda
gargajiyar Bahaushe ta amince da su, ga su kamar haka:
1
Yaƙi-
Ana iya mallakar bawa ta hanyar yin yaƙi.
Duk wanda ya ci galabar ɗan
uwansa, yakan kama duk mutanen garin dukkansu ya mayar da su bayinsa.
2
Kyauta- Wannan
ita ma hanya ce da za a iya mallakar bayi da ita, wanda wani sarki na iya aika
wa ɗan uwansa sarki
kyautar bawa ko bayi, ko wani mai hannu da shuni ya kai gaisuwa ga sarki don
girmamawa. Misali yadda Gwaggo uwar gida ta bayar da Gurzula kyauta a lokacin
auren Marafa Ɗan
Baba, domin aikace-aikacen yau da kullum.
3
Cira-
Wannan hanya ce da ake iya samun bawa, ta yadda za a samu wani tsakar rana ya
je wani gari ya ɗauko
wani a kan doki da ƙarfi,
ana bugansa har ya kai labari da haka.
4
Hari-
Wannnan ma hanya ce ta mallakar bawa yadda idan wani gari sun kai hari a wani
gari, suka kori mutunen garin duk wanda ya saura sai su ɗauki
shi a matsayin bawa.
5
Saya- Wannan
hanya ce da ake iya mallakar bawa ta hanyar saya. Idan mutum yana da kuɗi
zai iya zuwa kasuwa da kuɗinsa
ya saya, to in ya samu, to ya zama mallakarsa har abada. Misali a garin
Sakkwato yadda Gwaggo Uwar gida ta sayo Gurzula Silai biyu a tsohowar kasuwan
Sakkwato.
6
Biyan
Bashi-
Biyan bashi shi ma wata hanya ce ta mallakar bawa, wanda ake biyan bashi in ba
shi da abin da zai biya ko ya biya da bawa ko shi kansa ya zama bawan.
7
Gado- Gado hanya
ce ta mallakar bawa, wacce mahaifi ke mutuwa ya bar wa iyalansa. Wannan ma
kamar yadda iyalai za su iya mallakar dukiyarsa haka suke iya mallakar duk
bayin da yake da su.
Waɗanda
Shari’a ta amince da su kuma ga bayanin kamar haka: A zamanin Annabawa da suka
gabata an samu wasu ƙabilu
sukan bautar da mutanensu, a matsayin horo na laifi da girmansa ya kai miƙati; kamar sata da
sauran ire-iren su. Misali irin wannan, kamar yadda ya zo a cikin suratul
Yusufa. An bayyana cewa a lokacin da Annabi Yusufa yake ƙoƙarin riƙe ɗanuwansa.
Sai ya sa aka saka zobensa a cikin awonsa. Bayan tafiyarsu aka kira su aka
tuhume su, suka ce, su ba ɓarayi
ba ne. Sai Annabi Yusufa ya yi musu tambayar cewa wanda duk aka sami zoben a
cikin kayansa mene ne hukuncinsa? Suka ce shi ne hukuncinsa a bautar da shi. Ga
ayar nan kamar yadda ta zo a cikin Alkur’ani mai girma:
Sai suka ce “Sakamakon wanda aka
samu a kayansa shi ne sakamakon, kamar haka muke saka wa azzalumai” (Suratul
Yusufa 75)
A zamanin Jahiliyya kuwa a kan yaƙi mutane a bautar
da su don fin ƙarfi,
ko kuma wanda bashi ya yi masa yawa a kansa, ba zai iya biya ba; shi sai a
bautar da shi. To, amma da Musulunci ya zo sai duk ya hana wannan ya kuma
takaita hanyoyin mallakar bawa kamar haka:
1-
Yaƙi
Yaƙi don ɗaukaka
kalmar Allah Maɗaukaki
yana ɗaya daga
cikin hanyoyin mallakar bawa a Musulunci, kamar yadda ya zo a suratul Nisa’i:
Ubangiji
ya haramta muku katangaggun (wato masu mazaje,) sai abin da hannunku ya mallaka
(na kuyangi, waɗanda aka ribato su
a yaƙi).
suratul nisa’i 24)
Yaƙi na ƙwatar kai, shi ma
ana samun bawa ta sanadinsa. Misali a ce kafirai su auka wa musulmi, to ko don ƙwatar kansu da
rayukansu dole ne su ma su yaƙe
su kamar yadda Allah, maɗaukakin
yake cewa:
“Idan
suka yaƙe
ku, ku yaƙe
su. Wannan shi ne sakamakon kafirai” (Surah 2:191).
2-
Sayayya ko Biyan Bashi
Sayen
bawa ita ma wata hanya ce ta mallakar bawa da Shari’a ta amince da ita. Haka ma
za a iya mallakar bawa ta hanyar biyan bashi. Domin haka, za a iya ƙiyasi na kuɗi
a kan bawa, kuma bawa zai iya zama a matsayin kuɗi.
Shi ya sa za a iya biyan bashi da shi. Ashe ke nan wanda ya yarda aka biya shi
bashi da bawa, wannan biyan bashin ya zame masa sanadiyar mallakar wannan bawa.
3-
Kyauta
Kyauta
ita ma hanya ce ta mallakar bawa ko da kuwa shi mai ba da kyautar ba Musulmi ba
ne. Misali Sarkin Masar Muƙauƙisu ya yi wa Manzon
Allah Sallahu alaihi wa sallam kyautar Mariyatul Kifɗiyya
4-
Gado
A
cikin hanyoyin mallakar bawa akwai gado. Idan mutum ya mutu ya bar bayi, to
yadda za a raba dukiyarsa, haka za a raba bayinsa. (Amma ban da bayin waɗanda
Ubangijinsu ya kulle (saɗaka)
har sun haifu da shi). Shi ma bawa a matsayin dukiya yake, kuma a iya gadonsa
shi da abin da ya mallaka.
5-
Haihuwa
Idan
mutum yana da baiwa, to duk abin da ta Haifa na Ubangijinta ne, ko da kuwa aure
ta yi da wanda yake ba bawa ba, kuma suka haifu. Wannan abin da suka Haifa bawa
ne, domin ita bauta uwa take bi.
3.6 Hanyoyin Da Ake ‘Yan ta Bawa
Hanyoyin
da ake ‘yan ta Bayi a ƙasar
Hausa. Akwai hanyoyi da dama da Hausawa ke bi domin ‘yan ta Bawa. Ga hanyoyin
Kamar haka:
1-
Fansa
Fansa
na nufin ubangidan Bawa ya ɗora
masa wani sharaɗi
ya ce idan ka yi ka za ka fanshi kanka. Ya danganta da irin yarjejeniyar da
suka yi. Matuƙar
Bawan ya cika waɗannan
sharuɗa na
yarjejeniya to ya ‘yantu.
2-
Bawa ‘yantacce
Wannan
kuma, ubangidan da kansa ya ga dama ya ce na ‘yanta ka, to wannan Bawa ya ‘yantu
har tsawon rayuwarsa.
3-
Baiwa uwar ‘ya ‘ya
Uwar
‘ya’ya, wato idan ubangidanta ya haihu da ita, kuma Allah ya ɗauki
ransa. Wannan Baiwa ta ‘yantu. Wato ta zama mai ‘yanci
4-
Bakance
Bakance shi ne ubangidan Bawa ya yi bakance da
Bawa ya ce, idan ka za ya kasance zan ‘yanta ka. To! Wannan abin yana kasance wa
Bawan ya ‘yantu.
Haka
kuma, akwai hanyar da Musulunci ya sake kawo na ‘yanta da Bawa, waɗanda
suka haɗa da:
i-
kaffarar
kisa
ii-
Kaffarar
rantsuwa
iii-
Kaffarar
Zihari
iv-
Kaffarar
Karya Azumi
Duk
waɗannan hanyoyi
Musulunci ya kawo su domin Bawa ya samu yanci. Shi Musulunci yana ƙara ƙarfafawa da a
‘yanta Bawa.
3.7 Cinikin Bayi A Ƙasar Hausa
Ƙasar
Hausa da ma Nijeriya baki ɗaya,
da wasu ƙasashen
Afirka ta yamma sun zamanto a cikin wani yanayi na wannan ya kai wa wannan
hari, wancan ya kai wa wancan hari. Har idan ɗaya
ya sami galaba a kan ɗan
uwansa ya kama mutanen garin tare da kwashe musu dukiya baki ɗaya.
Mutanen idan Turawa daga Amirika da West Indian da Ingila suka zo, sai su dinga
sayan bayin, amma cinikin ya kasace na musaya ne. Ba kuɗi
za a bayar ba, Turawan kan zo wa da Sarakuna da Madubi ko Bindiga ko wasu
makamai ko wani abu makamancin wannan. Su kuma su bayar da bayin kwatankwacin
darajar abin da Turawan suka kawo musu.
Su kuma bayin da Turawan suka
saya za a kai su Legas a tara su a Barakon (wato wani abu mai kama da
kwantina), a jera su a layi; a sa musu turu a wuya wanda a cikin wannan
kwantina nan za a ajiye su. Tsabar wahala nan wasunsu za su mutu, wasu kuma su
kamu da cuttuka. Daga nan Legas za a ɗebe
su sai ƙasar
Turai. Idan an kai su can, za a kai su gonakai su dinga noman rake da abubuwan
da ba sa nuna da wuri, kamar Mangoro da Kwakwa da sauransu. Bayan aikin gona
kuma a kan kai su gidaje domin yin wasu aikace-aikace na cikin gida.
3.8 Gurbin Bayi a Masarautun Ƙasar Hausa
Sarauta
a ƙasar
Hausa tsohon al’amari ne wanda ya ɗauki
shekaru da yawa ana aiwatar da shi a yankin, wanda sha’anin sarauta baya gudana
yadda ya kamata har sai an yi maganar bayi a kai. Domin bayi suna taka
muhimmiyar rawa wajen gudanar da harƙoƙin mulkin a
masarautun ƙasar
Hausa.
Bayi
a ƙasar
Hausa suna da na su rawar da suke takawa a masarautun ƙasar baki ɗaya.
Kamar yadda Maradun (1992:52). Ya ce “An so ma samun sarautun bayi a masarautun
ƙasar
Hausa tun a kusan ƙarshen
ƙarni
na goma sha takwas”. A lokacin ne aka fara naɗa
bayin gidan sarki da kuma fadawa. Don haka, wannan aikin zai duba wasu
masarutun da suke ƙasar
Hausa kamar haka: Gobir da Katsina da kuma Kano, domin mu ga irin rawar da
sarautun bayi ke takawa a masarautun ƙasar
Hausa.
3.8.1 Gurbin Bayi Masarutar Gobir:
A
masarautar Gobir, bayi na da gurbi na musamman ta yadda kowa yana da aikin da
yake gudanarwa a fadar sarki. Wannan Sarauta ce da aka so ma ta tun lokacin da
ake yaƙe-
yaƙe
da kai hare-hare a tsakanin wannan gari da wancan.
An kuma samu ci gaba da samun sarautun bayi a ƙasar Hausa har
zuwan lokacin da aka samu canje-canjen zamani. Maradun (1992:52)
A masarautar Gobir akwai bayin gidan
Sarki da na fada da suka haɗa
da, kamar yadda Bangon Gobir ya tabbatar:[2]
i-
Sarautar
Galadiman gari
Galadiman
gari shi ne uban gijiya (Bayi) wato shi ne shugaban bayi duk wani abu da za a
yi a fada sai an sanar da shi. Kuma shi ne, wakilin bayi a fada. Ita wannan
sarautar har yanzu aikinta yana nan, duk da sauye- sauyen zamani da aka samu.
ii-
Sarautar
Baraya
Baraya
shi ne mai kula da dukkan lamuran da suka shafi abin da yake tsakanin mutanen
gari da sarki. Shi yake shige da fice tsakani. Ita ma wannan sarautar har yanzu
aikinta yana nan, duk da sauye- sauyen zamani da aka samu ba ta canja ba.
iii- Sarautar Bango
Bango
shi ne mai kula da duk matsalolin da suka shafi cikin gidan sarki da bargar
dawakin sarki. Ita wannan sarautar ta Bango har yanzu aikinta yana nan, duk da
sauye- sauyen zamani da aka samu.
iv- Sarautar Ajiya
Ajiya
aikinsa ɗaya da
Baraya akwai abubuwan da ake ba shi da ya yake kulawa da su, kamar ranar Sallah
ko yaƙi
ya kan ɗauko tambura
ya miƙa
wa sarki da hannunsa. Ita wannan sarautar Ajiya har yanzu aikinta yana nan, duk
da sauyin zamani da aka samu.
v-
Sarautar
Garkuwa
Garkuwa
aikinsa a masarautar Gobir shi ne mai kula da dukkan garkuwar da take fada,
kuma ko da yaƙi
za a fita shi yake raba wa mutane garkuwa ya kan ce, idan an dawo ka kawo mun,
in ka mutu magajinka ya dawo mun da ita. Wannan sarauta ta garkuwa aikinta ya
ragu saboda yanzu ba a yaƙi,
amma har yanzu yana da aikin da yake yi a fada. Duk da yake yanzu aikin da
garkuwa yake yi mafi yawanci ya koma wajen Bango.
vi-
Sarautar
Ma-ja- Sirdi
Kula
da sirdin da sarki yake hawa shi ne babban aikin maja sirdi. Wanda idan an ɗaura
sirdin ya kan zo ya saka hannu ya jijjiga ya ji ya ɗauru
ko bai ɗauru ba.
Idan ya ɗauru shi ke
nan, in bai ɗauru ba ya
kan ce a sake ɗaure shi.
Sirdi kuwa ko da yaƙi
za a je ko hawan Sallah dole ne maja- sirdi sai ya duba sirdin kafin hawan
sarki. Shi ma a halin yanzu aikin ya koma wajen Bango, shi yake yin aikin da
maja- sirdi yake yi yanzu. Amma in an zo hawan Sallah ya kan yi hawa shi asali
wanda aka bawa sarautar maja-sirdi.
vii- Sarautar Barga
Barga
aikinsa a fadar sarkin Gobir shi ne, bargar dawakin sarki shi yake kula da ita
da ɗaukar ɗawaniyarta
na kowane irin aikin ne. ita ma wannan sarauta akwai ta amma babu aikin.
viii-
Sarautar
Shamaki
Shamaki
shi jakada ne tsakani Barga da Sarkin Dawaki da magajin gida da sarkin zagi da uban turke shi yake kai kawo
tsakani.
ix- Sarautar Shantali
Lokacin
da sarki zai fita wajen yaƙi
ko wata lalura Shantali ne zai riƙe shantulan Sarki da
sarki yana son ɗahara
ko a wajen yaƙi
idan shantali sai ya bawa sarki. A da a Gobir guda sha biyu suke da shi, amma
yanzu bai wuce guda uku ba suka saura ba.
x-
Sarautar
Shimfiɗa
Shimfiɗa
shi mai kula da shimfiɗar
sarki duk inda sarki ya je in zai zauna shimfiɗa
ne yake yi masa shimfiɗa,
amma yanzu saboda sauye- sauyen zamani yanzu aikin shimfiɗa
ya kau saboda yanzu kujera ake sakawa.
xi-
Sarautar
Majidaɗi
Majidaɗi
ɗan mowa ne, wanda
ke jin daɗi sarki
wanda duk abin da ya nema gun sarki zai yi masa. Wanda haka ya sa duk wani abu
in ana buƙata
a gun sarki majidaɗi
ake samu. Shi kuma ya kai buƙatar
ga sarki.
xii-
Sarautar
Magajin Madawa
Magajin
Madawa yana cikin zarumai. Aikinsa a masarautar Gobir shi ne, idan sarkin bai
samu damar zuwa wajen yaƙi
ba sai ya wakilta shi, ya zama jagoran yaƙi, kuma ana
tsammata masa nasara.
xiii- Sarautar Ƙuwaru
Sarkin
kuwaru aikinsa shi ne, kula wa da kuwarun sarki duk lokacin da sarki zai yi
amfani da su ya kan ɗauko
ya ba shi su. Kuma shi ne yake yi wa sarki washi. Wato, kirari abin da ake nufi
da Kuwaru shi ne, wasu takalma ne da ake sawa wanda suke zuwa har guiwa. Wanda
ko harbi aka yi baya huda su.
xiv- Sarautar Cina Barka
Cina
barka yana tare da zarumai amma aikinsa shi ne yake ɗaukar
sarki ya ɗora bisa
doki.
xv-
Sarautar Sarkin Kanwa
Sarkin
kanwa karkara gare shi, idan wani yana buƙatar gona wajen sa
zai je ya ba shi, duka gonakai da dazuzzuka suna hannunsa ne. Duk wanda yake buƙata sai da izini
sarkin kanwa, haka kuwa ko da sarki ne zai bayar da gona sai ya haɗa
mutum da sarkin kanwa ya ba shi.
xvi- Sarautar Sarkin
Bazai
Sarkin
Bazai aikinsa a fadar Gobir shi ne, yana cikin manyan dakarun yaƙi.
xvii-
Sarautar
Sarkin Ƙofa
Sarki kofa ƙarƙashin sarkin bazai
yake, amma babban aikinsa shi ne kula da ƙofofin gari, wajen
buɗewa da rufewa. Kuma
shi yake raba mutane masu kula da ƙofofin
kullum.
xviii-
Sarakunan
Zarumai
a)
-
Sarautar Ƙyaure
Kyaure
shi ma yana cikin dakarun sarki. Kuma duk kyauren da aka yi su, shi zai sa a
kawo su.
b)
Sarautar
Baran Makka
Shi
ma Baran makka shi ne shugaban dakurun sarki wanda in ka ga an taɓa
sarki sai dai bayan ransu.
c)
Sarautar
Ara
Ara
shi ma yana cikin dakarun sarki.
d)
Sarautar
Tarno
Sarkin
tarno aikinsa a fada shi ne mai kula da masaƙa da masaƙu da suke ƙasar, wanda idan
sun saƙa
idan sarki yana buƙata
sai a kai masa. Yanzu wannan sarauta aikinta babu domin yanzu babu masaƙa.
e)
Sarautar
Makoda
Shi
kuma wannan babban aikinsa shi ne mai kula da masu sussuka da masissiku zai
dinga za ga wa suna biyan kuɗi
a matsayin haraji, har yanzu wannan sarauta ana amfani da ita.
f)
Sarautar
Makama
Duk
da yake wannan sarauta babu ita a ƙasar
Gobir aronta a ka yi, amma tana cikin sarautun bayi. Babban aikin mai riƙe da wannan sarauta
shi ne duk wanda ya yi laifi shi ake turawa domin kamo mai laifin.
g)
Sarautar
Kibiya
Babban aikinsa shi ne a lokacin
yaƙi
yana gaban sarki, kuma kwarensa akwai a ƙalla kibiya ɗari,
kafin a kai ga sarki sai dai ba shi da rai. Haka kuma bayan an dawo zai zo ya
tare ƙofar
gidan ya hana sarki shiga har sai an zo an ce masa ya ara wa sarki gidan saboda
shi yake gadin gidan. Nan za a ce za a sallame ka, shi kuma nan za a bashi
kyautar arƙila
ko kundumi wato zani ne irin na matan sarki.
h)
Sarautar
Tsara
Tsara
da kibiya aikinsu guda ne.
xix- Sarautar Garangamau
Shi ma yana cikin zarumai masu
tsayawa gaban sarki, haka kuma shi ne mai bai wa sarki nishaɗi.
Yana kuma faɗar gamtsi a
gaban sarki kowanne iri ne.
xx-
Sarautar
Masu
Shi ne mai kula da masu, haka
kuma shi ne yake sa ake ƙira
su. Wanda idan za a je wajen yaƙi
ko wani hawa shi yake raba wa mutane masu, amma in an dawo kowa zai dawo da su.
xxi- Sarautar Lifida
Shi ne shugaban masu lifida, wasu
abubuwa ne kamar garkuwa wanda in za a fita yaƙi mayaƙa kan saka su a
jiki, wanda duk harbin da aka yi bai samunsu.
xxii-
Sarautar
Tamindau
Babban aikinsa shi ne ba wa sarki
magani na kafin jiki da sauran asirai na kariya.
xxiii-
Sarautar
Uban Turke
Uban Turki aikinsa shi ne, duk
wani turke da yake nan shi yake da hakkin kula wa da shi, ko da kuwa a wajen yaƙi ne ko wata hidima
ta dabam. Sayensa da kafa shi. Haka kuma shi yake da hakkin kula da ƙasar da ake saka wa
dawaki ya tabbatar an zuba ta.
xxiv-
Sarautar
Sarkin Zagi
Sarkin zagi shi ne gaba ga sarki
a kowane lokaci, haka kuma lokacin da sarki ya saka kafarsa ɗaya
kan fangami shi ke tallafa masa ya ɗora
shi kan doki. Haka kuma in dare ya yi sarkin zagi ke zuwa ya yi masa matsa. A ƙarƙashinsa akwai:
a)
Sarautar
Sarkin Karma
Sarkin karma shi ke kula da duka
‘yan tauri da ke ƙasar
Gobir kuma yana ƙarƙashin sarkin zagi
ne.
b)
Sarautar
Sarkin Daji
Sarkin Daji aikinsa shi ne, duk
wani wanda yake harbin bindiga shi ne shugabansa. Shi ma yana ƙarƙashin sarkin zagi
xxv-Sarautar Tazal
Babban aikin mai riƙe da wannan sarauta
shi ne, dafa wa sarki magani da aka kawo ma sa.
xxvi-
Sarautar
Sarkin Arna
Aikinsu guda da Tamindau.
xxvii-
Sarautar
Inna
Shi ma aikinsu guda da tamindau
da sarkin arna
xxviii-
Sarautar
Saye
Shi ma babban aikinsa shi ma kawo
wa sarki magani buwaya da sauransu, amma aikinsu ɗaya
da sarkin arna da tamindau da Inna.
3.8.2 Gurbin Bayi a Masarutar Katsina:
A
ƙasar
Katsina ma tamkar sauran masarautun ƙasar
Hausa ne, wato akwai gurbin bayi a masarautar. Ana tunanin tun zamanin Sarki
korau a 1445- 95. Aka fara naɗa
masu riƙe
da muƙaman
bayi. Ga kaɗan daga
cikin muƙaman
bayi da suke Masarautar Katsina: Maradum (1992:25-27)
i-
Magayaƙi
Yana
daga cikin manyan bayin sarki da ke kula da al’amurran da suke da dangataka da
yaƙi.
ii-
Sarkin
Bai
Shi
yake taimaka wa magayaƙi.
iii-
Sarkin
Yara
Yana
ɗaya daga cikin
mataimakan magayaƙi.
iv-
Ajiya
Ajiya
wannan shi yake ajiye kayayyaki tare da kuɗi.
v-
Baraya
Shi yake kula da wajen kwanciyar Sarki (Baraya).
Aikinsa ne ya tabbatar da harabar baraya tana tsabtace a kowane lokaci. Haka
kuma shi yake kula da kayan da suke cikin baraya tare da dabbobi.
vi-
Sintali
Wanda ke riƙe
da wannan muƙamin
ana masa kirari da “Shantali na Bayin sarki”. Babu lokacin da za a ga sarki ba
a ga Shantali ba. Abin da kawai yake raba Shantali da Sarki shi ne bacci. Haka
kuma Shantali shi yake da alhakin ajiye butar sarki.
vii-
Turaki
Yana ɗaya
daga cikin fadawan sarki da a kan sa su ayyuka na musamman.
viii-
Kashaka
Yana daga cikin yaran sarki da
yakan sanya su ayyuka a lokacin da yake buƙata.
ix-
Ɗankafi
Aikinsa kula da wajen bizne mutane.
x-
Ubandawaki
Shi yake kula da dawaki.
xi-Sarkin Karma
Shi ne shugaban ‘yan tauri
xii-
Sarkin
Baka
Yana kula da masu harbin baka.
xiii-
Sarkin
Bindiga
Yana kula da maharba Bindiga.
xiv-
Sarkin
Zagi
Shi ne shugaban Dogarai
xv-
Ganuwa
Shi yake kula da ƙofofin Shiga birni,
tare da tabbatar da tsaro.
Wannan shi ya tabbatar mana da
cewa a masarautar Katsina matuƙar
aka fitar da bayi a sha’anin mulki lallai, babu wani abun da ya saura na daga
mulkin. muƙaman
bayi suna taka muhmiyyar rawa wajen bunƙasa da kyautatuwar
mulki da tsaro a duk masarautun da suke ƙasar Hausa.
3.8.3 Gurbin Bayi a Masarautar Kano:
A
ci gaba da bayanin yadda gurbin bayi suke a masarautun ƙasar Hausa, da
yadda suke gudana a sassa daban-daban na ƙasar, kamar yadda
wata Malama Zara’u Ibrahim Waya (2000) masaniyar tarihi da al’adun masarautun
Kano ta yi bayanin Muƙaman
sarautun bayi kan taimakawa sarkin Kano wajen al’amurran mulki. Malamar ta yi
bayani game da yadda tsarin sarautun bayin suke a shekarun baya da kuma yanzu. Sarautun
bayin Sarkin ma hawa-hawa ne. galibi an fi ba manya daga cikinsu sarautu na
musamman wanda yake kuma mataimaka za su riƙa taimaka masa
wajen gudanar da ayyukansa. Manya bayi sarkin Kano su ne:
1-
Shamaki
2-
Ɗanrimi
3-
Sallama
Waɗannan
bayi su ne manyan bayin sarki kuma kowanne daga cikin su yana da hakimansa a ƙarƙashinsa. Khalil
(2006:32)
1- Shamaki
ne babba a cikin bayin Sarki, wanda saboda haka ne ake masa kirari da “Shamaki Korau
kan bayi”. Babban aikinsa shi ne kula da tsakanin hakimai da Sarki. Shi ake
fara gani kafin sarki ya fito daga cikin gida, kuma shi ke yi wa mutane iso ga
sarki. Kowanne hakimi in zai gaida sarki sai da saninsa. Haka kuma da Shamaki
ake kama kafa idan ana neman wata sarauta a gun sarki. Haka kuma duk wata
Magana da ta shafi hakiman ƙauyuka
to Shamaki ne ki shigar da maganar gun sarki.
Idan
sarki ya zauna a fada, Shamaki ne yake fara yin gaisuwa, sannan sauran jama’a
su yi. In za a tsawatarwa mutum a fada shi ke yi. Kuma shi ke zama gaban motar
sarki yana riƙe
da sandar sarki, in kuma a kan doki sarki yake, shamaki yana dab da shi.
Akwai
wasu ayyuka da dama waɗanda
suke a ƙarƙashin mulkin
Shamaki, amma ba shi ne yake aikata su ba, kamar aikin da ya shafi gini da ƙira da dukanci da
sauransu, hakiman da suke ƙarƙashinsa ne ke yi.
Hakiman kuwa sun haɗa
da:
1-
Ciroman Shamaki
2-
Sarkin Lifida
3-
Madakin Shamaki
4-
Maƙaman Shamaki
5-
Sarkin Malafa
6-
Turakin Shamaki
7-
Sarkin Hawa
8-
Sarkin Dukawa
9-
Sarkin Maƙera Farfaru da
babbaƙu
10- Uban
Dawaki
11- Sarkin
Ruwa
12- Maja
Sirdi
13- Sarkin
ƙofa
14- Sarkin
Busa.
Waɗannan
hakimai da aka zayyana su a sama ƙananan
hakiman Shamaki ne, kuma duk gidansa suke zaune. Shi ne mai kula da su, ya kuma
ba su umarnin gudanar da duk wani aiki da ya ta so. Haka kuma akwai manyan
hakimansa waɗanda suma
suna da mataimaka a ƙarƙashinsu, kamar
haka:
Magajin Aska
Magajin
aska muƙami
ne da yake a masarautar Kano, wanda aikinsa shi ne, yi wa sarki aski da yi masa
ƙaho
idan buƙatar
haka ta ta so, da yi wa ‘ya ‘yan sarki kaciya da yi musu ɓalli-ɓali.
Duk waɗannan
Magajin aska ne kawai ke yin su.
A
ƙarƙashin Magajin aska
yana da mataimaka don aikinsu shi ne, su tabbatar sun biya buƙatar duk wani
bafade da yake cikin fadar, amma wanda ya shafi sana’arsu. A cikinsu akwai:
1-
Galadiman Aska
2-
Madakin Aska
3-
Ciroman Aska
4-
Makaman Aska
5-
Turakin Aska
Babban Zagi
Babban
zagi shi ma yana ƙarƙshin Shamaki ne,
kuma shi ne shugaban zagagen sarki. Babban aikinsa shi ne idan za a yi hawa ya
jera zagagen nan goma sha biyu a gaban sarki. Shida daga gefen Shamaki, biyar a
hannun Ɗanrimi,
guda gefen sallama. Haka kuma idan sarki zai hau ko sauƙa daga kan doki
babban zagi shi ne zai dafa masa.
Babban
zagi shi ma yana da muƙarrabai
a ƙarƙashinsa, kamar
haka:
1-
Galadiman zagi-
yakan rataya koriyar alkyabba kuma ya riƙe wuƙa da taƙobi. In sarki ya buƙaci amfani da su,
Galadima ya kawo.
2-
Makaman Zagi- Makaman
Zagi shi ne na uku a gaban sarki, shi yake riƙe da sandar girma.
3-
Turakin Zagi-
Turakin Zagi shi ne ya ke riƙewa
makaman zagi aikinsa idan wata lalura ta faru.
4-
Wazirin Zagi.- Yana
rataya bargo, sannan ya riƙe
buta a hannunsa. Kuma haƙƙinsa
ne kula da yadda aka gyara doki da sarki zai hau. Kuma idan sarki ya sauƙa shi zai je ya ɗaure
dokin.
Masu
Masu,
shi ne ƙarshen
zagagen da ke gaban sarki, shi ne yake riƙe da tagwayen masu
a hannunsa, yakan rataya bargo ya riƙe
takalman sarki waɗanda
idan ya sauƙa
daga kan doki zai sanya.
Madakin Zagi
Madakin
zagi kan rataya bargo ya riƙe
buta a cike da ruwa a ciki, hikimar yin haka shi ne, idan sarki ya nemi biyan
buƙata
cikin halin tafiya ba sai an nemo ba.
Sarkin Gini
Yana
cikin manyan hakiman Shamaki, babban aikinsa shi ne kula da gine-gine da suke a
gidan sarki. Yana da muƙarrabai
kamar haka:
1-
Madakin gini
2-
Makaman gini
3-
Galadiman gini
4-
Ciroman gini
5-
Turakin gini
Sarkin Kyankandi
Sarkin
Kyankyandi shi ma yana ƙarƙashin Shamaki ne, babban
aikinsa shi ne ɗaukar
kyankyandin kaya idan sarki zai yi hawa ko tafiya a kan ko da sarki zai buƙata ko ya yi kyauta
da su. Shi ma yana da muƙarrabai
a ƙarƙashinsa, kamar
haka:
1-
Galadiman
Kyankyandi
2-
Turakin kyankyandi
3-
Ciroman kyankyandi
4-
Madakin kyankyandi.
Sarkin Tamburra
Sarkin
tambura, shi ma yana ƙarƙashin Shamaki;
babban aikinsa shi ne kaɗa
tambura idan an naɗa
Sarki ko ana hawan Sallah. Ga muƙarrabansa
kamar haka:
1-
Makaman tambura
2-
Ciroman tambura
3-
Turakin tambura
4-
Galadiman tambura
2-
Sarautar
Ɗanrimi
Sarautar
Ɗanrimi,
sarauta ce daga cikin sarautun bayin sarki. Daga Shamaki sai Ɗanrimi a kan
darajar muƙami.
Aikin Ɗanrimi
ya fi yawa a fada, bayan haka kuma shi ne yake kula da gidajen sarki da suke
waje, kamar gidan Fanisau da Ɗorayi
da na Nasarawa. Haka kuma gonakin sarki duk suna hannun Ɗanrimi ne duk aikin
da za a yi shi ke da hakkin kula da su.
A
cikin gida kuma aikin Ɗanrimi
shi ne, kula da inda sarki ke zama a ƙofa
ta arewa a lokacin zaman fadanci. Haka kuma, a zamanin Turawa shi ne manzon sarki
tsakaninsa da Rasdan. Haka kuma yanzu da babu Turawa aikinsa yakan je wajen
gwamna ya sanar cewa sarki yana zuwa. Kuma ranar Sallah in shamaki baya nan shi
ke shigowa da hakimai domin gaisuwa. A lokacin hawan Sallah kuma yana kusa da
shi ta ɓangaren hagun.
Muƙarrabansa
sun haɗa da:
1-
Madakin Ɗanrimi
2-
Barden Ɗanrimi
3-
Ɗansarai
4-
Sarkin tukurwa
Sarkin Dogarai
Sarkin
dogarai shi ne kamar wakilin doka, kuma yana da dogarai da yawa a ƙarƙashinsa. Aikinsa duk
wanda ya gagara ko ɓarawo
ko wani mai laifi to shi ake turawa ya zo da shi. Haka kuma a lokacin yaƙi shi da Madaki ne
ke kan gaba. Babban aikin sarkin dogarai da yaransa shi ne tsaron lafiyar sarki
da iyalansa. Ga muƙarrabansa
kamar haka:
1-
Makaman Dogarai
2-
Madakin Dogarai
3-
Sarkin yaƙin Dogarai
4-
Turakin Dogarai
3-
Sarautar
Sallama
Sarautar
Sallama tana daga cikin manyan bayin sarki, wanda daga Ɗanrimi sai sallama,
a kan yi masa kirari da “ sallama alkhairin Bayi”, domin shi ba a yi masa gefe
a gidan sarki, ko’ina ya iya shiga komai dare idan ya zo da magana za a buɗe
masa ƙofa
ya ga sarki. Sallama ake gayawa idan ana buƙatar buga bindiga
shi kuma ya sanar da sarkin bindiga. Haka kuma idan sarki yana zaune a majalisa
idan wata Magana ta ta so ta cikin gida sallama ake yi wa ita ya gabatar da
ita.
Har
ila yau Sallama shi ke raba abinci in sarki ya yi tafiya, kuma duk wata kyauta
ta sarki shi ke raba wa. Idan sarki ya yi niyyar yin kyauta a wani talaka ko
malami sallama ake ba wa ya bayar da ita. Kuma sallama shi ke shigar da ƙara a gaban sarki.
Yana da hakimai kamar haka:
1-
Mabuɗi
2-
Barden sallama
3-
Kilishi- Kilishi
shi ke kula da shifiɗar
sarki, duk idan sarki zai zauna kilishi ne zai masa shimfiɗa.
4-
Magajin Ɗankama-
5-
Maitari- shi ne
shugaban ‘yan bindiga, shi yake ba da alburusai da kuma umarnin buga bindiga
idan ana buƙata.
Ta
la’akari da waɗannan, su ne
za su tabbatar mana da cewa lalle bayi suna da gurbi a masarautar Kano da ma
sauran masarautun ƙasar
Hausa baki ɗaya.
3.9 Haramta Cinikin Bayi
Haramta
cinikin Bayi a duniya baki ɗaya,
abu ne da aka fara shi shekaru da dama. Wanda Musulunci ya tarar ana harkar
bauta a duniya. Addinin Musulunci ya ba da gudumawa wajen kashe cinikin bayi a
duniya baki ɗaya. Wanda
kullum Musulunci kwaɗaitar
wa yake a kan a ’yanta bayi kamar yadda Allah (S.W.A) Yake cewa a cikin suratul
Mujadala aya ta uku
Waɗanda
suka zihari a matayensu sannan suka dawo kan abin da suka faɗa
a baya za su ’yanta baiwa muminakafin su shafi matansu. Wannan kuma ana yi muku
wa’azi ne da shi. Allah mai ba da labari a kan abin da kuke aikatawa.
Wannan
ayar tana nuna cewa duk mijin da ya kwatanta matarsa da mahaifiyarsa to zai
’yanta bawa, da wannan ya tabbatar da cewa musulunci shi kullum ƙarfin
guiwa yake bayar wa a kan a ’yantar da bayi ba wai a bautar da su ba.
Haka kuma,
Allah Ya sake cewa a cikin suratul Ma’ida aya ta 89 Allah ba ya kama ku saboda
yasassa a cikin rantsuwoyinku, kuma amma Yana kama ku da abin da kuka ƙudurta
rantsuwoyi (a kansa). To kaffararsa ita ce ciyar da miskini goma daga
matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalanku, ko kuwa tufatar da su, kokuwa
’yantawar baiwa munina. Sa’an nan wanda bai samu ba, sai azumi kwana uku.
Wannan ne kaffarar rantsuwoyinku idan kun rantse. Kuma ku kiyaye rantsuwoyinku
kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku kuna godewa.
Haka
kuma, Allah yana cewa duk wanda ya rantse to zai ciyar da abinci ga miskinai
guda goma, abincin ma irin wanda yake amfani da shi, ko kuma ya tufatar da su.
Idan haka ba ta sa mu ba to sai ya ’yanta bawa. Wannan ma ya nuna cewa
musulunci kullum hani yake a kan bauta.
Haka a cikin
suratul Nisa’i aya ta 19 Allah cewa ya yi bai kasance ba ga mumini ya kashe
mumini, sai dai a kuskure duk wanda ya kashe mumini a kuskure zai ’yanta baiwa
mumina, sannnan zai ba da diyya a iyalansa, sai dai iyanlan sun yafe. Idan kuma
mutum ya kasance yana daga cikin maƙiyanku
kuma mumini ne ba musulmi ba sai ya yi Kalmar shahada idan haka ta faru za a
’yanta baiwa mumina. Idan wanda aka kashe ɗan
tsakanin akwai alƙawari za a
ba da diyyar ga iyalansa sannan za a ’yanta baiwa mumina, idan kuwa mutum bai
samu damar baiwa ba zai yi azumi wata biyu a jere don neman gafarar Ubangiji.
Allah Ubangiji ya kasance akwai shi da hukunce- hukunce da yawa.
Haka
kuma, wannan ayar ma haka ta nuna cewa duk wanda ya kashe mumini da gangan to
zai ’yan bawa, sannan bayan ya ’yan bawa zai bawa iyalan mutumin diyar ran da
ya kashe, sai dai idan iyalan mutumin sun yafe masa to wannan babu laifi.
Haka
kuma akwai Hadisai daga Manzon Allah sallalahu alaihi wassalam da suke ƙara
tabbatar da cewa musulunci ya ba da gudumawa wajen hana bauta a duniya baki ɗaya.
Kamar yadda ya ce a cikin Sahihul Bukari
An karɓo
daga Muhammadu Ɗan Musana Al’nazi
daga Yahya Ɗan Sa’id daga Abdullahi Ɗan
Sa’id ana ce masa Ibn Abi Hundu an karɓo daga
Isma’il bin Abu Hakim daga Sa’idu bin Murjana daga Aba Huraira shi kuma daga
Manzon Allah Sallahu alaihi wassalam ya ce duk wanda ya ’yanta mumina Allah zai
‘yanta dukan gaɓa daga gare ta zuwa shi daga wutar Jahannama
Haka kuma,
daga Abu Huraira cewa Manzo Allah Sallahu alaihi wassalam yana cewa duk
musulmin da ya ’yanta musulmi Allah zai kuɓutar
da gaɓoɓinsa
daga wutar Jahannama.
Duk
waɗannan
suna nuna muhimmancin ’yanta bayi, da irin yadda musulunci ya ba da gudumowa
wajen haramta cinikin bayi a duniya, har Allah Ya yi alƙawarin
aljanna ga wanda ya ’yanta. Saboda shi addinin musulunci so yake a ’yantar da
Bawa. Shi musulunci bai taɓa cewa a yi bauta ba sai dai
a ’yanta. Wannan ita ce hanya ta farko da ta fara taimakawa wajen kashe bauta
ko cinikin bayi a duniya baki ɗaya.
Daga
baya kuma, a shekarar (1787) an samu wasu Malaman kirista suka haɗa
kwamiti wanda Reverend Thomas Clarkson da Wilberforce wanda su ne suka
jagoranci tafiyar suka fara yin wa’azi suna cewa duk mutum dai-dai yake da ɗanuwansa
ɗan Adam. Wannan
zalunci ne a dinga bautar da mutane. Kwance-ta-shi har ya samu ma goya baya
suka dinga yaƙar
take haƙƙin
bil adama da wayar da kan mutane daga wannan mugunyar hanya a duniya baki ɗaya.
(Crowder 1981:33)
An
samu waɗansu mutanen
Afirka da suke zaune a Ingila su biyu waɗanda
suka yi rubutu mai take Thought and
Sentiment on slavery in 1787. Da Olaudah Equiano wanda aka fi sani da
Gustavus Vassa sun yi rubutun ne aka irin yadda ake gudanar da kasuwar bayi a
Afirka. Bayan shekara 21 a ka samu wasu gungun mutune su ma masu yaƙi da sayar da bayi.
Haka kuma akwai lokacin da ‘yan majalisar
Ingila suka gabatar da ƙudirin
haramta cinikin bayi a shekarar 1807 wanda suka kafa kwamiti mai ƙarfi. Wanda suka
kafa wata kotu a Sierra Leone a ƙarƙashin vice Admiral
duk wanda aka kama dajirgi ya ɗauko
bayi za a yi masa hukunci a nan.
Sai
kuma wani dalilin Haramta cinikin bayi a duniya da ma ƙasar Hausa baki ɗaya.
Ita ce Industrial Revolution wato, ci gaban zamani da aka samu ta fuskar ƙere-ƙere a ƙarni na sha takwas.
Wannan hanya ta taimaka ainun wajen kawo ƙarshen cinikin bayi
gaba ɗaya. Domin
sun gano cewa a wancan lokaci aikin da inji guda zai yi a rana ɗaya
tafi ta bayi dubu da za su yi kwana biyu zuwa biyar suna yi. Da suka fahimci
haka sai suka ga cewa bayin ba su da wani sauran amfani a gun su. Sai kuma aka
shiga hidimar mayar da bayi daga wajen da suka fito. A wannan lokacin aka kai
su Laberiya da kuma Saliyo.
Waɗannan
hanyoyi su ne suka taimaka wajen daina saye da sayarwa da ake yi wa Bayi a ƙasar Hausa dama
duniya baki ɗaya.
3.10 Naɗewa
A
cikin wannan babin da ya gabata an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi
bauta a ƙasar
Hausa. Wanda mun duba zuwan Musulunci ƙasar
Hausa da kuma zuwan Turawa Nijeriya. Sannan kuma aikin ya duba me ake nufi da
bauta da kuma asalin bautar a ƙasar
Hausa, da kuma hanyoyin mallakar bawa da kuma ‘yanta shi. Daga bisani aka duba
gurbin bayi a masarautun ƙasar
Hausa domin duba irin rawar da suke taka wa. Da cinikin bayi yadda ya gudana da
yadda aka Haramta cinikin bayi.
[1] Wannan an
samu shi ne daga shafin yanar gizo ranar 14/07/2016 www.wiktionary.org
[2] Hira Abubakar Bangon Sarkin Gobir, a gidansa da misalin karfe
12:02pm 14/01/2017
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.