The aim of this study focuses on the traditional titles of slaves in Katagum. It is based on this aim that the research was presented in five chapters. The first two chapters focussed on general overview of the work and relevant literatures related to this research. Chapter three has taken broader look at the historical background of slevary in Hausaland. After the historical survey, the research narrowed to the slave-only traditional titles in Katagum. This has seen the research scrutinising indepthly all the issues surrounding slave-only traditional titles in Hausaland even before the emergence of Katagum. Similarly, the research has scrupulously found out the findings of the work. The research found out that some traditional titles have become extinct. Against this backdrop, traditional instutition have been recommended to establish a special traditional titles office that will handle the historical facts of the kingdom/emirate and other traditional title holders.
Tsakure
Ƙudirin wannan aiki tunkarar Sarautun
Bayi a ƙasar
Katagum. Bisa ga wannan ƙudirin an kasa binciken zuwa babuka
biyar. Goshin aikin ya tunkari gabatarwa da bitar ayyukan da suka gabace shi.
Kashi na uku na aikin ya yi dogon share fage a kan tarihin bauta a ƙasar
Hausa. Bayan an yi wa tarihi turke mai ma’ana sai aka dubi masarautar Katagum
da sarautun bayi da ke ciki. Wannan ya nuna an ƙoƙarin
kakkeɓe
duk wata ƙura a tarihi da al’ada da bautar take
ciki a ƙasar
Hausa gabanin a yi ƙasar Katagum dubi na nutsuwa. Binciken
ya yi kwakkwara da kammalawa wadda ta fito da ɗan sakamakon bincike da aka yi. Tabbas an
gano cewa wasu sarautun gargajiya a fada sun soma ɓata. Don haka, tilas a farfaɗo ko ƙirƙiro
wata sarauta cikin kowace masarauta a ƙasar Hausa da za ta kiyaye da tarihin
sarautun masarautarta.
Sarautun
Bayi A Ƙasar
Katagum (1814- 2016) – KASHI NA 5
Muhammad
Abubakar Zabi
muhammadabubakarzabi@gmail.com
08136844199
SADAUKARWA
Na
sadaukar da wannan aiki ga mahaifana, Malam Abubakar Wazirin Zabi da Malama
Hauwa’u Ahmad. Allah Ya ƙara
musu lafiya tare da imani, amin. Allah Ya saka musu da tarbiyar da suka yi
mana. Mun gode, Allah Ya biya.
GODIYA
Godiya mafificiya
ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki,
mamallakin sammai da ƙasai,
wanda Ya raya mu Ya kuma ba mu ikon kawowa wannan mataki. Tsira da amincin
Allah su ƙara
tabbata ga manzon tsira, Annabi Muhammadu (Sallahu Alaihi Wasalam).
Babu shakka, mutane da dama sun ba da gudummawa wajen ganin wannan aiki ya
kammala cikin nasara. Sai dai ambaton sunayensu duka ba zai yi wuya ba, ko da
kuma an ambata godiyar fatar baki ba za ta gamsar ba. Sai dai addu‘ar Allah Ya saka
wa dukkan wanɗanda suka taimaka da alheri.
Godiya ta musamman wadda ba za ta misaltu ba ga Malamina kuma jagoran duba
wannan aiki Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza, wanda duk da ayyuka masu dama da suke
gabansa, amma ya kula ya kuma yi ta taimakawa wajen duba aikin da kuma
gyare-gyare ga wannan bincike. Kazalika, ya yi ta ba da shawarwari masu dama tun
daga farkon aikin har zuwa ƙarshensa. Ina roƙon Allah Ya saka wa Malam da gidan Aljanna Fiddausi, amin.
Haka kuma, godiya marar misaltuwa ga Malamina kuma jagoran duba wannan aiki
na biyu wato Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi shi ma ya yi namijin ƙoƙari wajen ganin wannan aiki ya yi nasarar kammaluwa. Ba don haɗin kan da ya bayar ba, da wannan aiki bai tsayu da ƙafafunsa ba. Da fatar Allah Ya saka wa Malam da gidan Aljanna
fiddausi, amin.
Ina miƙa godiyata ta musamman ga malamina jagoran duba aikin na uku, Farfesa Y. Y
Ibrahim na Sashen Nazarin Addinin Musulunci (Islamic Studies Department), wanda
da taimakonsa aikin nan ya samu kai wannan mataki. Ina fatar Allah Ya saka wa Malam
da gidan Aljanna Fiddausi, amin.
Bayan haka, ina mai matuƙar bayyana jin daɗina da godiyata ga shugaban Sashen Nazarin Harsunan
Najeriya, Jami´ar Usmanu Ɗanfodiyo, Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa, ina yi wa Malam fatar Allah Ya saka
masa da alheri. Ina godiya ga dukannin Malamaina na Sashen Nazarin Harsunan
Najeriya na Jami`ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Waɗanda suka haɗa da: Farfesa Ibrahim Makoshy, da Farfesa Abdullahi
Bayero Yahya, da Farfesa Haruna Abdullahi Birniwa, da Farfesa Ahmad Halliru
Amfani, da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, da Farfesa Abdulhamid Ɗantumbishi, da Dr. Bello Bala Usman, da Dr. Ibrahim
Sarkin Sudan, da Dr. Yakubu Aliyu Gobir, da Dr. Abdulbasir Ahmad Atuwo, da Dr.Yahya
Idris, da Dr. Umar Aliyu Bunza, da Dr. Nasiru Aminu Kalgo, da Malam Naziru Ibrahim
Abbas da Malam Sama’ila Umar da Malam Dano Balarabe Bunza da Malam Mustafa Muhammad
da Malam Musa Shehu. Abokanin karatuna ma sun taimaka da shawarwari da addu’a
na gode Allah Ya biya. Waɗanda ta hanyar basira da ilmi da kyakkyawar fahimtarsu na
samu nasarar kammala wannan karatu.
Ba zan manta da Hakiman ƙasar Katagum ba, musamman Hakimin Itas da Hakimin Gamawa da Hakimin Sakuwa
da Hakimin Gaɗau da kuma Hakimin Azare, da iyayen ƙasa na masarautar Katagum da kuma, Majalisar Masarautar
Katagum wajen ba ni lokaci na musamman domin tattaunawa da su. Na gode Allah Ya
saka da alheri, Amin. Gadiya ta musamman ga Sarkin Garinmu Alhaji Muhammadu
Abdulkadir Madakin Zabi wanda ya taimaka wajen ba ni shawarwari da ƙarfafa mun guiwa wajen ganin kammaluwar wannan bincike,
shi ma Allah Ya saka masa da alheri. Ina miƙa godiya ga Ma`aikatar ilimin Firamare ta Giyaɗe, Jihar Bauchi da ta taimaka mun wajen ba ni damar tafiya wannan karatu.
Allah Ya saka da alheri.
Ba zan manta da abokaina ba, waɗanda suka ba ni shawarwari tare da taimako na ƙara ƙarfin guiwa kan wannan karatu. Musamman irin su Malam Abdullahi Zabi da
Muhammad Abubakar (Khalifa) da Umar Barde da Alhaji Muhmood Abba da Abduƙadir Namangi da Ibrahim Ɗanbaba da Ja’afar Bello da sauran Malaman da suke
Makarantar Firamare ta Baduware. Duk ina musu fatar Allah Ya saka da alheri.
Bayan haka, godiya ta musamman ga abokan karatuna na wannan jami`a ta
Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Irin su Ahmad Garba Aliyu da Jibrin Yusuf da Alhaji Musa
Abdulrahaman da Malam Imam Abdullahi da Hajiya Zara‘u da Shamsudeen Isma’il da ma
sauran waɗanda ban ambaci sunayensu ba. Duk ina musu fatar Allah Ya
sa mu haɗa wannan karatu lafiya, Ya sanya mana albarka a cikinsa.
Daga ƙarshe, ina miƙa godiyata ga mahaifana Malam Abubakar Wazirin Zabi da Hauwa’u Ahmad.
Sannan da matata Maijidda Bello da ‘Yayana Khadiji Muhammad Jaɓɓello. da Salmanu Muhammad Jaɓɓello da Al’amin Muhammad Jaɓɓello da Ibrahim Muhammad Jaɓɓello duk ina musu fatar Allah Ya saka musu da alheri
amin.
BABI
NA BIYAR
TSARIN
SARAUTU A FADAR KATAGUM
5.1
Shimfiɗa
Wannan ɓangare ne na gudanar da harƙar mulki a fadar sarkin Katagum, wato mataimaka wajen gudanar
da mulki. Sun kasu kashi biyu. Ga su kamar haka:
5.2 Hakimai masu Ƙasa
Hakimai masu ƙasa su ne waɗanda suke jagorantar al’umma a wasu
yankuna, wanda suke a ƙarƙashin jagorancin sarkin yanka. Wanda kuma suna zama a
matsayin wakilan sarkin Katagum ne a yankunansu, suna taimaka masa ta ɓangaren abin da ya shafi sha’anin
mulki. Kamar ta fuskar abin da ya shafi horo da hani da yin hukunce- hukunce da
aiwatar da doka da kuma saka ta a tsakanin jama’ar ƙasa. Misali kamar Zaki Galadima ne yake riƙe da ita, da kuma, Itas yadda ita kuma Tafida ne yake
jagorantar masarautar.
5.3 Hakimai masu Karaga
Su ne waɗanda suke riƙe da muƙaman da ake bayarwa a fada, wanda su ba
ƙasa ake ba su ba, domin taimaka wa
sarki ta ɓangaren abin da ya shafi sha’anin tafiyar da mulki, kama
daga shawara da duk wani abun da zai iya tasowa a fada. Hakimai masu karaga su
ne kamar Waziri da Galadima da Talba da Shamaki da Wali da sauransu. Su ma ana
iya ɗaukar ɗaya a cikinsu a ba su riƙon ƙasa.
A fadar Katagum akwai rabe-raben sarautu
a fada kamar haka:
5.3.1 Sarautun ’Ya’yan Sarki
Waɗannan sarautu ne da ake ba wa ‘ya’yan
sarki kawai. Wanda su ma a matsayinsu na ‘ya’yan sarki akwai irin gudumuwar da
suke bayarwa wajen gudanar da harƙoƙin mulki. Ta fuskar taimakawa sarki. Sarautun ga su kamar
haka[1]:
1-
Ciroma
2-
Yarima
3-
Ɗanmaje
4-
Ɗaniya
5-
Ɗanlawan
6-
Sardauna
7-
Ɗanburan
8-
Sarkin Dawaki
9-
Sarkin Dawakin Tsakar Gida
10- Sarkin Bai
11- Baura
12- Ɗanruwatau
13- Ɗandarman
5.3.2 Sarautun
Bayi
Waɗannan sarautu da ake ba wa bayin sarki
waɗanda aka aminta da su domin su ma su bayar da tasu gudumuwa
ta ɓangaren abin da ya shafi gudanar da harƙoƙin mulki a fada. Ga sarautun kamar haka[2]:
1-
Makama 11- Harɗo
21- Barade
2-
Sarkin Dogarai 12-
Maidala 22-Baraya
3-
Wambai 13-
Barwa 23-
Masu
4-
Sarkin Yaƙi
14- Ɗanrimi 24- Gado-da-masu
5-
Dandalma 15- Garkuwa 25- Jakada
6-
Shamaki 16- Ma-ja-sirdi 26- Harɗo mai Dawki
7-
Sallama 17- Kilishi 27- Sarkin Zagi
8-
Mabuɗi 18- Maga-yaƙi 28- Jarma
9-
Shantali 19-
Lifidi 29- Ƙaura
10- Tafida 20- Galadima 30-
Maitafari
5.3.3 Sarautun Barorin Sarki
Waɗannan sarautu ana ba wa masoyan sarki
ne waɗanda suka kasance ‘yan boko ko masu riƙe da wasu muƙamai na gwamnati da siyasa da sauran
mutanen gari waɗanda suka dace. Buƙata dai su taimaka wajen gudanar da abin da ya shafi harƙoƙin gudanar da mulki a fadar Katagum da
ci gaban masarautar. Sarautun sun haɗa da:[3]
1-
Waziri 16- Sarkin Busa 31-
Danejo
2-
Galadima 17-
Sarkin Fawa 32- Dallatu
3-
Majidaɗi 18- Sarkin Rafi 33- Magatakarda
4-
Turaki 19- Sarkin Ruwa 34- Dokaji
5-
Ɗan’amar 20- Sarkin Aska 35-
Ajiya
6-
karofi
21- Sarkin Kasuwa 36- San Turaki
7-
Madaki 22- Sarkin Tuke 37- Matawalle
8-
Magajin gari 23-
Sarkin Shanu 38- Sallanki
9-
Ɗanbadami 24- Magajin Rafi 39- Fagaci
10- Durɓi 25- Katika 40- Ɗanmasani
11- Talba 26- Marafa 41- Tafarki
12- Ɗanmaliki 27-
Shatima
13- Uban Doma 28- Zanna
14- Sarkin fada 29- Sa’i
15- Ɗangaladima 30-
Wali
5.4 Yaƙe-yaƙen
Ƙasar
Katagum
Katagum ƙasa ce wanda take da gwarazayen sarakuna waɗanda suka yi fice ta ɓangarori da dama, kamar ta fuskar
jarumta da yaƙe-yaƙe da dai sauransu. A wancan lokaci bincike ya nuna cewa a
irin halin da ƙasa take ciki wanda a cikin irin wannan
halin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya girma, ya kuma yi niyyar
gyarawa ya mayar da hali irin na Musulunnci. Akwai sarakuna da yawa a ƙasar Hausa waɗanda dangantaka tsakaninsu ba ta da
kyau. Akwai gaba da ƙoƙirin murƙushe juna, wato kullum ana cikin yaƙi, su manyan sarakunan lokacin suna da tsarin mulki daga
sarkin karaga sai sarakunan ƙauyuka da sarkunan noma, duk waɗannan suna taimakawa wajen nuna ƙarfin mulki. A lokacin hanyoyin samun kuɗin sarki shi ne ganimar yaƙi da harin kama bayi da harajin sana’a da haraji a kan
mazauna ƙauyuka bisa abin da suka noma. A waɗansu wararen sau uku ake karɓar jangali, ba mai iya tsawatarwa
sarki. ‘Ya’yan sarki da barorin sarki suna da ta su hanyar ta samun kuɗi ta kwace dukiyar talaka ko su mai da
talaka bawa su sai da shi. Aminu Sale cewa ya yi:
“Sarautar wannan lokaci ba ta Musulunci
ba ce, ba ta da manufa sai biyan buƙatun sarakuna ta dogara a kan mutuncin
mutane da dukiyarsu da rayuwarsu. Waɗannan su ne halayen hukumar kafirai, kada Musulmi su kuskura
su kwaikwaye su” Saleh (2004:7-8)
A wannan hali da ake ciki a wannan
lokaci ne Shehu da taimakon almajiransa suka tashi tsaye don jadadda addinin
Musulunci da halayyar Musulunci a ƙasa. Don haka, abin da Shehu da
almajiran suka yi shi ne, suka yaƙi kafirai da azzalumai da duk wani
musabbabin lalacewa. Waɗannan abubuwa na daga cikin dalilan da
suka jawo yaƙe-yaƙen da masarautar Katagum ta yi. Ga yaƙe-yaƙen kamar haka:
Yaƙin da Malam Zaki ya fara shi ne, yaƙi da sarkin Udubo wato Muhammadu bn Bukar bn Ahmed
Albarnawiyu. A wannan lokaci sarkin Udubo Muhammadu yana da ‘ya’ya 332 da bayi
600 da kuma ‘yan uwa 57. Wadata (2009:22)
Rundunar
Malam zaki ta tara Larawa (Barebari) da Fulanin Udubo, Malam Zaki bai ji daɗin yaƙin ba, sai ya ƙaura da jama’arsa zuwa Auyo yadda zai
haɗu da Arɗo Adu’a da Umaru da Sambo Digimsa duk
Fulani ne a jejin Auyo da Tashena. A wannan tafiya an yi yaƙe- yaƙe a kan hanya har aka kashewa Malam
Zaki mutum 29, tafiya da ta ɓaci sai suka dawo garin Shellum, domin
sake shiri. Sale (2004:14)
Daga
nan sai ya tafi Sakkwato, bayan dawowarsa daga Sakkwato bai zame ko’ina ba, kan
sa tsaye sai Yayu, kafin su ƙaura zuwa Shellum tare da Wazirinsa
Muhammadu Nayayu da Galadima Abubakar na II da Harɗo Dudu da Ladan Ibrahim Imrajo da Gwani
Yamma Umar da Ahmaduduwa da Ali Yaya da Muhammadu Sambo da Sarkin yaƙi Kari (Abubakar Dada) da Ja’o ɗan Hari da Dukko ɗan Abu da Ɗan uwansa Liman Adandaya da Alkali Usman da Yakudima Hamdi ɗan Haruna da kuma bayi guda bakwai (7).
Malam Zaki ya tafi Shellum da jama’ar fada don haka, sai aka so a yaƙi Sarkin Udubo, amma sai sarkin Udubo Muhammadu ɗan Abubakar da jama’arsa suka riga su kai
hari, suka same shi amma ba su kama shi ba. Daga nan sai Malam Zaki da
jama’arsa suka ƙaurato yamma zuwa wajejen ƙauyen Auyo, daga nan suka juya suka kama Tashena a 1201 AH
(1805-6). Da ya kama Tashena sai Malam Zaki ya maido da mazauninsa nan don kai
sabbin hare-hare. Daga nan sai ya kawo hari kan Gaɗau amma bai ji daɗin karon ba sai ya janye.
Da
ya sake shiri ya kuma sami gudumawa sai ya dawo da ƙarfinsa ya kama Gaɗau. Daga nan sai ya doshi Shira, a nan
ma an yi gumurzu, amma da dare sai Sarkin Shira ya zo wajen Malam Ibrahim Zaki
a asirce, shi Malam Ibrahim Zaki bai san cewa shi ne sarkin ba, ya zaci ɗan saƙo ne sai sarkin Shira ya zauna a gaban Malam Zaki ya bayyana
kansa. A ka yi ƙaramar yarjejeniyar cewa da safe sarkin
Shira zai kawo dukan manyan mayaƙansa da shugabannin gari su arba’in su
yi mubaya’a. Sarkin Shira ya yarda da haka bisa alƙawari mai ƙarfi. Da gari ya waye Sarkin Shira ya
cika alƙawarinsa ya zo da jama’arsa suka yi
mubayi’a ga Malam Ibrahim Zaki. Shi kuma, ya yi musu alheri mai yawa ya bar su
suka koma gida. Wannan shi ne mabuɗin ƙasar Shira a 1807. Daga nan Malam Zaki ya yi wajen Kurba da
yaƙi ya yaƙi Uzum da Burku da Faguji da Jarmawo da ya gama da su, sai
ya nufi Misau zamanin sarkin Misau Turi bn Magaji, amma ba a yi yaƙi ba don sun ji sarkin Shira bai yi yaƙi da Malam Ibrahim Zaki ba. Daga nan Malam Ibrahim Zaki sai
ya juya zuwa Udubo kan babban abokin gabarsa sarkin Udubo Muhammadu bn Abubakar
ran 27 ga Rabiyyul Auwal 1207, A.H. Jama’ar garin ba su son wannan yaƙin don haka sai suka juya wa Sarki baya. Hakan ne ya sa
Sarkin yaƙin Udubo tare da ‘ya’yansa ashiri da huɗu (24) suka kashe sarkin Udubo, don su
yi mubaya’a. Daga safiya zuwa azahar aka gama kama Udubo. Daga nan Malam Zaki
ya tafi wajen Gaɗiya. A hankali sai da ƙasar Katagum gaba ɗaya ta zama ƙarƙashin Malam Zaki. Ganin haka, sai Malam
Zaki ya himmatu wajen shirin mulkin Katagum. Malam ya yi mulkinsa ne tare da
shawarar jama’a, hatta mata ba a bar su a baya ba. Sale (2004: 15)
A
nan Tashena sai Shehu Usmanu Ɗanfodio ya ba da izinin a kai hari ƙasar Borno aka tara jama’a aka yi shirin yaƙi. An fita ranar ashiri da biyu (22) na Jimada-ula. Rundunar
Malam Zaki ta fara ne kan Kachalla Kayo, wani babban ɗan tawaye aka kashe shi a garin Kayuri,
yana tare da Usman bin Musa Muhammadu Almare, daga zuriyar Dilara na ƙasar Chadi. Ɗan Kachalla mai suna Kayo ya gudu ya
shiga cikin Gizmawa, a nan ma bai sami sauƙi ba, don mai Borno Bukar ya yaƙe su a Dawasa. Bayan nan sai Kayo ya koma Potiskum, a nan ya
yi ƙoƙarin gama da Kachalla Kayo Malam Zaki ya yaƙi Garko bayan sallar layya 1208 A.H. Daga nan ya ci gaba da
yaƙe- yaƙen da aka nisa gabas, da sarkin Dawasa Muhammadu bin Ahmadu
ya ji labarin Malam Zaki, sai ya janye daga garinsa. Malam Zaki ya zauna a
garin na tsawon wata uku da kwana ashiri da biyar (25). Saboda haka ne ake cewa
Malam Zaki ya mulki gabas da Dawasa. Malam Zaki yana zaune a nan ne ya aika
Sakkwato wurin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, don ya ji ko zai zauna a ƙasar Borno, inda Shehu ya ce, ya janye bai ba shi izinin
zama a ƙasar Borno ba. Don haka, Malam Zaki ya
janye don kar ya saɓa wa Shehu ya dawo ƙasarsa. Wasu sun ce saboda wannan mulkin da ya yi a Dawasa
ne, ake wa sarkin Katagum laƙabi da sarkin Borno. Sale (2004: 15)
Yaƙin Ngazargamu, Malam Zaki ya karkata daga gabashin ƙasarsa zuwa arewaci, wato gefen Haɗeja ya kama Auyo da Nguru da Marma a
1807 a cikin littafin Wadata 2009 ( Dr. Low shafi 110) wannan nasara da ya yi
ta sa ya kai hari na farko har Ngazargamu a 1808-1810.
Malam Zaki da rundunarsa sun kai hari
na farko birnin Ngazargamu a wannan lokaci an fafata sosai babu ɓangaren da ya yi nasara. Daga bisani
Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya umarci Malam Zaki ya kai
hari na biyu birnin Ngazargamu. A wannan lokaci ne mayaƙan Katagum da na Haɗeja suka sake kai hari na biyu. Malam
Zaki da rundanarsa sun yi nasara a kan Shehun Borno mai suna Mai Amadu, Malam
Zaki ya yi nasara a kan birnin Ngazargamu.
Binciken da Sale, ya gudanar ya nuna
cewa a nan Malam Zaki ya nemi izinin zama, amma Shehu bai yarda ba. Rashin a
bar shi ya zauna a ƙasashen da ya ci da yaƙi dan haka, ala tilas ta sa Malam zaki ya haƙura. Dr. Low ya ce, a zatonsa dalilin da ya sa Shehu bai bar
Malam Zaki ya zauna a Borno ba gudun kada ya kafa daula tsakanin Sakkwato da
Borno, ma’ana kada Malam Zaki ya fita daga ƙasar Usmaniyya. Wannan shi ne dalilin da ya sa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo yaƙi amincewa da buƙatar. Wadata (2009:24-27) da Sale (2004:13-14)
Bayan nan a lokacin Muhammadu Hajji yaƙi ya kaure tsakanin Katagum da ƙasar Ningi a lokacin sarkin Katagum yana kan hanyarsa ta
zuwa Sakkwato, wanda yaƙin an yi shi ne a Tumfafi a shekara
1883. Allah Ya ba wa Katagum nasara a kan Ningi, amma duk da nasara da aka ci
Katagum ta yi hasarar mutanenta ciki kuwa har da Buluzuma ɗan Sarki Abdulƙadir na I
Sai yaƙi na ƙarshe a ƙasar katagum, wanda aka yi tsakanin Katagum da Gamawa. A
lokacin sarki Abdulƙadir na II a shekarar 1900. Wanda
sanadiyar yaƙin shi ne Gamawa ta ce ita ma yanzu za
ta fita daga ƙasar Katagum, ta kafa ƙasarta nan fa aka fafata. Wanda sarkin Sakuwa Muhammadu shi
ya jagoranci yaƙin. Waɗanda suka tallafa masa kuma sun haɗa da Jakada Basharu da Muhammadu Gudidi
da Barde Haruna da Makama Zuloƙi da sauransu. Nan dakarun Katagum suka
murƙushe na Gamawa aka kashe sarkin Gamawa,
garin ya dawo ƙarƙashin ikon sarkin Katagum. Hira da Harɗon Katagum (16/02/ 2017, 04:00:08 na
yamma)
5.5 Kasuwar
Cinikin Bayi A Ƙasar
Katagum
Kasuwa waje ne da ake sayi da sayarwa,
domin hidimomin yau da kullum. Ciniki kuma na nufi sayar da abu bisa yardar mai
kaya da wanda ya sayi kayan. Bisa kula da waɗannan za mu iya cewa kasuwar bayi waje
ne da ake hada-hadar sayar da bayi.
A ƙasar Katagum an gudanar da kasuwar cinikin bayi a cikin
yankunan ƙasar kamar yadda aka gudanar a sauran
yankunan ƙasar Hausa.
1-
Disina
2-
Gamawa a Anguwar Tamsugugi
Ana kai bayi maza da mata kasuwa, idan
za a kai bawa kasuwa a kan tafi da ruwa a buta, wanda shi bawa a kan shafa masa
toka. Amfanin buta shi wanda ya zo sayan yakan ce a wanke masa shi ya gani ko
yana da wata illa a jikinsa da kuma bawa idan an je kasuwar wasu a kan ɗaure su a cikin mari wasu kuma haka ake
sake su, a lokacin da mai saye ya zo zai sayi bawan. Bawan na iya cewa bana
kaunarka ka da ma ka saye ni domin ba zan yi maka biyayya ba. Wani kuma bawan
kan ce masa zo ka saye ni zan maka duk abin da ka umarce ni. Ana gudanar da
cinikin da wuri da keso da zambar ko kuma ta hanyar musaya wato, mutum kan iya
kai bawa a ba shi wani abu da yake buƙata kamar Dawaki da kayan doki ko kayan
hawan dokin ko abinci ko kayan yaƙi. Ya dai danganta da yadda mutune suka
yarda. Hira da Burga (21/11/2016, 10:48:02am)
5.6 Fitattun
Bayi A ƙasar
Katagum
Ƙasar Katagum kasa ce kamar kowace ƙasa wanda tana da bayi da suka shahara a ɓangarori da dama, kama ga jarumta da
gagara a zamunansu da buwayar mutanen wannan lokaci da dai sauransu. Ga kaɗan daga cikin fitattun bayi da aka yi a
ƙasar Katagum:-
-
Makama Abare: Makama Abare ya shahara a lokacinsa. An
yi shi a lokacin Malam Ibrahim Zaki(1804- 1814). Ya shahara ta ɓangare jarumta. A lokacinsa sarki duk
wani abin da ya gagara shi ake sawa a gaba. Ɓangaren wanda suka yi laifi ko kuma faɗa tsakanin wasu jama’a ko kuma sarki ya
aika ya zo yaƙi ko kuma wani ɗan fashi ya damu al’umma to Makama Abare
za a tura domin ya zo da shi gaban sarki. Wanda ya gaje shi ne, ɗansa Makama Amadu.
-
Duma: Duma bawan sarki. Shi ma wannan bawa
ne da aka yi a ƙasar Katagum wanda ya buwaya a
zamaninsa. An ce, a lokacin har fashi da makami yake yi ko ya tare ayari shi ɗaya. Daga baya ya zama dogarin sarki. Saboda
tsabar jarumtarsa ne aka ba shi Sarkin Dogarai. Wanda shi duk wani mutum ko
gari in sun gagari sarki Duma ake tura musu ko a tura ya zo da shi. Wanda Mawaƙinsa Ibrema yake masa kirari da
Duma bawan sarki da a ce maka
Allah gara a ce maka ga aikin
sarki
Sarkin Dogarai Shehu ne ya gaje shi.
Bayan rasuwarsa.
-
Yayyafa: Yayyafa da Duma kusan lokaci guda
suka rayu a zamanin sarki Abdulƙadir (1947), wanda shi ya shahara amma
bai kai Duma ba. Shi ma ya zama Dogarin sarki a lokacin Sarki Abdulkadir III.
Shi ma ana masa kirari da:
Yayyafa ka nemi rabonka nan duniya bakka rabo
a lahira, walakiri da munkarin sun haɗa komai
Tsabar rashin tausayinsa da rashin imaninsa ne ake masa
wannan kirari, domin duk wanda ya shiga hannunsa ba ya share wa da daɗi.
-
Garkuwa Shehu: Garkuwa Shehu an yi shi lokacin Sarki
Umaru a shekarar (1948), wanda ya shahara ainun a ƙasar Katagum da ma maƙwabtan ƙasar. Garkuwa ya kai in zai je wajen
tun yana wani gari kafin ya iso garin an samu labarin isowarsa. Kuma wannan
lokaci kusan kowa tsoronsa yake yi domin duk fitinar mutum ba ya so a haɗa shi da Garkuwa. Kusan a wancan lokaci
Garkuwa Shehu sai da ya buwaya a zamaninsa kuma duk wani faɗa ko rikici da ake a ƙasar Katagum shi ake tura wa, zuwansa ke da wuya wannan
rikici ko faɗa ya mutu. Misali faɗan Gunda. Garkuwa yana cikin mutane da
suka taimaka wajen kawo ƙarshensa. Matsayinsa a fada ya fara riƙe matsayin Wakilin Doka sannan ya koma Sarkin Dogarai. Hira
da Alhaji Muhammadu Gaɗauji Turakin Katagum (10/11/2016
2:28:12 na yamma)
5.7 Ayyukansu
Sarautun Bayi a Ƙasar
Katagum
Kowace al’umma da ƙasa a duniya tana da tarihin asalin kafuwarta, tana da
al’adunta da ɗabi’unta waɗanda take alfari da su wanda su ne ke
bambanta wata ƙasa ko al’umma da wata. Ta hanyar
tarihi da al’adu da ɗabi’un al’umma ne ake sanin mashahurai
daga mutanenta da irin gudumuwar da suke bayar wa wajen ɗaukaka da martabar al’umma ko ƙasar tasu har ma ta kai ana buga misali da halaye da ɗabi’unsu.
Katagum ƙasa ce mai faɗi wanda a duk Jahar Bauci babu
masarautar da ta kai ta yawan ƙasa da Hakimai. Bauci tana da masarautu
shida da suka haɗa da: Bauci da Ningi da Dass da Misau
da Jama’are da Katagum. Katagun tana da hakimai goma sha biyu wato, Azare da
Madara da Chinade da Sakuwa da Gaɗau da Shira da Disina da Itas da Giade
da Gamawa da Udubo da Katagum mai kaba, wanda daga cikin Hakiman guda bakwai
‘ya ‘yan Sarki ne guda biyar kuma ba ‘yan Sarki ba ne. Wanda wannan aikin ya zaɓi Hakimai biyar da masarautar kanta,
domin a ga yadda sarautun bayin suke gudanar da ayyukansu a ƙasar Katagum jiya da yau.
Masana tarihi sun bayyana cewa
masarautar Katagum tana daga cikin masarautu na farko a cikin daular Usmaniyya.
Katagum tana da faɗin ƙasa kuma ta samu jerin sarakuna har guda goma sha ɗaya, wanda suka taimaka wajen bunƙasa ƙasar. Allah Ya arzurta ƙasar Katagum da ƙasar noma. Suna noman rani da na
damina. Wanda wannan ya taimaka wajen ƙaruwar gari ya cika ya tumbatsa. Mafi
yawan yaren da ake yi a yanki, sun haɗa da: Hausa da kare-kare da Fulantance
da Barbarci
5.7.1 Ayyukan
Sarautun Bayi a Masarautar Katagum
Masarautar
Katagum tana da nata sarautun bayi da take da su, wanda suna da ayyuka na
musamman da suke aiwatarwa a ƙasar.
A ɓangaren, za a
bayyana ayyukan irin waɗannan
sarautu na bayi jiya da yau, wanda za a ga yadda suke gudanar da ayyukan nasu a
masarautar, da irin gudumuwar da suke bayarwa ta fuskar ci gaban ƙasa da ma mulki da
tsaron ƙasa
kamar sauran sassan ƙasar
Hausa. Bisa ga abin da wannan aikin ya nuna, a ƙasar kowace fada
kusan tana da nata sarautun bayi wanda yawanci daga babbar fada suka kwaikwaya.
Ga su kamar haka:-
i-
Makama
Wannan
sarautar makama, babbar sarauta ce a masarautar Katagum, kuma an soma ta tun
lokacin sarkin farko, wato lokacin mulkin Malam Zaki (1814). Makama shi ne
shugaban bayi na fada. Babban aikinsa a fadar shi ne, mai kula da lamuran da
suka shafi Hakiman ƙasar
baki ɗaya, wanda
duk wani abu da yake tsakanin sarki da hakimai shi ne mai aiwatarwa. Wannan sarauta
har yanzu aikinta bai canja ba a masarautar Katagum. Duk cikin waɗanda
suke rike da sarautar bayi a masarautar Katagum babu kamar sa a wajen sarki.
Aikin mai riƙe da wannan sarauta
ta Makama a fadar Katagum shi ne, mai riƙe da makamai a zamanin
da, da ake yaƙi.
Sannan shi yake riƙe
da gari in sarki baya nan da sauran garuruwan Hakimai. Alal misali idan Hakimin
wani gari ya mutu ko ya yi wani laifi shi ake turawa domin ya wakilci sarki a
wannan garin kafin a zaɓi
wani. Haka kuma shi ne, mai kamawa sarki masauki in ya yi tafiya ta rangadi,
kuma shi ne idan an ba wa mutum sarauata yake kawo shi ya zaunar da shi a gaban
sarki kafin liman ya naɗa
masa rawanin sarautar da aka ba shi. Haka zalika Makama yana daga ciki mutum
biyar masu zaɓen sabon sarki
a masarautar Katagum. Bayan haka, kuma mai riƙe da sarautar Makama
idan an naɗa sabon
sarki a masarautar, shi yake ba wa sabon sarkin takobin Malam Zaki. Wanda yake
rike da wannan sarauta ta Makama kusan yanzu shi yake aiwatar da duk wasu
lamura na fada.
ii-
Sarkin Dogarai
Aikin
mai riƙe
da wannan sarauta shi ne, shugaban tsaro a fada wato, duk abin da ya shafi
tsaro a fada, to shi yake kula da shi. Ba yadda wani abu zai shiga fada kaya ko
mutum ba tare da sanin sarkin dogarai ba. Wannan sarauta har yanzu ba ta canja
ba, aikin ɗaya yake
jiya da yau.
iii-
Dandalma
Amfanin
wannan sarauta shi ne duk yadda muhallin fada yake to shi ne mai kula da shi.
Bayan haka, kuma duk wani taro da za a yi, in dai na fada ne, to shi ne mai
gabatar da taron a ‘yan majalisar sarki. Idan an yi aure a fada, idan dukkan
biyun jinin sarauta ne, wato ango da amarya. To Dandalma sai an biya shi kuɗin
filinsa da aka yi amfani da shi, haka kuma idan hidima a fada ce dole a sanar
da shi. Dandalma shi ne mai bayar da gida ko gona ga baƙo ko wani makamanci
haka. Dandalma yana cikin ‘yan goman sarki, wato waɗanda
suke tsayawa bayan sarki ranar sallah in an yi hawa. Wannan sarauta ita ma
zamani ya sa ta yi rauni ainu, saboda a yanzu zamani ya yi tasiri a kanta,
wajen rasa aikinsa
iv-
Harɗo:
Babban
aikin harɗo a fada shi
ne, karɓar kuɗin
haraji da jangali. Kuma yana daga cikin sharaɗin
riƙe
wannan sarauta sai kana jin fulatanci, domin kai ne wakilin sarki a wajen
Fulani. Wannan sarauta a yanzu kusan ta daina amafani ko kuma ba ta da ƙarfi sosai a fada
saboda canjawar zamani. Yana daga cikin ‘yan goma mazauna gefen sarki, wato
goma dama, goma hagun. Yakan je fada ya zauna duk wani aiki da fada take buƙata za ta iya saka
shi, amma yanzu babu wani takamaiman aiki da yake da shi a fada.
v-
Garkuwa
Aikin
mai riƙe
da wannan sarauta shi ne, kare sarki a fagen fama da gida, kuma duk wani kayan
sarki yana hannunsa. A ranar Sallah yakan yi ɗamaru
da sulke wato rigar yaƙi
ta ƙarfe
da hamilu da janjami a ƙugu
ake ɗaura wa
domin kare kai daga sara ya kuma riƙe
garkuwa a hannu. A yanzu aikinsa shi ne, kula da sarki a duk inda yake. Shi ma
yana cikin ‘yan goman sarki.
vi-
Lifidi
Aikin
mai riƙe
da wannan sarauta a masarautar Katagum shi ne, kula da marokan fada. Shi yake
naɗa su. Inda wani
maroki ya yi laifi shi yake ladafdar da shi. Kuma shi ne, wanda yake riƙe da ‘yan lifida,
wato yana gaban sarki a kowace fita da zai yi domin kariya wato dai yana cikin
dakaru masu kare lafiyar sarki. A da shi ne mai kula da kayan yaƙin sarki ko hawa
suka yi shigar yaƙi
yake yi. Ita ma wannan sarauta zamani ya rage mata ƙarfi ta wani gefen.
vii-
Sarkin Zagi
Babban
aikin sarkin zagi a masarautar Katagum shi ne, mai shiga gaban sarki in zai
fita rangadi ko hawan Sallah da dai duk wani muhimmin taro, su ne gaban sarki,
wato daga su sai sarki kuma wani lokaci a ƙasa suke tafiya ba
a kan dawakai ba, domin kare lafiyar sarki. Sukan yi shigar manyan kaya da
bakin rawani da yafa luru ko gwado na saƙi da dora alkyabba,
su kuma rataya takobi da ɗora
malafa kan rawaninsu. Haka kuma, shi sarkin zagi shi ne mai riƙe da ragamar dokin
sarkin.
viii-
Shamaki
Aikin
wannan sarauta shi ne kula da dawakan sarki da kuma kayan dawakin. Kuma shi ne
shugaban ‘yan barga wato (muri).
ix-
Shantali
Aikin
mai riƙe
da wannan sarauta a masarautar Katagum shi ne, rike buta idan sarki zai yi
tafiya ko rangadi domin ɗahara
ko wata buƙata
ta daban. Wannan sarauta ita ma zamani ya tafi da aikinta. wanda kusan yanzu
wanda yake riƙe
da wannan sarauta fada na iya saka shi duk aikin da ta ga dama.
x-
Barwa
Babba aikin mai riƙe da wannan sarauta
shi ne, bayar da ruwa a sarki. Wannan sarauta ta samu canji saboda zamani. Kawai
mai riƙe
da wannan sarauta yana matsayin yaron sarki ne, duk aikin da sarki ya so zai
saka shi.
xi-
Mabuɗi
Duk
wanda yake riƙe
da wannan sarauta shi ne mai kula da duk ƙofofin fada da sito
(Store) da duk wani abu da ake buɗewa
ake rufewa shi yake kula da shi. Wato wajen da ake ajiyar kayan abinci da
suturar sarki da dukiyar sarki da sauransu, amma yanzu mai riƙe da wannan sarauta
aikinsa ya kau saboda tasirin zamani. Za a iya cewa a yanzu kusan dukiyar sarki
tana hannunsa da ‘ya’yansa.
xii-
Galadima
Babban
aikinsa kula da zamantakewar mutanen gari da ba wa sarki shawara, kuma yana
cikin yan majalisar sarki. Duk wanda yake rike da sarautar Galadima a ƙasar Katagum mafi
yawa shi ake tura wa Hakimin Zaki. A da sarautar Galadima ita ce sama da ta
Waziri, amma a zamanin Ɗankauwa
(1816) ya mayar da Waziri shi ne gaba da Galadima. Wannan sarauta har yanzu ana
amfani da ita a masarautar. Bayan haka kuma tana cikin sarautun da suke zaɓar
sabon sarki.
xiii-
Maidala
Mai
wannan sarauta shi yake kula da tsaron ƙasa da kuma gidan
yari. Haka kuma, idan an naɗa
sabon sarki za a ba shi sanda shi yake ba da kwari da baka ta Malam Zaki ga
sabon sarkin da aka naɗa.
Sarautar Maidala babu wani aiki da yake da shi a fada a yanzu, sai dai sarki
zai iya saka shi kowane irin aiki ya ga dama.
xiv-
Ma-ja-sirdi
Sarautar ma-ja-sirdi babban aikinsa a
fadar Katagum shi ne, kula da yi wa dokin sarki kwaliya da ɗaura masa sirdi idan zai yi hawa.
Wannan sarauta har yanzu aikinta yana nan bai canja ba.
xv-
Ɗanrimi
Wannan sarauta tana da muhimmanci a
masarautar Katagum. Babban aikin wannan sarauta a da shi ne, kula da iyakokin ƙasa. Kuma Ɗanrimi idan an yi hawan Sallah shi ne a
hagun ɗin sarki ko da sarki zai yi magana yana yi da shi ne. kuma
yana cikin ‘yan goman sarki.
xvi-
Tafida:
Wannan sarauta a fadar Katagum tana
cikin bayin sarki. Duk wanda yake riƙe da Hakimcin Itas shi ne Tafidan Katagum.
Tafida babban aikinsa kula da shirya tafiye- tafiyen sarki da irin mutanen da
za a tafi da su, da duk wata hidima da ta shafi tafiya. Wannan ita ma zamani
yakau da aikinta.
xvii-
Kilishi
Mai riƙe da sarautar kilishi shi yake da ikon kula da duk wasu
shimfiɗun sarki da yake amfani da su, kama daga fada har zuwa
masallaci. Ita ma wannan sarauta zamani bai rage mata komai ba, wanda har yanzu
aikinsa yana nan, domin har yanzu kilishi shi yake shimfiɗa wa sarki shimfiɗa a masallaci ko a kujerar da zai zauna
a fada.
xviii-
Baraya
Mai wannan sarauta babban aikinsa a da shi
ne, raba abinci a wajen yaƙi, amma a yanzu shi ne jakada tsakani
gwamnati da sarki. Bayan haka, kuma yana cikin ‘yan goman sarki.
xix-
Ƙaura
Mai riƙe da sarautar ƙaura yana cikin masu kare sarki, wato
kula da lafiyar sarki domin kar wani abu ya taɓa shi na ƙi. A lokacin yaƙi ma su ne a gaba, shi ya sa ma ake
masa kirari da “Ƙaura ja yaƙi”. A yanzu yana cikin masu taimakawa liman in za a naɗa wani a fada.
xx-
Jakada
Mai riƙe da sarautar jakada shi ne mai kai saƙo Sakkwato ga sarkin Musulmi a zamanin da, amma yanzu wannan
sarauta zamani ya yi tasiri a kanta.
xxi-
Harɗo Mai Dawaki
Sarautar Harɗo mai dawaki, babban aikinta shi ne
kula da dawakin sarki. A yanzu wannan sarauta zamani ya yi tasiri a kanta.
xxii-
Barade
Babban
aikin mai riqe da wannan sarauta a masarautar Katagum, lokacin da za a tafi
yaqi sukan sa sulke wato rigar yanqi da janjami da xamaru kala-kala domin fita
yaqi. A lokacin hawan Sallah idan sarki ya yi hawa su Barde ne kan gaba, wato
masu shiga gaban sarki da xamaru kamar za a je yaqi. Duk wannan ana yi ne domin
kare lafiyar sarki. Shi Barade zamani ya tafi da aikinsa a yanzu.
xxiii-
Jarma
Sarautar jarma ita ma a masarautar Katagum
tana cikin dakarun sarki, wanda yana cikin masu kula da lafiyar sarki da
iyalansa.
xxiv-
Wambai
Wannan
sarauta ta wambai a yanzu amfanin ta a fadar Katagum shi ne wakiltar sarki a
wurin da bai samu damar zuwa ba. Saboda muhimmancin wannan sarauata ta wambai
akwai wani Baturen ingila da ya zo Katagum a shekara ta 1824, sai da ya fara
ganin wambai kafin su gana da sarki.
xxv-
Masu
Sarautar
masu shi ma yana cikin dakarun sarki, kuma shi yake raba masu in za a fita yaƙi. Kuma ranar Sallah shi ne mai wuce wa gaba yana kai
hakimai masu ƙasa da karaga suna gaisuwa gun sarki.
xxvi-
Sallama
Sallama shi ne mai iso inda an yi baƙo gun sarki. Zai tambaye ka abin da ya kawo ka kafin ya kai
ka gun sarki. Wannan sarauta har yanzu aikinta yana nan bai gushe ba.
xxvii-
Maga- yaƙi
Babban aikinsa shi ne kula da sha’anin
da ya shafi yaƙi, kuma ko kai wa hari a ka yi shi ne
zai jagoranta. Shi ake fara sanar wa yaƙi ya shigo gari, shi kuma ya sanar da sarki. Wannan sarauta
ita ma zamani ya yi tasiri a kanta.
xxviii-
Gado da Masu
Shi ma yana cikin manyan dakarun sarki
a zamanin da. A yanzu kuma wannan sarauta ta rasa aikinta sakamakon zamani.
xxix-
Sarkin Yaƙi:
Babban
aikinta a fada shi ne kan gaba a fagen fama wato shi ne ja gaban dakarun
rundunar mayaqa. A yanzu wannan sarauta ita ma zamani ya yi tasiri a kanta ta
fuskar kwace aikinta, a yanzu yana zaman yaron sarki ne, za a iya saka shi
kowane irin aiki ake buƙata
a fada
xxx-
Maitafari:
Wannan
sarauta aikinta a masarautar Katagum a da shi ne sanar da lokacin da sarki ya
fito daga cikin gidansa. Yana buga bindiga sau ɗaya
don sanarwar. A wannan lokaci wannan sarauta ta rasa aikinta sakamakon tasirin
zamani, sai dai ya je fada ya yi gaisuwa in da aiki a sa shi in babu kuma shi
kenan.
5.8 Tasirin
Zamani a Kan Sarautun Bayi A Ƙasar
Katagum
1. Akasari waɗannan muƙamai sun fita daga gidajensu na gado, sun zama na sha’awa.
Saboda haka, waɗanda suke da sha’awa za ka ga sun yi ƙoƙarin gani cewa an naɗa musu muƙaman da suka ga sun dace da su. Misali kamar Ɗanmaliki da Talba da sauransu.
2.
Rashin bayar wa wanda ya gaje ta. Wannan matsala ce da
zamani ya zo da ita, wanda haka ya taimaka wajen rashin ganin ƙimar sarautar a idon wasu jama’ar gari
3.
Yin watsi da wasu al’adu na gargajiya a fada, da maye gurbinsu
da na zamani. Misali kayan zama da shimfiɗu da ake amfani da su, da dai sauransu.
4.
Wasu sarautun sun rasa aikinsu, sakamakon tasirin zamani a
kansu
5.
Saboda tasirin siyasa wasu waɗanda ake ba wa sarautar ba su ma san
aikin sarautar ba a fada.
6.
Sakamakon tasirin
zamani musamman ta fuskoki da dama, saboda yanzu an daina harkar bauta da yaƙi, da kuma zuwan
Turawa, saboda yanzu mafi yawanci bayin sun ilmantu sun zama manyan mutune ta
yadda ba za su iya yin aikin bautar kamar da ba. Haka kuma, aikin gwamnati shi
ma ya taimaka wajen kawar da aikin masu riƙe da sarautun bayi
a yau. Hukuma ta samar da ma’aikata na musamman a fadoji maimakon a da bayi ne
ke yin aikin. Misali, kamar aikin da Jakada da ‘yan barga da sauransu suke yi,
yanzu babu shi a fada. Abin bai tsaya nan ba har abin da ya shafi Dogarawa aka
maye gurbinsu da ‘yan sanda, yanzu duk hukuma ce take kawowa.
5.9 Naɗewa
Wannan shi ya kawo mu ƙarshen babi na biyar. A nan mun ga yadda tsarin sarauta yake
a fadar Katagum da muhimmancin sarautun bayi da ayyukansu a fadar Katagumt,
yadda muka fahimci cewa muƙaman da bayi ke riƙe wa a fada suna taka muhimmanci a fada. Haka kuma, suna
taimakawa sarakuna wajen gudanar da mulkinsu ya tafi dai dai, ba tare da tangarɗa ba.
KAMMALAWA
Shimfiɗa
A wannan babin za a taƙaita binciken gaba ɗaya, wato tun daga babi na farko har
zuwa na ƙarshe. Sannan aka daddale sakamakon
binciken, inda aka ga yadda aikin ya tabbatar da hasashen binciken, wato
“Sarautun Bayi A Ƙasar Katagum.”
Taƙaitawa
Wannan bincike da aka yi mai taken
“Sarautun Bayi A Ƙasar Katagum” kasancewar mafi yawan
al’umma tana da irin hanyoyin da take ganin sun fi dacewa su gudanar da
rayuwarsu na yau da kullum. Irin waɗannan hanyoyi su ne suka taru suka zama
al’ada, waɗanda suka sha bambanta a tsakanin wannan al’umma zuwa wata.
To, amma yanayin zamantakewa kan haifar da wasu al’adu, idan aka sami cuɗanya a tsakanin al’ummomi daban-daban a
kan sami musayar irin waɗansu al’adun. Sarauta tana haifar da
kyakkyawar zamantakewa a cikin al’umma. Idan zamantakewa ta sami tauyewa,
wannan na iya kai al’umma ga lalacewa baki ɗaya. Kazalika, jama’a ko rukunin al’umma
kowa na iya ba da tasa gudumawa wajen gudanar da shugabanci ko iko (wato tsarin
sarautarsu) Haka ya sa sarautun bayi suna da muhimmiyar rawa ko gudumuwa da
suke bayar wa a masarautar Katagum. Wannan aiki ya binciko yanayin da ƙasar Katagum take, wato farfajiyarta a da can da yanzu. An
bayyana asalin mutanen Katagum da kuma ƙasashen da take mulka, da taƙaitaccen tarihin sarakunan masarautar, da masu zaɓen sarki a fadar Katagum da yaƙe- yaƙen masarautar, da kasuwar bayi da aka
gudanar a yankin. An kuma binciko fitattun bayi da aka taɓa samu a yankin. Ire-iren sarautun bayi
da ake da su a ƙasar Katagum da irin rawar da suke takawa
wajen ci gaban yankin da tasirin masu rike da sarautun.
A wannan babin, an yi bayanai a kan
bauta a ƙasar Hausa yadda aka nazarci zuwan
Larabawa da Turawa ƙasar Hausa, daga ina bauta ta samo
asalin da kuma yadda gurbin bayi suke a masarautun ƙasar Hausa, da hanyoyin da ake samu bayi da ‘yan tasu da
cinikin bayi a ƙasar Hausa yadda aka gudanar da shi, da
haramta shi. Daga ƙarshe an yi nazarin sarautun bayi a ƙasar Katagum, manufa irin tasirin da tsarin da yanayi
sarautun, misali ta fuskar kula da lafiyar sarki da iyalansa da al’ummar gari,
saboda muhimmancin su suna cikin masu zaɓen sarki a fadar Katagum.
Sakamakon Bincike
Wannan bincike mai suna “Sarautun Bayi
A Ƙasar Katagum”, ya yi nasarar gano cewa,
Sarautun bayi suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma da masarauta
baki ɗaya. An ci nasarar gano hakan ne ta hanyar nazartar
littattafai, tare da ziyartar waɗanda suke da alaƙa da sarautar, da tattaunawa tare da iyayen ƙasa ta la’akari da abin da suka faɗi a kan sarautar.
·
Binciken ya gano
akwai ’ya’yan bayi da suka zama Sarakuna a Masarautar Katagum a yau.
·
Binciken ya gano cewa bayi suna da ƙima a masarautar Katagum, da ma ƙasar baki ɗaya. A dalilin ƙimar su da darajarsu har mulki ake ba su na riƙon ƙasa. A yau haka abin yake domin sun
zama ‘ya‘ya masu ‘yanci, ta yadda babu mai tsangwamar su.
·
Haka zalika, binciken ya gano sarautun Bayi sun rikiɗe sun zama kowa yana sha’awa sakamakon
sun zama manya, haka kuma su ne Attajiran ƙasar. Wannan ya sa kowa yana sha’awar waɗannan sarautun da zarar an ji ta faɗi, kowa so yake a ba shi ita. To, akwai
irin waɗannan da dama.
·
Binciken ya gano
wasu sarautun a ƙasar
Katagum na bayi ne, amma a wasu masarautun na ‘ya‘yan Sarki ne. Misali,
sarautar Wambai a Katagum ta bayi ce, amma a Kano ta ‘ya‘yan Sarki ce. Haka
kuma, abin yake Sarkin Bai da Sarkin Dawaki a Sakkwato ta bayi ce, amma a
Katagum ta ‘ya‘yan sarki ce.
Shawarwari
Ya kamata dukkan hakiman ƙasar Katagum da masarautar kanta, a ƙirƙiri wata sarauta. Wanda aikinta zai
kasance kula da tarihin ƙasar da kuma masarautar kanta. Misali
yanzu za a tarar an zo neman wani abu na tarihi da kyar za a samu, amma idan
akwai wanda fada ta tanada na musamman sai a tura mutum gunsa.
Haka
kuma, ya kamata kowace masarauta ta yi ƙoƙarin ba wa wanda ya gada sarautar
gidansu. Hakan yana kawo zaman lafiya da kuma ƙara wa sarki daraja da ƙima a idon jama’ar gari.
Haka
kuma, idan ya zama dole sai sarautar ta fita, to! A ba wa mutumin kirki, domin
mai riƙe da muƙami shi yake ƙara wa sarautarsa daraja da ƙima a idon jama’a.
Naɗewa
Wannan shi ya kawo mu ƙarshen aiki baki ɗaya. A nan mun ga muhimman abubuwa game
da ƙasar Katagum da kuma sarakunan Katagum,
da irin rawar da suka taka a wajen haɓakar Daular Usmaniyya da kuma fito da
masarautar Katagum a fili ƙarara. A nan aka taƙaita aikin da kuma samun sakamakon bincike, yadda muka
fahimci cewa muƙaman da bayi ke riƙe wa a fada suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa da ɗaukaka al’adaun Hausawa da kuma
taimakawa sarakuna wajen gudanar da mulkinsu ya tafi dai dai, ba tare da tangarɗa ba. Wanda haka ya tabbatar mana cewa
lallai in babu bayi a fada babu wani abu da zai iya gudana a fada, musamman dangane
da sha’anin tsaro.
MANAZARTA
Abubakar, A. Y. (1974). “The
Establishment and Development of Emirate Government in Bauchi 1805-1903” kundin
digiri na uku, Sashen Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Abubakar, A. S. (2008). “Sarautar Sallama da ta Sarkin Hatsi
a Fadar Kano” kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero Kano
Abdullahi, U. M. (2011). Programme Event For Turbaning Of
Malam Usman Mahmood Abdullahi As Galdiman Katagum And Distric Head Of Zaki On
Saturday 5th Febuary 2011
Adamu, M. (1968). “A Hausa State In Decline: Yawuri In
Nineteenth Century” M.A Thesis. Zaria: Department Of History, Amadu Bello
University.
Adamu, M. (1974). “The Hausa Factor in West African History”. Ph’D. Thesis. Birmingham: Universiy,
UK.
Adamu, M. (1978). The Hausa Factor in West African History. Zaria: Ahmadu Bello Universiy Press.
Adeleye, R. A. (1971). Power And Develomacy In Northern
Nigeria, 1804-1906, Sokoto Caliphate And Its Enemies, Londom Longman
Argungu, A. I. (2017). “Tasirin Sauye
–sauyen Mulki ga Sarauta a Ƙasar Kabin Argungu (1803-2010). Kundin
digiri na biyu. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Alhassan, H. Ibrahim, U. Zarruk, M. R. 1(982). Zaman Hausawa. Lagos: Academy Press Limited. Bugu na
biyu.
Aliyu, M. (2013). Masarautar
Katagum da Kewaye. Kano, Digital Computer Center
Alkali, M. B. (1969). “A Hausa Community In Crisis: Kebbi in
The Nineteenth Century” M.A Thesis. Zaria Department Of History, Amadu Bello
University.
Augie, A. R (1984). “ The Gobir Factor In The Social And
Political History Of The Rima Basin C.1650 to 1808 A.D. Ph’D. Thesis. Zaria:
department Of History, Amadu Bello University.
Azare, G. D. (2012). Central
Primary School, Azare: The Premier School In Katagum Emirate. Azare: Ofas
Communication
Babani, A. T. (2017). Programme Event for Turbaning Of
Alhaji Abdullahi Tela Babani As Madakin Katagum On Saturday 15th
April 2017 at Emir of Katagum Place, Azare, Bauchi State.
Barnoma, M. T. (2013). Gaɗau In Brief Katagum Emirate. Ita/Gaɗau Local Government area, Bauchi State.
Bello, A. S. (2003). “Tasirin Tsarin Sarautar Gargajiya ta
Hausawa a kan Masarautar Ilorin” kundin digiri na biyu Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.
Bunza, A. M (2017). “Slave in Hausa Cultural Perspectives”
Takardar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa juna Sani na Ƙasa da Ƙasa, Wanda Sashen Nazarin Tarihi da
Tsaro na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Adu’a, Katsina
CNHN (2006).
Kamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano.
Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Crowder, M.
(1981). West Africa Under Colonial Rule. London:
Frank Cass and Company Limited
Ɗanmaigoro,
A. (2013). “Karamci Sarakuna A Cikin Littafin Ruwan Bagaja” Ruwan Bagaja In
Perspectives eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013)
Humanities In The Sub Saharan World Unicairo/ Umyuk Special Research in
Humanities, Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Gaya, A.M (2012).
Tasirin Siyasa A Masarautun Gargajiya, Musamman A Masarautar Sakkwato da
Katsina Da Kano Da Daura Daga 1960-2010 Kundin PhD, Kano :Jami’ar Bayaro.
Gobir, Y. A (2016).
Gobir Wani Jigo A Ƙasar Hausa:
waiwayon Tarihi da Diddigin Masarautun Gobir. 1st International Conference On The Hausa People,
Language And History (Past, Present, And Future) Organized
by, Kaduna: Nigerian Languages And Linguistics Kaduna State University.
Gusau, S.M. (1992). Sarautar
Matawalle da Tarihin Matawallen Gusau Alhaji muhammad lawal Mande, Kano: Zed
Press Nig. Ltd.
Hammani, M. D. (1975). “Adar, The Tuareg And Sokoto: Relation
of Sokoto with The Hausawa And Tuareg During The 19th Century” Sokoto Seminar Paper
Hari, P.G (1932). Sokoto Provincial Gazzeter. Unpublished.
Hussaini, I. (2008).
Gwarzayen Masarautar Kano, Kano: Cane Computer and Publishing services
Ibrahim, Y. Y. (1979). “Oral Art and the Socialisation
Process: A Socio-folkloric Perpective of Initiation From Childhood to Adult
Hausa Community Life” Volume I. PhD thesis. Kano: Jami’ar Bayero.
Ibrahim, Y. Y. (1979). “Oral Art and
the Socialisation Process: A Socio-folkloric Perpective of Initiation From
Childhood to Adult Hausa Community Life” Volume I. PhD thesis. Kano: jami’ar
Bayero.
Isa, M. (2000). Tarihin
Garin Azare. Offas Communication
Isa, S. S. (2014). “Rumbun Kalmomin Sarauta da Amfaninsu Ga
Al’umma” Garkuwan Adabin Hausa: A Festschrift In Tribute To Abdulkadir Ɗangambo. Zaria:
Ahmadu Bello University Press.
Isma’il, M. N. (1986). “Tsarin Sarautar
Gargajiya jiya da yau” Kundin digiri na ɗaya. Kano: Jami’ar Bayero.
Kafinhausa, A.U (1997). “Kirari Sarakuna da garuruwa” kano:
Harsunan Nijeriya, Vol; XVIII
Khalil, N. W. (2006). Bayi
A Gidan Dabo; Tarihin Shamakin Kano Inuwa Ɗan Sarkin Zage da Sauran Manyan Bayin
Sarki. Kano: Gidan Dibino Publishers
Magaji, A. da wasu (2003). “Gudumuwar Sarakuna wajen Haɗa Kan Al’umma” Cikin west African
Journal of language, literature And Criticism Vol.2, Kano: Bayero University
Malumfashi, I.A. (2009). Adabin
Abubakar Imam. Sokoto: Garkuwa Media Service, Nigeria.
Mani, A 1966. Zuwan
Turawa Nigeria Ta Arewa. Zaria: NNPC
Maradun, M. S. (1992). “Sarautar Gargajiya a Ƙasar Hausa, Nazarin Muƙaman Sarautar Gargajiya a Sokoto”.
Kundin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Mashi, A. A.
(2013). “Al’adun Hausawa A Tsarin Sarautar Gargajiya a Yau” Excerpts of
international Seminar on Taɓarɓarewar
Al’adun Hausa (the Deterioration of Hausa culture) Organized by Katsina State
History and Culture Bureau, in Collaboration with: Umar Musa Ýar’adua University,
Katsina. June, 2013
Memorandom
of Request For The Katagum State (2000)
Mode, A. (2010). “Sarauta da Muƙamai a ƙasar Hausa: Nazari a kan Fadar Sarkin Musulmi”
kundin BA, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Muhammad, A. B. (1991). “Tasirin Zuwan Turawa kan Sarautun
Gargajiya na ƙasar
Hausa: Tsokaci kan Sarautar Kano, kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero
Muhammadu, H. M (1987). Tasirin Sarautar Hausawa bisa Ƙabilar Urawa da Kamukawa A Ƙasar Kirangwama Ta jahar Neja. Kundin
Digirin farko a Sashen Nazarin harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Nadama, G. (1977). “The Rise And collapse Of A Hausa State:
A Social And Economic History Of Zamfara” Ph’D Zaria: History Department, Amadu
Bello University.
Sale, A (2004). Bicentenaty
of the Sokoto Coliphate 1804- 2004 (Jawaben Cika shekaru Metan Da Kafa Daular
Usmaniyya A Ƙasar
Katagum). Azare: Imad Network Graphics
Sale, G. (2006). “Nazarin a kan Sarautar Shamaki da Ɗanrimi a Masarautar Kano” kundin MA,
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero
Sale, M. (2012). Matsayin Jakadiya a Al’adun Masarautar
Katagum. kundin BA Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sale, M. D. (2016).
Tarihin Asalin Sarautar Waziri a Katagum. Azare: White shop Computer
Sami, S. (2004). Hausa Traditional Titles in Northern Nigeria. Zuru: Na-Hweraka Resources Ltd
Sarkin Gulbi, A. (2000). “Sarautun Gargajiya a Ƙasar Gumi Jiya da Yau” kundin BA.
Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sarkin Gulbi, A. (2016). “Dabarun Tsaro A Ƙasar Hausa: Bindiddiginsu A Masarautar
Gummi”. 1st International Conference On The Hausa People, Language
And History (Past, Present, And Future) Organized by
Kaduna: Nigerian Languages And Linguistics Kaduna State University,
Smith, M. G (1957).
“The Hausa System of Social Status” In Africa Vol. XXVII. No. 1.
Toronkawa,
M. U. (2008). Kyakkyawar Safiya Tarihin
Rayuwar Maigirma Sarkin Kabin Yabo Alhaji (Dr.) Muhammad Maiturare II. Sokoto
State Corporation.
Tsoho, S. M (2013). “Kirarin mata a Fadar Sokoto” kundin MA,
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Usman, B.B (1985). “Fadanci a ƙasar Hausa” Kundin BA. Zariya: Jami’ar
Ahmadu Bello.
Usaman, Y. B (1972). “Some aspects of The External Relations
of Katsina Before 1804” Savanna Vol. I No. 2.
Usman, Y.B. (1981). The
Transformation of Katsina (1400-1883). The Emergence and Overthrow of the Sarauta
System and Establishment of the Emirate. Zaria: ABU Press
Wadata, A.U.F. (2009). Tarihin
Kafuwar Masarautar Katagum. Kano: Triumph Publishing company Ltd. Gidan Sa’adu
Zungur,
Waya, Z. I (2000). Kano da Masarautarta jiya da yau. Zaria:
Gaskiya Corporation Limited
Waziri, U.
D. (2013). “Tasirin Sarautun Hausawa a Kan Na Ƙabilun
Kare kare da na Sayawa” Kundin
MA, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Yahaya, Y. I (1988). Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce- Rubuce
Cikin Hausa. Zaria NNPC
Zungeru, I. M. (1993). “Sarautun Gargajiya da Gudummawar da
suke bayarwa a ƙasar Hausa”. kundin BA, Sakkwato: Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Zuru, M. A. U (2011). Bayanin Sarautun Gargajiya Na Fada. Zuru: Hilton computer Production
Mutane da Aka Yi Hira da Su
1-
Alhaji Ahmad Muhammad Burga, a kofar gidansa. Yana da
shekara ɗari da ashiri a duniya. Da misalin ƙarfe 10:48:28pm. 21st , Sept 2016
2-
Muhammad Abdulƙadir, Dagacin Itas a fadarsa, yana da
shekara tamanin a duniya. An yi hira da shi da misalin ƙarfe 12:38:28pm. 16, Nov 2016
3-
Galadiman Gamawa Dagacin Cikin Gari. Yana shekara da sitti
da biyu, mun yi hira da shi a fadar Hakimin Gamawa ƙarfe 11:27:00am, 21st, Dec 2016.
4-
Muhammmad Abubakar, Aminu Sale, College of Education Azare.
History Department hira ta wayar salula. Yana da shekara arba’in da uku, da
misalin ƙarfe 11:08:30am 11, Aug 2016
5-
Maiduna, hira a shagonsa na cikin kasuwa Azare, yana da
shekara Hamsin da bakwai a raye, an yi hira da shi ƙarfe 04:46:38pm, 17 Nov, 2016.
6-
Sakataren cikin gida na Itas, Malam Aminu. Yana da shekara
ashirin da biyar, an yi hira da shi a cikin fadar hakimin Itas da ƙarfe 01:24:02. 16 Nov, 2016
7-
Turakin Katagum Muhammadu Gaɗauji, a gidansa da ƙarfe 02:28:12pm. 10 Nov, 2016.
8-
Abubakar Bangon Sarkin Gobir, a gidansa da ƙarfe 12:02:14pm, 14 Jan, 2017
9-
Kauran Katagum a ƙofar gidansa, yana da shekara arba’in
da takwas an yi hirar da misalin ƙarfe 09:44:14pm 11 Feb, 2017
10-
Harɗon Katagum Alhaji Muhammadu Gabi, yana
da shekara sittin da ɗaya a duniya, an gabatar da hirar a
gidansa da misalin ƙarfe 04:00:08, 16 feb, 2017
11-
Hakimin Sakuwa, Muhammadu Mustafa Bunni Abdulƙadir a gidansa da ke Azare, yana da shekara arba’in da tara
a duinya. Hirar ta kasance da ƙarfe 11:28:08, 30 Nov, 2016
12-
Hakimin Itas, Tafida Muhammadu Sagir Abdullahi a gidansa da
ke Azare, yana da shekara arba’in da tara. 02:30:08, 20 Dec, 2016
13-
Wazirin Gaɗau, yana da shekara hamsim da huɗu a duniya, an yi hirar a gidansa da ke
Gaɗau da misalin ƙarfe 11:00:08, 07 Jan, 2017
14-
Tafidan Azare, Shehu Azarema Mustafa yana da shekara arba’in
da takwas a gidansa da misalin ƙarfe 05:20:38, 08 March, 2017.
15-
Alhaji ado Itas, yana da shekara arba’in da ɗaya a raye a duniya, an gabatar da
hirar ta wayar salula ranar 7/01/2017 da misalin ƙarfe 05:20pm na yamma
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.