𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum. Malam miji ne baya kyautatawa matarsa har ma wani lokaci ya zage ta,
ita kuma sai ta rama. To meye hukunci wannan auren?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
wa
alaikissalam. dan ya zageki bai kamata ki ramaba, kamata ya yi kiyi masa nasiha
idan nasihar zata kwanto wata fitinar saiki nemi na gaba dashi ya yi masa Faɗa,
amma bai kyautu mace ta dinga zagin mijinta dan ya zageta ba, Zagin miji ko
cutar dashi da harshe, wannan yana daga cikin manyan laifuka a Musulunci (wato
Kaba'ira).
Manzon Allah
ﷺ ya lissafa matan da suke yin haka a cikin Manyan 'yan wuta. (ya Allah ka
tsaremu).
Manzon Allah
ﷺ ya ce: Masu zagegeniya guda biyu toh zunubin yana komawa kan wanda yafarayi.
Amma kuma karamci shi ne kada ki rama idan aka zageki. Musamman tsakanin Miji
da Mata idan mijin ya zageki toh kada kirama wannan shi ne karamci domin su
Mutanen kirki basa yin zagi kamar yadda Annabi ﷺ yafaɗa. Toh kuma idan aka
zagesu basa ramawa domin Allah ta'ala shi ne da kansa Yace kuyi haƙuri domin
yin haƙurin shi ne alheri ga masu haƙuri. Amma lefin wanda yarama zagi bekai
lefin wanda yafara yin zaginba. Amma kuma lada da falalar wanda aka zageshi ya
yi haƙuri be ramaba toh ba a kwatanta darajar me haƙurin akan wanda yafara yin
zagin.
Imamul
Bukhari kansa ya buɗe babi makamancin haka a cikin littafinsa Al-adabul mufrad.
Allah na masani
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.