𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam Mene
ne Hukuncin Matar Da take Zagin Mijinta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله رب
العالمين.
Idan mace
takasance tana cutar da mijinta da zagi da cin mutunci da munanawa, wajibi ne
ya zaunar da ita yai mata nasiha, ya tsoratar da ita, ya bayyana mata haɗarin
laifin datake aikatawa na zaginsa, musamman saboda miji shi ya fi can-canta ta
kyautata masa, kamar yanda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce:(Da ya
halatta wani yaiwa wani sujjada dana umarci mace taiwa mijinta sujjada) Abu
dauda(2140) da turmuzi (1159) Albani ya ingantashi a cikin sahihu Abu dauda.
saboda tsananin haƙƙin biyayya da kyautatawa
dake kan mace ga mijinta.
Ya kamata
mijinta yabi matakan ladabtar da ita wanda Allah ya ambata a cikin alƙur'ani
nayi mata wa'azi da tunatarwa, da kauracewa, da duka wanda bamai fasa jiki ba.
Idan
yaihakan duk bai amfaniba, yahadata dawani salihi cikin danginta yaimata
nasiha, saboda kiyaye zurriya dakuma lura da haƙƙin 'ya'ya idan akwaisu, Allah
madaukakin sarkin ya ce:
(الرجال قوامون
على النساء بما فضل الله بعضكم على بعض وبما أنفقوا من أموالهم فالصا لحات قانتات حافظات
للغيب بما حفظ الله والاتي تخافون نشوزهن فعظوهن وهجروهن في المضاجع واضربوهن فإن أطعنكم
فلا تبغوا عليهن سبيلا إن الله كان عليا كبيرا)، النساء 34
Mazaje sune
shugabanni akan matayensu saboda Abun da Allah yafifita sahinsu akan sashi,
saboda abun da suke ciyar damatayen nasu daka dukiyoyinsu, Nutsatstsiyar mace
saliha tagari ita ce, tsayayya akan dokokin Allah dana mijinta, mai kiyaye
mutuncin mijinta da dukiyarsa idan baya nan, da abun da Allah yakiyayeta waɗanda
kukaji tsoran fandarewarsu kuyi musu wa'azi ku ƙaurace musu awajan kwanciya
kudakesu, idan sundawo sun yi biyayya akan abun da suke saɓa muku sun daina,
kada kuce zaku bijiro dawata hanya ta cutarwa agaresu, lallai Allah ya kasance
madauki mai girma.
Daka wa'azin
dazai gabatar mata, shi ne yabayyana mata girman zunubin dake kanta na saɓawa
mijinta, da abun da Allah yatanadar mata na lada gwaggwaba idan tabi mijinta
takyautata masa.
Idan ta amsa
wa'azin yai mata tasiri takuma dawo tadena saɓa masa, wannan shi ne abun da ake
nema, idan kuma taci gaba da cin mutunci dazaginsa darashin biyayya, Anan babu
lafi yasaketa dan babu bukatar cigaba dazama da irin wadannan kangararrun
matan.
Malamai sun
ambaci saki yana iya zama halal yayinda bukatarsa takama, saboda mugun halin
mace, dakuma munana zamanta damijinta, da cutuwar da miji yake da ita, ba tare
da faruwar wani dalili daka gareta ba, Almugni (10/324).
Saboda haka
hukuncin matar datake zagin mijinta da saɓa masa, shi ne ita mai saɓo ce tana
cikin fushin Allah madaukakin sarki, wajibi ne ta gaggauta tuba zuwaga Allah,
takuma nemi yafiya daka gurin mijinta, lallai kasncewarta cikin wannan mummunan
aiki yana janyo mata fushin Allah dabala'in dabatasan karshensaba.
Wallahu
A'alamu.
سبحانك اللهم
لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.
Tambaya da
Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai
+2348123432272
+2348163731622.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.