Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Mazinaci Ne, Zan Iya Ƙaurace Masa A Shimfida ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Allah Ya Haɗani da miji mazinaci, shin in na daina haɗa shinfida dashi dan gudun ɗaukar wani ciwo inada laifi?.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum as salam, abin da ya fi shi ne ki yiwa magabatansa bayani, don su tsawatar masa ya daina, in kuma kin tabbatar ya ɗau cutar AIDS kina da damar da za ki je wajan Alkali don ya raba auren, tun da musulunci ya yi umarni da tunkude cuta gwargwadon iko, in har miji yana ciyar da matarsa to ya wajaba ta amsa kıransa, wannan ya sa ɗaukar matakin hana shi kanki zai iya jawo muku rigima, sanya Alkali ko magabaci a hukuncin shi ne daidai.

Allah shi ne mafi Sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments