Ticker

6/recent/ticker-posts

Meya Sa Aljanu Suke Shiga Jikin Mutane ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, me yake kawo aljanu jikin Ɗan adam, Kuma meza a yi a rabu da su?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, sakaci da ibada da zikirori na daga cikin abubuwan da suke kawo aljanu, duk mutumin da yake yawan azkar yake kuma kiyaye dokokin Allah, da wuya aljani ya shiga jikinsa, Saboda şu zikirorin safe da yamma da na kwanciya bacci da shiga banɗaki da fitowa suna kariya daga Shaiɗanu.

Saidai ko da mutum yana da nagarta, aljani yana iya shiga jikin mutum ta hanyar sihiri ko kambun baka, ko yawan fushi.

Ayoyin Alƙur'ani na korar aljani daga jikin ɗan'adam, musamman Suratul Bakara da Kula'uzai biyu da ayatul kursiyyu da surorin tauhidi guda biyu.

Allah ne mafi sani.

 Dr jamilu Zarewa.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments