𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalumu alaikum, Allah ya karawa
malam kaifin basira, Malam ina so ka taimaka mun ina neman shawara da mafita a
garaka, jiya na cika wata ɗaya da aurena amma wallahi tunda mukayi aure banajin
daɗin saduwa da matana itama jiya take fadamun cewa batajin daɗin saduwa dani,
tana yarda danine dan batason saɓamun amma wallahi tana sona kuma ba ta tunanin
zata iya rabuwa dani, kuma nima haka nakeji wallahi nafijin daɗin na rinka
kallonta da ace ina saduwa da ita, dan haka nace Bari na kawo kukana ko zan
samu maslaha, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To Shawarata ta farko ita ce ku
ziyarci babban asibiti domin ku yiwa likitan bangaren haihuwa (Ganaecologist)
bayanin abinda ke damunku. Ina zaton in Shã Allahu za ku samu shawarwari daga
garesu.
Bayan haka kuma daga cikin abubuwan
da za ku kula dasu akwai :
1. Gabatar da wasanni sosai kafin
saduwa. Sannan da nuna kulawa da Ƙauna atsakanin juna (shima yana Ƙara nishadi
atsakanin ma'aurata).
Kada ya zamto baka da lokacin da za
ka janyo matarka jikinka kuyi hira ko tattaunawa da juna ko ka sumbaceta
atsawon wuni baki ɗaya, sai dai in saduwa za ka yi da ita.
2. Abu na biyu idan tana da
matsalar ciwon sanyi yana da kyau ku maganceshi domin samun nishadi atsakaninku.
3. Hakanan shafar Aljanu , musamman
jinnul ashiƙ (namijin dare) idan yana tare da mace yakan ɗauke mata sha'awa,
yakan hanata jin daɗin jima'i kuma ya sanya mijinta ya kasa samun gamsuwa da
ita.
Manyan alamominsa sun haɗa da ciwon
kai, faduwar gaba, mafarkin saduwa, ko firgita, ko kasala wajen yin ibada, da
sauransu.
WALLAHU A'ALAM
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za
ku iya bi ta Links ɗin mu...
MATSALAR RASHIN JIN
DAƊIN SADUWA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mallam shin yana
yuwuwa a ce ana saduwa da na ce amma ta ce bai san saduwa ba ne, ma'ana ba ya
jin daɗin saduwa ɗin ko ta ce kwatakwata
bai san shigarta ake yi bah, ya ɗauka shafawa neh kawai mun gode mallam.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Ba zai yiwu ba a ce Namiji
ya Sadu da mace ko da a mafarki ne, Amma wai baiji daɗi ba. Sai dai idan
Mace Tana da Matsalar Sanyi (infection), Domin idan Mace Tana da infection,
yana ɗauke mata jin daɗin Jima'i, wani
lokacin Ma Sai dai tana jin Zafi, ko kuma idan tana da Matsala irin na Bakin
Aljani (Jinnul Ashiƙ). shi ma yana Ɗaukewa Mace sha'awa
kwata-kwata.
WALLAHU A'ALAM
ƘARIN BAYANI
Tambaya:
Matsalar Rashin Jin Daɗin Saduwa
Assalamu Alaikum Malam. Shin yana
yiwuwa a ce namiji ya sadu da mace amma bai ji daɗin saduwa ba? Wata mace ta ce
kwatakwata bai san yadda ake saduwa ba, yana ɗauka shafawa ake yi kawai.
Amsa:
Wa’alaikumusalam wa rahmatullahi wa
barakatuhu.
Abin da kike tambaya ba shi da
yiwuwa a hakikanin gaskiya idan saduwa ta kasance cikakkiyar saduwa tsakanin
namiji da mace, domin jin daɗin saduwa wani yanayi ne na dabi’a wanda ke fitowa
daga haɗuwar motsin sha’awa na jiki da kwakwalwa. A lokacin kusantar aure,
namiji da mace suna fuskantar sha’awa wadda take motsa jiki da kwakwalwa a
lokaci guda, wanda ke haifar da jin daɗin saduwa. Idan har mace ta ce ba ta jin
daɗi ko ba ta gane yadda ake shigarta, yawanci hakan yana nuna akwai matsala a
lafiyarta ko wani yanayi na waje da ke tasiri a jikinta.
Daya daga cikin dalilan da ke
haddasa rashin jin daɗin saduwa shine matsalar sanyi ko infection a farji.
Idan mace tana da cuta ko infection, wannan na iya rage jin daɗi, haifar da
zafi ko rashin nishaɗi, kuma a wasu lokutan zai iya hana ta jin daɗin kusantar
aure gaba ɗaya. Hakanan, wasu malamai suna bayyana cewa akwai wani yanayi na
ruhaniya da ake kira Jinnul Ashiƙ (Aljanin Soyayya) wanda ke iya shafar
mace ta yadda take ɗaukewar sha’awa ko jin daɗi yayin saduwa. Wannan yana nuna
muhimmancin yin addu’a, tsafta, da roƙon kariya ga Allah kafin kusantar aure.
A karshe, yana da kyau ma’aurata su
fahimci cewa rashin jin daɗi a farkon aure ba laifi bane kuma ba abin kunya
bane. Yana da muhimmanci a fara saduwa cikin hankali da tausayi, a kula da
tsafta, a yi amfani da man shafawa idan ya cancanta, sannan a ba juna lokaci da
haƙuri har jikinku ya saba da junanku. Idan har matsalar ta ci gaba ko ta
tsananta, ya kamata a tuntuɓi likitan mata don a duba lafiyar farji da jiki
gaba ɗaya domin tabbatar da cewa babu cuta ko wani yanayi na lafiya da ke
haddasa zafi ko rashin jin daɗi.
Wallahu A’lam.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.