Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafitar Mata 3 - Mafi Yawan Mata Suna Cikin Wuta - Dalili Na 4 - Kamanceceniya Da Maza

Mafitar Mata 3 - Mafi Yawan Mata Suna Cikin Wuta - Dalili Na 4 - Kamanceceniya Da Maza

Mace ta yi kaman-ceceniya da maza ta hanyar sutura ko kwaikwayo yana daga cikin manyan zunubai da musulunci ya tsawatar a kansu.

 Kaman-ceceniya kamar ta sigar magana ko kayan sawa ko sai-sayen gashi irin na maza ko wanin haka, yana jawowa mace shiga wuta.

 Daga Ɗan Abbas (R.A) Ya ce:

Manzon ALLAH {s.a.w} ya la'anci mata-maza da kuma maza masu kwaikwayon mata.

 Abu Huraira (R.A) Ya ce:

Manzon ALLAH {s.a.w} Ya la'anci namiji da yake sa kayan mata da macen da take sa kayan maza.

[Abu Dawud].

Waɗannan hadisai suna nuni da yadda aka la'anci mata masu saka kayan maza, ko mata masu kwaikwayon maza, ko mata masu yin murya irinta maza da sauransu.

 Wannan kaman-ceceniyar da sukeyi da maza yana daga cikin abinda yake jawowa mata shiga wutar jahannama.

 Akwai hanyoyi da yawa da mata suke kwaikwayon maza, masuyi sunsan kansu, saboda haka kuji tsoron ALLAH ku daina domin kuɓutar da kanku daga shiga wutar ALLAH.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanmu.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments