DALILI NA 5
*****
Daga cikin abinda yake jawowa mata shiga wuta shi ne bayyana tsiraici, tsiraici kuwa shi ne bayyana abinda ALLAH TA'ALAH ya yi umarni a suturce na ado kyau in ba ga muharrami ba.
Manzon ALLAH {s.a.w} yana cewa: Nau'o'i biyu
daga '‘yan wuta ban gansu ba, sun nutse a wuta.
Wasu mutane masu bulalu kamar jelar saniya
suna dukan mutane dasu.
Da wasu mataye masu tufafi, amma haƙiƙa
matsiraita ne, karkatattu masu karkatarwa, kawunansu kamar toron raƙumi, ba za
su shiga aljannah ba, bama za suji ƙamshin ta ba, kamar anajin ƙamshinta daga
tafiyar kaza da kaza.
Wannan hadisin
yakawoababe guda biyu dake jefa mata wuta, wato shiga ta tsiraici, da kuma wani
da akeyi da gashi a ƙeya ya yi tudu, (wato acuci) wannan acucin shima yana kai
mace ga shiga wuta.
Umayyatu '‘yar Rafikatu ta zo wajen Manzon
ALLAH {s.a.w} tana yi masa mubaya'a akan musulunci,
Sai ya ce:
Zanyi mubaya
dake akan ba zakiyi shirka da ALLAH ba, ba zakiyi sata ba, ba za kiyi zina ba,
ba zaki kashe ɗanki ba don tsoron talauci, ba za ki zo da wata ɓarna ba, da
zaki ƙirƙireta da hannunki ba, ba zakiyi kururuwar mutuwa ba, ba zakiyi tsiraici
irin tsiraicin jahiliyyar farko ba.
[Ahmd ne ya
rawaito shi]
Lura da yadda
Manzon ALLAH {s.a.w} ya haɗa tsiraici da manyan laifuka irinsu shirka da zina
da sata, to lallai saka kaya masu matse jiki wanda suke nuna komai na jikin
mace, wanda suke kama jikinta yana kaita ga shiga wuta.
Haka kuma kururuwa da mata keyi idan akayi
mutuwa suyita ihu sunata kuka, watama tana faɗuwa ana ɗaukarta, wata kuwa tana
suma, wannan shima yana jawowa meyinsa shiga wutar ALLAH.
Bayyana tsiraici kuwa ya haɗo da saka turare
mai ƙarfi a fito waje, ko man shafawa mai ƙamshi a fito waje, sai kuma saka
kaya masu bin jiki, masu fito da surar mace ko da kuwa masu kauri ne, da kuma
kaya masu shara-shara.
Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce: Duk sanda mace ta
saka turare ta fita wajen mutane don aji ƙamshinsa, to ita mazinaciya ce ga
kowanne ido daya ganta.
Ma'ana duk
wanda yaganta za a rubuta mata laifin zina, ga duk mutum ɗaya daya kalleta.
Shigar banza, saka kaya masu kama jiki, masu
fito da surar mace suna jawo mata tsinuwar ALLAH kuma suna jawo mata shiga
wutar ALLAH.
Haka kuma yin acuci da gashi wato a cure
gashin a ƙeya ya yi wani tudu shima wannan yana kai mace ga shiga cikin
jahannama.
Ina kira gareku mata da kuji tsoron ALLAH ku
kiyaye saka kayan da suke bayyana surarku domin duk mai irin wannan zata haɗu
da ALLAH yana mai fushi da ita, kuma sakamakonta ita ce wutar jahannama.
ALLAH ka bamu
ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka yafe
mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.