Ticker

6/recent/ticker-posts

Haddin Luwaɗi Da Maɗigo

 An karɓo daga Ɗan Abbas (R.A) Ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

Wanda kuka sameshi yana yin aiki irin na mutanen Ludu, to ku kashe wanda ya yi da wanda akayi dashi.

 Wannan hadisi kai tsaye yana mana nuni da duk wanda aka kamashi yana luwaɗi da me yin da wanda akeyi dashi hukuncin kisa yahau kansu.

 Idan ance luwaɗi akwai ta maza akwai ta mata wato maɗigo, kuma dukkansu hukuncin su ɗaya ne.

 Na farko meyinsu ya halatta  abin da ALLAH ya haramta, hallata  abin da ALLAH ya haramta kuwa kafirci ne, duk wanda ya halattawa kansa  abin da ALLAH ya haramta ya kafirta.

 Yin luwaɗi ko maɗigo da mai dashi sana'a wannan halatta shi ne, ko da iya laifin halattawar kaɗai hukuncin kisa yana hawa kan mutum, balle kuma nassi kai tsaye ya nuna akashe meyin da wanda akeyi dashi.

 Yaku masu luwaɗi da maɗigo kuji tsoron ALLAH ku daina wannan mummunan aiki, lallai abune mai mutuƙar muni, ku tuba wa ALLAH lallai ƙofar tuba a buɗe take.

 Kada ka sake ka koma ga ALLAH kana aikata irin wannan aiki, ka yi ƙoƙari ka tuba tun anan duniya ka kuma nisanci laifin, za ka sami dacewa a gurin ALLAH.

ALLAH ka bamu ikon aiki da  abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments