Kutsen Bakin Al’adu A Kamun Amarya Jiya Da Yau A Garin Gusau

    A wannan bincike an yi nazari ne a kan yadda al’adar Kamun Amarya take a garin Gusau a da, da kuma irin yadda ake gudanar da ita a yanzu a garin Gusau. Haka kuma, an yi duba na tsanaki a akan irin sauye sauyen da baƙin al’adu suka haifar a cikin wannan al’ada ta kamun Amarya a garin Gusau da ke cikin wani yankin ƙasar Hausa, da ake kira Jihar Zamfara a yau, wadda ke da mazauni a Arewa maso yammacin Nijeriya. Sannan kuma an kawo ma’anar al’ada da ire-iren al’ada, da ma’anar aure, ire-iren Aure tare da tarihin garin Gusau, sannan da irin tasirin da baƙin al’adu suka kawo a wannan lokaci a cikin al’adun kamun Amarya.

     

    Kutsen Baƙin Al’adu A Kamun Amarya Jiya Da Yau A Garin Gusau

    Na

    NAFISA GARBA DANAZUMI

    GODIYA

       Dukkan  godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) fiyayyen talikai wanda aka aiko shi da mafifincin zance domin shiryarwa da tafarki madaidaici.

      Sannan kuma ina miƙa godiya mai ɗimbin yawa ga dukkan iyayen mu da y’an uwan mu bisa irin  goyon baya da addu’oin da suka taya mu da su.Allah ya saka da Alkhairi.

      Haka kuma, ina miƙa godiya mai tarin yawa ga Malamin da ya duba wannan aiki wato Mallam Bashir Abdullahi, tare da ba da managartan  shawarwari da gyare -gyare don tabbatar da wannan bincike ya zama mai amfani,a al’umma baki ɗaya. Haka kuma ya taka gagarumar rawa wajen ganin binciken ya kammala a cikin lokaci ba tare da ya nuna gajiyawa ba. Ina roƙon Allah ya saka masa da mafificin Alheri Amin.

        Haka kuma ina miƙa godiya mai tarin yawa ga malamai na kamar su, shugaban sashen Dr. Adamu Rabiu Bakura, Farfesa Aliyu muhammad Bunza, Dr  Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, ,Mallam Musa Abdullahi, Mallam Isah S Fada, Mallam Arabi muhammad Umar, Malam Abu-ubaida Sani da Malama Halimatu Mansur Kurawa.  ma sauran waɗanda ba’ a ambaci sunayen su ba duk ina mika godiya ta gare su.            

         Haka zalika ina miƙa godiya ta marar adadi ga mai gidana wanda ya yi tsayuwar daka wajen ganin ya ba da goyon bayansa don ganin na samu nasarar wannan karatu ba tare da gazawar sa ba, Ina  roƙon Allah Ubangiji ya biya masa dukkan buƙatunsa na alkhairi, Amin. Ina kuma miƙa godiya ta ga dukkan abokan karatuna da roƙon Allah yasa karatun da muka yi ya zama mai amfani gare mu da sauran al’umma baki ɗaya Amin.

    SADAUKARWA

      Na sadaukar da wannan aiki ga dukkan iyayena. Haka kuma, na sadaukar da wannan aiki ga dukkan masu nazarin harshen Hausa da ke faɗin Nijeriya da sauran masu sha’awar harshen Hausa da al’adun Hausawa.

     

    BABI NA ƊAYA

    GABATARWA

    1.0.          SHIMFIƊA

          Wannan aikin bincike mai taken kutsen baƙin al’adu a kan kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau ya yi duba ne a kan al’adar nan ta kamun Amarya wadda kuma ɗaya ce daga cikin al’adun da akan gabatar a lokacin gudanar da bukin aure a ƙasar Hausa, sai dai ya danganta daga gari zuwa gari ko ƙasa zuwa ƙasa. Al’ada ta ƙunshi hanyoyin zamantakewa na al’umma kamar zaman aure da sana’oi da tsirface-tsirface da sauran matakan tattalin arziki da dangogin abinci da sutura da nau’oin wasanni na al’umma da halaye da ɗabi’u da makamantan wadannan hanyoyi na rayuwar dan’adam da suke gudana tun daga goyon ciki da haihuwa da balaga da aure zuwa bayan mutuwa.(Gusau, 2012;163).

           Haka kuma, an karkasa wannan aikin bincike ne a kan abubuwa har guda biyar, a inda babi na ɗaya aka yi Magana a kan shimfiɗa da kuma manufar bincike da hasashen bincike da farfajiyar bincike da matsalolin bincike haɗi da bayani a kan hanyoyin da aka bi wajen yin wannan binciken duk a cikin babi na ɗaya.

          Sai kuma a babi na biyu inda binciken ya yi bayani a kan bitar ayyukan da suka gabata, sai hujjar ci gaba da bincike haɗi da tarihin garin Gusau da kuma naɗewa.

        A babi na uku kuwa, an yi magana  a kan shimfiɗa da kuma bayani a kan ma’anar al’ada da ire-iren al’ada haɗi da bayani a kan ma’anar aure da ire-iren aure sai kuma naɗewa.

    Sannan a babi na huɗu, an yi shimfiɗa da kuma bayanin al’adun kamun Amarya a da a garin Gusau da kuma bayanin al’adun kamun Amarya a yau a garin Gusau. Sai kuma bayani a kan irin tasirin da zamananci ya yi a kan al’adun kamun Amarya a garin Gusau sai daga ƙarshe aka yi naɗewa.

    Daga ƙarshe, a babi na biyar na wannan bincike da aka gudanar, an yi shimfiɗa sannan aka kawo sakamakon bincike, da kuma shawarwari sai kuma naɗewa.

    1.1 MANUFAR BINCIKE

       Babbar munufar wannan bincike ita ce a zaƙulo wasu daga cikin al’adun kamun Amarya a garin Gusau jiya da  yau. Watau a waiwayi al’adun da akan gudanar a da can kafin Hausawa su haɗu da wasu baƙin al’adu, sannan a dube su ta fuskar zamani.

       Haka kuma, ta haka ne za a bayyana yadda al’adun Hausawa suke dangane da sha’anin aure musamman al’adu da sukan gudana a wajen bukukuwa kamar wanɗan da suka shafi kamun Amarya wanda kuma ya kasance  ɗaya ne daga cikin al’adun aure a garin Gusau da a kan aiwatar a zamanin da da kuma wannan zamani da muke ciki a yau.

         Hakazalika, manufar wannan aiki ne a yi bayani tiryan-tiryan a kan abin da ya shafi al’adar kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau.

         Bugu da ƙari, yana daga cikin manufar wannan aikin bincike a samar da wani kundin karatu,wanda zai zama abin karantawa ga ɗalibai da manazarta a nan gaba.

    1.2  HASASHEN BINCIKE

       Wannan aikin bincike da aka gudanar a wannan sashe na wannan jami’ar tamu mai albarka  an gudanar da shi ne a kan tsari, watau yadda ya kamata duk da kasancewar an gudanar da wannan aiki ne domin cike  gurbin waɗansu abubuwa da ake buƙatar ganin an samu a wannan bincike da aka yi.

       Domin ganin an samu abin da  ake buƙata ga wannan aiki da aka yi, ana fatan Allah ya ba mu nasara a kan wannan bincike da ya gudana cikin nasara da kuma samun yadda ake so a wajen Allah Subuhanahu Wata’ala da ya nuna mana an kammala wannan aikin lafiya, amin.

    1.3 FARFAJIYAR  BINCIKE

       Wannan bincike zai taƙaita ne kawai a cikin wasu al’adun Aure na Hausawa a inda aka taƙaita bayanin a kan baƙin al’adun  kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau. Bugu da kari, wannan bincike ya tsaya kaɗai a kan al’adun  da da na yanzu da suka shafi kamun Amarya a garin Gusau kawai.

     

    1.4 MATSALOLIN BINCIKE

       Kowane irin bincike yana da nau’oin matsalolin da suke da dangantaka da shi waɗanda za su ja rashin kammalar aikin a cikin lokacin da aka diba domin gudanar da shi.

    Waɗannan matsaloli su ne kamar haka:

           I.            Rashin sanin makamar aiki : Watau rashin sanin inda aka dosa

        II.            Rashin isassun kayan aiki : kamar Kundaye, Muƙalu, Litattafai

     III.            Rashin wadatattun kuɗi:  Don yawon zirga-zirga

    IV.            Rashin samun na’urorin da za a yi amfani da su wajen tattara da kuma wallafa aikin binciken.

       V.            Rashin samun shawarwari ga masu gudanar da bincike daga masana da kuma ƙwararru a fannin al’adun Hausawa  da sauransu.

    1.5 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

        Da yake binciken ya shafi maganar al’adar kamun Amarya. Kuma al’ada na nufin  nazarin rayuwar ɗan’adam  wadda ta shafi yadda yake gudanar da ɗabi’unsa tun daga haihuwa har zuwa mutuwa. Saboda haka, ya  zama wajibi ga ƙudurin binciken ya tattara bayanai daga litattafan da aka wallafa waɗanda aka samu a dakunan karatu daban-daban, musamman waɗanda suka shafi Al’adun Bahaushe. Haƙiƙa irin waɗannan littattafan su ne hanya ta farko ta samun bayanai da ke da dangantaka da wannan bincike. A kowane ɓangare na ilimi, littattafai ne kan samar da sahihan bayanai a duk lokacin da ake neman su.

       Abu na biyu a kan wannan shi ne, kundayen bincike da aka rubuta a manyan makarantu da jami’oin na ƙasar nan da kuma na ƙasashen waje. Waɗannan kundaye na fannoni daban-daban, suna nan jibge a   manya da ƙananan  ɗakunan karatu da sashe-sashe na ilimi daban-daban a ƙasar nan.

    Bugu da ƙari, wannan nazari ya duba  irin wadannan kundaye, kuma anyi nazarin su,  sannan  an yi tsakure  na wasu mahimman bayanai da ke da dagantaka da wannan aikin bincike. Har ila yau an  duba waɗannan bayanai ta hanyar yin amfani  da su cikin wannan aikin bincike,  da niyyar inganta binciken.

         Hanya ta uku kuwa  ita ce, ta hanyar duba mujallu da nufin sannin  mahimmancinsu ga irin wannan aiki. Kasancewar mujallu na cikin mahimman hanyoyin samun bayanai na ilimi ya sa wannan aiki bai bar su ba sai da ya duba irinsu. Domin kuwa duba irin waɗannan mujallu ya bayar da damar samun mahimman bayanai a kan al’adun Hausawa musamman waɗanda suka shafi sha’anin aure ga al’ummar Hausawa a rayuwarsu ta yau da kullum .

    Har ila yau, Jaridu ma suna cikin ɓangaren da wannan aikin bincike ya duba domin samun bayanai da ka yi ƙarin haske ga mai bincike . Malammai kan ba da shawarwari kan cewa, ɗalibai su rinka duba jarida domin su ma su na ba da gudunmawa wajen samun bayanai. Wannan bincike yi ƙoƙarin gudanar da kyakkyawan nazari a kan jaridu  na Hausa da Turanci da nufin samun bayanai ta yadda wanka zai biya kuɗin sabulu domin ganin an samu abin da ake buƙata sosai. Haƙiƙa, jarida muhammiyar hanyar samun ilimi ce ga fahimtar da aka samu daga wannan aikin bincike .

    A ƙarshe, sauraren da aka yi wa wasu daga cikin kafofin yaɗa labarai ta hanyar nazarin al’adun Hausawa a cikin gidajen rediyo  da talabijin inda aka saurari ire – iren waɗannan labarai har kuma aka nazarce su sosai. Su ma waɗannan labarai da sauran shirye-shirye sun ba da gudunmawa mai yawa kuma an yi amfani da su wajen sharhi a kan abin da ya shafi al’adun aure a ƙasar Hausa da ma garin Gusau ta Malam Sambo.

       Haka kuma, tattare da wannan fanni  akwai yanar gizo inda aka samu bayanai sosai a wannan zamani, wannan na nuna cewa, mai bincike na buƙatar duba ɓangarori da yawa da nufin inganta wannan aikin bincike .

    Waɗannan hanyoyi ne da a wannan zamani  sukan taimaka  ƙwarai da gaske wajen gudanar da  bincike. Saboda haka, bincike –binciken ya sa an ƙaru, domin kuwa irin waɗannan kafofi na ba da cikakkiyar gudumawa ta fuskar wayar da kan jama’a, ilimantarwa da kuma bunƙasar harshe da al’adun Hausawa.

     

     

    1.6   NAƊEWA

    A wannan babi an yi shimfiɗa wato gabatarwa, sannan da  dalilin yin wannan bincike Daga ƙarshe kuma an faɗi manufar binciken da farfarfajiyar binciken da matsalolin bincike, haɗi da kuma hanyoyin gudanar da shi duk a cikin wannan babi na ɗaya.

     

    BABI NA BIYU

    BITAR AYUKAN DA SUKA GABATA DANGANE DA AL’ADUN KAMUN AMARYA

    2.0. SHIMFIƊA

    Wannan babi na Biyu ya yi Magana ne dangane da bitar ayyukan da suka gabata waɗanda suke da dangantaka ko alaƙa da wannan aiki na al’adun kamun Amarya a garin Gusau. Kuma a cikin wannan babi na biyu an yi bayanin hujjar cigaba da bincike, da kuma bayanin tarihin garin Gusau, sai nadewa, duk a cikin wannan babi na biyu.

    2.1. BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA:

    Masana da manazarta da dama sun yi ayyuka da dama wadanda aka gabatar masu kama da wannan aikin bincike. Daga cikin ayyukan da aka yi bitar su akwai bugaggun littafai da kundayen bincike da kuma muƙalu. 

    Bunza, (2006) A littafin sa mai suna gadon fede al’ada da kuma ire-iren al’adar Bahaushe. Malamin ya tabo bayani kan al’adun gargajiya na Bahaushe, wanda ya hada da addininsa na gargajiya.

    Haɗi da  bayanin tattalin arziki, da kuma yanayin rayuwa baki ɗaya.

    Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin domin dukkansu suna magana ne a kan al’adar Bahaushe. Sai dai inda aikin namu ya bambanta, shi ne, nawa aikin yana magana ne a kan kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau.

    Daura da wasu, (1968) a cikin littafinsu mai suna “Hausa Customs” sun yi cikakkun bayanai a kan al’adun Bahaushe, tun daga haihuwa har zuwa mutuwa. Sun kawo bayani a kan ma’anar aure, da ire-iren auren Hausawa, haɗi da al’adun da ake gudanarwa a cikin sha’anin aure da haihuwa da kuma Mutuwa. Duk dai a cikin littafin marubutan sun yi bayani a kan ire-iren sana’o’in Hausa da kuma ire-iren wasannin da suke gudanarwa duk a matsayin al’adun da Hausawa suke aiwatarwa a cikin sha’anin rayuwarsu ta yau da kullum.

    Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin, saboda duka suna bayani ne  a kan al’adun da Hausawa suke gudanarwa a rayuwarsu ta yau da kullum. Sai dai inda aikinmu ya bambanta shi ne ni nawa aikin yana Magana ne akan al’adun kamun amarya jiya da yau a garin Gusau.

    Zarruk da wasu, (1988) a cikin littafinsu mai suna zaman Hausawa: Bugu na biyu, Sun kawo bayani a kan ƙasar Hausa ita kanta a ina ne take, sai kuma bayanin da suka kawo na cewa wane ne Bahaushe? Kuma a cikin littafin sun kawo bayanin al’adun hausawa da suka shafi suturarsu, da abincinsu da al’amuransu da suka shafi aure da haihuwa da kuma mutuwa. Har ila yau a cikin littafin sun kawo bayani kan ma’anar aure da kuma al’adun da akeyi wajen auren, kama daga neman auren da lefe da ɗaurin aure, da zaman lalle, da tarewa, da sayen baki da budar kai, da fene.Bugu da kari a cikin littafin sun yi bayanin kasha-kashen aure da Hausawa suke da shi. Sannan sun yi bayanin ire-iren sana’o’in Hausawa da kuma sha’anin sarautar gargajiya ta Hausawa.

    Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aiki. Saboda duka muna Magana ne a kan al’adun Hausawa. Sai dai inda aikin namu ya bambanta shi ne. Nawa aikin ya keɓanta ne kawai a kan daya daga cikin al’adu auren Hausawa, watau kamun amarya jiya da yau a garin Gusau.

    Gusau, (2012) a cikin littafin sa mai suna bukukuwan Hausawa. Malamin ya yi bayanin asalin Hausawa da sana’o’insu. Bayan haka ya kawo asalin bikin Hausawa, da ire-iren bukukuwan Hausawa.Haka kuma a cikin littafin ya kawo ma’anar aure da al’adun da ake gudanarwa a sha’anin aure na Hausawa. Ya yi bayanin yadda Hausawa ke bukin aure na gargajiya da bayanin kudin raba wa dangi da kamun amarya, da wankan amarya, da yadda ake wankan amarya, da yadda ake zaman lalle duk a cikin wannan littafi nasa mai suna Bukukuwan Hausawa.

    Wannan littafi mai taken bukukuwan Hausawa, aikin yana da kama da nawa aikin. Saboda muna Magana ne a kan al’ada. Sai dai abin da ya bambanta aikinsa da nawa aikin shi ne, Ni nawa aikin yana Magana ne kawai a kan al’adun kamun Amarya a garin Gusau jiya da yau.

    Yakasai, (2011) a cikin muƙalarsa mai suna “Al’adun auren zawarawa a ƙasar Hausa. A cikin takardar an yi bayanin ma’anar al’ada da kuma ma’anar Kalmar aure.Haka kuma an  kawo bayanin wace ce Bazawara? Sai kuma bayanin al’adun neman auren Bazawara, da bambanci tsakanin neman auren Bazawara, da Budurwa. Duk dai a cikin wannan takardar.

    Al’adun aure Zawarawa a ƙasar Hausa wannan aiki nasa yana da kuma da nawa aikin, saboda duk muna Magana ne akan al’adun auren Hausawa. Sai dai inda aiki na da nasa suke sha bamban shi. Nawa bincike ya ta’allaka ne akan al’adun kamun amarya a garin Gusau jiya da yau.

    Gusau, (2010) A cikin muƙalarsa mai suna “Al’adun Hausawa a cikin makarantun Allo”: Nazari a kan wasu al’adu da suka danganci karatu da zamantakewa a cikin makarantun Allo’. A cikin mukalar ya yi gabatarwa inda ya kawo bayanin cewa Hausawa al’umma ce maitarin al’adu da yawa. Kama daga neman aure, haihuwa har zuwa mutuwa. Ganin haka sai ya duba wasu al’adun da ake samu a cikin makarantun Allo, inda ya kawo ma’anar al’ada da makarantar Allo. Duk a cikin takardar ya yi bayani al’adar karatun Bahaushe, wadda ya yi amfani da ita wajen fahimtar Haruffan Alkur’ani. Haka ma acikin takardar ya yi bayanin al’adar Bahaushe wadda ta shafi zamantakewa, sai daga karshe ya nade.

    Wannan aiki ya na da alaƙa da nawa aiki, saboda duk muna Magana ne a kan al’adun Hausawa, da kuma yadda suke gudana a cikin rayuwar Hausawa. Sai dai inda inda aikinmu ya bambanta shi ne nawa aikin yana magane a kan al’adun kamun amarya jiya da yau a garin Gusau.

    Abdullahi, (2010) A cikin takardarsa da ya gabatar mai suna “Bukukuwan Hausawa na gargajiya”. A cikin takardar ya yi gabatarwa ya kuma kawo bayanin bukukuwan gargajiya na Bahaushe inda ya kawo ma’anar aure da kuma dangantakar masoya da bayanin shigowar iyaye. Haka kuma ya kawo kamun amarya da ƙunshi da ɗaurin aure,buɗar kai da sayen baƙi, da bayanin haihuwa da neman taimako da goyon ciki, wankan biki, zanen suna, kunun biki, ƙauri, yadda ake samun suna duk a cikin takarda. Sai daga ƙarshe ya yi naɗewa.

    Wannan aiki ya yi kama da nawa aiki, inda duk muna Magana ne a kan al’adu da suka shafi aure, sai dai inda aikin namu ya sha bamban shi ne ni nawa aikin ya tsaya ne a kan kamun amarya a garin Gusau jiya da yau.

    Abubakar da wasu, (2006) A cikin kundin su mai taken “Tasirin zamananci a kan al’adun aure na Hausawa: keɓaɓɓen Nazari a garin Gusau. A cikin kundin sun yi bayanin a kan tasirin da zamananci ya yi a kan al’adun aure, Ma’anar al’ada bayanin al’adun aure a garin Gusau kafin zuwan Turawa da kuma bayan zuwan Turawa.

    Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aiki, saboda duk muna Magana ne a kan al’adun aure a garin Gusau jiya da yau. Inda aikinmu ya bambanta shi ne nawa aiki ya tsaya ne akan kamun amarya a garin Gusau jiya da yau.

    Ibrahim, (1982) A kundinsa na digiri na biyu mai suna “Dangantakar Al’ada da Addini”. A cikin wannan littafi nasa ya kawo gabatarwa kuma da yin bayani dangane da ma’anar al’ada da kuma nuna muhimmancin al’ada ga rayuwar dan,Adam. Duk acikin littafin marubucin ya kawo bayani a kan mene ne addinin gargajiya da kuma yadda Hausawa suka reƙe shi a matsayin abin da suke gudanar wa a rayuwarsu ta yau da kullun.

    Wannan aiki nasa yana da alaƙa da nawa aiki. Saboda duk muna Magana ne akan al’adun Hausawa. Sai dai inda aikin namu ya sha bamban da nasa shi ne ni nawa aikin yana Magana ne a kan al’adun da Hausawa ke yi a wajen sha’anin aure. Kuma aikin ya keɓanta a kan yadda ake gudanar da al’adar kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau.

    Bala, (2011) A cikin kudinsa na neman digiri na daya. Mai taken “ Tasirin Zamanci Akan Auren Gargajiya A kasar Kwatarkwashi”. A cikin aikin ya kawo gabatarwa inda kuma marubunci ya kawo ma’anar aure da kashe-kashensa da kuma yadda ake yinsa ada a gargajiyance.

    Sai kuma ya kawo ma’anar zamani. Duk a cikin nasa ya kawo yadda ake gudanar da al’adun aure a zamance, Sai tarihin kasar Kwatarkwashi da ya kawo duk a cikin aikin nasa daga ƙarshe sai ya naɗe.

    Wannan aiki nasa yana da kama da nawa aikin, Saboda muna Magana ne akan tasirin da zamani ya kawo ga al’adunmu na aure a kasar Hausa. Sai inda aikin namu ya bambanta shi ne ni nawa aikin yana Magana ne a kan wata ala’ada ta aure wadda ake yi mai suna kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau.

    2.2. HUJJAR CI GABA DA BINCIKE:

    A fagen ilimi babu wanda zai iya bugun kirji ya ce ya kai iyakar ilmi, amma ana iya cewa a yanzu tafiya ta fara nisa dangane da binciki-bincike da nazarce-nazarce da akan gudanar a fannoni daban-daban.

    Domin kuwa, masana da manazarta al’adun Hausawa sun yi bincike da rubuce-rubuce a kan wannan fanni da dama. Musamman ma a fannin sana’o’in Hausawa da Haihuwa da na aure.

    Har wa yau, akwai buƙatar yin aiki a kan wani fanni da masana yan kaɗan ne suka yi aiki a kansa. Wannan fanni kuwa shi ne na al’adun da ake gudanarwa a sha’anin aure na Hausawa. Manazarta da marubuta sun yi ta aiki a kan sana’o’in hausawa da kuma auren hausawa, da addinin Bahaushe, musamman irin su Furofesa  Aliyu Muhammad Bunza, wanda ya yi aiki a kan ɓori a matsayin addinin Bahaushe na gargajiya.

    Haka kuma,  Dakta Aminu Lawal Auta shi ma ya yi rubutu a kan Tattalin Arzikin Al’umma: Nazarin Sana’o’i da Kasuwancin Hausawa. A cikin wata “Journal” mai suna “ALGAITA” kano a shekarar 2006.

    Haka shi ma Dakta Murtala Garba Yakasai a cikin “Algaita Journal” 2011 ya yi rubutu a kan Al’adun Auren Zawarawa a ƙasar Hausa. A iya binciken da na yi na ga cewa ba a yi aiki a kan al’adun kamun amarya jiya da yau ba musamman a garin Gusau. Don haka ne wannan bincike zai ɗora a kan inda aka tsaya. Amma nawa bincike zai maida hankali ne a kan Tasirin Zamananci da ake samu a wayen Al’adun Kamun Amarya a garin Gusau.

    Ganin wannan al’ada ta kamun amarya ya dace a yi wannan aikin binciken domin a gano abin da ya ƙunsa a fagen nazari. Musamman ta fuskar al’adun Hausawa da suka shafi bukukuwa da sauransu.

    Tare da fatan wannan bincike zai kara wa manazarta da ka biyo baya ƙwarin gwiwa a fagen bincike ta hanyar adana shi a dakunan karatu (Libraries) da kuma yanar gizo (Internet)

     

    2.3. TARIHIN GARIN GUSAU

    Kamar yadda bayani ya gabata an kafa garin Gusau ne a shekara ta 1811 bayan tasowa daga tsohon mazauninta da ke  ‘Yandoto a shekara ta 1806.

    Garin Gusau yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan tsohuwar jihar sakkwato, kafin daga bisani ya zama babban birnin jihar zamfara a shekarar 1996. Kuma kamar yadda kundin bayanin tarihin ƙasa na 1920 ya nuna, garin yana bisa titin sakkwato zuwa zariya ne; kilomita 179 tsakaninsa da zariya, 210 kuma tsakaninsa da sakkwato. Daga gabas ya yi iyaka da ƙasar katsina, da ta Kwatarkwashi. Daga arewa kuma ya yi iyaka da ƙasar ƙaura Namoda. A yayin da ya yi wata iyakar daga yamma, da ƙasar Bunguɗu. Ta ɓangaren kudu kuwa ya yi iyaka da kasar Ɗansadau da Tsafe.

    Kasancewarsa  almajirin Shehu Usman Danfodiyo, watau Malam Sambo ɗan ashafa ya kafa Gusau, wanda yake shi da jama’arsa ba ruwansu da duk harkokin da suka shafi bautar iskoki ko tsafi, irin wanda Hausawa suke yi kafin zuwan addinin musulunci. Watau, garin Gusau ba ya da tarihin jahiliyyah. Hakan ne ta sa duk al’adun Gusawa, al’adu ne irin na musulunci. Kuma shigowar wasu mutane, wato baƙi a Gusau, ba ta gurɓata waɗannan kyawawan al’adun ba, don kuwa mafi yawan baƙin da ke tahowa Gusau, malamai ne na musulunci da almajirai, Fulani da wasunsu, da kan taho garin don tsira da addininsu, da mutuncinsu, da kuma dukiyarsu.

    Zuwan Bature da cinsa ƙasar Hausa da shimfiɗa tsarin ilimin boko, ya sa wasu al’adu tsinuwa. ana cikin haka kuma sai ga shari’ar musulunci ta sake kunno kai ta godaben tafdidi. Wannan sabon lamari a wannan ƙarni, shi ma ya kawo canje-canje na alhairi a al’adun mutanen garin Gusau a matsayinsa na babban birnin jiha. Mutane da yawa na halartar masallatai don tafsiri da ittikafi fiye da  can baya. Kawowa yau akwai malamai da dama da suka shahara da gudanar da tafsiri a masallatan juma’a da wasunsu a garin na Gusau. (Gusau, 2014:98).

    Garin Gusau a matsayin babban birnin jihar zamfara yana da murabba’in faɗi na kilomita 3,469 (Dangusau, 1998:29). Gusau babban gari ne, mai albarkatu nau’I – nau’I, kuma kamar yadda aka yi bayani a baya, garin Gusau ya yi zama a matsayin hedikwatar ƙasashen sakkwato ta gabas. Kuma a garin Gusau ne wakilin Sarkin musulmi ya zauna.

    Haka kuma, garin Gusau yana da hanyoyin sadarwa da hanyoyin sufuri na gargajiya da na zamani tun da jimawa. Garin Gusau gari ne na sana’o’in gargajiya da huldodin kasuwancin cikin gida da na waje tare da manya kuma yalwatattun masana’antu da kamfanoni. (Gusau, 2012:110).

    Kuma kamar yadda aka gani, wadannan mazauna farko na garin Gusau sun kasu gidaje biyu ne, akwai Gidan ‘yandotawa da kuma Gidan Ashafawa.

    Masarautar Gusau, kamar yadda littafin masarautar mai taken “Gusau Emirate” ya nuna, ta kafu ne, a shekara ta 1806 a hannun malam Muhammad sabo dan ashafa. A wannan shekara ne, a birnin gada, malam muhammadu bello dan Shehu usmanu ya tsaga kasar katsina biyu: gabas da yamma, gar saba’in – saba’in, tsakanin shi malam sambo din da kuma malam ummarun dallaje. Tun daga wannan lokaci ne kuma garin na Gusau da masarautarsa suke ci gaba da bunkasa ta hanyoyi daban–daban. Kafin rasuwar malam Sambo, an yi wani lokaci da hedikwatar wannan masarauta ta koma garin wonaka da ke garin Gusau a yanzu.

       Kamar yadda bayani ya gabata birnin Gusau ya yi ta samun bunƙasa da habaka da ƙare-ƙaren garuruwa saboda zuwan wasu mutane baki, A sakamakon ƙaruwar Gusau an sami wasu shiyyoyi da unguwanni da yawa waɗanda suka haɗa da :

    -         Birnin Ruwa

    -         Sabon Gari

    -         Yar’loko

    -         Filin Gunza

    -         Sabon fegi

    -         Unguwar toka

    -         Unguwar mangwaro

    -         Tudun wada

    -         Unguwar zabarma

    Waɗannan wasu daga cikin shiyoyi da unguwanni ne da ke garin Gusau.

    2.4. NAƊEWA:

    A wannan babi na biyu an yi bayani a kan bitar wasu ayyuka da suka gabata, an yi bayani a kan shimfida, da kuma bitar ayyukan da suka gabata, sai bayanin da aka yi a kan hujjar ci gaba da bincike, sai bayanin tarihin garin Gusau a taƙaice.

     

    BABI NA UKU

    FASHIN BAƘI A KAN MA’ANONI DA SUKA SHAFI AL’ADUN KAMUN AMARYA.

    3.0 SHIMFIƊA

       A wannan babi na uku an yi bayani a kan ma’anar al’ada da ire-iren al’ada, sai kuma bayani a kan ma’anar Aure da ire-irensa duk a cikin wannan babi na uku. Sai kuma naɗewa. Kuma an yi hakan ne domin a samo bayanai dangane da ra’ayoyin masana a fagen al’adun Hausawa na gargajiya musamman waɗanda suka shafi aure da sauransu.

    3.1 MA’ANAR AL’ADA:

    Kalmar Al’ada ta sami ma’anoni daga masana daban-daban, kadan daga cikin irin waɗannan ma’anoni dam asana suka bayar sun hada da:

         Ibrahim, (1982) ya bayyana ma’anar al’ada kamar haka “Abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Ya kuma shafi yanayin rayuwar al’umma da harkokin da suke yi don zaman duniya”.

         Umar, (1987)  Ya ce, dukkan abubuwan da akasari jama’a na kowane al’umma suka amince da su, su ne al’adunsu. Idan wadannan abubuwa sun yi zaune da gindinsu, bayan sun samo asali daga kaka da kakanni, shi ke nan sun zama al’adun gargajiya.

          Bunza, (2006) Yana ganin al’ada a luggar larabci na nufin “ Wani abin da aka saba yi ko ya saba wakana ko aka san da shi”. Da wannan ne wasu masana furu’a suke da wani zancen hikima mai cewa “Al’adul baladi Kal Sunna”. Ma’ana al’adar da gari ya saba da ita kamar sunna ce, sai dai a Hausa kalmomin da suka fi kusa da al’ada su ne Kalmar “Sabo” ko “gado” ko “hali” ko kuma gargajiya”.

       Bisa la’akari da waɗannan ma’anoni kan al’ada sai a fahimci al’ada tankar wani burgame ne na rayuwar al’umma da ke ƙoƙarin bayyana al’umma ko jininsa da nahiyoyi mabambanta.

        Muazu, (2013) ya ce, Al’ada hanya ce da al’umma take gudanar da rayuwarta ta yau da kullum ta fuskar zamantakewa da abinci da muhalli da tufafi da gine-gine da bukukuwa da ma dukkanin wasu abubuwa da suka shafi al’umma da rayuwarsu ta yau da kullum.

     A bisa waɗannan ma’anoni na al’ada za a iya  cewa, al’ada ba wata abu bace illa nazarin rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwa har zuwa ƙabari.

    3.2 IRE-IREN AL’ADA:

     A kwai ire-iren al’adun Hausawa kashi biyu.

    1.     Cuɗaɗɗun al’adu da addini

    2.     Cuɗaɗɗun al’adu da zamani

    3.2.1      Cuɗaɗɗun Al’adu da Addini:

        Wannan yana nufin al’adun Hausawa bayan zuwan Addinin Musulunci da wasu addinai a ƙasar Hausa. A nan za a ci karo da al’adun larabawa ko addinin Musulunci ko addinin Bani Israil, su yi naso cikin wasu al’adun Hausawa. Wannan shi ne  rukuni na farko. (Gusau, UG. (2012).

     

     

    3.2.2      Cuɗaɗɗin Al’adu da Zamani

       Bayyanar Bature a ƙasar Hausa ya yi naso sosai a al’adun Hausawa musamman abubuwan da suka shafi aure, da haihuwa, da siyasa, da kasuwanci, da zamantakewa.

        Al’adun da suka shiga irin wannan hali sun zama cuɗaɗɗun al’adu idan ba a yi hattara ba za su salwanta, ido na ganin ido.

      3.3 MA’ANAR AURE

          Manazarta da masana da dama sun yi bayanin me ake nufi da wannan kalma ta aure? Masana irin su:

     Yakasai, (2011) A cikin wata takarda da ya rubuta a wata ‘Journal’ mai suna

    “ALGAITA”  ya ce, “Aure wata yarjejeniya ce da ake ƙullawa tsakanin mace da namiji domin su yi zamantakewar aure a matsayin miji da mata sannan su iyakance rabon ayyuka a tsakaninsu, watau hakkin miji ne ya samar wa da matarsa abinci da sutura da muhalli da tsaron lafiyarta da kare mutuncinta. Ita kuma mata hakkinta ne ta dafa masa abinci ta share gida da kula masa da ‘ya’yansa da kuma sauran haƙƙoƙi makamantan waɗannan.

        CNHN (2006), A cikin kamusun Hausa an ba da ma’anar aure da cewa shi ne haɗa namiji da mace ta hanyar shari’a ko kuma ɗabi’a ko dacewa, ko karɓo.

        Gusau. (2012), Ya ce, shi dai “aure amanar Allah ce, kiwo ne, a wajen Hausawa, aure wata alaƙa ce halattacciya, wadda ta halatta zaman tare tsakanin ma’aurata guda biyu, wato miji da mata. Ana yin sa ne saboda abin da aka Haifa ya sami asali da mutunci da kiyayewar uwaye. Aure maganin zina ne da haihuwar ‘ya’ya nagari a cikin al’umma. Saboda muhimmancinsa ga al’ummar Hausawa musulmai, aure ya kasance bai wanzuwa sai da abubuwa uku, wato waliyyai da sadaki da kuma shaidun taron jama’a”.

     A bisa waɗannan ma’anoni na aure za a fahimci cewa, aure shi ne wata alaƙa ce ta hallaccin zaman tare tsakanin namiji da mace, domin samar wa abin da aka Haifa asali.

     

    3.4 IRE-IREN AURE

         Aure ya kasu kashi-kashi akwai auren soyayya, da auren tilas da auren zumunta da auren sadaka, da auren ɗiban wuta, da auren dangana-sanda da auren gayya, da auren diban haushi ko ɗiban takaici, da ɗiban tsuwa ko kece raini, da kashin kwarnafi da sauransu. (Alhassan, da wasu.1988:15).

    3.4.1 AUREN SOYAYYA

        Aure ne wanda yaro ke ganin yarinya ya ce yana sonta da aure, ita kuma ta amince, iyayenta  su yarda da maganar, sannan a yi haramar ɗaurin aure. Wannan irin auren shi ake kira auren soyayya, kowa na so.

    3.4.2 AUREN TILAS (DOLE)

        A wannan nau’in auren yaro yakan ga yarinya ne ya ce yana son ta da aure, amma ba ta amince ba. Iyayenta kuma su zartar da hukunci, watau wasu na so, ko suna ki. Harma akan ba da yarinya ga wanda yake sa’an mahaifinta ne, ko sa’an kakanta, alhali kuma ba ta so. Kuma akan nema wa yaro yarinya ba tare da yana so ba, saboda wata alaka ko yarjejeniya tsakanin iyayensu. Wannan ma auren tilas ne.

    3.4.3 AUREN ZUMUNTA

        Auren zumunta, wannan aure ne wanda aka nema wa yaro yarinya daga cikin dangin uwa ko na uba, ba tare da an shawarci yaron ko yarinyar ba. Irin wannan aure ana yin sa don kara daukaka dankon zumunta tsakanin ‘yan’uwa.

    3.4.4 AUREN SADAKA

       Shi kuma aure ne da a kan bayar da yarinya ga wani, saboda neman tubaraki (albarka), kamar irin sadakar da a kan ba malamai, almajiransu, musamman idan yarinya ta girma ba ta sami manemi da wuri ba.

    Haka kuma, a kan yi auren sadaka don gudun kada ta jawo wa iyayenta abin kunya. Wani lokaci kuma idan mutum bai sami haihuwa da wuri ba, yakan yi alƙawarin cewa, zai ba da ita saboda ya samu, yakan ce wa wani idan ya samu  zai yi sadaka da ita.

    3.4.5 AUREN KISAN-WUTA

        Wannan wani nau’in aure ne wanda bayan an saki mace saki uku,alhali kuwa matar tana son mijinta, shi ma yana son ta, dole sai ta auri wani kafin ta sami damar komowa ga mijinta na farko, to auren nan da ta yi da kudurin cewa za ta dawo wurin mijinta na da wannan shi ne auren diban wuta. Kuma a kan yi irin wannan aure ne saboda kauce wa sabawa shari’ar musulunci.

    3.4.6 AUREN ƊAUKI-SANDA

         Shi wannan aure, mutum yakan auri matar da ke zaune a gidan kanta. Sai ya kasance ba za ta iya tasowa ta zo gidansa ta zauna ba saboda waɗansu dalilai. Haka shi ma ba zai iya zuwa gidanta ya zauna ba. Sai dai ya rinka zuwa can gidanta yana kwana. Irin wannan aure abin da ya sa ake kiransa auren dauki-sandarsa shi ne, mijin yakan jingina sandarsa a bakin kofar dakinta ne kana ya shiga ya kwanta. Kuma, yakan riko sandar ne saboda namun daji ko kuma wani abinda zai tare shi a hanya.

     

    3.4.7 AUREN GAYYA

         Wannan irin aure na gayya shi ne idan matar mutum ta fita, alhali kuwa yana son ta, ya dai sake ta ne don ta addabe shi to, maza sai ya yi sauri ya yi wani aure kafin ya sake ta, ko kafin ta gama idda. Ba don komai ba zai yi wannan auren sai don kurum ya huce haushinsa, ko kuma don kada matar ta riga shi yin aure. Akan kira wannan aure da auren huce takaici.

    3.4.8 AUREN ƊIBAN HAUSHI

        Wannan auren kuma shi ne ake kira auren ɗiban takaici ko auren ɗiban tsiwa ko na keceraini da kashin kwarnafi. Idan matar mutum ta dame shi da fitina, yakan tashi takanas ya je ya auri wata mace mai kyau ko dukiya ko asali ko addini, fiye da wadda ke gidansa, ko wadda ya saka. Ana yin wannan aure ne don kawai huce haushi ko debe takaici ko don gusar da wulaƙanci da raini da tsiwace-tsiwace na ba gaira ba dalili.

    (Alhassan, da wasu, 1988:15-16)

     

    3.5 NAƊEWA

       A wannan babi na uku an kawo bayani a kan shimfiɗa, sannan an yi bayanin ma’anar al’ada da rabe-rabenta duk a cikin wannan babin.

      Sai kuma bayanin ma’anar aure da ire-iren auren Hausawa da suke da shi a kasar Hausa kuma yadda masana suka kawo.

     

     

     

     

     

     

     

     

       BABI NA HUƊU

    BAYANI A KAN BAƘIN AL’ADUN KAMUN AMARYA

    4.0 SHIMFIƊA

        Wannan babi na huɗu ya yi Magana ne a kan Al’adun Kamun Amarya a da da kuma a yanzu. Yadda ake yin sa a garin Gusau. Duk a cikin wannan babi na huɗu za a yi bayanin Tasirin zamani a kan kumun Amarya a garin Gusau. Daga ƙarshe sai naɗewa.

    4.1 AL’ADUN KAMUN AMARYA A DA A GARIN GUSAU

     A yayin da iyayen ango suka gama shirye-shiryen inda Amarya za ta zauna da sauran hidimomin biki, sai su shawarci iyayen Amarya dangane da tsai da ranar biki. Kafin iyayen ango da amarya su saka ranar biki akwai kayan sa rana da ake kaiwa. Su waɗannan kaya ba waɗansu masu yawa ba ne. Akasari akan sayi kayan shafe-shafe ne da goro akai gidan amarya. Su kuma iyayen Amarya daga sun ga waɗannan kaya sai su fara shirye-shiryen kai yarsu ɗaki. Bayan sun gama shawara a tsakaninsu sai su aika wa iyayen ango su zu a sa rana. A wajen sa rana kowa zai faɗi ranar da ya fi so. Kamar ciniki ne wannan ya taya wancan ya ce albarka har sai an daidaita sannan kowa ya yarda. Idan an tsayar da rana guda sai kowa ya tashi yana raha ana irin guɗar nan tasu ta mata. Daga nan, sai kowa ya shiga raba goro da sauran shirye-shirye. Idan Ango na da ragowar ‘yan gyare-gyare ya yi maza ya gama kafin ranar. Su kuma iyayen Amarya su sassayo ragowar kayan ɗakin da ba su saya ba. Daga ranar da aka sa rana iyayen amarya basu sauraren komai daga wajen Ango sai kayan ƙunshi. Ranar da aka kai kayan ƙunshi kuwa an kama yarinya, ke nan an shiga hidimar biki sosai. (CNHN, 1981:11).

       Wannan al’ada haka take gudana ko a garin Gusau. “Kowane Allazi da nasa Amanu” A nan garin Gusau yadda ake kama amarya shi ne. Kafin ranar ɗaurin aure da sati guda, ko kwana biyar ko huɗu, akan kama amarya, watau a shafa mata lalle. Idan lokacin ya yi wasu amaren tare da ‘yan matansu su kan gudu su buya. Akan sha faman neman su, sai daga  baya a gane su, a shafa wa amarya lalle. Da zarar an shafa wa amarya lalle sai ta kama kuka, sai a kama ta a tafi da ita zuwa gidan maƙunshiya. Ita da ‘yan matan nata Lallen da akan shafa wa amarya a lokacin akan kwaɓa shi da tazargade da turaren juda don ya yi ƙanshi, ita ma amarya ta rinƙa ƙanshi.

     A nan garin Gusau yadda akan kama amarya shi ne yawo ne da ake yi na neman amarya da ‘yan mata ƙawayenta ke yi sako-sako, lungu-lungu da zimmar gano wurin da ta ɓuya don a saka ta lalle.

    Ga al’ada, ‘yan mata ƙawayen amarya sukan fita neman amarya ne, da magariba zuwa isha’i. A kan hanyarsu ta zuwa kamo Amarya, akwai ‘yan waƙe-waƙe da suke rerawa. Misali a wajen kamun an fi rera waƙoƙin mai Rimaye” da “Allin Allah”. Manyan mata da ‘yan mata ne sukan rera waɗannan waƙoƙi a kan hanyarsu ta zuwa kamo amarya.

    Ga Misalin waƙar “Mai rimaye”

    Mai ba da waƙa: Mai gidan kalage,

           Mai rimaye.

    Y/Amshi :            Mai gidan kalage,

                     Mai Rimaye.

     

    M/waƙa :           Mai gida kalage,

            Da ka mutu da na so.

     

    M/Waƙa:              Na baro zane na,

           A kan gadon masoyi.

    Y/Amshi           Mai gidan kalage,

            Mai Rimaye.

     

    M/waƙa :           Kwarkwata da kukan aure,

          Ade ya same ku,,

          Raƙumin dawa da Katanga,

          Me ya same ku,

          Aure ne dai ya same mu.

    Y/Amshi           Mai gidan kalage,

          Mai Rimaye.

     

    M/waƙa ;           Iro bayya cin gero,

       Iro bayya cin dawa,

     Alkama da shinkafa shi ma,

    Na baki ne,

    Markaɗe dabino da nono,

    Yakan sha shi.

    Y/Amshi     Mai gidan kalage,

    Mai Rimaye.

     

    M/waƙa ;       Na baro zanena a kan,

    Gadon masoyi.

    Y/Amashi     Mai gidan kalage,

    Mai Rimaye.

      Wannan waƙa ita ce manyan mata da kuma ‘yan matan amarya suke rerawa a lokacin da suke zuwa kamun Amarya a al’adance.

    ( Galadanci da wasu, 1992:86)

      A bisa ga al’adar nan ta alkunya. A nan garin Gusau idan iyaye da dangi na wajen amarya da na wajen ango sun tsaida rana, to Amarya kan ƙaurace wa gidansu, ta tafi wani gida na ƙawarta wurin da take zaton ba a iya gane ta da sauri, Sai da magariba uwayen ƙawarta su mai da ita gidansu, don ci gaba da sauran hidimomi. Su kuwa sauran abokan amarya, Idan sun kwaɓa lallen za su yi shiri sosai na neman amarya, a duk wurin da ta shiga domin shafa mata wannan kwaɓaɓɓen lallen. Da zarar sun yi nasarar ganin ta, shi ke nan fa sai su shafa mata wannan kwaɓaɓɓen lallen, daga nan Amarya ta shiga Lalle ke nan ba sauran wata magana.

       Har wa yau, wajen kamun amarya wata al’ada da akan yi a nan garin Gusau ita ce, Uwayen yarinya ne kan yi mata dabara ko wayo, watau na babba da yaro. Sai su tura ta wani gida na ‘Yan uwa ko maƙwabta don a sa ta lalle a can.

    Akan sanar da ita cewa, ta tafi ta kai saƙo a wajen wance. To, da zarar ta isa gidan shi ke nan sai a shafa mata lallen, da ma su sun san da maganar shi ke nan amarya ta shiga lalle ke nan ta zama “Amarsu ta Ango” Wasu kuma kakar yarinya ce za ta sa ta a lalle. Wasu kuma kan zaɓi wani gida daga cikin gidajen dangi, a inda a can ne za a sanya wa amarya lalle.

     Daga nan, sai ‘yan mata, ƙawayen amarya su taru su taya amarya juyayi tare da yin yan koke-koke saboda baƙin cikin (juyayi) rabuwa da ita da kuma sanar da maƙwabta halin da ake ciki ta hanyoyin buga dundufa ko ƙada ƙwarya ko shantu, don faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa ta fuskar baje kolin fasaha da al’adun Bahaushe na gargajiya.

     A al’adance amarya kan yi kwana biyu ko uku ko ma mako ɗaya a cikin lalle, amma wannan ya danganta da wuri ko tsari wasu suna yin haka ne don su sami damar kai amarya gidajen danginta a yi mata gargaɗi da ja mata kunne.

      Wannan zaman kwanakin da ake yi ana yawo gida-gida na ‘yan uwa shi ake kira da zaman lalle. A wannan lokaci ne ake yi wa amarya cuda da kwababben lalle wanda aka haɗa da turaren juda da tazargade, domin ƙamshi. ‘Yan matan amarya ne ke yi wa amarya wannan cuɗar sau biyu, ga yini har tsawo lokacin da aka ɗiba. Daga nan sai ranar wankan amarya da kuma tarewa.

    4.2 AL’ADUN KAMUN AMARYA A YANZU A GARIN GUSAU.

      Hausawa sun jima suna yin aure a tsakaninsu, kamar na saurayi da budurwa da ya fi ƙunsar al’adu a lokacin aiwatar da shi. Akan aiwatar da shugulgula daban-daban da kuma wasu muhimman abubuwa na al’adu kamar baiko, sa rana, da gudu ko kamu. Sannan akwai ƙunshi da kuma wankan amarya har zuwa ɗaurin aure. Duk wadannan shekarun baya ana gayyatar mutane ne ta hanyar aika musu da goro ko danƙo ko kuma a faɗa masu da fatar baki. Amma a wannan lokaci an samu sauyi sakamakon zamani da ya shigo, ana gayyatar mutane ta hanyar aika masu da katin ɗaurin aure.

      A bikin auren saurayi da budurwa a abin da aka fi sani a shekarun baya kafin ɗaurin aure aƙula: wasu ranaku da ake gudanar da wasu muhimman al’adu kamar gudu ko kama amarya.Sannan da ƙunshi da kuma wankan amarya. Yanzu abin bah aka yake ba, Saboda canjin zamani an keɓe wasu ranaku da ake gudanar da wasu abubuwa mabambanta wadannan ranakun su ne:

    4.2.1      Ranar ƙauyawa: (ƙauyawa Day) A wannan rana abokan ango da ƙawaye amarya za su yi shiga irin ta mutanen ƙauye da kuma kayan sauti suna zagaya gari ko kuma su zauna a wani wuri da aka ware.

    4.2.2      Ranar Larabawa (Larabawa Day) A nan ango da abokansa za su yo shiga irin ta larabawa, jallabiyya da maka-wuya, su kuma bangare amarya da ƙawayenta za su shigo dogayen tagunoni na matan larabawa haɗi da gyale a samu wani wuri a chashe ana lashe-lashe da tanda-tande da raye-raye irin na larabawa.

    4.2.3      Ranar sa kati : ita wannan rana za’a tanadi katin da za a yi amfani da shi.

    4.2.4      Ranar Shar Rake: A wannan rana za a kawo rake isassa a kuma ci gaba da sha.

    4.2.5      Ranar cin Fara: Rana ce da ƙawayen amarya ke haɗuwa don cin fara da sauran kaɗe-kaɗe da raye-raye. ( Yunusa, 2020).

    4.2.6      Ranar Uwa: (Mothers Day) Hausawa sun ce zamani riga. A halin yanzu ƙunya ta kau idon y’anmata inda har ta kai yanzu yarinya ita da kanta ke fadin ranar da za a yi hidimar bikinta.

       Har wa yau zamani ya zo da cewa a ranar kamu da ake bin yarinya a kamo ta a sa mata lalle, yanzu abin bah aka ba ne. Wasu ko lallen bas u sawa sai da a faɗi ranar hidima kawai. Wasu kuma maimakon a sanya musu lalle a’ a su da kansu za su tsoma hannunsu a cikin lalle, wai an shiga lalle ke nan.

        Kuma a da idan yarinya ta shiga lalle to shi ke nan ba wani sauran yau da zata yi sai gidan angonta. Amma a halin yanzu sai ka ga amarya a sa rana kuma ta shiga lalle amma bai hana ta fita zuwa yawo wajen ƙawayenta.

       Kukan da amarya da ƙawayenta ke yi lokacin da aka kama ta, zamani ya sauya wannan al’ada yanzu sun bar yin kukan. Shi ke sa wasu maƙwabta ma ba za su san an kama wance ba sai ranar biki.

       A nan garin Gusau zamani ya sanya ana kama amarya ne ana gube ɗaurin aure maimakon sati biyu ko ɗaya da wasu ke yi idan an kama amarya, to abin ya canja saboda zuwan zamani.

       A yanzu maimakon tsofafi da ke kama amarya, saboda canjin zamani yanzu a nan garin Gusau yara y’anmata su ne ke kama amarya.(Balkisu,2021).

    4.3 TASIRIN ZAMANI A KAN AL’ADUN KAMUN AMARYA A GARIN GUSAU.

       Zamani asali Kalmar larabci ce wato, ‘zaman’, wato lokaci. Hausawa suka ara, suke amfani da ita daidai da ma’anarta ta larabci.Wannan ya nuna cewa zamananci na nufin duk abin da yake lokacinsa ne. Kalmar zamani tana tafiya kusan da komai ka haɗa ta.

      To, a halin yanzu idan muka duba tasirin da zamani ya yi wa al’adar kamun amarya a garin Gusau shi ne na gurɓata al’adunmu na asali da muka saba da su yau da kullun.

       Zamananci ya yi tasiri kwarai a kan al’adar nan ta alkunya. Yanzu babu ita ta kau.

     Sai wani tasiri da zamani ya yi ga al’adun kamun amarya, shi ne a da ana kama amarya ta kwana uku, ko sati ɗaya ko ma fiye da haka. Yanzu kuwa saboda shigowar zamani an bar wannan al’adar gaba daya.

        Zamananci ya yi tasiri a kan kamun amarya, inda ya kawo mana taɓarɓarewar zumunci wanda a da idan an kama amarya za a kai ta wani gida daga cikin gidajen ‘yan’uwa don a karfafa zumunci  amma a yanzu ba haka ba ne, saboda shiguwar zamani duk an yi watsi da waɗannan al’adun.

      Kukan da amarya da ƙawayenta ke yi idan an kama amarya yana matsayin shaida wa jama’a cewa, wance ta shiga lalle amma yanzu saboda zamani an bari sai dai kawai ka ji cewa yarinya ta tare ɗakinta, wannan duk zamananci ne ya kawo hakan.

      A taƙaice dai wannan shi ne tasirin da zamani ya yi wa al’adun kamun amarya a garin Gusau. Dalilin wannan shi ya kawo mana cigaban mai gina rijiya wanda sanadiyar hakan al’adunmu na gargajiya sun fara ƃacewa, wasu kuma sun suma, wasu an jefa su a kwandon shara duk dai saboda shigowar zamani. Saboda Hausawa sun ce “ Zamani Riga” in ya ɗinka sai a sa. Kuma Allah shi ne mai zamani. (Balkisu, 2021).

    4.4 NAƊEWA

     Wannan shi ne ƙarshen babi na hudu inda na yi shimfiɗa kuma na kawo bayani a kan al’adun kamun amarya jiya da yau a garin Gusau. Duk a cikin wannan babin na huɗu na yi bayani a kan tasirin da zamani ya yi a kan al’adun kamun amarya a garin Gusau.

                                                    BABI NA BIYAR

                                             SAKAMAKON BINCIKE

    5.0 SHIMFIƊA

     Wannan babi na biyar shi ne na karshe a cikin wannan aikin bincike nawa da na yi mai taken kutsen  Baƙin al’adu a kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau. A cikin wannan babi an yi bayanin sakamakon abin da aka gano a cikin wannan bincike. Sai shawarwari da aka bayar sai kuma nadewa duk a cikin wannan babi na biyar. Daga karshe kuma ankawo manazarta.

    5.1 SAKAMAKON BINCIKE

       Daga cikin abubuwan da aka ci karo da su a wannan aiki ko kuma bincike an fahimci cewa, al’ada ta kasance hanyar gudanar da rayuwar dan Adam tun daga haihuwa har zuwa mutuwa.

    A sakamakon wannan bincike da na gudanar ya sa an gano cewa Gusau gari ne mai matuƙar tarihi, musamman na musulunci. Wanda mun ga cewa a cikin tarihin garin na Gusau annuna cewa almajiran Shehu ne, da mabiyansa waɗanda da suka zauna a garin Yandoto su ne suka zo suka kafa garin Gusau, Har suka iso a wannan mazauni da ake kira Gusau.

    Ta hanyar wannan bincike an gano cewa, mutanen Gusau, mutane ne masu son biki kuma mutane ne waɗanda suka riƙi ko karƃa addin musulunci gadan-gadan.

     Har wa yau, a sakamakon wannan nazari an gano cewa, mutanen garin Gusau sun riƙe ad’adunsu na gargajiya ba su bari suka salwanta ba.

    Wani sakamako da aka gano a dalilin wannan bincike, shi ne na sanin ma’anar al’ada da kuma ire-iren al’ada daga ra’ayoyin masana daban- daban Kuma a ilmance mun ga me ake ce wa aure, kuma da yadda ake nemansa, duk a dalilin wannan bincike.

     A dalilin wannan bincike,an gano ya ake aiwatar da kamun amarya a al’adar Bahaushe musamman a garin Gusau. Kuma a sanadiyar wannan binciken ne muka san’al’adun da ake gudanar wa a wajen kamun Amarya musamman a garin Gusau.

     Daga ƙarshe, sakamakon wannan binciken an gano irin rawar da zamanenci ya yi wa al’adun kamun Amarya a garin Gusau.

    5.2 SHAWARWARI          

    Hausawa na cewa “ Shawara daukar daki” Kalmar shawara, kalma ce mai matukar muhimmanci da ma’ana Kalmar tana nufin ba wani ko wasu shawarwari akan abin da suka yi marasa kyau su daina ko kuma abin da suke yi mai kyau da su ci gaba da yin su.

     Da farko dai shawarar da na ke ba duk wanda zai karanta wannan bincike don wani nazari ko don wani abu daban,  to ya lura da aikin da aka yi mai taken “ AL’ADUN KAMUN AMARYA JIYA DA YAU A GARIN GUSAU”.

    Haka kuma ɗalibai y’an uwana ina ba ku shawara da ku riƙe aikin da aka baku a makaranta da muhimmanci musamman aiki irin na bincike domin yakan taimaka sosai wajen sanin fannoni na rayuwa da kuma yadda al’adu sukan canza daga zamani zuwa zamani tare da sanin dabarun zamantakewa nay au da kullum.

    Bugu da ƙari, kuma ina mai bada shawara ga dalibai masu kudurin shiga makaranta, da kuma yin nazari a kan Harshen Hausa da cewa su dauka daga inda na ajiye ko na tsaya. Musamman dangane da aiki irin wannan wanda ya danganci al’adun Hausawa.

    5.3 NAƊEWA:

       “Iyakar gudu Kuryar daki” In yi Hausawa. Wannan babi shi ne karshen wannan bincike ko nazari da aka gabatar a kan Al’adun kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau. Inda da farko an fito da kunshiyar aikin da aka yi domin zaman sa a matsayin  jagora ga wannan aikin.

       A babin na ɗaya an yi bayani a kan gabatarwa, shimfida, manufar bincike da kuma has ashen bincike, hadi da bayanin farfajiryar da binciken ya kebanta da ita, sai

    matsalolin bincike da hanyoyin gudanar da binciken sai nadewa duk a cikin wannan babi na ɗaya.

        Sai babi na biyu, inda aka yi bayani a kan shimfiɗa da kuma waiwaye ga wasu ayyuka da suka gabata makamancin wannan aiki nawa. Sai hujjar ci gaba da bincike da kawo bayani a kan tarihin garin Gusau sai naɗewa ta zo daga ƙarshe.

    Har ila yau, a babi na uku an yi bayani a kan shimfida da kuma kawo ma’anar al’ada da kuma ire-irenta da ma’anar aure da kashe-kashensa sai nadewa duk a cikin babi na uku.

    A babi na huɗu  kuwa an kawo shimfiɗa sai bayani a kan al’adun kamun Amarya jiya da yau a garin Gusau da kuma yadda a ke gudanar da al’adun sai naɗewa.

    Babi na biyar wanda kuma shi ne na ƙarshe a cikin wannan aiki an yi bayanin shimfiɗa da kuma kawo sakamakon abin da binciken ya ƙunsa. Sai kuma a ka  kawo manazarta daban.

     

     

    MANAZARTA

    Abdullahi . N.W. (2010) Bukukuwan Hausawa na Gargajiya. Muƙala da aka gabata Don Neman Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu   Danfodiyo.

    Abubakar, A.da wasu (2006). Tasirin zamananci a kan Al’adun Aure na Hausawa: Kebabben Nazari a garin Gusau. Kundin Neman Diploma Gusau. Sashen Hausa kwalejin kimiya da fasaha.

    Alhassan, H. Da wasu (1988) Zaman Hausawa Lagos.Islamic Publication Bureau.

    Bunza, A.M (2006) Gadon feɗe Al’ada Lagos. Tiwal Nigerian Ltd,16 Akinbaruwa Street, off Akinrase Street Surulere

    Bala, S. (2011) Tasirin zamananci a kan Auren Gargajiya a ƙasar Kwatarkwashi. Zariya.Kundin Digiri na Farko Sashen Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka Jami’ar Ahmadu Bello.

    CNHN(1981) Da wasu (1968) Hausa Customs. Zariya: Northern Nigerian Publication Company.

    Gusau, R.A (2014) Mai Dubun Nasara Rayuwa, Halaye Saƙonni, da jawaban Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau. Alhaji, (Dr) Kabir Ɗanbaba. Gusau Alhudah Ventures, ƙofar Masallacin Juma’a Na Rabi’a Sabon Gari Gusau Jihar Zamfara.

    Gusau, U.G. (2010) Al’adun Hausawa a cikin makarantun Allo : Nazari a kan wasu Al’adu da Suka Danganci karatu da Zamantakewa cikin Makarantun Allo. Gusau Sashen Koyar Da Harshe, Hausa. Kwalejin Fasaha Da Kimiya.

    Gusau, U.G (2012) Bukukuwan Hausawa. Gusau.01- Faith Prints.

    Galadanci, M.K.M Da wasu. (1992) Hausa Don Kananan Makarantun Sakandare na 2.Ibadan. Langman Nigerian Plc.

    Ibrahim, M.S.(1982) Dangantakar al’ada da Addini: Tasirin musulunci kan rayuwar   Hausawa ta Gargajiya. Kano kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Mu’azu, A. (2013) Baƙin Al’adu a kagaggun littattafan soyayya na Hausa. Zaria Ahmadu Bello University Press Limited.

    Yakasai, G.M.(2011) Al’adun Auren Zawarawa a ƙasar Hausa. Takarda da aka Gabatar a Mujallar Algaita Vol.2 No 1. Kano. Jami’ar Bayero.

    Yunusa, M.(2020) Tasirin Baƙin Al’adu a bukin Auren Hausawa. Takarda da aka Gabatar. Gusau. Ɗakin Malamai Kwalejin Fasaha da Kimiya.

    Zarruk, M.R Da wasu (1988) zaman Hausawa bugu na biyu. Lagos Islamic Publication Bureau.

    Hira:

    Hira da Hajiya Balkisu

    Rana : 5,9-2021.

    Wuri :Kofar Jange. Gusau

    Lokaci : 3 : 30 Pm

    Hira da Malam Abdulkadir Ahmad Mada.

     Rana: 8-9-2021.

    Wuri : Makarantar kwalejin fasaha da kimiya (ZACAS) Gusau.

    Lokaci : 5 : 00 Pm

                                                                 RATAYE

    Mai ba da waƙa:      Mai gidan kalage,

             Mai rimaye.

    Y/Amshi :            Mai gidan kalage,

                     Mai Rimaye.

     

    M/waƙa :             Mai gida kalage,

            Da ka mutu da na so.

     

    M/Waƙa:                Na baro zane na,

           A kan gadon masoyi.

    Y/Amshi           Mai gidan kalage,

            Mai Rimaye.

     

    M/waƙa :           Kwarkwata da kukan aure,

          Ade ya same ku,,

          Raƙumin dawa da Katanga,

          Me ya same ku,

          Aure ne dai ya same mu.

    Y/Amshi                Mai gidan kalage,

           Mai Rimaye.

     

    M/waƙa ;           Iro bayya cin gero,

            Iro bayya cin dawa,

            Alkama da shinkafa shi ma,

            Na baki ne,

            Markaɗe dabino da nono,

           Yakan sha shi.

    Y/Amshi               Mai gidan kalage,

          Mai Rimaye.

     

    M/waƙa ;              Na baro zanena a kan,

        Gadon masoyi.

    Y/Amashi          Mai gidan kalage,

       Mai Rimaye.

    Kutsen Baƙin Al’adu A Kamun Amarya Jiya Da Yau A Garin Gusau

    Kutsen Baƙin Al’adu A Kamun Amarya Jiya Da Yau A Garin Gusau

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.