MA'ANAR KISHI
Kishi wata
kalma ce ta Hausa dake nuna abin da mutum
ko waninsa ke ciki na son abu da ƙoƙarin kare shi ta hanya mai kyau ko mummuna.
In za a fadada za a iya cewa kishi wasu tunane-tunane ne da mutum ke yi waÉ—anda
ke bayyana a fuskarsa ko mu'amalolinsa, ko ma a maganganunsa yayin da da yake
zaton cewa akwai wani a kusa wanda yake ƙoƙarin hambare gwamnatinsa a daidai
lokacin da yake matuƙar son wani abu, ko da kuwa shi wancan din ya san da halin
da wannan yake ciki ko bai sani ba.
Kishi a wurin
Bahaushe kai tsaye kan rabu zuwa gida biyu ne, sai dai kowanne da dalilinsa:-
1) Akwai kishi
mai kyau, wanda ake kwadaitar da mutum ya yi, galibi yana nuna tattali ne da
son kariya, kamar kishin ƙasa ko na al'umma, ko miji ya yi kishin matarsa ta
wurin gyara suturta, muryarta, jikinta ko ma mutuncinta, ya killace ta sai dai
shi kadai, ko mace ta yi kishin mijinta ta wurinta kare sirrinsa da sirrin
gidansa. Wannan kam abin zargi ne ma in mutum bai sifantu da shi ba, yakan kuma
zama abin magana ga kowa.
2) Akwai kishi
mummuna wanda galibinsa son kai ne zalla, mutum kan rufe idonsa ya ƙi gane duk
wata gaskiya matuƙar ba za a bar masa abu shi kadai ne ba. Wannan kam abin
zargi ne ko da kuwa a tsakanin ma'aurata ne, wato: A maza dai akan sami namijin
da zai yi mummunan kishin da hujjar bai son ya rasa ne. A mata kuwa mace kan yi
ne hujjar tsoro galibi, ko da kuwa ita ce mai ƙarfin.
Ba yadda za a
iya cewa kishin namiji ko mace abu ne mai kyau ko mummuna sai an san haƙiƙaninsa,
in na ba da kariya ne ta hanya mai kyau wannan kam abin yabo ne, in ya fito na
son kai yadda mutum zai nuna shi kadai yake son ya mori abu wannan kam mummuna
ne, amma komai yana da dalilinsa, wani lokacin abu kan bayyana mummuna ne amma
in aka lura da dalilinsa sai ya yi bakan-zata. Ba duka kishi ne kyakkyawa ba,
haka ba kowanne ne za a watsar ba, abin
da muke so wannan dan littafi ya karanta ke nan a wannan lokacin.
Wai da gaske
ne kishin da mace ke yi a gida na ƙiyayya da duk wata matar da shiga rayuwar
mijinta ko da ba tare za su zauna a gida daya ba tsabar ƙauna ne ga maigida ko
tsoro ne na kar ta rasa falalar da da take samu a wurin maigidan? Ko tana jin
cewa ne amaryar za ta saka ta yin wasu abubuwan da da a baya ba ta yi? Ko kuma
gudun kar amaryar ta kore ta ne a gidan? Ko ba ta son a raba komai ne biyu ita
kadai take? Wasu dai a bayyane suke, wasu kuma Allah kadai ya bar wa kansa
sani.
Amma mun sani
wace za ta shigo ba cewa take wa uwargidan fita ki bar min gidan ni ma na dana
ba, akan sami taƙaddama ne a tsakaninsu, a ƙarshe shi maigidan ne alƙali, kuma
a hannunsa ne auren kowa yake, kodai amaryar ta bar gidan don ƙashin kanta in
taga azaba ta yi yawa, ko uwargidar ta kama gabanta da izinin wanda ya kawo ta
saboda ya ga Allah a zuciyarta. abin da babu
shakka a ciki da yawa amaren kan yi shakkun uwargida, masamman in sun ji
dabi'unta ba abin a yaba ba ne, wasu ma sukan fasa auren. Wasu lokutan kuma
uwayen gidan ne kan ta da hankulansu saboda tsoron waÉ—anda za su shigo,
masamman in amaren ba yara ba ne, ko kuma waɗanda idanunsu ya bude ne, ko wasu ƙabilu
ne da suka yi suna a wani fanni na rayuwa wanda ita uwargidan take ganin za a
bar ta a baya.
Bisa ga wannan
dan bayani za a fahimci cewa kishi na tattare ne da mummunan zato wanda ake
yanke hukunci a kan abin da bai da
tabbas don cimma buri. Kishi dai halittaccen lamari ne ga namiji ko mace. In ya
yi muni yakan kai ga yin kisa a kowani bangare, namiji kan iya kashe abokin
karawarsa don samun abin da yake nema.
Mace ma kan iya kashe wata don ta zauna ita kadai ko ta kai ga kwanciyar
hankalin da take zato. ko da yake mafi yawancin lokuta abin da mata ke fadi ba su ne ainihin dalilan
ba.
Duk muna sa
rai bayani zai zo sanka-sanka sai dai akwai kishin da in mutum ya yi yakan fasa
ne kowa ya rasa. Wani kuwa yakan haƙura ne da abu duk tsananin buƙatarsa da
shi, wani yakan fara bibiyar mafita ne, tare da sa rai da samun nasara. Wani
kuwa kan gwammace ya yi abida zai iya zama ajalinsa, da dai ya bari wani ya yi
tarayya da shi a abin da yake zaton a
hannunsa yake kuma nasa ne shi kadai. To in haka ne wasu abubuwan ne ke motsa
wa mutane kishinsu?
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.