ME KE KAWO KISHI?
Domin amsa
wannan tambayar dole sai an raba kishin zuwa gida biyu: Mai amfani da maras
amfani:
a) Za a iya
cewa akwai wasu 'yan dalilai dake kawo kishi mai amfani kamar:
i) Ƙauna:
Sonka da abu zai iya saka wa ka miƙe tsaye wajen tabbatar da shi, domin kana da
masaniyar cewa digirgire da shi zai iya kawo tintsirewarsa don haka za ka iya
amfani da harshe da harsashi wajen ganin ba
abin da ya ba ta shi. Duk lokacin da wani ya gigi wurinsa da wata manufa
za ka yi tsayuwar daka don kubutar da shi don shi ke ranka kuma shi kake ƙauna.
Muslunci bai
hana wannan ba, sai ma ƙarfafa shi ya yi, duk namijin da bai kishin iyalinsa,
ma'ana bai ba su kariya ta fannin da mummunan abu ba zai shafe su ba to ba
namiji ba ne, daga cikin waÉ—anda aka haramta musu aljanna akwai wanda bai iya
tsare iyalinsa. Da wannan kishin mutum ga iyalinsa yake nuna ƙaunarsa da su,
kuma ya zama wajibi.
ii) Ba su
Kariya: Ƙoƙarin da mutum yake yi wurin ba wa iyalinsa kariya alama ce dake nuna
ƙaunarsa gare su. Lallai ya tsare musu addininsu, da shigarsu ta sutura, ya
kare su daga shedanun aljanu da mutane yadda wani ba zai yi musu maganar banza
ba, ko ya kusance su da alfahasha ta kowani bangare. Wannan nuni ne ga kishin
da mutum yake wa iyalinsa.
iii) Janyo
Alkhairi: Duk yadda mutum ya ga wasu sun sami alkhairi ya yi kwadayin a ce nasa
ma ya samu, ko da kuwa ƙasa ce ko mutanensa ko ma iyalinsa. Matuƙar wasu can
nesa za su samu to ai kaima ya dace a ce iyalinka sun rabauta. Wannan ma kishi
ne amma mai kyau. A tsakanin mata in wata tana kyautata wa maigidanta wajen yi
masa duk abin da yake buƙata ke ma fara,
yi masa har da gyara, wannan ma kishi ne amma mai amfani.
b) Shi kuwa
kishi maras amfani yana da nasa dalilin da suka saba wa wannan, galibinsa ba da
aninyar alkhairi ake yinsa ba, wata manufa ce ta daban.
i) Ƙarancin
Imani: Idan imanin mutum ya yi ƙasa don ya ta da mummunan kishi ba wani abu ba
ne, duk wanda ke da imani ba zai je wajen boka ba, in har ya tafi ya yi wa
bautarsa babbar illa, Sharia ta ce mutum bai da rabo a lahira in ba dace ne ya
yi da rahamar Allah ba.
In imani ya yi
ƙasa mai mummunan kishi zai iya kisa, ko dai ya kashe mijin, ko kishiya ko ma
'ya'yanta. In wurin aiki ne zai iya kashe kowa, don abin da yake zuciyarsa mai zai sa wane ya
sami kaza, wannan kawai ya isa domin ya yi kama da hassada sosai.
ii) Yaranta ko
wautar ƙuruciya: Wannan ma wani dalili dake kawo mummunan kishi, idan muka ce
yaranta ba ma nufin ga yaro, haka ƙuruciya ba wai ma'anar mai ƙaramin shekaru
ba ne, a'a.
Duk babban da
ya aikata ayyukan da yaro ne zai yi to ya yi yaranta; kamar imani da abin da ba zai yuwu ba, misali namiji ya ce
wa matarsa ita ce tauraruwarsa ƙwara daya a sararin samaniyarsa, ita kuma ta
sani sarai taurarin dake sararin subhana Allan da ya yi su shi kadai ya san
yawansu. Ba yadda namiji zai ce mace ƙwaya daya ce a zuciyarsa bayan Allah SW
ya ba shi damar da zai so mata da yawa a zuciyarsa. Irin wannan yarda ke sakawa
ta amince wa kanta to ita kadai ce, duk lokacin da ya fara son wata sai ta ga
cewa ita ce ke ƙoƙarin shiga mata rayuwa, alhali amincewar da ta yi ta ba zai
so wata ba ta jawo mata.
Maganin irin
wannan kishin rashin saka wa kai cewa maigida ya kulle ƙofa ke nan wata ba za
ta shigo ba, bayan ke kina cikin gidan ne shi kuma kullum yana waje, kuma matan
ga sunan kala-kala a waje. Wace ta yi imani da cewa maigidanta zai iya ƙara
aure to ko ya yi maganar auren ba zai zama sabon abu a wurinta ba. Abu ne da ta
sani cewa zai iya faruwa, kuma in ta yi ƙoƙarin hana shi yin abida ya riga ya
yi niyya to sai dai cikin biyu a yi daya: Kodai ta haƙura akan dole ya yi auren
da ya yi niyya, ko kuma ta kama gabanta amaryar ta zauna a dakinta.
Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.