𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, malam ina so a yi min bayani kuma a taya ni addu'a, idan ina sallah
sai in shiga tunanin matsalolin rayuwa kuma abin yana damuna kuma na kiyaye da
abubuwan da na ji malamai suna cewa yana kawo hakan.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam, yawan yin waswasi da tunanin al'amuran duniya a cikin sallah yana rage
wa sallar mutum kamala har zuwa mutum ya sallame sallarsa, amma ba ya ɓata
sallar, kuma hakan na sa ba za a rubuta wa mutum komai na sallar ba face rabi
ko ɗaya bisa huɗu, ko ɗaya bisa goma, kamar yadda Sheikh Ibn Uthaimeen ya
bayyana.
Duba Fatáwá
Nurun Alad Darb 8/2.
Hadisi ya
tabbata daga Usman ɗan Abul Ási Allah ya ƙara masa yarda cewa: Shi Usman ɗin ya
zo wurin Manzon Allah ﷺ sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai shaiɗan ya shiga
tsakanina da sallata, yana rikita mini karatun sallata, sai Manzon Allah ﷺ ya
ce: "Wannan wani shaiɗani ne da ake kiransa da Khanzab, duk lokacin da ka
ji shi ka nemi tsarin Allah a kansa, ka tofa a ɓangaren hagunka sau uku",
sai Usman ɗin ya ce: Sai ko na aikata hakan, sai Allah ya tafiyar da shi daga
gare ni. Muslim 2203.
Wannan sai
ya nuna cewa duk lokacin da mai sallah ya yawaita jin waswasi da tunanin zuci a
sallarsa, to ya yi 'A'uzhu Billahi' ya tofa a ɓarin hagunsa sau uku, in Allah
ya so Allah zai tafiyar masa da wannan waswasi ko yawan tunani.
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.