𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam ina son bayanin hukuncin keɓance ranar Juma'a da Azumi idan ya dace da ranar Arfa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To Ɗan'uwa Annabi ﷺ ya kwadaitar game da yin Azumi ranar ARFA, inda ya tabbatar da cewa yana kankare zunubin shekaru biyu, Kamar yadda Tirmizi ya rawaito, sai dai ba a son wanda ya je aikin Hajji ya Yi azumin a ranar ARFA, ana so ya shagala da addu'a da zikiri a ranar.
Bukhari da Muslim sun rawaito hadisi daga Annabi ﷺ Yana cewa: "Kada ɗayanku ya azumci ranar Juma'a ita kaɗai, sai dai ya haɗa ta da ranar da take gabanta ko ranar da take kafin ita".
Bisa Hadisin da ya gabata za mu fahimci idan Arafa ta faɗo ranar Juma'a abin da yake daidai shi ne mutum ya azumci yinin da yake kafin ranar ARFA tare da ranar, saboda ba zai yiwu ya azumci yinin da yake bayan ARFA ba, tun da ya dace da ranar Sallah, Azumi kuma ranar Sallah ya haramta Kamar yadda ya zo a Hadisin Umar Ɗan Kaddab.
Duk da cewa akwai malaman da suka halatta keɓance ranar Juma'a da Azumi idan ta faɗo ranar ARFA saboda hujjar cewa an hana yin azumi ranar Juma'a ne ita kaɗai saboda Kar a keɓance ranar Juma'a da girmamawa, Wanda Kuma ya Yi azumin ARFA ranar Juma'a, ya yi ne saboda ARFA ba saboda girmama Juma'a ba, sai dai azumin ARFA duk girman falalarsa azumi ne na Nafila, Kuma Hadisin da ya hana keɓance ranar Juma'a da azumi akan azumin Nafila yake magana.
Duka kwanaki goman farkon Zulhijja kwanaki ne masu girman falala, babu kwanakin da suka fi su daraja a duniya, idan mutum ya azumci ranar takwas ya haɗa da ranar ARFA Yana kan alkairi Mai girma da kabakin lada mai maiko, sannan zai fita daga saɓanin malamai, Kuma zai samar da nutsuwa a zuciyarsa.
Allah ne Mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.