HUKUNCIN YIN MAGANA ACIKIN BANƊAKI

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

    Aslm mlm dan Allah inasan akaramin bayani akan magana cikin banɗaki (toilet) naji wasu nacewa akwai mala'iku suna tsinewa wanda ya yi magana abayi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

    Makaruhine ambaton Allah awajan biyan bukata, dan girmama sunan Allah maɗaukakin sarki bai kamata ka ambaceshi agurin najasaba, wanda kuma makwancin Shaiɗan ne.

    Imamun nawawy rahimahullah ya ce: acikin littafin al'azkaar, [ makaruhine ambaton Allah alokacin da mutum yake biyan buƙata, a sahara yake jeji kenan dajin Allah ko agurin da angina shi dan biyan bukata kawai, bawai Ambaton Allah kawai ba, dukkanin zikirai da zance na duniya inba da lalura ba, idan mutum ya yi attishawa abanɗaki bazaiyi tahmidi ba kuma baza'a amsa masa ba, haka idan mutum yana biyan bukata bazai amsa sallama ko ya mayar ba, haka kuma ba zai amsawa mai kiran sallah ba, zance a waɗannan gurare makruhine, dan tsarkake sunan Allah maɗaukakin sarki amma ba haramun bane, idan mutum ya yi attishawa sai ya godewa Allah azuciyarsa, harshensa bai motsa ba babu laifi, haka zai aikata ahalin dayake jima'i da matarsa.

    Dalili shine hadisi daka Abdullahi ɗan umar Allah yakara yarda dasu ya ce: Wani mutum ya wuce manzan Allah ﷺ yana fitsari sai yayiwa manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam sallama bai amsa masaba,) Muslim (370).

    Sabida haka idan wajen alwala yakasance acikin banɗaki ban dakin kuma bawajen wankane kawai ba, hukuncin karhancin ambaton Allah maganganun malamai sunci karo da juna awannan wajen tare da halaccin yin bismillah, wasu malaman suntafi akan zaiyi bismillar azuciyarsa ba tare daya furta da harshen saba.

    Wasu malaman kuma suka ce: zai yi bismillah da harshen sa ayayin alwala abanɗaki awannan lokacin babu karhancin.

    Yazo afatawar lajnatul da'ima cewa:"makaruhine ambaton Allah agurin da ake biyan bukata dan tsarkake sunan Allah da girmama shi, amma ya halatta ya yi bismillah yayin fara alwala domin wajibice awajen da yawa daka cikin malamai.

    Idan wajen alwala yakasance wajen banɗaki koda a jikin banɗaki yake kamar katanga daya gurin yake data banɗaki, Ya halatta ga mai alwala yafurta bismillah awannan hali domin awajen banɗaki ne.

    Saboda haka zance abanɗaki makruhine koda ba ambaton Allah bane, amma idan bukata ta kama Ya halatta kamar kana wanka ruwa yakare ma, zakayi magana dakarfi akawo ma ruwa ka karasa, ko kana gidan wanka na kuɗi shawa tadauke ruwa zakayi magana babu ruwa da makamantan uzuruka dazaka bukata aima kanada daka cikin banɗaki.


    ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠم


    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.