Hukuncin Yin Anfani Da Certificate Ɗin Wani

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne hukuncin mutumin da ya yi amfani da takardun shaidar kammala karatun da wani ya yi (Certificate) kuma yaje ya nemi aiki da su? Sannan kuma a shari'anace meye matsayin albashin da yake karɓa ta wannan hanyar?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    A shari'ance ba ya halatta mutum ya yi amfani da takardun shaidar sakamakon kammala karatun da wani yayi, wato (Certificate) ko kuma yaje ya nemi aiki da su, ko ya yi amfani da su ya nemi gurbin ƙaro karatu a wata makarantar, ko kuma Mutum yaje a yi masa waɗansu takardun bogi dan ya yi amfani da su wajen shiga wata makaranta ko kuma neman aiki da su, to dukkansu haramun ne bai halattaba. Domin idan har ya yi haka to ya karɓi abin da ƙwarewarsa ba ta cancanta ta sa ya karɓa ba.

    Hakanan ba ya halatta ga dukkan wani dalibin ilimi wanda zai riƙa satar amsar jarrabāwar wasu shi ma yana rubutawa a tasa, domin yin hakan kamar yāyi amfani ne da ƙokarin wasu ba nasa ba, kuma a bisa ga kā'ida a na so ne kowa ya yi amfani da irin ƙokarinsa da kuma ƙwarewarsa wajen fahimtar dukkan wani nau'i na Ilimi, ba wai mutum ya yi amfani da ƙwarewar wasu ba.

    Domin yin hakan ha'incine, dan haka haramun ne bai halattaba, haka nan kuma ba ya halatta ga dukkan wani Mālami a makaranta ko shugaba a wata ma'aikata wanda zai riƙa ɗaukan sakamakon karatun wasu dāliban ilimi māsu hazāƙa da ƙwāzo kuma yana sayarwa da wasu daƙiƙai, ko shakka babu wannan harāmun ne, domin yin hakan cin amāna ne babba.

    Sannan kuma duk wanda ya yi haka to ya sani cewa duk kuɗin da ya karɓa ta wannan hanya to yana cin harāmun ne, kuma sai Aʟʟαн(ﷻ) Yā tambaye shi a kan cin amānar da ya yiwa al'ummar da ya ke shugabanta, domin yā ɗauki ƙwarewarsu da ƙwāzonsu yā baiwa daƙiƙai waɗanda basu cancanta ba, haka kawai saboda zālunci da kuma son abin duniya.

    Sannan kuma a wasu makarantun a kan sāmu wasu daga cikin Mālamai marasa tsoron Aʟʟαн(ﷻ) kuma marasa kishin al'ummarsu waɗanda duk irin ƙwāzo da ƙokarin da Ɗālibi zai yi a makarantar to sai irin waɗannan Mālaman sun kāyar da shi matuƙar dai bai bā su wani cin hanciba, to a irin wannan yanayi idan ya kasance dālibi yāsan cewa tsakāninsa da Aʟʟαн(ﷻ) yana da ƙokarin da ya cancanta a bashi sakamako mai kyau a wajen karātunsa amma saboda zālunci irin na wasu Mālaman waɗanda zā su kāyar da shi idan bai basu wannan cin hancinba, to a nan sai Mālamai sukace babu laifi a kansa idan ya basu cin hanci ɗin saboda ya samu ya karɓi haƙƙinsa da suka riƙe masa, to amma su da suka karɓi wannan kuɗin su sani cewa sunci haramun ne, domin kuwa Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) ya ce:

    كل لحم نبت من سحت فالنار أولي به،

    MA'ANA:

    Dukkan nāman da ya tsiro daga cin hanci, (duk mutumin da yake ci ya koshi ta hanyar kuɗin haram) to wutā ce tafi cancanta da shi:

    Amma dangane da hukunci a kan wanda ya yi amfani da takardun wani ko kuma takardun bōgi yaje ya nemi aiki da su ya keyi, ko shakka babu wannan mutum yāyi algus, kuma Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) Yāfaɗa cewa:

    من غشنا فليس منا،

    رواه مسلم،

    MA'ANA:

    Duk wanda ya yi mana algus to bāya daga cikinmu, (Mu Muminai):

    Danhaka wājibi ne ya tuba zuwaga Aʟʟαн(ﷻ) a kan wannan babban zunubi da ya aikata, to amma dangane da abinda ya shāfi hukuncin kuɗin da ya ke karɓa a wajen aiki ko kuma hukuncin karatun da ya yi da takardun bōgi, abinda Mālamai sukace shi ne, idan har ya kasance ya yi karatun da matakinsa ya kai ga samun darajar da ta kai ko kuma ta haura wancan (Certificate) ɗin na wani da ya yi amfani da shi, Mālamai sukace babu komai a kansa sai dai ya tuba zuwa ga Aʟʟαн(ﷻ) a kan wancan hā'inci da ya aikata, amma idan ya kasance ya nemi aiki da takardun bōgi ko kuma takardun shaidar kammala karatun da wani yayi, to idan ƙwarewarsa a kan aikin ba ta kai na wanda ya samu irin wancan (Certificate) ɗin ba, to duk abinda ya karɓa haramun yake ci, domin yā karɓi albāshin da ƙwarewarsa ba ta kai ya karɓi irinsa ba, amma idan dāma yā ƙware sosai wajen iya wannan aikin da a ka ɗauke shi ɗin sai dai bashida takardar da za ta sa a ɗauke shi aiki a wajen sai ya yi amfani da takardun wani, to alal-haƙiƙa a nan ma ya yi ha'inci, amma idan yana aiwatar da yanayin aikin dai dai kamar yadda ake buƙāta to Mālamai sukace duk abinda ya ke karɓa na albāshi ya halatta, domin dama asali a shari'ance ba sharaɗi ba ne sai in mutum ya kāwo takardar shaida sannan za a ɗauke shi aiki ba, asali dāma ƙwarewarsa kawai ake buƙāta a kan wannan aikin da za a ba shi.

    Sai dai in dāma wannan ma'aikatar ta kafa sharaɗin cewa sai in mai sahihiyar shaidar karatu kaza-da-kaza za ta ɗauka aiki, to a nan kam komai ƙwarewarsa idan ya yi amfani da takardun bōgi a ka ɗauke shi aiki a wajen, to wasu daga cikin Mālamai sukace bai halatta ya yi wannan aikin ba, idan kuma ya yi to duk abinda ya karɓa na albāshi a wajen haramun yakeci.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

     Mυѕтαρнα Uѕмαи

     08032531505

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.