Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saƙonnin Da Ake Cewa Wanda Bai Tura Ba Zai Haɗu Da Bala'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Don Allah malam mene ne hukuncin saƙon da za a turo ana faɗin cewa an yi mafarki cewan duk wanda ya tura zai kasance cikin alkhairai masu yawa, wanda kuma bai tura ba bala'i da musiba za su afku mishi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam. A gaskiya Ire-iren waɗannan saƙonni da a ƙarshensu ake cewa idan ka tura wa adadin mutane kaza za ka ga abin alheri, idan kuma ka ƙi tura ma kowa za ka haɗu da bala'i da musiba nan da kwana kaza, duk irin waɗannan maganganu ƙarya ce kawai tsabarta, domin ko addini ba a ce dole ne sai an tilasta mutum ya yi ba, balle kuma tura wani saƙon da ba shi da asali.

Sau da yawa masu ƙirƙirar ire-iren waɗannan saƙonnin suna jingina ƙarya ga limamin Makka ko Madina ne, ko su jingina ƙarya ga mai gadin masallacin Annabi ﷺ su ce wai limamin Makka ko na Madina ko mai gadin masallatan ya yi mafarkin Manzon Allah ﷺ ya ce masa kaza da kaza, kuma Annabi ﷺ ya umarce shi ya isar wa da mutane wannan saƙo, kuma duk wanda ya ji ko ya ga wannan saƙo idan bai isar wa da adadin mutane kaza ba, to bala'i da musiba za su same shi nan da kwana kaza, idan kuma mutum ya isar wa da adadin mutane kaza ko kaza zai ga alheri a rayuwarsa.

Wani lokacin ma har da rantsuwa suke haɗa wa su ce wai wani mutum a wani gari ko wata ƙasa ya ga wannan saƙo ya tura wa adadin mutane kaza sai ya sami alheri mai yawa a rayuwarsa, wani kuma ya ga saƙon sai ya ƙi tura ma kowa sai Allah ya mayar da shi biri, ko kare, ko su ce wai ya sami karayar arziki saboda ƙin tura ma kowa.

A gaskiya duk irin waɗannan saƙonni ƙarya ce tsantsa suke jingina ma waɗancan limamai ko masu gadin Haramain, kuma ƙarya ce tsantsa suke wa Annabi ﷺ Kuma Annabi ﷺ ya ce: "Duk wanda ya jingina mini ƙarya da gangan ya jiraci masaukinsa a wuta".

Bukhariy 1291. Muslim 3004.

Addini ya riga ya cika, babu wani alheri da Annabi ﷺ ya bar shi bai nuna ma al’ummarsa ba, haka kuma ba wani sharri da bai faɗakar da mu shi ba. Don haka mu guji yi wa Annabi ﷺ ƙarya da yaɗa ƙaryar da aka yi masa, Allah ya kare mu da yi wa Annabi ﷺ ƙarya, amin.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.watsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments