Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Aiki A Banki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam na kasance mai aiki a unionbank na wata shida a shekara sai na huta na wata shida , ba a biya na salaryi dan ina hutu. to kwanakin baya na saurari wani scholar yana bada fatawa cewa babu kyau musulmi ya yi aiki a banki wai ko da aikin security ne. haramu ne saboda akwai haramci a ayukan da banki keyi kaman bayar da bashi kuma abiya da kuɗin ruwa help me out saboda yanxu lokaci ya kai wanda zan koma bakin aiki amma ina tsoron ciyar da iyali na da haramu

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Indai irin bankunan da suke amfani da kuɗin ruwa ne, to bai halatta ka yi aiki a cikinsu ba. Ta kowacce fuska.

Hujjah anan ita ce Hadisin Jabir bn Abdillah Al-Ansary (ra).

"Manzon Allah ﷺ ya tsine wa mai cin Kuɗin ruwa, da mai bayarwa, da mai rubutawa, da mai shaidawa. Yace Dukkansu daidai da daidai suke a cikin laifin (zunubin).

(Sahihu Muslim, Hadisi na 1598).

A cikin Sharhin da ya yi ma wannan hadisin, IMAMU SHARAFUDDEEN AN-NAWAWY (rah) ya ce: "Wannan hujjah ce Ƙarara wacce take nuna haramcin yin aikin rubutu ko shaidawa a cikin duk wata hulda tsakanin mutum biyu masu cinikin kuɗin ruwa. Kuma ya nuna haramcin taimakawa wani a cikin Aikata saɓon Allah".

Babu makawa duk mutumin da yake aiki a irin waɗannan bankunan dole ne zai taka rawa a cikin harkar kuɗin ruwa.

Ko mai gadi ne, ko mai shara ne, ko Clerk ne. Sannan kuma dole ne abiyashi albashi da kuɗin ruwa.

Don haka gara ka nemi wani aikin mai tsafta.

"Duk wanda yaji tsoron Allah, to Allah zai sanya masa Mafita. Kuma zai azurtashi ta inda ba ya zato. Duk wanda ya dogara da Allah, to shi Allah ɗin zai isar masa"

(Suratul-Talaƙ ayah ta 2 - 3).

WALLAHU A'ALAMU.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments