𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah, Don Allaah ina son a tambaya mini Malam: Kwana nawa ne adadin kwanakin jinin biƙin haihuwa; domin na ji wani yana cewa wai idan jinin bai tsaya a kwana arba’in (40) ba, za a iya kai wa har kwanaki sittin (60). Ina son ƙarin bayani, please .
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Al-Imaam Abu-Daawud da Al-Imaam At-Tirmiziy da Al-Imaam Ibn Maajah duk sun riwaito hadisin da Al-Imaam Al-Muhaddith Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Al-Irwaa’u (lamba: 201), daga Sahabiya Ummul-Mu’mineen Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa:
A zamanin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ita mai jinin haihuwa tana zama a cikin jininta har zuwa kwa…
ADADIN KWANAKIN JININ
HAIHUWA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa
Rahmatul Laah, Don Allaah ina son a tambaya mini Malam: Kwana nawa ne adadin
kwanakin jinin biƙin haihuwa; domin na ji wani yana cewa wai idan jinin bai
tsaya a kwana arba’in (40) ba, za a iya kai wa har kwanaki
sittin (60). Ina son ƙarin bayani, please.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Al-Imaam Abu-Daawud
da Al-Imaam At-Tirmiziy da Al-Imaam Ibn Maajah duk sun riwaito hadisin da
Al-Imaam Al-Muhaddith Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Al-Irwaa’u (lamba:
201), daga Sahabiya Ummul-Mu’mineen Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: A
zamanin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ita mai jinin
haihuwa tana zama a cikin jininta har zuwa kwanaki arba’in ne. Kuma ba ya
umurtan ta da rama sallolin da ba ta yi su a halin tana jinin haihuwar ba.
Al-Imaam Abu-Isaa
At-Tirmiziy a ƙarshen riwayarsa ga wannan hadisin ya ce: ‘Malamai
ma’abuta ilimi daga cikin Sahabban Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu
duk sun haɗu a kan cewa: Ita mai
jinin haihuwa tana barin yin sallah na tsawon kwanaki arba’in ne, sai dai ko in
ta ga tsarki kafin hakan. Daga nan sai ta yi wanka ta ci gaba da sallah. Idan
kuma ta ga jinin a bayan kwanaki arba’in ɗin ne, to mafi-yawan malamai masana ilimi sun
ce, ba za ta bar yin sallah a bayan kwana arba’in ba. Wannan kuma shi ne
maganar mafi-yawa daga cikin malaman Fiƙhu, shi ne maganar
Sufyaan At-Thawriy, da Ibn Al-Mubaarak, da As-Shaafi’iy, da Ahmad, da Is’haaƙ.’
Shaikhul Islaam Ibn
Taimiyah (Rahimahul Laah) ya ce: ‘Jinin haihuwa ba shi da iyaka ta fuskar ƙaranci ko ta fuskar
yawa. Don haka, idan aka ƙaddara cewa wata mace ta ga zuban jinin fiye da kawanaki
arba’in ko sittin ko saba’in
kuma a yanyanke, to dai jinin haihuwa ne. Amma idan a haɗe da juna ne, to shi
jinin istihaalah ne, kuma a lokacin sai a ce: Bakin iyakan kwanakinsa arba’in
ne, domin shi ne iyakan kwanakin yawancin mata, kamar yadda hadisi ya nuna.’
(Tamaamul Minnah: 1/144).
Ibn Ƙudaamah Al-Maƙdisiy a cikin
littafinsa Al-Mughnee: 1/392 ya ce: ‘Idan jinin haihuwa ya zarce kwanaki
arba’in sai kuma ya dace da lokacin al’ada, to shi haila ne. Idan kuwa bai dace
ba, to shi Istihaalah ne.’
Game da matar da ta
tsarkaka daga jinin haihuwa kafin kwana arba’in, daga baya kuma sai jinin ya
dawo mata kafin cikan kwanaki arba’in ɗin, shi ne Al-Allaamah Ibn Al-Uthaimeen
(Rahimahul Laah) a cikin As-Sharh Al-Mumti’: 1/450 ya ce: ‘Sai ta lura da
alamomin jinin: Idan ta ga siffofin jinin haihuwa a tare da shi, to jinin
haihuwa ne. Idan kuwa alamun ba su nuna shi jinin haihuwa ba ne, to ita mai
tsarki ce. Kuma Allaah shi ne Masani.’
Al-Imaam Al-Muhaddith
Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) kuma ya ce: ‘Mace tana zama har kwana arba’in ne a
matsayin mai jinin haihuwa. Idan kuma jinin ya yi ta-zarce a bayan haka, to sai
a ba ta hukuncin mai Istihaadah.’ (Al-Mausuu’ah: 1/269).
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad
Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.