𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ina son bayani a kan ayoyin da ake sujjada idan an biyo ta kansu wajen karatu, shin idan ina jan mutane sallah sai ayar ta zo, ya halatta in tsallake ta domin gudun kawo rudani?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله العليم
الحكيم.
Guraren da ake sujjada acikin Alƙur'ani guda goma sha biyar ne, daka Amru bin Ãass Manzan Allah ya karantar dashi sujjada goma sha biyar acikin Alƙur'ani daka cikinsu akwai, guri uku asurori masu tsawo tsaka-tsakiya, acikin suratul hajji akwai sujjada guda biyu.
"Abu dauda da Ibnu majah da hakim da darul Ƙudny munzry ya kyautatashi, Sune:
1- إِنَّ الَّذِينَ
عِنْدَ رَبِّكَ لَا يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيُسَبِّحُونَهُ وَلَهُ يَسْجُدُونَ
۩
Suratul A'araf /206.
2- وَلِلَّهِ يَسْجُدُ
مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ طَوْعًا وَكَرْهًا وَظِلَالُهُمْ بِالْغُدُوِّ
وَالْآصَالِ ۩
Suratul ra'adi /15.
3- وَلِلَّهِ يَسْجُدُ
مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مِنْ دَابَّةٍ وَالْمَلَائِكَةُ وَهُمْ
لَا يَسْتَكْبِرُونَ
Suratul Nahli/49
4- قُلْ آمِنُوا
بِهِ أَوْ لَا تُؤْمِنُوا ۚ إِنَّ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ مِنْ قَبْلِهِ إِذَا
يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ يَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ سُجَّدًا
Suratul Isra'i/107
5- إِذَا تُتْلَىٰ
عَلَيْهِمْ آيَاتُ الرَّحْمَٰنِ خَرُّوا سُجَّدًا وَبُكِيًّا ۩
Suratu Maryam/58
6- أَلَمْ تَرَ
أَنَّ اللَّهَ يَسْجُدُ لَهُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَمَنْ فِي الْأَرْضِ وَالشَّمْسُ
وَالْقَمَرُ وَالنُّجُومُ وَالْجِبَالُ وَالشَّجَرُ وَالدَّوَابُّ وَكَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ
ۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيْهِ الْعَذَابُ ۗ وَمَنْ يُهِنِ اللَّهُ فَمَا لَهُ مِنْ مُكْرِمٍ
ۚ إِنَّ اللَّهَ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ ۩
Suratul Hajji /18.
7- يَا أَيُّهَا
الَّذِينَ آمَنُوا ارْكَعُوا وَاسْجُدُوا وَاعْبُدُوا رَبَّكُمْ وَافْعَلُوا الْخَيْرَ
لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ ۩
Suratul Hajji/77.
8- وَإِذَا قِيلَ
لَهُمُ اسْجُدُوا لِلرَّحْمَٰنِ قَالُوا وَمَا الرَّحْمَٰنُ أَنَسْجُدُ لِمَا تَأْمُرُنَا
وَزَادَهُمْ نُفُورًا ۩
Suratul Furƙan/60.
9- أَلَّا يَسْجُدُوا
لِلَّهِ الَّذِي يُخْرِجُ الْخَبْءَ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا
تُخْفُونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
Suratul Namli/25.
10- إِنَّمَا يُؤْمِنُ
بِآيَاتِنَا الَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُوا بِهَا خَرُّوا سُجَّدًا وَسَبَّحُوا بِحَمْدِ
رَبِّهِمْ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ ۩
Suratul Sajada /15.
11- وَظَنَّ دَاوُودُ
أَنَّمَا فَتَنَّاهُ فَاسْتَغْفَرَ رَبَّهُ وَخَرَّ رَاكِعًا وَأَنَابَ ۩
Suratu Sããd/24.
12- وَمِنْ آيَاتِهِ
اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ ۚ لَا تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلَا
لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ
Suratul Fussilat/ 37.
13- فَاسْجُدُوا
لِلَّهِ وَاعْبُدُوا ۩
Suratul Najmi/63.
14- وَإِذَا قُرِئَ
عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لَا يَسْجُدُونَ ۩
Suratul Inshiƙaƙi/21.
15- كَلَّا لَا
تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِبْ ۩
SuratulAlaƙ/19.
Duba fiƙhussunnah(1/186-188).
Shaik Albany Allah yajikansa acikin tamamul Minnah shafi na (269) Ya ce: Wannan hadisi ba hasan bane, acikin Isanadinsa akwai wadanda ba'a sansu ba mutum biyu, Haƙiƙa Alhafiz bin hajar yafada acikin *Attalkees bayan ya ciro kyautata hadisin da Munziri da Nawawi sukaiwa hadisin, Abdul haƙƙ ya raunanashi da ibnu ƙaddaan, acikinsa akwai Abdullahi bin muneen, wanda ba'a san shi ba, wanda yaruwaito shi daka gareshi shi ne Haris bin Sa'eed utƙy Shima bai sanshi ba, ibnu Makulah ya ce: Bashi da wani hadisi daya ruwaito banda wannan.
Saboda haka Addahawy yazabi cewa babu Sujjada ta biyu acikin "Suratul Hajji kusa da karshenta, ita ce Mazhabar ibnu hazama acikin Muhallah ya ce: domin Babu wata sunnah data inganta daka Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam, bakuma ahadu akanta ba, ya inganta daka Umar da Ɗansa Abdullahi da Abiy dar-da'i sun yi sujjada acikinta.
Sannan ibnu hazam yatafi akan shar'antuwar yin sujjada dayan gurin na suratul hajji acikin littafin, ya Ambaci na goman farko Malamai Sun haɗu akan shar'antuwar sujjada acikinta awajan malamai, hakama addahawy ya hakaito ittifaƙi akanta acikin "Sharhul Ma'any (1/211).
saidai shi yasanya sujjadar cikin suratul fussilat amadadin sujjadar suratu Saaad, sannan yafitar musu da isnadai ingantattu daka Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya yi sujjada acikin ( Sààd) da (Annajmi) da (Al'inshiƙaƙi) da (Iƙra'a)wadannan guda ukun na karshe suna cikin surori matsakaita wadanda hadisin Amru da Muka Ambata afarko yai nuni akansu.
Adunƙule hadisin duk da Raunin isnadinsa, Haƙiƙa ittifaƙin Al'ummah ya shaideshi akan aiki da mafi rinjayensa, dakuma Samun hadisai ingantattu dasuke bada shaida akan sauran, sai sujjadar Suratul hajji ta Biyu ba'a samu Abunda yabada shaida akan yinta ba daka cikin Sunnah, da Ittifaƙi, saidai aikin wasu sahabbai dasuke sujjada insunzo kanta, wannan zai iyasa anutsu da shar'antuwar yi mata sujjadar musamman ba'asan wanda ya saɓa musu akai ba.
Atakaice sujjadar tilawa anayinta Agurare sha bakwai da Muka Ambata.
Sujjadar tilawa Sunnah ce Awajan jamhur din Malaman fiƙhu, domin Yatabbata Acikin Sahihul Bukhary Umar Ɗan Khaddab yakaranta Suratul Nahli ranar juma'a akan Munbari harsaida yazo wajan yin Sujjada ya sakko daka munbari yai sujjada mutane ma suka yi sujjadar tare dashi, dawata juma'ar tazo saiya sake karantata harsaida yazo wajan yin sujjadar saiya ce: Yaku Mutane Zamu wuce wajan yin Sujjada wanda yai Sujjada yadace wanda baiyiba babu komai akansa, Umar baiyi Sujjadar ba. Sahabbai suka tabbatar dashi Akan haka babu Wanda yai Masa Inkari koya Saɓa masa, wannan yanuna ijma'in sahabbai akan haka, wannan kuma raddine ga wadanda suke wajabta sujjadar tilawa gamai karatu idan yakaranta Ayar da'akewa Sujjada.
Anayin Sujjadar tilawa acikin Sallah da Wajen Sallah, idan awajen Sallah ne, Sunnah shi ne kayi sujjada ahalin da kake, idan atsaye kake za ka duka kayi sujjadar, idan azaune kake za kai sujjadar kana zaune, Ba sharadi bane saika tashi tsaye sannan ka duƙa kayita, Wasu malamai sun mustabbantar da miƙewar, kamar yanda ibnu taimiyya ya hakaito daka daliban Imamu Shafi'iy da Ahmad da wasunsu kamar yanda aka ciro daka Aisha.
Idan kakaranta Ayar sujjada Kana cikin Sallah sunnah ne kayi sujjadar kana kai ayar, saika cika sallarka, kanada zaɓi, inkaso za ka karanta ta saikayi ruku'u kokai ruku'u batare da ka karanta ta ba, sunnah ne acikin sallar ɓoye karatu dawacce ake bayyana karatu.
Saidai bai kamata liman ya yi Sujjadar Asallar da'ake ɓoye karatuba domin hakan zai rikita Masu bin sallar, saboda haka wasu malaman fiƙhu suka karhanta.
Sujudul tilawa ba ta da Wasu sharudda nayinta. kawai dakazo za ka duƙa kayi sujjadar ne, kayi addu'ar da'ake asujjadar shikenan.
سَجَدَ وَجْهِيَ لِلَّذِي خَلَقَهُ، وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَرَهُ، بِحَوْلِهِ وَقُوَّتِهِ، فَتَبَارَكَ اللهُ أَحسَنُ الْخَالِقِي
"Fuskata ta yi Sujada ga wanda Ya halicce ta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta, da iyawarsa da kuma Karfinsa. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita."
Sannan Ba wajibi bace, bakuma dolene liman sai yayiba idan yakarantata acikin sallah, saboda dalilin da muka gabatar asama.
Kuma batsallake ayar zaiyiba, zai karanta batareda ya yi sujjadar ba.
Idan kuma yasan mamu dinsa suna da ƙarancin sanin Addini to Anan kwarewar fahimtar shari'a shi ne yakaranta yawuce ba tare dayayi sujjadar ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Tambaya
Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya
bi ta Links ɗin mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.