Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mace Mai Janabah Za Ta Iya Shayar Da Jaririnta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malan ina wuni. Dan Allah ina da tambaya: An ce in mace tana da janaba a jikin ta babu kyau ta shayar da ɗan ta. Shin yaya abun yake? Nagode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Gaskiya dai ni ban san wata ayah ko hadisin da a cikinsa aka haramta wa mace ta shayar da yaronta alokacin da take da janabah ba. Hasali ma ban taɓa jin haka daga bakin wani Malami daga Maluman Fiƙhu ba, ko awani littafi daga litattafan Fiƙhu.

Sai dai abin da ya zamto tabbatacce shi ne ya halatta mace mai haila ko mai janabah ko mai jinin biƙi ta shayar da jaririnta awannan yana yin da take ciki. Domin babu abin da yazo a kan haramcin yin haka, kuma shi addinin musulunci sauki gareshi babu Ƙuntatawa.

Abin da bai halatta gareta ba, shi ne aiwatar da wata ibadah wacce ake bukatar tsarkin jiki a cikinta. Misali kamar sallah, ko dawafi ko ɗaukar Alƙur'ani Mai girma. Hakanan ba ya halatta ga mijinta ya sadu da ita bayan daukewar jini har sai ta yi wanka.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments