Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyar Tuba Da Kuma Rabuwa Da Istimna'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahamatullah. Da fatan malam ya tashi lafiya Allah ya kara wa malam lafiya da nisan kwana. Allah ya sa agama da duniya lafiya Allah yasaka da alkhairi da taimakon mu da kakeyi.

 Malam inada tambaya kamar haka. Nine Allah ya jarrabeni da yin istimna'i abun ya dameni sai na daina tsawon lokaci sai wani photo na banza da na gani sai sha'awata ta motsa har sai naje na aikata wannan aikin.

Gaskiya na dade ina yi kuma gashi ina azumi lokaci lokaci domin in daina amma na gagara don dai yanzu ma na daina duk abin da zai jawo min yin facebook ne ko opera ko Instagram dadai sauran chatting duk na gogesu awayata kuma bana yi sai naga photon banza ko shigar banza don yanzu na karfafa niyyata a kan ba zan sakeba.

Ataimakeni da addu'a nadaina Allah ya shiryeni Allah ya sa nagaji fili Allah ya horemin halin yin aure nagode.

Amma fa babu wanda yasan ina yin wannan abun sai Allah sai malam da nake tambaya.

 A taimakeni da addu' a Allah ya ba ni damar yin aure kar na mutu a kan wannan mummunar hanya ta istimna'i. nagode malam daga dalibinka

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika dukkanmu masu kuskure ne, sai dai mafiya alkhairi a cikinmu sune masu tuba daga kusakurai tare da neman gafarar Allah da afuwarsa bisa abin da suka gabatar na kusakurai.

Naji dadi sosai bisa bayanin da kayi game da kyakkyawar niyyarka ta yin cikakkiyar tuba daga wannan babban kuskure, kuma ina yi maka fatan Allah shi karbi tubanka da namu baki daya, ya sanyamu cikin waɗanda yake shafe dukkan zunubansu, yake juyar da munanan ayyukansu su zama ayyuakan lada, kuma ya keɓancesu da falalarsa Maɗaukakiya.

Irin wannan tuban tana da wasu sharudan da ya kamata ka tabbatar ka kiyayesu kamar haka:

1. Yin nadama bisa abin da ka aikata abaya.

2. Daukar niyyar ba zaka sake aikatawa ba, har abada.

3. Guje wa duk wani dalili ko hanyar da za ta kaika zuwa ga sake tsunduma cikin irin wannan laifin.

Ina nufin kamar kauracewa shiga websites na batsa, ko groups ba batsa a facebook ko whatsapp, da sauransu.

Sannan kayi kokari kayi aure domin taimaka wa zuciyarka wajen kiyaye umurnin Allah da Manzonsa ﷺ ta wajen runtse idanuwanka daga kallon matan da ba su halatta gareka ba, da kuma kiyaye al'aurarka daga dukkan nau'o'in saɓon Allah. Har dukkan gabobin jikinka ma.

Sannan ka lazimci yawan zikirin Allah da karatun Alƙur'ani da azkar safe da yamma da zama da mutanen kirki, da yawaita nafilfilin dare da rana tare da yawaita yin addu'a bisa kanka da iyayenka da 'yan uwanka da dukkan Musulmai baki daya.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments