Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Yi Zina Da Dabba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam Khamis da fatan ka wuni lafiya. Allah ya saka da alkhairi. Tambaya ta ana shi ne na kasance ina yin zina da dabbobi saboda tsananin sha'awa. mene ne Hukuncin Wanda ya yi zina da dabba a musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Allah Ya Tsinewa Wanda duk Ya Sadu da Babba. Dabban nan Safiya Ce Ko Tinkiya Ko Akuya Ko Agwagwa Ko Kaza; da Makamantansu. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عن إبن عباس رضي الله عنه قال: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: ”ملعون من ‏ ‏وقع ‏ ‏على بهيمة.

{رواه أحمد}

An Kar6o Daga Ibn Abbas (ra) Ya ce: Manzon Allah (ﷺ) Ya ce: “Tsinanne Ne Duk Wanda Ya Aukawa Dabba;”.

{Ahmad Ya Ruwaitoshi}

Saboda Munin Wannan Aiki Ne Ubangiji ya yi Umurni da Kashe Duk Wanda Aka Kama Yana Saduwa da Dabba, Kai Har Ita Dabbar ba ta tsira ba Domin Itama Kashe ta Za'ayi. Wannan Ke Nuna Munin Zakkewa Dabba Yafi Munin Zina. Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عَنْ عِكْرِمَةَ عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ”مَنْ وَجَدْتُمُوهُ وَقَعَ عَلَى بَهِيمَةٍ فَاقْتُلُوهُ وَاقْتُلُوا الْبَهِيمَةَ

{الترمذي: ١٤٥٥}

An Kar6o Daga Ikramah, Daga Ibn Abbas (ra) Ya ce: Manzon Allah (ﷺ) Ya ce: “Duk Wanda Kuka Sameshi Yana Saduwa da Dabba, To Ku Kashe Shi Kuma ku Kashe Dabbar”.

{Tirmizi: 1400}

Amma sai malamai sukayi bayani cewa hadisin akwai kokonto A ingancisa dan haka sukace ba za a akashe shiba saide ayi masa bulala kuma akaishi kurkuku wasu malamai kuma su kace yanada hukuncin mazinaci idan ya yi aure a jefeshi har ya mutu. Idan baiyi aure ba ayimasa bulala.

ALLAH shi ne mafi sani

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments