Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Mu'amalar Aure Mun Yi Da Wanda Ba Mijina Ba, Amma Ban Da Jima'i, Yaya Hukuncina?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Da fatan ka tashi lafiya, tambayata ita ce dan Allah a yi min bayani, wata yarinya ce mijinta yana aikin kwana sai ya kawo dan haya gidan, amma kofar kowa daban take, to malam ya nuna kanshi shi kamar yana da kirki suna gaisawa har yake ba wa yaranta kyauta, ya kan siyo musu kyaututtuka tin suna kin karɓa har aka bar su suna karɓa, malam sai ya ce ba komai shi dan Allah yake ba su, to har ya zamana suna gaisawa da matar har suna hira, shi ne har ya fara mata wasan banza, shi ne sai ta daina kula shi, sai ya ba ta hakuri, to malam a takaice dai wataran yana rungumarta har ya kawo maniyyi a jikinta ko a cinyarta, to malam ita ma har ya fara kawo mata sha'awa idan ya danne ta da kayanta yana nishi ita ma takan ji daɗi, amma ba su taɓa haɗa gabansu ba wajen aikata zina, amma yanzu tana ta kuka tana neman gafarar Allah ya tsare ta daga sharrinshi, da na mijinta, saboda shi ma yana ɗaukar hakkinta, ta yi ta yi ya komar da ita gun aikinshi ya ki, to dan Allah mlm shi ne nake neman fatawa ya matsayin abin yake? Shin ya zama zina ko sai an samu saduwa ne tsakanin mace da na miji shi ne zina? a taimaka mana malam, na gode Allah ya saka ma da alkairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Inna lillahi wa innah Ilaihi Raji'un! Wannan mummunan aiki ne, kuma cin amana ce, yaya za ta ji idan ta sami labarin cewa mijinta yana neman matan banza a waje? Wannan aiki ne haramtacce abin ƙyama a addinin musulunci, har ma a al'adar rayuwa. Duk da cewa kai tsaye ba za a kira wannan aikin da zina ba, to amma kuma muninsa ya kai na zina, saboda zina kala-kala ne, akwai zina da idanuwa, akwai zina da kunnuwa, akwai zina da harshe, akwai zina da hannuwa, akwai zina da ƙafafuwa kamar yadda Annabi ya bayyana a hadisi.

Manzon Allah ya ce: "Ka ga idanuwa, zinarsu ita ce kallo, zinar kunnuwa kuma ita ce saurare, zinar harshe kuma ita ce magana, zinar hannu kuma ita ce shafa, su kuma ƙafafuwa zinarsu ita ce tafiya (zuwa ga zina), ita kuma zuciya sai ta yi ta buri da sha'awa, abin da ke gaskata waɗannan abubuwa, ko ya ƙarya ta su shi ne farji (azzakari).

Bukhariy 6612, Muslim 2657.

Wannan dalili ne da ke nuna wannan aiki da wannan mata ta yi da wancan bawan Allah, ba za a kira shi da zina na asali ba, saboda bai sadu da ita kaciya da kaciya ba, inda za a iya kiran zina yaya da ƙaninsa, da sai a kira wannan baƙin aiki da suka yi ƙanin zina, Allah ya kare mu.

Abin da za ta yi shi ne, ta yi cikakkiyar nadama, ta tuba zuwa ga Allah, irin tubar da babu tunanin komawa ga wannan saɓon Allah ɗin har abada, ta yi ta yawaita istigfari. In Allah ya so muna fatan Allah ya karɓi tubanta, Allah ya shiryar da mu, ya kare mu da mugun ji da mugun gani, amin.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments