Ticker

6/recent/ticker-posts

Tun Da Abokiyar Zamana Ta Je Gida Jego, Mijinmu Bai Ƙara Kwana A Ɗakina Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam brka da asuba dftr an tashi lfy dan Allah inada tammbaya mijina ne to mu biyu ne agurinshi sai matar shi ta tafi gida wanka jego to wlh mlm tun lokacin da tatafi bai kara shiga dakina ba da sunan wai yadawo kasuwa kamar yadda yakeyi in tana nan saidai yashiga ya dauke abin da xai dauka yafita Amman jiya tana dawowa daga jegon sai yashiga dakinta ya yi adalci shin ko baiyi ba Allah yakarawa malam lfy

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumussalam warahmatullah

Todai farko sai ki tambaye shi ko hakan yana da asali a addini, domin akwai wadanda suke da tunanin gargajiya, wai idan mace daya tatafi jego gidansu alhalin yana da wata matar sai ya daina shiga dakin dayar, waikuma ahakan yana ganin adalci ya yiwa wadda ta tafi gidansu, yanzu dan Allah idan ban da rashin tunani ai auren mace sama da daya baiyi masa anfani ba, wannan matsalar kuma tasamo asaline adalilin rashin karatu, dan haka kifara tambayarsa idan ya ba ki irin wannan hujjar sai ki fada masa kuskurene cikin hikima, idan bai gane ba a fada wa wadanda yake jin maganarsu, amma zancen gaskiya wannan zalunci ne an danne miki hakkinki, a ƙa'ida idan mace ta yi tafiya ba a rama mata kwanakin da ta yi, amma idan namiji ne ya yi tafiya yadawo to dole ne a sake sabon rabon kwana sai dai idan ya tafi da ragowar bashin kwanan wata a kansa wannan dole sai ya rama mata

Allah ya sa mu dace.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments