Ticker

6/recent/ticker-posts

Gasar Rubutattun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmed Musa Dangiwa - Zagaye Na Biyu

GAME DA GASAR RUBUTATTUN LABARAN HAUSA TA ARC. AHMED MUSA ƊANGIWA ZAGAYE NA BIYU, 2022

Gasar Rubutu

1. Gasa ta fara daga ranar 20 ga watan Fabrairu, 2022 (20/02/2022), don haka masu sha'awar shiga za su tura samfurin (tsakuren) labarinsu tun daga wannan rana har zuwa 20 ga Maris, 2022 (20/03/2022), in da za a rufe amsar samfurin. Wato kwanaki 30 kawai masu aika samfurin labari suke da shi. A tura somin-taɓin labari a fasalin PDF ko Word Document zuwa ga adireshin imel na dangiwaliterary2020@gmail.com.

2. Za a tace samfuran labaran duk da aka tura ta wancan imel a kan lokacin da aka ƙayyade, sai a fito da guda 30 daga cikinsu, waɗanda suka fi ƙayatarwa da dacewa ta ƙa'idoji da dokokin wannan gasa. Labaran da suka sami nasara su ne suka tsallake zagaye na farko kenan. Za a yi taciyar ne a tsakanin 20 ga Maris, 2022 (20/03/2022) zuwa 4 ga Afirilu, 2022 (04/04/2022). Za a bayyana ma duk wanda samfurin labarinsa ya ƙetare zuwa zagaye na biyu, sannan a buƙaci da ya kawo ƙarashen labarin wanda bai gaza a kalmomi 3000 ba, bai kuma wuce kalmomi 4000 ba.

3. Za a fara aikawa da cikakken labarin ne tun daga 15 ga Afirilu, 2022 (15/04/2022) zuwa 15 ga Mayu 2022 (15/05/2022), in da za a dakatar da aika labaran. Kwanaki 30 kawai masu aika cikakken labari suke da shi kafin rufe amsar labaran. Duk wanda labarinsa ya ƙetare wannan tsakani to ba za a ɗauke shi cikin wannan gasa ba.

4. Alƙalai za su yi aikin ba da maki ga labarai 30 domin fito da sakamako na labarai 13 da suka fi yin zarra, wanda za a bayyana su a ranar 5 ga Yuni, 2022 (05/06/2022). Hukuncin alƙalai shi ne zai kawo ƙarshen amsar kowane irin ƙorafi daga masu shiga wannan gasa.

JIGOGIN LABARAN DA ZA A SHIGA GASA DA SU.

1. Shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi a tsakanin al'umma, musamman matasa.

2. Zaman banza da rashin samar wa kai abun yi a tsakanin matasa.

Ƙarin bayani: Marubuci yana iya ɗaukar ɗaya daga cikin jigogin ya gina labarinsa a kai, idan kuma zai iya haɗe duka jigogin a labari guda, babu laifi a yi hakan.

WANE LABARI NE YA DACE A SHIGA GASA DA SHI?

Kowane labarin Hausa wanda aka gina shi a kan waɗancan jigogi da ke baya to ya cancanta, amma dole ne a kiyaye da cewar:

-Ba a taɓa buga labarin a kowace irin kafa ta sada zumunci ko jarida ko mujalla ko karantawa a kafafen yaɗa labarai ba.

-Ba a taɓa shiga wata gasa da shi ba kowace iri.

-Labari ya zama mallakin mai shi ne, babu sofanen satar fusaha a cikinsa.

-Labari ya zama cikin Daidaitaciyar Hausa tare da bin ƙa'idojin rubutunta.

WAƊANDA ZA SU SHIGA GASA.

1. Matasa daga shekaru 18 zuwa 30 ne kawai za su iya shiga wannan gasa. Don haka za a haɗo da kwafi ko hoto na takardar haihuwa ko wani katin shaida mai ɗauke da shekarar haihuwa a yayin aiko da samfurin labari.

2. Ba a buƙatar wata takardar karatu ko ƙwarewa, in dai mutum ya iya tsara labari da Hausa, to yana iya shiga a dama da shi.

3. Babu togaciyar jinsi; matasa maza da mata kowa yana iya shiga.

4. Mutum ɗaya ko haɗaka ta mutane biyu za su iya shiga da labari guda ɗaya, amma kar a wuce haka.

MENE NE SAMFURIN KO TSAKUREN KO SOMIN-TAƁIN LABARI?

Abin da za a tura a matsayin samfurin (tsakuren) labari daga kalmomi 500 ne zuwa 1000 na gundarin labarin da za a shiga gasa da shi. Misali an tanadi labari mai kalmomi 3000 ko 4000, to sai a tsakuro wani sashe na cikinsa, walau farko ko tsakiya ko kuma ƙarshe, in da ya fi yi wa marubuci daɗi dai, sai a tura. Idan an yi nasara shi ne za a buƙaci da a tura labarin baki ɗayansa a zagaye na biyu. Haka ma ko da yanzu ne za a fara ƙirƙira labarin, wato babu shi a ajiye, to iyakar kalmomi 500 zuwa 1000 kawai za a samar, sauran kuma sai a tanade su har idan an yi nasarar zuwa zagaye na biyun sai a tura. Dole ne dai a ga tsakuren labarin da aka aika a cikin labarin da za a aika cikakke.

Duk da haka idan akwai wani abu da ba a gane ba, ko kuma ana neman ƙarin bayani game da wannan gasa, a nemi kwamitin tuntuɓa ta lambobin waya kamar haka:

08060767379

09033492760

07030319787

08109787949

08063548290

#Muhallisuturasecondedition

Post a Comment

0 Comments