Ticker

6/recent/ticker-posts

Almara: Cakwalkwalin Cakwakiya

Wasu mutane biyu sun haɗu a tashar mota, sai ɗaya ya dinga ƙorafi a kan matsalar gida. Ƙarshe dai ɗayan ya kasa haƙuri, ya ce:

"Wai kai a tunaninka har wata matsala ce da kai?

To, saurari matsala ta ka ji,

A shekaru kaɗan da suka wuce na haɗu da wata bazawara muka yi aure. To da ma tana da ‘ya wadda ta isa aure. Jimawa kaɗan, baba na ya auri 'yar tata. Hakan yasa agola ta ta zama matar ubana, kuma uwa ta. Baba na kuma ya zama suruki na don ya auri 'yar matata.

Haka nan kuma matata ta zama surukar babana, tun da ya auri 'yarta.

Ana nan a haka, sai 'yar matata ta haihu a gidan babana. Yaron da aka haifa sai ya zama ƙanina tun da ɗan babana ne. Amma kuma ai ɗan 'yar matata ce - ka ga ke nan ƙanina ya zama jikana.

Wannan fa duk bai zama tashin hankali ba sai da mata ta ta haihu. To, yanzu yayar ɗana (matar baba na ke nan) ta zama kakar ɗana, tun da ɗan mijinta ne ya samu ƙaruwa.

Wannan ya sa babana ya zama surukin ɗana, tun da yayarsbabana ke aure.

Sai na zama surukin matar babana.  Matata ta zama gwaggon ɗantaƊana ya zama ɗan babana. Ni kuma na zama kakana.

Idan ba ku ruɗe ba ku yi comment a ƙasa.

Almara
Source: WhatsApp Group (Comedy Arena)

Post a Comment

0 Comments