Ticker

6/recent/ticker-posts

Sayen Tsoron Cutarwa A Al’adun Hausawa

A wannan takarda an yi sharhi game da sááyèn tsoron cutarwa a wasu al’adun Hausawa. Ta haka ne aka yi bayani dangane da sááyè da bori da cuta wajen Bahaushe tare da kawo misalan sááyè a mahangar ‘yanbori da kuma sááyèn tsoro a tsarin zamantakewar Hausawa ta yau da kullum.

Magungunan Gargajiya

Sááyèn Tsoron Cutarwa A Al’adun Hausawa

Dr. Nura Lawal
Department of Nigerian Languages
Bayero University, Kano 

And

 

Dr. Yakubu Aliyu Gobir

Department of Nigerian Languages

Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

08035605024

Tsakure

A wannan takarda an yi magana ne dangane sááyè a mahangar bori. Daga cikin abubuwan da aka yi tsokaci a kansu akwai; sááyè da bori, sannan kuma aka yi magana dangane da sááyèn tsoro a mahangar ‘yanbori da kuma sááyèn tsoro na wasu cututtuka a mahangar Hausawa. Haka kuma, a wannan takarda an yi amfani da ra’in Brown da Levinson (1987) mai suna Ra’in Ladabin Zance[1]. Wannan ra’i, da kuma ayyukan da suka biyo bayansa, sun tabbatar da sááyè muhimmin ɓangare a cikin al’adun al’umma, wato ta fannin cuɗanya domin nuna ladabi da ɗa’a da kunya da nisanta da kuma dangantaka. Har ila yau, waɗannan abubuwa (ladabi da ɗa’a da kunya) sanannu ne a al’adu da kuma tunanin kowace al’umma. Hakan ta sa sááyè yake taka muhimmiyar rawa wajen cuɗanya tare da ƙoƙarin inganta da kare mutuncin mutane. Wannan ra’i ya dace da yadda al’ada take tafiya tare da hikimomin amfani da matanonin sááyè wajen cuɗanya da kuma aiwatar da wasu al’adunsu. Har wa yau, an yi la’akari da wasu muhimman matakai na wannan ra’i da suka haɗa da: ma’ana da asali da rukunin al’ada da kuma yanayi ko lakacin yin al’adar. Haka kuma, a wannan takarda, an lura cewa, yin sááyè a wannan siga yakan ƙara cusa aƙida da kuma yin imani da wasu abubuwa. A wannan takarda an gano, cewa wannan al’ada ta sááyèn tsoro, wasu Hausawa suna amfani da ita a matsayin rigafi. Hakazalika, sááyèn tsoro, musamman a wajen ‘yanbori, yakan taimaka masu wajen samar da magunguna da kuma kyakkyawar alaƙa da aljanu a yanayin aiwatar da ayyukansu na bori.

Muhimman Kalmomi: sááyè, bori, tsoro, cuta

1.0 Gabatarawa

Sááyè na ɗaya daga cikin al’adun Huasawa masu cusa aƙida da kuma inganta tarbiyya a tsakanin al’umma. Manasa da manazarta sun gudanar bincike daban-daban, musamman a kan abin da ya shafi sááyè a bori da kuma cututtuka. Daga cikin su akawi: Salim (1978) da Bunza (1990, 2006) da Fermabdez (2006) da Guo (2010) da Gobir (2012) da Yahaya (2012, 2013) da Kuta (2014) da Pour (2016) da Rushida (2016) da Rawso da (2018) da sauransu, sun gudanar da bincike dangane da sááyè da bori da cututtuka da magunguna, amma, waɗannan ayyuka ba su nazarin sááyè ba a matsayin rigakafi ko tsoro ba. wannan dalili ya sa aka ga akwai buƙatar a cike wannan giɓi. Sááyè yana nufi ƙin fadar wani abu da sunansa na asali, a maimakon haka sai a yi amfani da wata kalma ko kalmomi waɗanda al’adar al’umma ta aminta da su da za su iya bayyana wancan abin domin tsoro ko cusa aƙida ko kyautata tarbiyyar al’umma (Lawal, 2019). Amma, Salim (1978:92) ya bayyana sááyè shi ne ƙin kiran abu da sunnansa, ta hanyar sauwa, a yi amfani da wasu kalmomi da suke da kusan ma’ana ɗaya da shi, amma kuma aka ɗauka cewa su waɗannan kalmomi an yarda da amfani da su a wannan waje. Shi kuma, Bori ba addini ba ne, wata hidima ce da wasu ‘yan tsiraru ke yi wa iskoki tsakanin ƙarya da gaskiya, har abin ya bi jikinsu da hankalinsu suka ɗabi’antu da ɗabi’aɗaya da ake iya rarrbe su da sauran wasu ba su ba (Bunza, 2016:37). Cutu tana nufin rauni ko raɗaɗi tare da wahala da mutum kan gamu da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci (Adamu, 1998:35). Wannan takarda ta yi sharhi ne a kan sááyèn tsoro, musamman wanda ya shafi ‘yanbori da wasu cututtuka a al’adun Hausawa.

1.1  Hanyoyin Gudanar da Bincike

A wannan bincike an yi amfani da hanyoyi guda biyu wajen tattaro bayanai da kuma matanonin sayen ‘yan bori. Waɗannan hanyoyi su ne; Ginshiƙan hanyoyi da kuma sauran hanyoyi. Gishiƙan hanyoyi su ne tattaunawa da ‘yan bori kai-tsaye da kuma ziyartar wasu wuraren gudanar da bori ko bikin ‘yan bori ko a yayin bayar ko samar da magana. Hanyar lura ta kai-tsaye (obserɓation) a wannan bincike an yi amfani da hanyar nazari ta lura kai-tsaye domin kauce wa zato ko shakku ko shaci-faɗi a kan sayen ‘yan bori. Sannan kuma an tattauna da wasu masana harkokin tsafe-tsafen al’adu a wasu sana’o’in Hausawa, kamar abin da ya shafi maita da noma. Sauran hanyoyi kuwa su ne bitar ko nazartar wasu ayyukan magabata, kamar littattafai da maƙalau da kuma kundayen bincike. Haka kuma, an tattauna da wasu masana da manazarta, musamman masu bibiyar al’adun Hausawa da suka danganci bori.

2.0 Sááyèn Tsoro a Mahangar ‘Yanbori da Matsafa

Ma’ana: Bori wata dabarar warkarwa ce da bokaye suka yi fice da ita. Da Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa ya tarar da ‘yan bori ne jagororin al’umma. Da aka rinjaye su, suka miƙa wuya karkace. Kasancewarsu cikin summa kafaru summa amanu sai bori da Musulunci suka cakuɗe wuri ɗaya Musuluncin, sai bori ya koma barbarar yanyawa. Taho-mu-gaman aƙidojin addinin Musulunci da aƙidojin bori ya sa da wuya a tantance kama da wane ba wane ba ne. Bori ba addini ba ne, wata hidima ce da wasu ‘yan tsiraru ke yi wa iskoki tsakanin ƙarya da gaskiya, har abin ya bi jikinsu da hankalinsu suka ɗabi’antu da ɗabi’aɗaya da ake iya rarrabe su da sauran wasu ba su ba (Bunza, 2016:37).

Tsafi yana nufin bin wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa iskoki hidima da yanka da bauta domin biyan wata buƙata ko samun wani amfani ko tunkuɗe wata cuta. Hidima a nan, tana nufin yi musu wasu ayyuka ko taimaka musu da abinci ko wasu abubuwa (Bunza, 2006:35). Shi kuma, Gobir (2013:370) yana ganin cewa ‘yanbori suna cikin nau’i na bokaye a ƙasar Hausa, domin duk wani ƙasurgumin boka daga bori ya fara. ‘Yanbori su suka fi hulɗa da Iskoki, musamman miyagu masu haddasa ciwon hauka da sauran rashin lafiya. Hanyoyin bayar da magungunansu su ne ta fuskar wasan bori da girka.

Asali/Dalili: ‘Yanbori da Matsafa kan yi sááyèn wasu sunaye, musamman na aljanu domin girmamawa da kuma camfi a yanayi na tsoron kar su cutar da su, ko kuma, domin neman biyan buƙata da waɗannan aljanu da sukan sáyà sunayensu. Da kuma dalili na nisanta kai da cutarwa da kuma dantankar aljanun da magani da kuma waraka.

Sharhin Rukunin Al’ada: A sakamakon waɗannan dalilai ne ‘yanbori da matsafa kan kiyaye wannan al’ada ta sááyè. Misali, Farar aljan suna sakaya sunanta da Dogowa. Ta lura da siffarta, wato tana da tsawo da kwarjini a wajensu.

Haka kuma, masu tsafin noma suna sakaya sunan Bagiro/Magiro da sááyèn Baba, sannan masu tsafi suna yi masa kirari da ‘Bagiro ka fi ƙarfin girka sai dai tsafi’. Saboda girmamawa da kuma irin dangantakar da ke tsakaninsu da kuma neman biyan buƙatunsu. Har wa yau, suna sakaya tsamiya da Gunki, a dalili yadda a da, an mayar da tsamiya wajen yin wasu al’adu, musmman da suke da nasaba da tsafi.

Mushe kuma, suna ɓoye sunansa da Dagui, idan za a yi tsafi da shi, saboda neman dace da kuma lura ko tunanin cewa, mushe shi ma yana tattare da aljanu ko iskoki ko kuma suna da butaƙa da shi ko wani abu daga gare shi. Wannan lokaci kuma mayu da matsafa suna ganin cewa aljanu ne ko iskoki suka shanye jinin wannan abu, shi ya sa ya zama mushe.

Haka zalika, sááyèn sunan aljanu a wajen ‘Yanbori mafi shahara shi ne Suwa, watoYanbori ba su ambaton yawanci sunaye da aka yi sááyèn sunan aljanu da su, saboda tsananin girmamawa da biyayya ga aljanun sai dai su sakaya sunan da Suwa. Suna haka ne domin kauce wa yin suɓul-da-baka, su ambaci sunan da zai ɓata masu rai, har ya kai ga sun yi ɓarna ko su yi fushi da su, ta yadda idan suka buƙaci su biya masu wata buƙata su ƙi. Saboda haka, da zarar an ambaci suwa duk wanda ya yarda da su ya san su wane ne ake magana a kansu.

Har ila yau, ‘yanbori sukan yi sááyè ga wasu aljanu, musamman Musulmai, tare lura da masu sarauta ko muƙami a cikin aljanun da suke hulɗa da su. Misali, ‘yanbori suna sakaya sunan Ibrahim da Sarkin Rafi, sun samar da wannan sááyèn ne ta la’akari da cewa shi Sarkin aljanu ne, musamman masu zama a rafi ko ruwa. Sannan kuma, Usman da suke sakaya shi da Wanzami, suna sakaya shi da wanzami ne saboda shi alƙali ne, shi ke yi musu shari’a. Haka kuma, a yayin yin bori idan ana so a yi wa aljanu shari’a to, mai hawa wanzami shi ake kira ya hau bori domin alƙalin ya zo. Akwai kuma, Dikko wanda suke yi wa sááyè da Mairuga, shi ma Sarkin Fulani ne. Sai kuma, Yakubu da suke yi wa sááyè da Sarkin Fulani ko Harɗo.

Haka zalika, akwai Aliyu da suke yi wa sááyè da Malam Alhaji, dalili kuwa shi ne, shi malami ne sannan kuma, ya je aikin Haji. Haka kuma, ‘yanbori sun yi imanin cewa kullum da shi ake yin jam’in sallar asuba a Makka. Akwai kuma, sarki Zurƙallaini da suke sááyèn sunansa da Sarki da Ƙaho, wanda shi ma sarki ne. Adamu da suke yin sááyènsa da Maiwada ko almajiri ko Namalam. Wanda shi ma almajirin Malam Alhaji ne. Sannan akwai Ali da ake sááyènsa da Kunnau saboda fushi. Sai kuma Idris da suke sayawa da Maigizo da Muhammadu suna saya shi da Ɗangaladima. Bello kuma, ana saya shi da Uda su kuma, Haruna da Musa ana saya su da Nawaila.

A ɓangaren mata aljanu kuma, akwai A’isha da suke sakayawa da Masoshiya ko Bobuwa. Saboda a fagen bori masu wannan Iskan, idan suka hau bori jikinsu yana yin ƙaiƙayi ne. Maimuna da suke sayawa da Inna ta gida ko Inna Doguwa, wanda hannunta ɗaya kuma ƙafarta ɗaya. Wannan dalili ne ya sa idan ta kama mutum hannunsa ɗaya ko ƙafarsa ɗaya ko duk suke shanyewa. Sai kuma, Fatima da suke sakayawa da Baƙar Doguwa ita hannunta ɗaya kuma ƙafarta ɗaya, sannan kuma, duk mai ita idan za ta ba shi magani sai dai ya yi amfani da baƙaƙen abubuwa kamar baƙar kaza ko baƙar akuya ko baƙin zane. Haka kuma, akwai Asma’u da Hauwa da Rakiya da Adama da ake sááyènsu da Barahaza, kuma an ce ‘yan gida ɗaya ne.Yawanci aljanu arna, suna yin sááyènsu da Masu Magani, amma Sarkin aljanu arna suna saya shi da Ɗankawu, sai kuma Duna na ƙarƙashin ƙasa da na ƙarƙashi ruwa.

Lokaci/Yanayi: ‘Yanbori da matsafa kan aiwatar da wannan al’ada ne a yayin gudanar da ayyukansu tun daga lokacin da mutum ya shiga wannan harka ta bori ko tsafi, har zuwa lokacin da ya daina ko zuwa ƙarshen rayuwarsa. Bahaushe a tunaninsa ya fito da wasu laƙabi da dalilan waɗannan laƙabi da Hausawa suke yi wa aljanu, musamman ‘Yanbori da Matsafa kamar haka:

i)       Kayehi: ‘Yanbori da masu matsafi, su ne suka fi amfani da wannan laƙabi. Kayehi na nufin buwayayye, mai yin aikin tafi-da-hankali da ɓatar da hankali da wayon mai sauraro ko ɗan kallo da kuma saɓa wa al’adar da aka sani ta yau da kullum. Daga cikin dalilan da ya sa ake yi wa aljanu ko iskoki wannan laƙabi Kayehi akwai; tashi sama, da sauri, da ƙarfinsu, da buwayar ɗan’adam da suka yi, da sauransu (Gobir, 2012:87).

ii)     ‘Yangabsa/ ‘Yanjangarai: ‘Yanbori da matsafa sun yi imanin cewa babban mazauni kuma babban birnin da aljanu ko iskoki suke zaune shi ne birnin Jangarai[2], kuma wannan birnin yana can Gabas mai nisa. Jangarai shi ne babban garin aljanu ko iskokin duniyar nan gaba ɗaya. Dalili wannan laƙabi na ‘Yangabas/’Yanjangarai shi ne tsoro, wato kauce wa saɓa wa aljanun domin kar su ƙiya wa ‘yanbori da matsafa wasu buƙatu da suke nema a wajensu (Gobir, 2012:89).

iii)   Ƙwanƙwamai: Ana yi musu wannan laƙabi na ƙwanƙwamai ne saboda cikin ƙwanƙwamin ƙwaƙwalwa suke shiga su gigita mai hankali. Sannan kuma, ana yi musu wannan sááyè na ƙwanƙwamai, musamman waɗanda aka gada daga wajen iyaye, musamman mahaifi (Bunza, 2012:3).

iv)   Ajiya: Wani lokaci Hausawa sukan yi wa aljanu laƙabi da ajiya, musamman idan suna son alaƙanta su da wuraren da suke zama ko ake samun su (Gobir, 2012:89).

v)      Mutanen Ɓoye/Mutanen Kogo: A al’adu da adabin tarihin Hausawa ta fuskar riwayar bokayen ƙasar Hausa, lokacin da Annabi Adamu (A.S) ya haifi ‘ya’ya, Allah ya nemi ya zo da su wani wuri a gan su. Gabanin ya isa wurin ya zaɓe masu kyau mata da maza ya ɓoye cikin kogon tsamiya ko kuka, ya isa da sauran ya nuna. Da ya dawo ya ɗauki waɗanda ya ɓoye a kogon sai ya tarar sun zama iskoki. Don haka ake ce musu Mutanen Ɓoye ko Mutanen Kogo (Gobir, 2012:88).

vi)   Mutantani: Saboda tarayyar da suke yi da mutane a harkokin rayuwa ta yau da kullum duk da cewa, mutane ba sa ganin su, amma su suna ganin mutane. An ciro sunan daga mutum ya koma mutantani, wato kamar mutum amma ba mutum ba. Ke nan, sun yi kama da mutane amma ba mutane ba ne. Wato kamar yadda Bahaushe yake yin mutum-mutumi ya kafe shi a tsaye a gonarsa, don korar tsuntsaye masu yi musu ɓarna.

vii) Masu abu: Wannan sunan yana nuna isa ne ga iskoki a kan komai suka sa gaba za su yi, za su iya yin shi kamar ƙyaftawar gira, yadda suke son a gan shi kai tsaye ko nan take, wato sha yanzu magani yanzu.Wa zai iya yin wannan, ai sai masu abu (Gobir, 2012:88).

viii)           Maleka: su kuma, waɗannan aljanu ne da ke zaune a dokar daji, ba su shigowa gari cikin mutane (Gobir, 2012:87).

 

3.0 Sááyèn Wasu Cututtuka a Mahangar Camfi

Ma’ana: Cuta tana nufin rauni da raɗaɗi tare da wahala da mutum kan gamu da su a sanadiyyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci (Adamu, 1998:35). Cuta wata damuwa ce da ta shiga jikin ɗan’adam don raunana lafiyarsa. Ko kuma ta shafi zuciyarsa ta fuskar buƙatocinsa na jin daɗi ko ɗaukaka darajarsa da sunansa (Bunza, 1990:132).

Shi kuma, Sallau (2000:101) ya bayyana cuta na nufin shiga cikin wani yanayi na rashin jin daɗi, ko halin da kan sa damuwa ga mai rai, ko wani ɓangaren jiki ya sami nakasa, ko hankali ya taɓu, wanda a wani lokaci irin wannan yanayi ko halin da aka shiga kan yi sanadiyar mutuwa ga wanda ya shiga irin wannan yanayin ko halin.

Asali/Dalili: Bahaushe ya samar da wannan al’ada ne a tunaninsa na nisanta kai da kamuwa da cuta, a bisa imani na camfi.

Sharhi Rukunin Al’ada: Akwai wasu cututtuka da a tunanin Bahaushe faɗar sunayen waɗannan cututtuka tsirara za su iya kama mutum har ma su gama da shi. Wannan dalili ne ya sa da yawa daga cikin wasu cututtukan ƙasar Hausa suna da sakayen yadda ake fuskantar furta sunayensu da aka sani na asali. Misali, Bahaushe yakan sakaya sunan cutar Kuturta da Zafi da kuma cutar hauka da Rashin lafiya ko taɓin hankali ko ciwon gamo. Haka kuma, ana sakaya Amai da harsawa da kuma Zawayi da Gudawa. Haka zalika, akan sakaya cututtukan da suka shafi aljanu da cuta ko ciwon Iska da sauransu.

Bahaushe kan sakaya cutar kuturta da zafi, ta la’akari da yanayi halaye da ɗabi’u na kuturu, wato a bisa al’ada Kuturu mutum mai zafi ta fuskar yanayi na mu’amalla da mutane, Kutura mutum ne mai sauri fushi. A bisa imani na camfin Bahaushe idan mutum ya cika faɗar sunan cutar kuturta kai-tsááyè to, zai iya kamuwa da wannan cuta ta kuturta. Hakan ta sa Bahaushe ya kauce wa faɗar sunan cutar kuturta tsirara.

Har ila yau, Bahaushe yana sakaya sunan cutar hauka da rashin lafiya ko taɓin hankali, saboda camfinsa na cewar faɗar cutar hauka tsirara zai sa mutum ya kamu da cutar. A wannan dalili sai Bahaushe ya lura da yanayi wanda ya kamu da cutar hauka, wato yana aikata abubuwa na rashin hankali da tunani. Ke nan Bahaushe ya lura da cewa duk wanda ya kamu da wannan cuta ta hauka, to hankalinsa ya taɓo, wato babu hankali ko aikata ayyuka na hankali tare da mai wannan cuta.

Haka kuma, akwai wasu dabbobi da ƙwari da Hausawa kan sakaya sunansu, su kira su da wani suna, don tsoron camfinsu da ke cewa, idan ka ambaci sunansu, to za su zo su cuta wa wanda ya faɗi sunan. Misalan waɗannan dabbobi ko ƙwari su ne: Maciji ana saya masa sunan Igiyar ƙasa. Ita kuma kunama aka sakaya mata suna a ce Maiƙari. Zaki a sakaya masa sunan Kare ko Manyan dawa. Kura kuma ana kiran ta Karen daji ko Yaya ta daji. Damisa kuma a kira ta Mussar daji, da sauransu.

Lokaci/Yanayi: Hausawa suna aiwatar da wannan al’ada ne tun daga haihuwa har zuwa mutuwu. Haka kuam, har a yau, suna aiwatar da wannan al’ada ta sááyè duk da irin tasirin addinin Musulunci da zamananci da Bahaushe ya tasirintu da su.

4.0  Kammalawa

A wannan takarda an yi sharhi game da sááyèn tsoron cutarwa a wasu al’adun Hausawa. Ta haka ne aka yi bayani dangane da sááyè da bori da cuta wajen Bahaushe tare da kawo misalan sááyè a mahangar ‘yanbori da kuma sááyèn tsoro a tsarin zamantakewar Hausawa ta yau da kullum. Haka kuma, an lura Hausawa suna aiwatar da sááyèn tsoro ne domin kauce wa cutarwa ko kuma domin samun biyan buƙata, musamman daga aljanu ko iskoki a yayin gudanar da wasu al’adu na musamman. An lura yin sááyè a wannan siga yakan kare cusa aƙida da kuma yin imani da wasu abubuwa. A wannan takarda an gano, cewa wannan al’ada ta sááyèn tsoro wasu Hausawa suna amfani da ita a matsayin rigafi. Hakazalika, sááyèn tsoro, musamman a wajen ‘yanbori yakan taimaka masu wajen samar da magunguna da kuma kyakkyawar alaƙa da aljanu a yaniyin aiwatar da ayyukansu na bori. Har yau, an gano sááyèn tsoro wata hanya ce ta cusa ƙaida da kuma tarbiyya a tsarin al’adun Hausawa, musamman a mahangar camfi.

 


 

MANAZARTA

Brown, P. & Levinson, S. (1987). Politeness: Some Universals in Language Usage. Cambridge: University Press.

 

Bunza, A.M. (1990). Hayaƙi fid da na Kogo: Nazarin Siddabaru da sihirin Hausawa. Kundin Digiri na Biyu (M.A Thesis). Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

 

Bunza, A.M.(2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos:Tiwal publishers.

 

Fermandez, E.C. (2006). The Language of Death: Euphemism and Conceptual Metaphorization in Victorian Obituaries. SKY Journal of Linguistics. Vol 19.

 

Gobir, Y.A. (2012). Tasirin Iskoki ga Cutuka da Magungunan Hausawa. Kundin Digiri na uku (Ph.D Thesis). Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

 

Gobir, Y. A. (2013). Najasa a Mahaɗin Maganin Iska. In Harsunan Nijeriya Volume XXIII, Special Edition. Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University. Zariya: Ahmadu Bello University Press.

 

Guo, Ƙ. (2010). Cultural Difference in Chinese and English Euphemisms. In Cross-Cultural Communication vol.6 (4). P.135-141.ISSN:1923-6700. Canadian: Academy of Oriental and Occidental Culture. Htt://citeseerx.ist.psu.edu

 

Kuta, H.M. (2014). Kwatantacin Borin Hausawa da na Gbagyi. Kundin Digiri na Biyu (M.A.Thesis). Sashen Harsunan Afirka da Al’adu, Zariya:Jami’ar Ahmadu Bello.

 

Lawal, N. (2019). Nazarin Sááyèn a Tunanin Bahaushe Jiya da Yau. Kundin Digiri na Uku (Ph.D Thesis) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

 

Pour, B.S. (2016). A Study Of Euphemisms From the Perspectives of Cultural Translation and Linguistics. In Translation Journal.vol.14 (4) (online) 

Available at http://transtionjournal.net/journal/54euphemisms.htm

 

Rawson, H. (1981). A Dictionary of Euphemisms and Other Doubletalk. New York: Crown Publishers, Inc.

 

Rusdiah (2016). Code-Switching Servers a Euphemism. In Intertional Journal of Social Science and Research (IJSR). vol.5 (1). ISSN:2319-7064. (online) Available at www.ijsr,net

 

Sallau, B.A. (2010). Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: M.A. Najiu Professioinal Printers.

 

Yahaya, N. (2012). Euphemism Expressions for Death in Hausa Language. In Amfani, A.H. da Alhassan, B.S.Y. da Malumfashi, A.I. da Tsoho, M.Y. da Amin, M.L. da Abdullahi, B. (Editoci). In champion of Hausa cikin Hausa a festchrift in honour of Ɗalhatu Muhammad. Zaria: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

 

Yahaya, N. (2013). Sááyèn Suna a Ƙasar Hausa : Jiya da Yau Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa. Zaria: Ahmadu Bello University Presss Limited.

 

Mutanen Aka Tattuana da su

Lamba

Suna

Shekar

Matsayi

Wuri

 Rana

1

Alhaji Ali Ya’u

80

Sarkin Borin Kano

Gidansa a Aisami, Cikin Birnin Kano

02-12-2018

2

Abubakar Ɗandada

59

Mai Bori

Bakin Kasuwa, Ɗanmusa, Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa, Jihar Katsina

03-01-2019

3

Yahaya Maye

50

Sarkin Mayun Ɗanmusa

Bakin Kasuwa, Ɗanmusa, Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa, Jihar Katsina

03-01-2019

4

Alhaji Bawa Babban Kada

65

Sarkin Noman Jihar Katsina

Ugunwar Babban Kada Ƙaramar Hukumar Safana, Jihar Katsina

04-01-2019

 

 

 [1] Politeness Theory.

[2] Hausawa sun yi imani cewa, Jangarai can ne babbar alƙaryar kowace irin iska da take a doron duniyar nan. Dangane da nahiyar da wannan alƙarya ko birni yake kuwa, ya haifar da jayayya, domin akwai hasashen daban-daban. Akwai hasashen cewa, birnin na Kudu da ƙasar Kano, kusa da garin da ake kira Bawda, kuma bakin ƙofar garin na Bawda, akwai wani ƙaton iccen kuka da rijiya. Wasu kuma, na hasashen cewa, birnin na kusa da Argungu, can yammacin ƙasar Hausa (Kabi). Wasu kuma, na da’awar cewa, sunan wannan birni sunansa Ƙwanƙwambilo ba Jangarai ba, kuma yana can ƙasar Gobir ta jihar Sakkwato da wani sashen na ƙasar Nijar. Haka kuma, Hausawa sun yi imani cewa, ba wani bil’adama da ya taɓa zuwa wannan birni na iskoki, inda suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum, kamar yadda mutane ke yi. Duk abubuwan da mutane suke da su, aljannu ma suna da su a can, kamar kasuwa da masallatai da sarakunan mulki da sauran al’amuran al’ada. Haka kuma, a cikin wannan birni akwai zauruka goma sha biyu (12) kuma kowane zaure yana cike da aljannu fiye da dubu biyar da ɗari biyu da sittin(5260) (Gobir, 2012: 126-128).

Post a Comment

0 Comments