Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakabi Linzamin Makaɗa da Mawakan Hausa

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2021) “Laƙabi Linzamin Makaɗa da Mawaƙan Hausa” International Academic & Research Journal of Humanities and Social Sciences, Vol 2, Issue 2. ISSN Print: 2708-6259 ISSN Online: 2708-6267.  DOI: 10.47310/jiajhss.v02i02.005.

Laƙabi Linzamin Makaɗa da Mawaƙan Hausa

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
08036153050

Sunayen Hausawa

TSAKURE

Wannan bincike da aka yi wa suna “Laƙabi Linzamin Makaɗa da Mawaƙan Hausa” an gudanar da shi ne domin tabbatar da tasirin amfani da sunayen laƙabi ga Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Manufar binciken ita ce a nazarci sunayen rukuni daban-daban na Makaɗa da Mawaƙan Hausa domin a karkasa sunayensu na laƙabi ta yadda za a sami wakilcin rassan laƙubban Hausa bisa mizanin awon ayyukan da suka gabata. Haka kuma nazarin yana da manufar tabbatar da tasirin laƙabi ga al’ummar Hausawa musamman ga mutanen da suka yi fice a kan wasu harkoki na rayuwa kamar Makaɗa da Mawaƙa. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari su ne tattara bayanai musamman na sunayen Makaɗa da Mawaƙan Hausa waɗanda aka samu a ayyukan da aka yi a kansu a littattafan magabata. Haka kuma an yi amfani da waƙoƙin Hausa da dama waɗanda ke ɗauke da sunayen makaɗan. Misalan da aka kawo na sunayen makaɗan su ne makamashin nazarin. Wannan nazarin ya yi nasarar tabbatar da cewa, yawancin Makaɗa da Mawaƙan Hausa suna amfani da sunayen laƙabi ba kamar sauran jama’a ba da za a iya samun masu amsa sunan yanka kawai. Haka kuma nazarin ya yi nasarar gano cewa, sunayen laƙabin mawaƙan Hausa shi ya fito da su a fili. Jama’a sun fi riƙe da amfani da sunayen laƙabi na Shata da Ɗanƙwairo da Ɗandawo da Ɗan’anace da Narambaɗa fiye da sunayensu na yanka.

 

Fitilun Kalmomi: Laƙabi, Suna, Makaɗa, Mawaƙa

 

1.0 Gabatarwa

Suna shi ne abu na farko da yake jagorancin fahimtar abu ko gane zancen da ake yi. A duk lokacin da za a yi magana, to ambaton sunayen abubuwan da ake magana a kan su shi ke taimakawa wajen fitar da alƙiblan saƙon. Ta fuskar mutane kuwa, kowane mahaluki a kowace al’umma ta duniya an tanadar masa suna domin bambanta shi da ɗan’uwansa. Wannan fasaha ta ɗan’adam ta taimaka ƙwarai wajen sauƙaƙa al’amurra.

 

Maƙasudin wannan nazari shi ne a kalli yadda wani rukuni na sunayen Hausawa ya mamaye wani rukuni na jama’a da suka keɓanta a kan abu ɗaya. Wato nazarin ya ɗauki sunayen Hausawa na laƙabi ya ɗora shi a kan makaɗa da mawaƙan Hausawa domin tabbatar da hasashen da ke nuna cewa, babu makaɗin da ba ya da sunan laƙabi, kuma wannan suna shi ya fitar da shi a bainar jama’a. Wannan hasashe ya ci gaba da kafa dugadugan nazarin da ke nuna cewa, in fa ba a yi amfani da sunan laƙabi ba ga duk wani makaɗi da mawaƙin Hausa to ba za a san wanda ake son ambato ba. Duk da yake nazarce-nazarcen da suka gabata kamar Yahaya (1979) da Aminu (1992) da Abdullahi (1997) sun tabbatar tasirin sunan laƙabi a tsakanin Hausawa, amma ana samun Hausawan da sunayensu na yanka kawai suka yi fice. Wannan nazari ya yi ƙoƙarin tabbatar da akasin haka musamman ga makaɗan Hausa. Wannan nazari yana son tabbatar da hasashen cewa, babu makaɗin Hausa da ba ya da sunan laƙabi, kuma wannan suna da shi aka san shi a wannan fage na kiɗa da waƙa.

 

2.0 Tubalan Take

Manyan tubalan taken wannan nazari da ke bukatar fashin baƙi su ne Laƙabi da kuma Makaɗa da Mawaƙan Hausa. A wannan fasalin, za a bayar da haske ne a kan waɗannan domin su jagoranci mai karatu ko nazari ya fahimci jigo da warwarar jigon maƙalar.

 

2.1 Laƙabi

Waiwayen wasu ayyukan da suka gabata ya gano cewa, duk sun yi matsaya ɗaya a kan ma’anar wannan kalmar duk da yake furucinsu ya bambanta. Ƙamusun Hausa (2006) ya bayar da ma’anar kalmar laƙabi da ‘Sunan mutum wanda yake bin sunan haƙiƙa.’ Abdullahi (1997:7) ya nuna laƙabi da:

                                 duk wani suna da ba na yanka ba. Wato suna ne da akan samu baya ga sunan yanka wanda al’umma kan laƙa wa mutum ko ya laƙa wa kansa ko wani ya laƙa masa saboda wani dalili ko wasu dalilai na musamman, kamar wani hali da aka san mutum da shi mai kyau ko mara kyau ko wata siffa da dai sauransu.

Aminu (1992) ya kira laƙabi da laƙani. Ya nuna cewa, wani suna ne da akan laƙana wa ko saka wa wani mutum ko kuma wani abu. Ya nuna irin wannan suna ya fi karɓuwa ga jama’a. Abubuwa da yawa tattare da mutum suna iya sa a ba shi laƙabi.

Yahaya (1979) ya kira sunayen laƙabi da Laƙabobi, a inda ya fayyace cewa, sunaye ne da suka samu tare da sunayen yanka ko taƙaitattun sunayen yanka. Ya nuna wasu sunaye, laƙabobi ne da ake yi wa sunayen yanka.

Idan aka yi la’akari da waɗannan ma’anoni ko bayanai, za a fahimci cewa, laƙabi dai suna ne da Hausawa suka samu baya ga sunansu na yanka. Duk wani suna da aka yi wa mutum ko ya yi wa kansa, idan dai ba sunan yanka ba ne to Hausawa suna kiransa Laƙabi. Abdullahi (1997) ya ƙara tabbatar da cewa, duk Bahaushe yana da sunan laƙabi. Wasu sunansu na laƙabin shi ke yi wa sunan yanka rakiya, wato tare ake ambaton su a kowane lokaci. Misali Hassan Wayam ko Garba Super. Ba a Ambaton Wayam ba tare da Hassan ba, ko a ambaci Garba, ba a ce Super ba. Idan kuma aka ambaci Hassan ko Garba ba za a iya gane wanda ake magana a kansa ba sai an ƙara da Wayam ko Super. A wasu lokutan kuma, sunan laƙabin ne ke rufe gabaɗayan sunan yanka ta yadda ba a ma sanin sunan mutum na yanka sai an bincika, Misali, akwai wani mawakin Hausa da ake kira Makaɗa Sagalo. Idan ba Sagalo aka ambata kai tsaye ba ba za a gane shi ake nufi ba.

Akwai hanyoyi da yawa da Hausawa suke bi wajen samun waɗannan sunaye na laƙabi. Wasu sunaye na yanka su ke zuwa da laƙabi, ko Hausawa suka samo musu. Misali, akan yi wa mai suna Abubakar laƙabi da Garba. Haka kuma mai suna Musa ana yi masa laƙabi da Kalla ko kallamu. Wasu sunayen na laƙabi, al’ummar da mutum yake zaune, su suke ba shi ta la’akari da wani hali nasa ko siffan jiki, kamar a kira mutum Dogo ko Gajere. Haka kuma Hausawa suna amfani da sunayen ranakun da aka haifi mutum wajen samar masa da sunan laƙabi. Misalin irin waɗannan sunaye su ne: Ɗanlami, Ɗamjuma, Ladi, Asabe, Laraba da sauransu. Haka ma Hausawa da yawa sukan amsa sunayen garinsu na haihuwa ko na asali a matsayin sunan laƙabi da yake ƙara taimakawa wajen tantance su. Misali, Aminu Kano, Shehu Shagari, Hassan Haɗeja.

 

A can baya kafin Bahaushe ya musulunta, ya yi amfani ne da sunayen gargajiya ga mutane. Su waɗannan sunaye, an same su ne ta hanyar la’akari da lokacin da aka haifi yaro ko wani abin tarihi da ya auku a lokacin haihuwar, ko yanayin da haihuwar ta zo. Misalin irin waɗannan sunaye su ne : Citumu, Ciwake, Tanoma, Bawa, Barmani, Giwa, Jatau da dai sauransu. Bayan da Bahaushe ya karɓi Musulunci kuma ya sami sunan yanka, sai waɗannan sunaye suka koma matsayin laƙabi. A taƙaice dai, duk wani suna da aka ji Hausawa suna amsawa, in dai ba sunan yanka (sunan Musulunci) ba ne to kai tsaye laƙabi ne.

 

2.2       Makaɗa da Mawaƙan Hausa

Makaɗa da mawaƙan Hausa wasu rukunin mutane ne da Allah ya ba fasahar sarrafa harshe ta haryar zaɓen kalmomi da jera su a kan wani salo ko tsari na musamman da amfani da wasu kayan kiɗa domin ilmantarwa ko nishaɗantarwa ko kuma bisa wani dalili. Wannan zance ko saƙo da suke isarwa a irin wannan yanayi da tsari shi ake kira waƙa. Kiɗa da waƙa ababe ne da suka yi tasiri a rayuwar Hausawa shekaru aru-aru da suka wuce. Yawan makaɗa da mawaƙan Hausa da karkasuwansu da kuma nau’o’in kayan kiɗansu su za su ƙara tabbatar da cewa, abu ne da ya daɗe kuma ya tasirantu a rayuwar Hausawa. Kusan a iya cewa, duk wani rukuni na rayuwar Hausawa an tanadar masa mutane na musamman da suke masa kiɗa da waƙa. Gusau (1996) ya bayyana wasu daga cikin muhimman rukunonin waɗannan makaɗa da mawaƙa kamar haka :

(i)        Makaɗan Yaƙi – Makaɗa na musamman da suka shahara wajen zuga gwarzayen maza a fagen fama

(ii)       Makaɗan Fada/Sarauta – Makaɗa da mawaƙan da suka shahara kuma suka keɓanta wajen yi wa sarakuna da zuri’arsu kiɗa da waƙa.

(iii)      Makaɗan Jama’a – Makaɗa da mawaƙan da suke yi wa sauran jama’a waƙa. Wato duk wanda suka ga ya dace a yi masa waƙa suna yi masa, kamar attajirai da makamantansu muddin dai za a ba su wani abu.

(iv)      Makaɗan Sana’a – Su ne mawaƙan da suke yi wa masu aiwatar da wata sana’a ta gargajiya waƙa. Misali kamar makaɗan noma da makaɗan maƙera (’yan zari)

(v)       Makaɗan Maza - Su kuma sun keɓanta ne ga yin waƙa ga mazajen da suka shahara wajen aiwatar da wani wasa kamar dambe ko tauri ko kokawa da sauransu.

(vi)      Makaɗan Ban-dariya- Su ne makaɗan Sharholiya. Suna kiɗa da waƙa ne don su ba mutane dariya da annashuwa. Ana kiran galibin waɗannan mawaƙa ’yan gambara.

(vii)     Makaɗan Sha’awa - Su ne waɗanda suke kiɗa da waƙa a sakamakon wani abu da ya ba su sha’awa kamar wata dabba ko tsiro ko wani wuri na musamman.

Ibrahim (1983) shi ma ya kawo rukunan waɗannan makaɗa da mawaƙa. Saɓanin Gusau (1996), ya ƙara da makaɗan Kasuwanci da na Sa-kai da kuma na bori. Daga ciki kowane rukuni na waɗannan makaɗa da mawaƙa akwai waɗanda suka shahara suka yi suna, duniya ta san da su a matsayin mawaƙan Hausa.

 

3.0 Rukunnan Laƙabin Makaɗa da Mawaƙan Hausa

Wannan fasali zai mayar da hankali ne wajen rarraba laƙabin wasu shahararrun makaɗa da mawaƙan Hausa zuwa wasu azuzuwa na laƙabin ta la’akari da abin da sunayen suka ƙunsa ko kuma wani tanadi a al’adance na samar da sunayen.

 

3.1  Sunayen Laƙabi Masu Ɗan ko ’Yar

A Ƙamusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar ɗan da, “Makusanciyar dangantaka tsakanin wani abu da wani.” Wannan yana nufin cewa, duk wani abu da aka Haifa, to ya zama ɗan wannan abin da ya haihu. Idan ba a so a ambaci sunan mutum ko wannan abin da aka haifa to akan yi amfani da kalmar ɗan a haɗa shi da sunan wanda ya mallake shi ta haihuwa. Misali, Ɗanmani, Ɗanshu’aibu, Ɗan’indo, Ɗanba’u. A nan sunayen Mani da Shu’aibu da Indo da Ba’u sunaye ne na mutane da aka maƙala wa “ɗan” don su nuna wannan da aka haifa. A al’adar Hausawa, ba lallai sai wanda ya haihun ake nuna wannan da aka sakaya sunansa da ɗan” a matsayin ɗansa ba. Wani majiɓincinsa kamar ’yan’uwa suna iya samun wannan alfarmar. Misali, idan mutum yana da ƙanin uba mai suna Hassan, sai ya kasance an sa masa sunan yanka mai nauyi wanda ba a iya ambato kai tsaye, to mutanen wannan gida suna iya sakaya sunan da Ɗanhassan duk da yake ba sunan uban da ya haife shi Hassan ba. Irin haka ya faru da samuwar sunan Ɗanƙwairo. Gusau (2019:5) ya nuna mutumin da ainihi ake kira Ƙwairo, wani bara ne daga cikin barorin mahaifin Musa, wanda daga baya aka laƙaba masa sunan wannan baran (Ƙwairo) ta amfani da “Ɗan” ya koma Ɗankwairo, sai aka ci gaba da kiransa Musa Ɗanƙwairo. Jinsin mata masu irin wannan suna, ana fara sunan ne da ’Yar…. ko Ɗiyar …. Makaɗa da mawaƙan Hausawa da dama suna amfani da irin wannan laƙabi mai farawa da ɗan, ya biyo da sunan mutum, ya kuma kasance sunan ya yi tasiri a rayuwarsu. Misalin sunayen waɗannan makaɗa da mawaƙa su ne:

                                i.            Sani Ɗan’indo

                             ii.            Musa Ɗanba’u

                           iii.            Ɗanshu’aibu Tungan Rini

                           iv.            Buda Ɗantanoma

                              v.            Abdu Wazirin Ɗanduna

                           vi.            Ali Ɗansaraki

                        vii.            Muhammadu Bawa Ɗan’anace

                       viii.            Amadu Ɗanmatawalle

                            ix.            Fati Ɗiyar Isah

                              x.            Ɗanmani Caji

                            xi.            Sani Ɗanbalɗo

                         xii.            Musa Ɗanƙwairo

                       xiii.            Nana Asma’u ’Yarkana

 

Baya ga waɗannan kuma, Hausawa suna amfani da Ɗan ga wasu mutane da suka sami kansu da wata nakasa ko kuma wani yanayi na rayuwa. Zai iya kasancewa waɗanda aka ba laƙabin su ke da nakasar ko su suka kasance cikin yanayin. Haka kuma yana iya kasancewa iyayensu su ke ɗauke da nakasar, sai a yi amfani da kalmar ɗan a danganta mutum da mahaifinsa mai nakasar. Misalin makaɗan Hausa da suke da ire-iren waɗannan sunaye kuma suka yi tasiri a rayuwarsu su ne:

                    i.                        Abu Ɗankurma Maru

                  ii.                        Isa Ɗanmakaho

               iii.                        Adamu Ɗanmaraya Jos

 

Hausawa sukan haɗa kalmar ɗan da wani gari. irin wannan yana nuna ko dai mutumin da yake amsa sunan ɗan wannan garin ne, ko a garin aka haife shi. Misali, Ɗanborno, Ɗangusau, Ɗanzuru, ’Yarhaɗeja da dai sauran su. Akwai makaɗa da mawaƙan Hausa da ire-iren waɗannan sunaye suke yi musu linzami. Misali:

                    i.                        Musa Ɗanbade

                  ii.                        Bage Ɗansala

Har wa yau dai ana samun sunayen Hausawa na laƙabi musamman masu nuna ranakun haihuwar mutane (Maza) da suke zuwa da wannan kalma ta Ɗan. Misali. Ɗanladi, Ɗantani, Ɗanjuma, Ɗanlami (Abdullahi 1997). A matsayinsu na Hausawa, wasu makaɗa da mawaƙan Hausa suna amsa ire-iren waɗannan sunayen. Misali:

                    i.                        Ɗanlami Nasarawa

 

 

Akwai wasu laƙubba na Hausawa masu zuwa da kalmar ta ɗan wadda ake maƙalawa da wata kalma bisa wani dalili na musamman. Bin diddigin tarihin samar da sunan ga ɗaiɗaikun mutane masu amsa su, shi zai samar da ma’anar ko dalilin sanya su. Ga misalai daga sunayen wasu makaɗa da mawaƙan Hausa.

                    i.                        Aliyu Ɗandawo

                  ii.                        Garba Ɗankyana

               iii.                        Idi Ɗangiwa Zuru

               iv.                        Garba Ɗanwasa

                  v.                        Mu’azu Ɗan’alalo

 

3.2 Sunaye Laƙabi Masu ‘Mai’

Idan Bahaushe ya fara ambaton ‘Mai’ a suna to yana nufin mallaka. Wato wannan mutun shi ya mallaki wannan abin. Misalin irin waɗannan sunaye a Hausa su ne Maihulla, Maidaura, Maikudu, Mairiga da dai sauransu. Idan an lura, za a fahimci wasu daga cikin waɗannan sunaye suna danganta mutum ne da wani wuri (kamar gari- Maidaura) ko kuma wani abu (kamar Mairiga). Galibin masu amsa ire-iren waɗannan sunaye suna daga cikin makaɗa da mawaƙan Hausa sukan kasance an danganta su ne da kayan kiɗan da suke amfani da su. Haka kuma akwai waɗanda laƙabi ne kawai na Hausawa da yake nuna mallakar wani abu ko wani wuri. Misali:

                    i.                        Sa’idu Maidaji Sabon Birni

                  ii.                        Amadu Mailauni Bakura

               iii.                        Garba Maitandu

               iv.                        Ubale Maikukuma

                  v.                        Muhammadu Ango Maitabshi

               vi.                        Garba Mainakada

             vii.                        Babba Maigoge

           viii.                        Maigari Maijauje

                ix.                        Ango Maizari

                  x.                        Alu Maituru

                xi.                        Uwaliya Mai’amada

 

A waɗannan sunayen, da zarar an cire ‘Mai’ to ba za a iya gane ko wa ake magana a kansa ba. A taƙaice dai laƙabin shi ne linzamin sunan makaɗin.

 

3.3 Laƙabin Sunayen Gargajiya

Bahaushe yana da wasu laƙubba waɗanda kafin ya zama musulmi su ne sunayensa na gargajiya. Bayan da ya musulunta ne ya sami sunayen da ake kira na yanka. A da Hausawa suna samar da irin waɗannan sunaye ne ta la’akari da yanayin abin da aka haifa ko siffar jiki ko lokacin da aka haihu ko kuma wasu abubuwa da suka faru kafin ko bayan haihuwar. Misalin ire-iren waɗannan sunaye su ne Ciwake, Tarana, Bawa, Jatau, Kura da dai sauransu (Yahaya 1979, Abdullahi 1997). Bayan da Hausawa suka sami sunayen yanka, sai ire-iren waɗannan sunayen suka zama wani rukuni na sunayen laƙabi. Kasancewar makaɗa da mawaƙan Hausa su ma Hausawa ne, an sami wasu daga cikinsu da ke amsa ire-iren sunayen. Haka kuma sunayen sun yi tasiri a rayuwarsu ta kiɗa da waƙa. Misali:

                    i.                        Bawa Ɗan’anace

                  ii.                        Rabo Ango Yabo

               iii.                        Ƙwazo Bagega

               iv.                        Gero Zartu

                  v.                        Barmani Coge

               vi.                        Buda Ɗantanoma

             vii.                        Abdu Wazirin Ɗanduna

          viii.                        Ciwake Namaiyaƙi

                ix.                        Jatau Kamba

                  x.                        Amali Sububu

 

Waɗannan duk sunaye ne na gargajiya waɗanda a yanzu suke a matsayin sunayen laƙabi.

 

3.4  Sunayen Garuruwa da Ƙauyuka a Matsayin Laƙabi

Al’ada ce ta Hausawa mutum ya amsa sunan garinsu ko ƙauyensu ko kuma inda aka hafe shi ko wurin da yake zaune a matsayin wani sashe na sunansa. Da farko ana yin haka ne saboda kunyar da suke da shi na amsa sunan iyaye kai tsaye. Bahaushe yana jin nauyin ambaton sunan iyayensa. Akan sakaya sunan mai amsa sunan iyaye kuma a girmama shi albarkacin wannan suna komai ƙanƙantarsa. Idan Hausawa suna zaune a wani gari da ba nasu ba, akan sami sauƙin tantance su ta hanyar amfani da sunan gari ko ƙauyen da suka fito. Sannu a hankali har sunan wannan gari ko unguwa ya rijayi sunan nasu na yanka ko laƙabi. Misalin irin waɗan sunye da aka saba da su su ne, Shehu Shagari, Aminu Kano, Amadu Raɓa, Abubakar Gummi da dai sauransu.

 

Makaɗa da mawaƙan Hausa su ma sun bi sahun ire-iren waɗannan mutane wajen amsa sunayen garuruwa da wurare a matsayin sunayensu na yanka. An wayi gari idan ba a haɗa sunan mutum da sunan gari ko wuri wajen ambaton waɗannan mawaƙa ba to ba za san wanda ake magana a kansa ba. Ga misali sunayen waɗannan makaɗa da mawaƙan.

    1. Sa’idu Faru
    2. Taudo Inugu
    3. Atta Dabai
    4. Abubakar Kassu Zurmi
    5. Abdu Inka Bakura
    6. Rabo Ango Yabo
    7. Musa Illon Kalgo
    8. Ƙwazo Bagega
    9. Abdu Karen Gusau
    10. J. B. Zauro
    11. Adamu Ɗanmaraya Jos
    12. Ɗangiwa Zuru
    13. Ɗanlami Nasarawa

 

3.4              Laƙabin Zamani

Hausawa sukan ce ‘Zamani abokin tafiya.’ Akwai laƙubba da yawa waɗanda Hausawa suke amsawa a sakamakon haɗuwa da zamani. Wasu suna da alaƙa da karatun boko ko harshen Ingilishi ko wasanni irin na ƙwallon ƙafa ko kirari ko sunan wani abu da ke da alaƙa da zamani da dai sauransu. Abdullahi (1997) ya kawo misalan ire-iren waɗannan sunaye kamar Pele, TK, TJ, Jimmi. Wasu makaɗa da mawaƙan Hausa da suka riski irin wannan wayewar, sun kwatanta amfani da ire-iren waɗannan laƙubba na zamani. Sunayen sun yi musu rinjaye wajen adana tarihin nasu musamman ta fuskar kiɗa da waƙa. Akwai sanannun makaɗa da mawaƙan Hausa masu amsa ire-iren waɗannan sunaye na laƙabi. Misali:

                    i.                        Garba Super

                  ii.                        Hassan Wayam

               iii.                        Sani Sabulu

               iv.                        Ɗanmani Caji

                  v.                        J. B. Zauro

               vi.                        Idi Loga

 

3.5 Laƙabin Ná

Ná a Hausa harafi ne mai nuna mallakar abu namiji (Ƙamusun Hausa 2006:355). Hausawa suna amsa sunayen laƙabi masu farawa da wanda ke bayyana kusanci tsakanin mai laƙabin da wannan da aka nuna nasa ne. Irin wannan laƙabi yakan zo da sunan mutum ta yadda za a fahimci cewa, wanda ake yi wa laƙabin yana da kusanci ƙwarai da mai wannan sunan, kamar a kira mutum ’amadu. Haka ma irin wannan laƙabi yana ɗaukar suna gari ko wata dabba ko kuma wani abu. Akwai makaɗa da mawaƙan Hausa da aka sani sun yi fice da ire-iren waɗannan sunaye na laƙabi.Misali:

                    i.                        Ibrahim Narambaɗa

                  ii.                        Jibo Nakwakwai

               iii.                        Abdu Nagusau

               iv.                        Mamman Nakaka

                  v.                        Roƙo Namatuga

               vi.                        Nagambo Maikotso

 

3.7       Laƙabin Wasu Sunayen Yanka

Hausawa suna da wasu laƙubba na musamman da ake yi wa wasu sunaye na yanka. A duk lokacin da aka ambaci ire-iren waɗannan laƙubba to Bahaushe ya san asalin sunan na yanka. Misali, sunan Muhammadu ana iya kiransa Inuwa. Abubakar a kira shi Garba, ko Sadik. Ita kuma A’ishatu a kira ta Indo (Yahaya 1979). Kasancewar makaɗa da mawaƙan Hausa su ma Hausawa ne, wasu daga cikinsu masu amsa ire-iren waɗannan sunayen na yanka sun ci gajiyar sunayen laƙabi na Hausawa da aka laƙaba musu. Misali:

                    i.                        Shehu Ajilo

                  ii.                        Kulu Mukunu Wasagu

               iii.                        Binta Zabiya Katsina

               iv.                        Garba Ɗanwasa

                  v.                        Garba Maitandu

               vi.                        Garba Super

             vii.                        Garba Mainakada

 

3.8       Laƙubban Sunayen Gida

Daga cikin sunayen yanka da Hausawa suke ba ‘ya’yansu, akan sami wasu waɗanda suke da nauyi ga wasu mutane a cikin zuri’ar wannan gida. Makusantan masu amsa sunayen da suke da nauyi ambato, sukan ba su wasu sunaye na daban. Misali Babangida ko Abba (idan aka sa sunan maigida) Uwa, ko Uwani Da dai sauransu. Akwai wasu daga cikin makaɗa da mawaƙan Hausa waɗanda ire-iren waɗannan sunaye suka yi tasiri a rayuwarsu. Misalin waɗannan makaɗan su ne:

                    i.                        Asma’u Uwani Mai’amada

                  ii.                        Uwaliya Mai’amada

               iii.                        Ubale Maikukuma

               iv.                        Babangida Kaka Dawa

                  v.                        Uwani Zakirai

 

3.9       Laƙubba Daga Ƙabilar Fulani

Alaƙar zaman tare na lokaci mai tsawo a tsakanin Hausawa da Fulani ta haifar da aron al’adu a tsakaninsu. Akwai al’adun Hausawa da yawa waɗanda idan aka zurfafa bincike sai a tarar da asalinsu na Fulani ne. Haka su ma Fulanin da suka kusanci Hausawa, sun ajiye al’adunsu da dama sun rungumi na Hausawa. A irin wannan yanayi ne aka sami wasu sunaye na Fulani da yawa sun yi tasiri a al’ummar Hausawa har aka wayi gari an manta asali na Fulani ne. Misalin waɗannan sunaye su ne, Tukur, Bello, Modibbo. Akwai makaɗa da mawaƙan Hausa waɗanda ko dai asalinsu Fulani ne ko kuma Hausawa ne da suka jiɓinci Fulani amma da harshen Hausa suke waƙa kuma suna amsa ire-iren waɗannan sunayen. Misali,

                    i.                        Buba Ɗantanoma

                  ii.                        Tukur Jabo

               iii.                        Ɗanmanu Wababe

               iv.                        Tauɗo Inugu

 

3.10 Ararrun Laƙubban Shahararrun Makaɗa da Mawaƙa

Shaharar wasu mawaƙan Hausa kamar Alhaji Mamman Shata da Alhaji Musa Ɗankwairo ta sa aka sami wasu mawaƙa masu amfani da kayan kiɗa irin nasu da sigar waƙa irin tasu sun laƙaba wa kansu wannan sunan na makaɗin. Ire-iren waɗannan mawaƙa za a fahimci ba wata alaƙa ta jini ko ta barantaka a tsakaninsu da wancan shahararren mawaƙin. Hasali ma garinsu ba ɗaya ba. Irin waɗannan sunaye sukan bayyana ne bayan rasuwar shararren mawaƙin. Sha’awa da ƙoƙarin kwaikwayon irin waƙoƙin shahararren mawaƙin sukan taimaka a mallaki irin waɗannan laƙubban. Misali,

                    i.                        Shatan Gorau

                  ii.                        Ɗanƙwairon Gwambe

               iii.                        Miko Audu Shatan Nasarawa

               iv.                        Haruna Ɗanƙwairon Maƙarfi

                  v.                        Salihu Inuwa Ɗanƙwairon Kano

 

3.11 Sauran Laƙubban Makaɗa da Mawaƙan Hausa

Baya ga waɗannan rukunai na laƙubban makaɗa da mawaƙan Hausa da aka ambata, akwai da yawa daga cikin waɗanda ba su faɗo a kowane rukuni ba. Sun sami waɗannan laƙubban ne bisa wasu dalilai na tarihi da mawaƙan suka bayyana ko bincike ya gano. Wani abin lura a nan shi ne, laƙubban da ake kiran waƙannan mawaƙa da su sun yi tasiri a rayuwar da suka yi na waƙa ta yadda dole sai an ambaci sunan za a iya fahimtar wanda ake magana a kansa. Misali,

  1. Amadu Doka
  2. Audu Kara-kara
  3. Haruna Uji
  4. Mamman Shata
  5. Salihu Jankiɗi

 

 

4.0 Kammalawa

Wannan nazari ya yi ƙoƙarin tabbatar da hasashen da aka yi tun farko na cewa, sunayen laƙabi su suke jagoranci wajen fayyace makaɗan Hausa. Duk da yake akwai tabbacin cewa, kowane Bahaushe ba ya rasa sunan laƙabi, amma wasu dalilai musamman a yanzu sun sa ana samun Hausawan da laƙabinsu ya ɓace. Wato sunayen yanka kawai suke amsawa. Wannan nazarin ya tabbatar da cewa, samun irin wannan yanayin ya ƙaranta ƙwarai ga makaɗa da mawaƙan Hausa. Nazarin ya ci nasarar zaƙulo rukuni goma sha ɗaya (11) inda makaɗa da mawaƙan Hausa suke watayawa a farfajiyar sunayen laƙabi. Baya ga amfani da laƙubban da Hausawa suke amfani da su, kamar na ranaku da na gargajiya da na garuruwa, nazarin ya gano akwai wasu laƙubba da suka keɓanta ga makaɗa da mawaƙan Hausa su kaɗai. Wannan ya shafi laƙubba waɗanda suke da dangantaka da kayan kiɗan da suke amfani da su ko rukunin waƙar da suke yi ko kuma sunayen da aka samo daga sha’awar alaƙanta kai da wani Shahararren mawaƙi. Haƙiƙa nazarin ya tabbatar da makaɗa da mawaƙan Hausa ba su yin fice, duniya ta ji su sai da sunan laƙabi. Wannan suna shi ke bambanta su da juna, shi ke bambanta su da sauran jama’a da ba makaɗa ko mawaƙa ba. Da sunaye irin su Shata ko Narambaɗa ko Ɗanƙwairo ko Ɗandawo ko Ɗan’anace ko Jankiɗi aka san masu su. Da irin waɗannan sunaye ne ake tabbatar da shahararsu ta yadda idan ba sunayen aka ambata ba, zance a kan su ba zai kammala ba domin ma’ana ko saƙon ba zai fito ba.

5.0 Manazarta

 

Abbas, N. I. (2012) ‘’Nahawun Sunayen Hausawa ‘’ Kundin Digiri na Biyu (M. A. Hausa) Sakkwato: Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Abdullahi, I. S. S. (1997) “Tasirin Zamani da Illolinsa Kan Sunayen Hausawa.” Sakkwato: Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Al-ma’sumi, B. M. A (1999) A Guide to Islamic Names. Saudi Arabia: Publish by Ad-Dar As-salafiah.

Aminu, M. (1992) Matsayin Sunaye a Aladun Hausawa. Kano: Aminu Zinaria Recording and Publishing Company Sagagi

Buba, M. (2008) “Naming Names” Presented at the Faculty Seminar Series, Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

CNHN (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Gusau, S.M. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa 1. Kaduna: Fisbas Media Services.

Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa Yanaye-Yanayansu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2016). Makaɗa da Mawaƙan Hausa Littafi na Biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, S. M. (2019) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Huɗu Wasu Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo Maradun (1909-1991). Kano: Century Research and Publishing Limited.

Ibrahim, M.S. (1983) Kowa ya Sha Kiɗa. Zaria: Longman Nigeria Plc.

Madauci, I. Yahaya, I. and Daura, B. (1968) Hausa Customs. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

Umar, M. B. (1985) Ɗan-maraya Jos. Ibadan : University Press Limited

Yahaya, I. Y. (1979) “Sunayen Hausawa na Gargajiya.” Kano: Cibiyar Nazarin Harsuna Nijeriya, Jami’ar Bayero 

Post a Comment

0 Comments