Ticker

6/recent/ticker-posts

Giya Madarar Arna: Nazarin Tu’ammalin Bamaguje da Giya

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2021) “Giya Madarar Arna: Nazarin Tu’ammalin Bamaguje da Giya” East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature Vol.4 Issue 4 ISSN- 2617-7250 (Online) ISSN 2617-443X (Print) East African Scholars Publishers, Kenya Pages 173-178 DOI: 10.36349/easjehl.2021.v04i04.004.

Burkutu Gida

Giya Madarar Arna: Nazarin Tu’ammalin Bamaguje da Giya

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
08036153050

Tsakure

An gina wannan maƙala ne kan ƙoƙarin fito da irin shaƙuwar da Maguzawa suka yi da giya wadda har ake ganin rayuwarsu gaba ɗaya ba ta iya gudana ba tare da giya ba. Manufar wannan bincike ita ce, tabbatar da irin kallo da fahimmtar da musamman Hausawa suke yi wa al’umar Maguzawa. An yi amfani da dabarar mu’amala ta kusa da kuma hira da waɗannan mutane da ake kira Maguzawa daga sassa da dama wanda hakan ya tabbatar da hasashen da ake yi na irin alaƙar da ake hange a tsakanin Maguzawa da giya. Wannan zanari ya gano lungu da saƙo na aladun Maguzawa waɗanda suka shafi muamala da giya. Nazarin ya gano cewa wasu aladu na Maguzawa ba za su iya gudana ba idan ba a sa giya a ciki ba. Hakan yana faruwa ne saboda muhimmancin da aka ba giyar a wajen aiwatar da aladun. Nazarin ya fahimci cewa, duk da irin nagartar da ke ga Maguzawa wajen riƙe amana da kyakkyawar muamala, hulɗarsu da giya ta sa yanuwansu Hausawa suka ƙyamace su.

Fitilun Kalmomi:  Maguzawa, Giya, Mu’amala, Al’ada

1.0 Gabatarwa

A nazarce-nazarcen da aka yi kawowa yanzu a kan rayuwar Maguzawa an fahimci cewa mutane ne masu sha’awar tu’ammali da giya matuƙa. Giya ta sami ratsa wasu matakan rayuwarsu kamar na aure da mutuwa. Haka ma abin yake a cikin akasarin harkokin da suka shafi bauta. Ta fuskar karimci da shaƙatawa ma, duk za a ga sha’anin giya tana ta kai da kawo. Shan giya a wurin Maguzawa babu babba ba yaro. Sai dai dattijai masu shekaru da yawa sun fi sakewa wajen tu’ammali da ita. Wannan nazarin zai mayar da hankali ne a kan alaƙar Bamaguje da giya. Hasashen wannan binciken shi ne Bamaguje ba ya rayuwa sai da giya, kwatankwacin yadda rayuwar Bahaushe da goro take a yanzu. Wannan nazari zai yi ƙoƙarin tabbatar da tunanin cewa, tu’ammalin Bamaguje da giya ita ta nesanta shi da Bahaushe. Nazarin zai tabbatar da giya a matsayin ɗaya daga cikin dalilan kasa nashewar Bamaguje da Bahaushe duk da kasancewar su abu ɗaya ta wasu fuskoki kuma na lokaci mai tsawo.

2.0 Fashin Baƙi

Wannan fasali zai bayar da haske ne a kan tubalan taken nazarin. Waɗanan tubalai kuwa sun haɗa da kalmomin giya da Bamaguje. Haka kuma fasalin ya waiwayi matsayin giya a duniyar mutane.

2.1     Giya

Ga dukkan alamu, wannan kalma ta giya Bahaushiya ce. Wato ba aro ta Bahaushe ya yi daga wani harshen ba. Ƙoƙarin waiwayen tarihi ya tabbatar da Bahaushe yana da wannan kalmar da fasaha ko kimiyyar duk abin da ta ƙunsa kafin haduwarsa da wata al’uma. To sai dai akwai wata kalma ta Ingilishi da ta shigo wa Bahaushe daga baya wadda ya ɗauki furucin kalmarsa ta giya ya ɗora mata. Bahaushe ya yi haka ne saboda kusanci da ke tsakanin kalmomin guda biyu wajen furuci. Wannan kalma ta Ingilishi ita ce Gear wadda ake sa wa mota ko mashin ko wani injin don ya motsa ya yi aiki. Bahaushe ya kira wannan kalmar da giya kai tsaye kwatankwacin yadda furucin yake da harshen na Ingilishi. Abin da kawai yake bambanta wannan kalmar ta Ingilishi (wadda aka Hausantar) da wadda ake nazari a kai shi ne muhallin da ta fito a cikin zancen da ake yi. Misali, idan mutum ya ji ana maganar mota aka ambaci giya to ya san giyar sha ake nufi. Alaƙarsu a nan kawai ta furuci ce.

A Ƙamusun Hausa (2006: 168) an bayar da ma’anar giya da:

Wani abin sha da ake yi da hatsi ko alkama ko inabi wanda ake sha a yi maye.

Wannan ma’ana ta nuna cewa, giya nau’in abin sha ne. Wato ta faɗo a rukunin abincin Bahaushe mai ruwa-ruwa dangin kunu ko koko ko hura da dai sauran su. Muhimmiyar kalmar da za ta bambanta wannan abin sha da sauran da aka ambata kuma ya yi tasiri a wannan ma’ana ita ce maye. Wannan kalma ta maye, ita ya kamata a ce ta ja hankalin wannan nazari musamman a wannan mataki, kasancewar ganin tana da alaƙa ta ƙud-da-ƙud da giya. Bisa ma’ana, idan aka ce “maye” ana nufin tangaɗi saboda shan wani abu mai bugarwa. Da zarar mutum ya sha wani abu wanda ya sa ya fita cikin hayyacinsa, to kai tsaye akan ce yana cikin maye. A taƙaice, fita cikin hayyaci musamman ta hanyar yin tangaɗi shi ake kira maye. Wata kalmar kuma mai alaƙa da kalmar giya ko maye ga Bahaushe ita ce Marisa. Ita ma wannan kalmar tana nufin “Maye da gushewar hankali da tangaɗi wanda mai shan ƙwaya ko giya yake yi” (Ƙamusun Hausa 2006: 333). Baya ga waɗannan kalmomi kuma, akwai wasu kamar Barasa wadda ita ma take nufin giya. Haka kuma akwai Burkutu wanda suna ne na giyar gargajiya ta dawa.

Ta la’akari da bugarwa da giya take yi wa mutum ya fita cikin hayyacinsa har ya aikata wani abin da bai dace ba, Bahaushe yakan ari wannan kalma ya danganta ta da wani abu da aka aikata mai alaƙa da fita cikin hayyaci irin na shan giya. Misali, Idan basarake ko wani shugaba ya yi amfani da ƙarfin mulki fiye da kima, akan ce

-         Giyar mulki ta ja shi.

-         Giyar mulki ke aiki.

Haka kuma idan mutun ya rufe ido, ya cire kunya da sani da sabo, ya ci mutumcin wasu mutane, akan ce:

          - Ya sha musu giyar kansu, ya gaya musu magana.

          - Ai sai da na sha musu giyar kansu.

 

2.2  Bamaguje

Malamai da manazarta da yawa sun yi ittifaƙi a kan wanda ake kira Bamaguje a ilmance. Daga cikkinsu akwai: Krusius (1915), Fletcher (1929), Ibrahim (1982), Yusuf (1986), Kado 1987, Safana (2001), Akodu (2001), Malumfashi (2002), Abdullahi (2008), da dai sauransu. Waɗannan masanan sun tafi a kan cewa, Bamaguje shi ne Bahaushen asali wanda ba Musulmi ba, mai gudanar da rayuwarsa ta hanyar bin tanadin da aka yi a al’adarsa da addininsa na gargajiya. Bamaguje suna ne na jinsin namiji. Ana kiran mace Bamagujiya ko Bamaguza. Jam’i kuma a ce Maguzawa.

2.3  Giya a Duniyar Mutane

Giya tsohuwar abin sha ce da ke sa maye wadda ta yi tasiri a ƙasashe da yawa na duniya. Kusan a ce duk inda ɗan Adam yake ko inda ya taɓa zama, an sami wani abu da aka sha ko ma ake sha mai gusar da hankali kwatankwacin giya. A bayanin Wikipedia, giya tana ɗaya daga cikin abin sha mafi tsufa a duniya. Haka kuma binciken ya gano, giya ita ce abin sha na uku mafi karɓuwa ga mutane baya ga ruwa da shayi. A wasu sassa na duniya, ana yin giya ne ta hanyar tsima shinkafa ko masara ko alkama da dai sauransu. Haka kuma wasu al’ummomi suna amfani da tsirrai ko itatuwa iri-iri musamman waɗanda suka ci karo da su a kewayen wurin da suke zaune, suna haɗa su da hatsin da suka tsima domin su sami ɗanɗano ko kuma gamsuwar da suke bukata daga wannan giyar.

Bayanai sun tabbatar da ’yan adam sun ilmantu da samar da abin da za a kira giya tun a wajejen shekara 8500 kafin bayyanar Annabi Isah (AS). Haka kuma, rubuce-rubucen da aka samu na mutanen da suka zauna a tsaunukan Zagros na kudancin ƙasar Farisa sun nuna cewa, giya ta samu a wannan yankin kusan shekaru 10,000 kafin bayyanar Annabi Isah. Haka kuma labaran wanzuwar giya sun fito a cikin littattafan tarihin tsofaffin daulolin Iraƙi da Misira. Misali, a daular Misra ta wancan lokacin, an nuna an yi ta raba wa ma’aikatan da suka gina Dala kwatankwacin litoci 4 na giya a kowace rana a matsayin wani abin nishaɗantar da su wanda hakan aka nuna yana da muhimmanci matuƙa a lokacin da ake gina wannan dalar.

Idan aka dawo yankin nahiyar Turai kuma, an sami tabbatattun bayanai da suka nuna giya ta karaɗe sassa da yawa na nahiyar a shekarar 3,000 kafin bayyanar Annabi Isah (AS). Sai dai bayanan sun nuna abin da mutanen wannan yanki suka sha a wancan lokacin duk da yake tana bugarwa, ba za a kira ta giya a yanzu ba. A wancan lokacin suna haɗa tasu giyar ce da ’ya’yan itace, da zuma da ɓawo ko ganyayyakin itatuwa da kayan yaji da dai sauran su.

A yankin nahiyar Afrika kuma, nan ma bayanai sun tabbatar da kusan kowace ƙabila tana da hanyoyin da take samar da abubuwan da suka danganci shaƙatawa wanda daga ciki akwai giya. Fasaha da kimiyyar harhaɗa abubuwan da za su sa a yi maye tun a wancan lokacin sun dogara ne ga ko dai abin da muhalli ya samar ko kuma abin da aka gada daga iyaye da kakanni. Misali a wasu sassa da ke da kurmi ko yalwar itatuwa, za a ga ana samar da giya kai tsaye daga jikin itacen kwakwa. Irin waɗannan dabaru sun yi ta samun sauye-sauye daga lokaci zuwa lakaci musamman a sakamakon wayewa ko haɗuwa da baƙin al’ummu.

A taƙaice dai, tarihi ya tabbatar cewa, al’amarin giya abu ne da ya zaman ruwan dare ga al’umomi da yawa na duniya tun kafin su waye ko su haɗu da wasu baƙin. Giya musamman ta gargajiya, tana da matuƙar muhimmanci ne a wajen wasu ƙabilun ta yadda suka alaƙanta ta da abin da suke bauta wa. Wasu kuma ita kaɗai ce hanyar da za a karrama baƙi. Wasu al’umomin sun ɗauke ta a matsayin hanyar shaƙatawa a lokacin da ake so. 

3.0 Matakan Samar da Bamagujen Giya

Giyar da Maguzawa suka laƙanta kuma suka fi tu’ammali da ita musamman a gargajiyance ita ce giyar dawa. Wannan giya da dawa ake yin ta, kuma ita ce wasu suke kira Burkutu. Ba abin mamaki ba ne Maguzawa daga yankuna daban-daban su bambanta a kan matakan da suke bi wajen samar da wannan nau’i na giya a gargajiyance. To sai dai a binciken da aka gudanar, hanyar da aka ambata a wannan fasali kusan a ce shi ne karɓaɓɓe kuma mafi sauƙi da akasarin Maguzawan suke amfani da shi. Wani muhimmim abin jawo hankali a nan shi ne, Maguzawa sun bar wannan al’ada ta samar da giya a hannun jinsin mata. Wato kamar yadda al’ada ta keɓe dafa abinci a hannun mata, haka ita ma giya.

Idan Bamagujiya za ta yi giya, akan sami dawa mai kyau gwargwadon yadda ake bukata, a jiƙa ta a ruwa ta kwana ɗaya. Idan ta kwana sai a tsame, a zuba a leda a rufe da ganye (kamar nikawa). A haka za a bari ta kwana biyu cikin leda. Bayan waɗannan kwanakin, sai a buɗe. Za a ga ta fara tsirowa, daga nan sai a shanya ta bushe. Sai a niƙa ta zama gari. Daga wannan garin za a ɗebi wani a ajiye. Ana kiran wannan da aka ɗiba “miji”. Sai a dama sauran garin. Tsaki zai taso sama, gasara (ƙullu) zai kwanta na ƙasa. Za a kwashe tsakin a dafa, a haɗa shi da gasarar da ba a dafa ba, a motsa shi gaba ɗaya. Idan ya huce sai a mayar da shi kan tukunya. In ya fara zafi sai a ɗauko miji a zuba a motsa sosai har sai ya haɗu. Idan aka ga tana kumfa da maiƙo-maiƙo ta dahu ke nan, sai a sauke, a bar ta ta kwana. Alamar da ke tabbatar da giyar ta haɗu za a ji tana ƙara ƙu-lu-lu. Da an sha sai buguwa. Ɗanɗanonta zai kasance tsami-tsami. Alamar buguwa kuma shi ne za a ta tangaɗi ko mashalo ko surutai, a cire kunya wajen magana ko aiki.

Maguzawa suna adana irin wannan giyar ne a cikin manyan tukwane na ƙasa. Idan za a kai ta wani wuri musamman wurin taro, akan kai ta ne cikin tulu. A lokacin da za a ba mutane su sha kuma, akan tanadi ƙoƙo (ƙaramar ƙwarya) a rinƙa zuba wa mutane suna sha. Idan mutum ya shanye yana bukatar a ƙara masa, sai a daɗa tsiyayo masa daga cikin tulun.

4.0 Giya a Kasuwanin Maguzawa.

A kasuwannin ƙauyukan Maguzawa, akan keɓe wuri na musamman inda aka yi runfuna don sayar da giya da shan ta. A duk ranar kasuwa, za a ta fitowa da giya daga wurare daban-daban don sayarwa. Mashaya giya masu cin kasuwa sukan ta zuwa wannan wuri suna saye suna sha musamman wadda aka kawo daga wasu wuraren da ba ƙauyukansu ba. Kamar abinci, giyar da ta fi daɗi takan fi saurin ƙarewa a irin wannan wuri. Jinsin mata masu manyan shekaru su ke sayar da giyar a irin waɗannan kasuwanni tare da taimakon ’ya’yansu ko ma jikoki. Runfunan sayar da giya a kasuwannin Maguzawa sun fi cika da yamma kafin a watse, bayan mutane sun sayar da abin da suka kawo. Akan sami makaɗa a irin wannan wuri suna zuga ko wasa masu sha. Haka ma akan sami waɗanda sukan bugu su kasa tashi. A irin haka, ’ya’uwansu za su ɗauke su su kai gida.

5.0 Kimar Giya a rayuwar Bamaguje

Muhimmancin giya a ayuwar Maguzawa ta sa sun samar mata da matsayi na musamman a harkokin rayuwarsu da dama. Wasu Maguzawan tun a wajen adana dawar da aka noma za a cire na shan giyar maigida. Wannan dawar ita za a riƙa yi masa giya da ita daga lokaci zuwa lokaci yana sha, yana karrama baƙin da suka ziyarce shi. Idan kuma har ba a yi giya a gidan Bamagujen ba, to wannan dawar za a rinƙa ɗiba yana sayarwa yana shan giya da kuɗin. Wasu kuma sukan ɗibi daga cikin dawar da aka cire musu na shan giya su tafi da ita gidan da ake shan giyar. Akan a dubi kimar dawar, a karɓa, sai a ba shi giya na kwatankwacin kuɗin dawar. Idan tsoho ya sha giyar ya ƙoshi ba ta ƙare ba, to ko dai ya dawo gida da sauran ko kuma a ba shi sauran dawar ya dawo gida da ita.

’Ya’ya ko jikokin Bamaguje sukan bi shi warin da yake zuwa shan giya. Idan ya sha ya bugu ya kasa tashi, to sai su ɗauko shi su dawo da shi gida. Wasu kuma daga gidan shan giyar idan an lura ba zai iya kai kansa gida ba, sai a aika gidansa a ce su zo su ɗauke shi.

A lokacin rani, Maguzawa sukan raba kwanakin shan giya gida-gida. Wato kowane magidanci (tsohon da ya manyanta) akwai ranar da aka keɓe masa na yin giya a sha a gidansa, kamar dai ranakun cin kasuwa. A wannan gidan kaɗai za a yi giya, mutane su taru su saye su sha. Gobe kuma a koma wani gidan. Haka za a ta zagaye gida-gida.

Maguzawa sukan ajiye giya a gidajensu a matsayin abin karrama baƙi. Idan Bamaguje ɗan’wansu ya ziyarce su, sukan kawo musu giya a matsayin abin karramawa. Shi kuma baƙo a nasa ɓangare, yakan ji daɗi an karrama shi da giya. To sai dai a irin wannan wuri, ba zai sha giyar ta yadda zai fita hayyacinsa ya kasa kai kansa gida ba. Zai sha daidai gwargwado ya bar saura.

6.0 Gurabun Giya a Wasu Al’adun Maguzawa

Maguzawa suna tu’ammali da giya a yawancin sha’anonin rayuwarsu musamman waɗanda suka shafi karrama jama’a ko bukukuwa ko bauta. A wannan fasalin, za a nazarci wuraren da giya take da tasiri ko ta yi tasiri a rayuwar ta Maguzawa.

6.1 Giya a Al’adun Auren Maguzawa

Maguzawa suna shigo da giya a cikin matakansu na ƙulla aure da ma shagulgulan da suka shafi auren. Muhallin farko da suke shigo da giya shi ne, idan saurayi da budurwa suka aminta da junansu, saurayin ya tura iyayensa wurin iyayen budurwa, da giya za su tafi. Misali, Maguzawa Ƙwanƙi a ƙasar Bakori idan za su je nemar wa ɗansu matar aure, sukan dafa giya ne su tafi da ita, su zauna da iyayen yarinya a sha, sannan su ce ga abin da ya kawo su. Su kuma iyayen yarinya ba za su ce komai ba illa godiya. Sai an yi haka kamar sau uku sai su ba da baki, bayan sun tuntuɓi duk wanda ke da hakki, ko kuma sun tuntuɓi yarinya. (Abdullahi 2008: 148)

A matakin baiko, daga cikin kayan da iyayen saurayi za su kai gidan iyayen budurwa akan haɗa da giya gwargwadon tanadin da al’adar wuri ta yi. Misali, a al’adar auren Maguzawan Gidan Bakori, idan za su tafi wurin baikon ɗansu, suna zuwa ne da tabarmi goma sha biyu da gishiri kwano goma sha biyu da kuma gorunan giya goma sha biyu. (Abdullahi 2008: 154)

A wurin ɗaurin aure ma Maguzawa sukan tanadi giya. Tun kafin ranar, uban amarya zai fitar da damman dawa a dafa giya wadatacciya wadda za a kwana uku ana sha. Haka kuma dangin uwa da uban amarya da abokan arziki sukan kawo tasu gudummuwa kafin ranar buki ko kuma a ranar bukin. Baya ga kayan abinci, wasu suna haɗowa da giya. A ɓangaren ango kuma, giya tana daga cikin kayan ɗaurin aure da dole akan haɗo da ita kafin a ɗaura aure. To sai dai adadin tulunan giyar da akan kawo a matsayin kayan ɗaurin aurre sun bambanta daga wuri zuwa wuri. Misali, Maguzawan Ƙwanƙi (cikin ƙasar Bakori) sukan ɗaura aure ne da tulunan giya da ’ya’yan gauɗe. Idan uba ko uwar amarya sun riga sun mutu to za a ce su zo da ɗan akuyar maraici. Su kuma Maguzawan Lezumawa Babban Kada, giya ake kawowa da tabarmi da kuma goro in akwai. Su kuma Maguzawan Gidan Bakori, iyayen ango za su zo ɗaurin aure ne da tulu huɗu na giya da awaki guda biyu da kaji guda biyu da dukiyar aure da kuɗin kalwa da kuɗin mai. A al’adar Maguzawan Kainafara, iyayen ango suna kai kayan ɗaurin aure ne kwana ɗaya kafin ɗaurin aure. Za a kai baƙin ɗan akuya da sabon másássábí da kibiya biyu (ɗaya mai kunne biyu, ɗayan kuma mai kunne ɗaya) da tulunan giya huɗu zuwa goma sha biyu. A hannun uban yarinya waɗannan kaya za su kwana (Abdullahi 2018: 170).

Duk wannan giyar da aka kawo a wajen baiko ko ɗaurin aure akan rarraba ta ga mutanen da suka halarci wannan wurin. Haka kuma akan keɓe wani sashe a matsayin na iyaye da kakannin amarya. Bayan jama’a sun watse, sai su rarraba ko su nemi wuri su zauna su sha abinsu.

Baya ga wannan al’ada ta kawo giya a matsayin kayan ɗaurin aure, Maguzawan Gidan Bakwai a wurin ɗaurin auren za a kira abokin ango a cika masa ƙoƙo da giya ya kafa kai ya shanye a gaban jama’a. Idan ya kasa ko ya sarƙe babu wannan aure. A dalilin haka ne kowane ango yake yin ƙoƙarin ya zaɓo cikin abokansa wanda aka san zai iya fitar da shi wannan tarkon. Yakan zama abin alfahari ga abokan ango a ce wane ne ya sha giyar auren abokinsa wane.

Kafin Maguzawa su kai amarya ɗakinta sukan yi al’adar tabbatar da ɗiyaucin ’ya mace. Wannan al’ada takan bambanta daga wuri zuwa wuri. Ibrahim (1982: 172) ya gano cewa, Maguzawan da ke bautar tsafin Bagiro, a ranar da za ta tare akan ɗauki ɗan akuya da zakara da goran giya a kai wurin da tsafin yake (gindin dutse ko wata bishiya). A nan za a bar waɗannan kayan su kwana. Idan gari ya waye, za a koma wannan wuri a gani. Idan an tarar da ɗan akuyan da zakaran sun mutu, kuma babu giya a cikin gorar, to amarya ta isa barka, ta kai budurcinta. Bagiro ya gamsu da auren shi ya sa ya shanye jinin dabbobin kuma ya shanye giyar. Amma idan aka tarar da kayan yadda aka kai su, to hakan yana nuna Bagiro bai karɓi waɗannan kayan ba, saboda amarya ba ta kai budurcinta ba. Wato ta taɓa sanin ɗa namiji kafin wannan lokacin.

6.2 Giya a Al’adun Mutuwar Maguzawa

Giya ta yi tasiri matuƙa a al’adun Maguzawa na mutuwa. Tunanin Maguzawa na tu’ammali da giya a wajen hidindimunsu na mutuwa yana da fuskoki guda biyu. Ta fuskar dangi ko ’yan’uwan mamaci ko kuma duk wanda yake da alaƙa da mamacin, idan suka sha giya a lokacin zaman makokin to suna ganin takan rage musu raɗaɗin zafi da juyayin rashin. Ta fuskar masu kawo gudunmuwar giyar kuma, Bamaguje yana ganin karimci ne idan ɗan’uwa yana cikin wata hidima da ta shafi tara jama’a to a taimaka da giya domin jama’a su sami abin kurɓawa. A wannan fasalin za a bibiyi irin shige da ficen da giya take yi a al’adun mutuwar Maguzawa.

Idan aka yi wa Maguzawa mutuwa, hidimar farko da za a sa a gaba ita ce ta binne gawa. Bayan an gama binne gawa sai a zauna zaman makoki na kwanaki bakwai. Tun daga wannan lokaci za a fara tu’ammali da giya. Wasu Maguzawan tun kafin tsoho ya mutu yakan bar saƙon cewa, idan ya mutu a ɗebi dawar da ya bari a cikin rumbu a yi abinci, a yi giya a ba mutane a lokacin bukukuwan mutuwarsa. Yana mutuwa za a fara ƙoƙarin tanadin giyar kamar yadda ya ba da umurni.

Da yawa daga cikin masu zuwa gaisuwar mutuwar Maguzawa, musamman masu alaƙa da mamaci sukan riƙo giya su zo da ita a matsayin gudunmuwa. Wannan giyar za a fara ba jama’a kafin a tanadi na gidan makokin. Daga baya idan an yi giya a gidan mamacin, sai a rinƙa haɗawa da wadda jama’a suka kawo ana ba masu zaman makokin da waɗanda suka zo gaisuwa. Wasu Maguzawan sukan ɗebi kaɗan daga cikin giyar a je a zuba a saman kushewar mamacin a ce “wane ne ya kawo maka, a ambaci sunan wanda ya kawo (Ibrahim 1982: 233, Abdullahi 2008: 333)

Ga Maguzawan da suke yin bukin kwana uku da mutuwa, sukan tanadi giyar da za a yi wannan bukin. Za a dafa giya a gidan mamacin, ga kuma wadda aka kawo gudunmuwa. Wannan giyar za a haɗa da abinci a ba mutane a wurin wannan bukin. Za a yi ta kaɗe-kaɗe da raye-raye. Jikokin mamacin su yi ta masa shaƙiyanci.

Maguzawan Kainafara sukan yi bukin kwana biyar da mutuwa a maimakon kwana na uku. Su ma sukan tanadi giya don bukin wannan ranar ya yi armashi. Akan ba jama’ar da suka taru a wamman wuri giya da abinci (Abdullahi 2008: 340)

A rana ta bakwai, ranar da Maguzawa suke share makoki, sukan yi tu’ammali da giya sosai. Wasu sukan ajiye giyar da ake ta kawowa gudunmuwa sai a wannan ranar za a fito da ita a raba wa jama’a. Idan yaro ne ya mutu, galibi Maguzawa ba su yin bukin kwana uku ko biyar. A wannan ranar ta bakwai jama’a za su haɗu a ci abinci a sha giya a share makoki ba tare da an yi wani shagali ba. Rashin yin shagalin yana da alaƙa da rashin jikoki ga mamacin waɗanda su ke ƙara wa bukin armashi. Amma duk da haka sai an ba jama’a giya sun sha.

Wasu Maguzawan sukan yi bukin kwana arba’in da mutuwa. Tun da safiyar wannan ranar za a fara taruwa a gidan da aka yi mutuwar. Dangin mamaci daga cikin masu zuwa wannan bukin sukan zo ko dai da ɗan akuya ko kuma giya. Ga wanda bai sami zuwa da ɗan akuya ba, to yakan zo da giya. A irin wannan buki na kwana arba’in, wasu ma har sa suke yankawa, su tanadi giya ma’ishi a ba mutane su sha.

Bayan bukin kwana arba’in, Maguzawa ba su sake yin wani bukin na mutuwa sai an shekara. Suna kiran wannan buki da “Bukin Juya Kadaɗa” (Ibrahim 1982: 235). A wannan bukin, duk giyar da aka tanada da wadda aka kawo gudunmuwa, ba za a fara sha ba sai an ɗibi kaɗan an je an zuba a kan kushewar mamacin. Daga nan sai a fara ba mutane tare da abinci da nama. Tun daga wayewar gari har zuwa faɗuwar rana za a ta kaɗe-kaɗe da raye-raye.

Wasu Maguzawan sukan kira wannan bukin na shekara da mutuwa da bukin “Hawan Sadaka” (Abdullahi: 2009). Buki ne da ake yi na tsawon kwanaki uku. Za a gayyaci mutane daga wurare daban-daban. A wannan bukin, akan yi gasar cin tuwon noma da fasa gida da kuma sukuwa. Kafin a shirya wannan bukin, sai an tanadi giyar da za ta ƙosar da duk mutanen da aka gayyata har ma da ’yan kallo. Yana daga cikin sharuɗɗan wannan buki, uban sadaka ya tanadi hatsin da za a yi giya da kuma abincin da zai ƙosar da mahalarta (Abdullahi 2008: 355). Shi ma wannan buki kamar sauran da suka gabata, ko da ya kasance uban sadaka ya shirya, dangi sukan taimaka da giyar da za a sha a wurin a matsayin gudunmuwa. Wasu Maguzawan sukan ƙi shan giyar da aka kawo a wurin wannan bukin domin tunanin ana iya sa musu guba/magani a kashe su. Wasu kuma sukan sha giyar sai dai ba su yarda a zuba musu cikin ƙoƙo. Maimakon haka, sai su zuba da kan su.

Bayan bukin hawan sadaka, wani buki mai alaƙa da mutuwa wanda ya bayar da damar a yi tu’ammali da giya shi ne bukin fita takabar matan mamaci. Misali, Maguzawan Gidan Gwarzo a ƙasar Matazu, sukan yi shagali sosai a ranar da matan mamaci za su fita takaba. A wannan ranar sukan fara bukin ne da almuru. Akan kwana ana ta kaɗe-kaɗe. Maza da mata su yi ta rawa. Idan gari ya waye, sai manya-manyan Maguzawan ƙauyen ko unguwar su haɗu a sha giya tare da matan da kowa da kowa. Daga nan sai matan su je su yi wanka, sun fita takaba ke nan. Matsayin da giya take da shi a rayuwar waɗannan maguzawan shi ya sa da ita ake rufe irin wannan taro.

6.3 Giya a Tsafin Gida na Maguzawa

Wasu Maguzawa sukan yi tanadin tsafi a gidajensu wanda a kansa sukan dogara rayuwarsu ta yau da kullum. Shi wannan tsafi yakan bambanta daga gida zuwa gida. To sai dai tsarin bautar tasa da kuma hidindimun da ake yi masa duk ɗaya ne. Ana sa alamar mazaunin wannan tsafin ne ta amfani da wani dutse da ake kafawa a ƙofar gidan ko a tsakar gida ko a bayan gida. Maguzawa sukan ƙudurta cewa, a cikin wannan dutsen iskar gidan take. Idan mutanen gidan za su yi rantsuwa, a wurin wannan dutsen ake zuwa a rantse. Haka kuma idan za a fita neman abinci, ko wata tafiya, za a zo wajen tsafin a nemi sa’a. Ibrahim (1982: 33) ya nuna cewa, hatta da abinci aka dafa a gidajen Maguzawa masu bautar irin wannan tsafin to za a zuba kaɗan a dutsen don ya sa albarka. An nuna cewa, duk giyar da aka dafa a wannan gidan, kafin kowa ya sha ko kafin a wuce da ita kasuwa, sai an ɗibi kaɗan an zuba a wurin dutsen (inda tsafin yake) wai don tsafin gidan ya sa albarka.

6.4 Giya a Bukin Kaciyar Maguzawa

Maguzawa suna da al’adar tara yara da yawa daga cikin dangi ko maƙwabta a yi musu kaciya a rana ɗaya kuma a wuri ɗaya. A ranar da ake yin wannan kaciyar, buki ake yi na musamman inda dangin kowane ɗan kaciya za su taru a yi ta kiɗa ana rawa. A wuri wannan bukin, akan tanadi abincin da ake raba wa jama’a. Haka akan dafa giya a raba wa jama’a domin ƙara wa bukin armashi. A ranar da yaran za su sa wando ma, Maguzawa sukan yi buki. Ana kiran wannan bukin da bukin fito (Ibrahim 1982: 139). A wannan ranar na fito ma akan tanadi abinci da giya a ba jama’a su ci, su sha.

7.0 Kammalawa

Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin duban irin tasirin da giya take da shi a rayuwar Maguzawa. A nazarin an dubi yadda giya ta sami gindin zama a sha’anin aure da mutuwar Maguzawa ta yadda a iya cewa, gudanar da kowane daga cikin hidimomin ba zai yiwu ba sai da giya. Giya ita ke ƙara wa hidimomin Maguzawa armashi ainun. Nazarin ya fito da muhimmacin giya ga Maguzawa ta yadda kafin a adana dawar da aka noma a shekara sai an fitar wa maigida ta shan giya. Keɓe ranakun shan giyar kowane gida da kuma matsayin da ta samu a kowace kasuwa sun ƙara fito da matsayin giya a rayuwar maguzawa. Haƙiƙa wannan tu’ammali da giya da Maguzawa suke yi, ita ta raba su da Bahaushe. Tana daga cikin abin da ya sa ida Bamaguje ya musulunta, ba ya ƙaunar a kira shi Bamaguje. Tana daga cikin abin da ke sa Maguzawan da suka tuba suke nesanta da ’yan’uwansu ’yan gargajiya. A ɗaya ɓangaren kuma, tunanin halin da za a shiga idan aka yanke mu’amala da giya shi ke hana wasu Maguzawan su kasa musulunta. Komai mutuncin Bahaushe, da ɗa’arsa da hazaƙarsa da wayonsa, da gaskiyarsa da riƙon amanarsa, yakan rasa kima a idon ’yan’uwansa Hausawa muddin yana tu’ammuli da giya.

Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008). ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Sakkwato: Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Abdullahi, I. S. S. (2008). “Fitattun Ɗabi’un Maguzawa” Maiduguri Journal of Linguistics and Literary Studies (MAJOLLS) Vol. X. Department of Languages and Linguistics. Maiduguri: University of Maiduguri.

Abdullahi, I. S. S. (2009). “Bukin Hawan Sadaka na Maguzawa” Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol. 1 No. 1. Department of Nigerian Languages. Katsina: Umaru Musa ’Yar’adua University.

Abdullahi, I. S. S. (2012). “Falsafar Ɗaurin Auren Maguzawa.” Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, Cibiyar Nazarin Hausa. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Akodu, A. (2001). Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Zariya: Gaskiya Corporation Limited.

Fletcher, D. C. (1929). “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment Report on ’Yanɗaka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833. Kaduna: National Archives and Monuments.

Gennep, A. V. (1960). The Rites of Passage. USA: The University of Chicago Press.

Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Kano: Jami’ar Bayero.

Ibrahim, M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci. Cyclostyled Edition. Zaria: Hausa Publications Centre.

Kado, A. A. (1987). “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

Krusius, P. (1915). “Maguzawa” in: Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

Maikano, M. M. (2002). “Maguzawan Yari Bori: Tarihinsu Da Al’adunsu”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Malumfashi, A. A. (1987). “Hausa Language Speech Usage Norms: A Case Study of Maguzawa Society in Malumfashi Area” (B. A. Hausa Project). Kano: Bayero University.

Mashi, B. U. (2001). “Maguzanci Da Zamananci: Nazari A Kan Al’adun Maguzawan Ɓula A Gundumar Mashi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Nyamwaya, D. and Parkin, D. (1987). Transformation of African Marriage. United Kingdom: Manchester University Press.

Ottenberg, P. and Simon (Ed.) (1960). Cultures and Ethics of Africa. U.S.A: H. Wolff Book Mfg.Co., Inc.

Safana, Y. B. (2001). “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Yusuf, A. B. (1986). “Wasannin Maguzawan Ƙasar Katsina”, Kundin Digirin farko. Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.


Post a Comment

0 Comments