Wannan ɗaya ne daga cikin jerin bidiyoyin taron gabatar da rubutattun waƙoƙin gasar da Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato ta shirya. Jigon waƙoƙin gasar shi ne "Tsaro a Arewacin Nijeriya." A cikin bidiyoyin taron za ku kalli yadda fasihai 30 daga jahohi daban-daban a faɗin Nijeriya suka fafata. Daga ƙarshe an ba da kyaututtuka masu tsoka ga waɗanda suka taka rawar gani.
Wani abun burgewa shi ne, bayan rubutattun waƙoƙi da aka gabatar, akwai kuma gasar "ja-in-ja" da "ga-ni-ga-ka." A wannan gaɓar haziƙan sun nuna bajintarsu nan take.Duba sauran bidiyoyin domin kallon sauran ɓangarorin taron.
Masha Allah. A gaskiya wannan kafa mai suna Amsoshi tana da matukar muhimmanci ba wai ga dalibai masu nazarin harshen Hausa ba a'a hatta duk wani mai amfani da harshen Hausa a ko'ina yake a fadin duniya zai amfana da wannan kafa wadda ta tara ilimi a cikinta.
ReplyDeleteMuna godiya ga wanda ya assasa wannan kafa wato Abu-Ubaida Sani Allah ya kara mai hazaka da basira amin. Haka kuma, muna mika godiyarmu maras adadi ga malamai masana harshen Hausa musamman malami uban malamai wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza Allah ya karamai lafiya da tsawon rai da kuma, daukaka amin.
Daga dalibin harshen Hausa Abdulrashid S Pawa Gusau.
(B.A Hausa. FUG graduand 2019).