Ticker

6/recent/ticker-posts

Makwabtakar Hausawa

Wannan bincike da aka aiwatar a kan Maƙwabtakar Hausawa ya mayar da hankali ne ga duban irin tunanin Bahaushe dangane da abin da maƙwabtakarsa ta ƙunsa wanda ake tunanin ya ƙara bambanta shi da saura al’ummu na duniya. An gudanar da nazarin ne domin duniya ta fahimci cewa, zaman muhallin Hausawa kusa da juna yana ƙunshe da wasu hikimomi da tanade-tanade da suke da alaƙa da kyakkyawar rayuwar mutanen. A ƙoƙarin tattara bayanan da suka gina wannan maƙala an nazarci irin cuɗanyar da Hausawa suka yi da juna a birane da ƙauyuka musamman a dauri ta yadda zai bayar da hoton ainihin abin da maƙwabtakarsu ta ƙunsa. Haka kuma an yi mu’amala da mutanen da suka fahimci zamantakewar Hausawa da hikimomin da ta ƙunsa. An bibiyi yadda zamantakewar Hausawa take a yanzu a wasu sassa na birane da ƙauyuka inda ake ganin har yanzu akwai wannan tunani a zukatan mutane. A ƙarshen wannan nazari an fahinci cewa, Bahaushe yana ɗaukar maƙwabcinsa kamar ɗan’uwansa na jini. Abubuwan da Bahaushe ya ɗauka maƙwabtakar su ne taimakon juna da kyakkyawar fata a tsakanin mutanen da muhallansu suke kusa da juna. Wannan tunani na Hausawa an fahimci bai tsaya ga magidantan da suka mallaki muhallin ba. Hatta da matan aure da yara ƙanana suna tafiya a kan wannan tunani da kuma tsari. Binciken ya tabbatar da maƙwabtakar Hausawa ta ƙunshi ɗabi’a mai kyau wadda ta taimaka musu wajen samar da zaman lafiya da rayuwa mai inganci.

 Fitilun Kalmomi: Maƙwabtaka, Hausawa, Zamantakewa, Muhalli

Ƙasar Hausa a Da


Maƙwabtakar Hausawa

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
E-main: ibrasskg@gmail.com

Phone +2348036153050

1.0              Gabatarwa

Hausawa mutane ne da suka fita daban ta hanyar yi wa kansu kyakkyawar tanadi wajen gudanar da al’amurran yau da kullum. Irin yanayin zamantakewarsu ta gargajiya da abin da ta ƙunsa ita ta samar musu da wasu al’adu masu ban sha’awa musamman idan an kwatanta da ire-iren waɗannan al’adu na ƙabilun da ba Hausawa ba.  Bahaushe yakan ɗauki irin waɗannan al’adu na zamantakewa zuwa duk inda ya sami kansa domin wadatar da kansa da kuma samun gamsuwa na gudanar da al’adun nasa cikin sauƙi kamar yadda ya saba. Rashin samun walwala da damar gudanar da ire-iren waɗannan al’adu shi ke takura wa Hausawa idan suka sami kansu a ƙasashen da ba nasu ba.

Wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen duban ƙunshiyar maƙwabtakar Hausawa. Wannan lamari ko ɓangare na zamantakewa da kuma salon da yake tafiya da shi abu ne da ya taimaka wa Bahaushe wajen gina wasu al’adu nasa. Wannan yunƙuri zai yi ƙoƙarin ɗora maƙwabtakar Hausawa a kan faifan nazari don zaƙulo abin da ta ƙunsa da kuma bayyana hikimomin Bahaushe na ɗabi’antuwa da al’adun da ke tattare da zama irin na maƙwabtaka.

2.0       Ma’anar Maƙwabtaka

A Ƙamusun Hausa (2006) an bayar da ma’anar maƙwabtaka da “Zaman kusantar gida ko wurin zama.” Wannan ya nuna kenan duk mutanen da wurin zama ya haɗa su to maƙwabta ne. A zahiri, Bahaushe yana ɗaukar duk gidajen da ke manne da shi, a ƙalla gida biyar zuwa goma, gabas da yamma, kudu da arewa a matsayin maƙwabta. To sai dai waɗanda suka fi kusanta da gidajen juna sun fi more wa ni’imomin da Bahaushe ya tanadar wa kansa dangane da maƙwabtaka.

 

Duk da yake Bahaushe ya fi ba nuhallin kwana muhimmanci wajen bayyana ma’anar kalmar maƙwabtaka, akan ɗauki duk wani kusanci na zamantakewa rayuwa a matsayin maƙwabtaka kamar a tsakanin gonaki da wuraren sana’a, ko tsakanin shaguna/rumfuna a kasuwa da dai sauransu.

 

Bahaushe yana kiran makusancinsa dangane da irin wannan zama na kusasanci a matsayin Maƙwabci. Idan mace ce kuma sai a ce Maƙwabciya. Jam’in mutanen da suka kusanta da juna ta fukar wurin zama su ne Maƙwabta. Zumuncin da suke gudanarwa albarkacin wannan kusanci na wurin zama ita ake kira Maƙwabtaka. Haka kuma ita ce wannan maƙalar za ta mayar da hankali a kai wajen nazartar yadda take a tsakanin Hausawa.

 

3.0       Kimar Maƙwabtaka a Tunanin Bahaushe

Tunanin Bahaushe a kan Maƙwabtaka da kuma ɗaukar mutum a matsayin maƙwabci, yana da alaƙa da hulɗar da ake yi da mutum mai kyau a sakamakon wannan zama na kusanci. Idan Bahaushe ya bugi ƙirji ya ce wane maƙwabcina ne, to tabbas akwai kyakkyawar hulɗa ta zamantakewar kusancin wurin zama a tsakaninsu. Kowane daga cikin su zai iya kashe zarafinsa da lokacinsa da ƙarfinsa wajen yi wa ɗayan hidima gwargwado, albarkacin wannan kusancin. Bahaushe ba ya ɗaukar lamarin maƙwabci da muhimmanci idan akwai zargi ko fahimtar ƙuntatawa ko rashin mutunci a tsakanin makusanta wurin zama. Wannan zai tabbatar da cewa, maƙwabtaka a wurin Bahaushe ya ƙunshi kyakkyawar hulɗa ta fahimtar juna da taimakekeniya da kuma amana da ke tsakanin mutanen da suke zaune kusa da juna. Idan har aka sami akasin haka, to maƙwabtakar takan zama suna kawai, ko a ce ba ta amsa sunanta ba.

 

4.0       Yanayi da Ƙunshiyar Maƙwabtakar Bahaushe

Bahaushe yana ɗaukar duk wani makusancin gidansa a matsayin maƙwabcinsa. Wannan ya ba shi damar yin hulɗa ta kai-tsaye musamman wadda ta shafi taimakon juna. To sai dai abin da namiji yake yi na nuna maƙwabtaka ba shi mace ke yi ba. Haka ma abin da ke tsakanin yaran Hausawa na maƙwabtaka ya bambanta da abin da al’ada ta tanadar wa manya (maza da mata). A wannan fasalin, za a fayyace abin da kowane jinsi ko rukunin mutane suke iya gudanarwa dangane da maƙwabtaka a al’ummar Hausawa.

 

4.1              Maƙwabtakar Mazan Hausawa

A lokacin da mazan Hausawa suke maƙwabtaka da juna, sukan ɗaukar wa kansu ɗawainiya a cikin rai na wasu hidimomi da kulawa don tabbatar da wannan zama na kusanci. Duk da yake ba wani zama na musamman Hausawa suka yi ba don shata waɗannan lamurran, amma kusan kowane magidanci ya san abin da ya dace ya aikata na maƙwabtaka a aƙidance. Haka kuma ba lallai ne kowane magidanci ya iya ɗauke duk nauyin maƙwabtakar a Bahaushiyar al’ada ba saboda bambancin yanayin mutane da uzurori. A wannan fasali an kawo mafi ƙarancin tunani Bahaushe dangane da maƙwabtakar maza ko magidanta.

 

4.1.1        Tarbiyya

Tarbiyya ga Bahaushe tana nufin “koyar da hali na gari” (Ƙamusun Hausa 2006: 429). Tarbiyyar Bahaushe ba ta tsaya a kan ’ya’yansa kawai ba. Duk hanyar da Bahaushe yake bi wajen tarbiyantar da ’ya’yansa ita yakan bi wajen tarbiyantar da ’ya’yan maƙwabcinsa, sai ɗan abin da ba a rasa ba musamman kasancewar ba a cikin gida ɗaya ake zaune ba. A al’adance, daga cikin waɗanda aka ɗora wa alhakin tarbiyantar da yara baya ga iyaye su ne maƙwabta (Yahaya da wasu 2001: 79).  Bahaushe yakan tsawata wa ɗan maƙwabci idan ya ga yana ba daidai ba kamar yadda yake tsawata wa ɗansa. Misali idan Bahaushe ya sa dokar hana zagi ko ashar a gidansa, sai ya fito waje ya ji ɗan maƙwabcinsa yana zage-zage, nan take yakan hana shi, ya kuma ɗaukar masa mataki kamar yadda yake ɗaukar wa ’ya’yansa idan sun saɓa wannan dokar. Maƙwabcin da aka yi wa ’ya’yansa tarbiyya yakan ji daɗi ainun idan ya fahimci irin ƙoƙarin maƙwabcin nasa. Hikimar yin haka a nan ita ce, duk tarbiyyar da mutum zai yi wa yara a gida, muddin za su fita su yi wasa da yaran maƙwabta, to za ta iya lalacewa idan har su ma ’ya’yan maƙwabtan ba su ɗabi’antu da wannan tarbiyar ba. Bahaushe yana ɗaukar ɗan maƙwabcinsa kamar ɗansa musamman a kan abin da ya shafi tarbiyya.

 

4.1.2        Gudunmuwa

Bahaushe ya ɗauki gudunmuwa a matsayin duk wani taimako da mutum zai ba wani a lokacin da yake tsananin bukatar yin hakan ko a lokacin da wata lalura tasa ta taso. Ita gudunmuwa ba lallai sai da wani abu da aka mallaka ake yin ta ba, hatta da yi wa mutum wani aiki musamman na gaggawa wani nau’i ne na gudunmuwa.

 

A duk lokacin da wani abu ya sami maƙwabci wanda yake bukatar kawo gudunmuwa, to maƙwabci ake sa ran ya fara kawo irin wannan ɗaukin. Wasu daga cikin ire-iren waɗannan ɗaukin akan kawo su kai-tsaye ba tare da an tuntuɓi maƙwabcin da ke da bukatar ba. Misali, matsala kamar ta gobara ko wani ya faɗa rijiya, ko ɓarnar iska ko tsinkewar wata mafaɗaciyar dabba da ake kiwo da dai sauransu. Duk waɗannan ƙaddarori ne munana da ka iya faɗa wa mutum, maƙwabci ya gaggauta kawo gudunmuwa na warware matsalar cikin sauri. Idan gobara ce ga misali, maƙwabci yakan gaggauta kwashe iyalin maƙwabcin da abin ya shafa ya kai gidansa. A nan za su zauna har hankali ya kwanta. Haka kuma da shi za a yi ta fafutikar kashe wutar. Ta fuskar gudunmuwar abin alheri kuma, nan ma maƙwabci yakan yi saurin taimakawa kamar da muhallin baƙi idan ana buki a gidan maƙwabci ko abincin da za a ci da dai makamantansu.

 

4.1.3        Zirga-Zirga da Ɗauke Nauyi

Bahaushe yakan bayar da taimako na musamman ta hanyar yin zirga-zirga idan wata lalura ko hidima ta maƙwabci ta taso. Maƙwabci yakan ba maƙwabcinsa dama wajen yin ruwa da tsaki a hidimar wani buki na gidansa. Irin zirga-zirgar da za a ga maƙwabci yana yi, ka ce ɗan’uwansa ne na jini.  Bahaushe yakan shiga gaba wajen hidimar maƙwabci kamar bayar da aure ’ya’yan maƙwabci ko karɓar wa ’ya’yansa maza aure. Idan kuma lalura ce ta rashin lafiya, akan ga maƙwabci yana ta zirga-zirga wajen neman magani da jinya. Haka ma idan rasuwa aka yi a gidan maƙwabci, maƙwabta su sukan ɗauki nauyin duk abin da za a yi kamar wankar gawa, samar da likkafani, binne gawar, zaman makoki, da sauransu.

4.1.4        Hidimomi na yau da Kullum

Dangantakar maƙwabtaka a al’ummar Hausawa takan sa a shaƙu da juna a riƙa sha’awar biya wa juna bukatu na rayuwa. Idan maƙwabci ya yi tafiya, yakan yo tsaraba har da ta iyalin maƙwabcinsa. Maƙwabcin Bahaushe yakan yi wa ’ya’yansa (ƙanana) kayan salla tare da ’ya’yan maƙwabcisa. Idan maƙwabci ya kira wanzami zai yi wa ’ya’yansa maza aski ko kaciya, yakan haɗa da ’ya’yan maƙwabcinsa ba tare da ya tambaye shi ba. Maƙwabcin Bahaushe yakan biya wa maƙwabcisa bashi, ya kuma ba shi zakka idan lokacin fitarwa ya yi. Maƙwabci yakan sa ’ya’yan maƙwabta makaranta kuma ya biya musu kuɗin makarantar. Maƙwabci yana samar wa ɗan maƙwabci aikin yi ko ya koya masa wata sana’a musamman wadda yake yi. Maƙwabcin Bahaushe yakan samar wa ɗan maƙwabci muhalli a gidansa tun yaro yana ƙarami har girmansa. Duk waɗannan misalai ne na taimakawa da ake samu a al’ummar Hausawa waɗanda suka shafi rayuwa ta yau da kullum. Haka kuma ana gudanar da su ne ba tare da jin nauyi ko ƙyashi ko wata damuwa ba.

4.1.5        Kalihu

Kalihu a taƙaice yana nufin mutum ya damƙa wani lamari nasa a hannu wani musamman a lokaci ko wurin da ba ya nan. A al’adance, idan wata tafiya ta kama Bahaushe kuma ya fahimci zai ɗauki lokaci mai tsawo, to yakan damƙa kalihun gidansa a hannu amintaccen maƙwabcinsa ko da kuwa wasu danginsa suna kusa. Aikin Hajji yana ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan tafiye-tafiye. A irin wannan yanayi, maƙwabcin da aka bar wa kalihu zai tsaya tsayin daka wajen ganin ba a sami matsala ba a al’amurran gidan maƙwabcin nan da ya yi tafiya. Hasali ma dai za a ga kulawar da mutum yake ba nasa gidan ba ta kai ta gidan maƙwabcin ba. Zai tabbatar da rayuwar mutanen wannan gida ta gudana ba tare da matsala ba. Abin alfahari ne ga Bahaushe a ba shi irin wannan kalihu kuma a tarar da ya ɗauke nauyin da aka ɗora masa.

4.1.6        Alƙalanci da Sasantawa da Shawarwari

A al’adar Bahaushe, maƙwabci yakan zama alƙali kuma ya jagoranci sasantawar gidan maƙwabcinsa. Irin haka yakan faru ne idan aka sami saɓani tsakanin ma’aurata maƙawabta ko tsakanin ’ya’yan maƙwabta da iyaiyensu. Idan aka sami maƙwabta waɗanda suka san ya-kamata, sukan yi amfani da damar maƙwabtaka su sasanta saɓani ba tare da an bari lamari ya lalace ba.  Maƙwabci yakan shiga cikin alƙalanci ko sasantawa na gidan maƙwabci ba sai an gayyace shi ba. Da zarar maƙwabci ya ji ko ya fahimci an sami matsala a gidan maƙwabcinsa, nan take yakan gayyaci waɗanda abin ya shafa ya sasanta. A wasu lokutan kuma, wasu ke ba da shawarar maƙwabci ya shiga tsakani dangane da matsalolin gidan maƙwanci Haka ma ta fuskar shawarwari, maƙwabta Hausawa sukan dogara ga juna wurin neman shawarar lamurran rayuwa. Akan wayi gari a ga maƙwabci ba ya da abokin shawara kamar maƙwabcinsa, kuma a daɗe ana jin daɗin juna ta fuskar wannan amana ta ba juna shawara. Irin wannan amanar takan kai ga har a iya yin wasici a tsakanin maƙwabta. Wato maƙwabci ya bar wasici ga maƙwabcinsa na abin da yake so a aiwatar musamman ga iyalinsa idan ba shi da rai.

 

4.1.7        Ayyukan Haɗin kai

A al’umomin Hausawa da yawa idan maƙwabtaka tsakanin magidanta ta yi daɗi, za a ga suna gudanar da wasu ayyuka na haɗin kai don ya taimake su da iyalinsu. Ire-iren waɗannan ayyuka sun haɗa da gyaran magudanan ruwa don kauce wa matsalar ambaliyar ruwa a lokacin damana. Idan ana fuskantar matsalar ruwa, sukan haɗa kai su haƙa rijiya wadda kowa zai amfana da ita. Idan akwai matsalar tsaro, maƙwabta sukan haɗa kai su hana kansu bacci don kare lafiyarsu da ta iyalinsu, ko kuma su ɗauki masu sintiri a unguwar suna biyan su. Maƙwabta sukan haɗa kai su samar da makaranta musamman ta Islamiyya su ɗauki nauyin biyan malamai a rinƙa karantar da ’ya’yansu. Haka ma ta fuskar kula da masallatai na unguwa, maƙwabta su ke haɗa kai su tabbatar da kula da masallatan ta fuskar tsabta da ruwa da tsaro. A al’ummar Hausawa ne haɗin kan maƙwabta ya kai ga a kullum magidanta (maƙwabtan juna) za su fito da abincin dare, su haɗu a wuri ɗaya su ci tare. Wannan yana ƙara kawo haɗin kai da zumunci a tsakaninsu.

 

4.1.8    Riƙon ’Ya’yan Maƙwabta

Yanayin maƙwabtakar Hausawa ta bayar da damar ’ya’yan maƙwabci su mayar da gidan maƙwabci kamar gidansu. A nan za su kwana, a nan za su ci abinci, a nan jama’a za su san su. Sai in wani abu ya taso sannan wasu za su san ba ’ya’yan gidan ba ne. Akan samu haka ne ta hanyar bin abokai ana kwana a gida ɗaya, har wannan gidan maƙwabcin ya zama musu wurin kwana. Sannu a hankali su girma a nan. A duk wannan tsawon lokaci, iyayen ba su damu ba. Magidancin da yaran suka tare a gidansa bai damu da ɗawainiya da su ba. Su kuma iyayen yaran da ’ya’yansu suke kwana a gidan maƙwabta ba su damu ba, musamman da yake sun san ana ɗaukar ’ya’yan nasu da mutunci. Fahimtar juna da ƙauna ita ta kai ’ya’yan nasu gidan maƙwabta ba kasawarsu ba. A wasu lokuta kuma, idan yaro ya rasa iyayensa ko ɗaya daga cikin iyayen, maƙwabci yakan iya ɗaukar dawainiyar marayun su girma a gidansa a hannun iyalinsa. A haka ire-iren waɗannan yara za su girma a gidan maƙwabci har a wayi gari su zama wani abu a al’umma.

 

4.2              Maƙwabtakar Matan Hausawa

Matan Hausawa suna da wasu al’adu da suke wakana waɗanda suka samu ko suka ƙarfafa a sakamakon maƙwabtaka tsakaninsu da juna. Mazaje a al’ummar Hausawa sukan ba matansu dama su yi mu’amala da matan maƙwabta musamman ta fuskar taimakon juna. A wannan fasalin, za a nazarci irin tanadin da maƙwabtaka ta yi a tsakanin matan Hausawa.


4.2.1        Taimakon Juna

Yanayin maƙwabtakar Hausawa ya bar ƙofa a buɗe ga matan Hausawa su yi mu’amala da juna. Wannan mu’amala ita ke samar da shaƙuwa a tsakaninsu. Matan Hausawa da sukan kasance maƙwabtan juna idan zama ya yi kyau sukan ƙulla zumunci a tsakaninsu ta hanyar taimakon juna. Misali, idan matan maƙwabci ba ta da lafiya.

 

A ɓangaren haihuwa, da zarar mace mai ciki ta fara naƙuda matan maƙwabta za su yi ta kai da kawo wajen ƙoƙarin taimaka mata a ga ta sauka lafiya. Idan ta haihu lafiya, matan maƙwabta za a fara gaya wa ta hanyar guɗa ko a aika yaro (Mairukubta 1999). Matan gida da sauran maƙwabta za su taimaka wa mai jegon  wajen ayyukan gida kamar shara da wanke-wanke da daka da dafa abinci da dai sauransu. Idan kuma rashin lafiyar ta jinya ce, za a ga matan maƙwabta sun zage dantse wajen taimaka wa marar lafiyar ta kowace fuska. Haka ma idan mace ta rasu a unguwa, mata maƙwabtan za su yi wa gawar sutura ba sai an jira dangin mamaciyar ba. Matan Hausawa da suka kasance maƙwabta suna dogara da junansu wajen kitso da renon ’ya’ya. Sukan amfana da juna wajen aron kayayykin amfani a gida kamar taɓarya da turmi da rariya ba tare  da an nemi izinin magidantan ba. Rayuwar maƙwabtakar matan Hausawa na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka ne. Kusan kowa yana amfana da wani ta hanyar taimakekeniya.

 

4.2.2        Shawarwari

Matan Hausawa da suke maƙwabtaka da juna sun fi maza amfana da wannan yanayin wajen tuntuɓar juna a kan shawarwari musamman na matsalolin da suka shafi junansu mata. Kai-tsaye sukan gaya wa juna matsaloli kuma su yi shawara a tsakaninsu ba tare da mazajensu sun san abin da ke faruwa ba. Wannan dama ta maƙwabtaka takan taimaka musu wajen riƙe amanar juna da taimaka wa juna wajen neman mafita a kan matsaloli da yawa musamman waɗanda suka shafi zamantakewar aure da na ‘ya’ya da hanyoyin inganta tattalin arziki da dai sauransu.

 

4.2.3        Tarbiyyar Yara

Su ma mata kamar maza, suna taimaka wa junansu wajen tarbiyyar ’ya’yansu musamman mata. Uwa takan kula da tarbiyyar ’ya’yan maƙwabta kamar yadda take kulawa da nata ’ya’yan. Yara mata suka fi cin wannan moriya ta maƙwabtaka idan ya kasance suna da  natsuwa. A daidai lokacin da ’ya mace take girma, iyayen sukan ba ta kyakkyawar kulawa da tarbiyantar da ita yadda rayuwar ’ya mace take. Wannan kulawa da koyar  da tarbiyya ba ya tsayawa ga ’ya’yan da mace ta haifa. Su ma ’ya’yan maƙwabta sukan amfana ta hanyar koya musu abin da ya kamata su yi da lokacin da za a yi. Wannan ƙoƙari na matan Hausawa yana taimakawa wajen inganta tarbiyyar yara mata da kuma zumuncin  maƙwabtaka

 

4.2.4        Hanyoyin Inganta Tattalin Arziki

Matan Hausawa da suke maƙwabtaka da juna suna da al’adar aiwatar da wasu dabaru na inganta tattalin arzikinsu. Ire-iren waɗannan dabaru sun danganci muhallin da suke zaune da kuma irin damar da wannan muhalli ya bayar na aiwatar da wasu al’amurra da za su tallafa wa tattalin arzikinsu. Daga cikin ire-iren waɗannan dabaru akwai ƙananan sana’o’i waɗanda ake aiwatarwa a cikin gida, kamar hura ko ƙosai ko wani abincin ƙwalama. Haka ma suna sayar da wasu abubuwa na adon mata da kayan miya kamar su barkono da kuka da daddawa da dai sauransu. Wasu kuma sukan yi kiwon dabbobi kamar awaki da tumaki da nau’o’i na tsuntsaye. Daga cikin matan maƙwabta, akan sami waɗanda suke aikace-aikacen kuɗi kamar surfe da daka da sussuka da ga-ruwa. Daga cikin su maƙwabta ake samun waɗanda ke ba su waɗanan ayyukan domin su taimaka wa juna. Idan ya kasance mace ba ta iya yin sana’a ita kaɗai, to sukan yi haɗin guiwa tsakanin maƙwabta. Wasu kuma akan sami ɗaya daga cikinsu ta bayar da jari, ɗaya kuma ta aiwatar da sana’ar. Ta hanyar ire-iren waɗannan sana’o’in ne mata ke yin asusu ko kuma su yi adashi a tsakaninsu, (Alti 2012). Fahimtar juna da suka samu albarkacin maƙwabtaka ita ta ba su damar yin adashi ko tallafa wa juna da jari. Matan sukan yi anfani da waɗannan kuɗaɗe wajen warware wasu larurorin da ba sai an tambayi miji ba. Haka kuma da irin waɗannan hanyoyi na tattalin arziki ne suke sayen kayan ɗakin ’ya’yansu mata a hanlali kafin lokacin aure.

 

4.3       Maƙwabtakar Yaran Hausawa

 Aiwatar da al’amurran da suka shafi maƙwabtaka a al’ummar Hausawa bai tsaya ga magidanta ko matan aure ba. Su ma yara suna ba da tasu gudunmuwa ga wannan zamantakewar wadda daga nan suke kwaikwayo ko fara gogewa wajen aiwatar da ita kafin su girma. Haka kuma wannan zamantakewar da suke gudanarwa a dalilin maƙwabtaka ita ke taimakawa wajen ƙulla kyakkyawar zumunci da abokantaka mai ƙarfi tun suna yara har girmarsu. A wannan fasali za a yi bitar wasu al’adun da yara suke gudanarwa waɗanda suke da alaƙa da maƙwabtakar gargajiya ta Hausawa.

 

4.3.1 Wasa

Abu na farko da yake gudana a tsakanin yaran maƙwabta wanda wani reshe ne na ainihin maƙwabtakar ita ce wasa. A al’adar Hausawa, yara suna da lokuta na musamman da suke haɗuwa da juna suna wasa. Wato kamar da daddare bayan an ci abincin dare sukan haɗu a dandali inda yara mata za su yi ta wasannin gaɗa, su kuma yara maza su yi wasannin motsa jiki. Muhammad (2019: 42-43) ya kira wasan yara mata da gaɗa, su kuma na yara maza ya kira su da wasa kawai. Haka ma a wasu lokuta da yara ba su aikin komai da rana, yaran maƙwabta sukan riƙa haɗuwa a gidajen juna suna wasa. Ta hanyar irin wannan haɗuwa sukan yi zumunci a tsakaninsu. Misali idan ba a ga wani ya fito wasa ba, akan bi shi har gida a ga ko lafiya. Idan kuma wani ya ji rauni a wurin wasan, shi ma yaran za su taru su ɗauke shi ko su raka shi gida. Za su yi ta zuwa suna gaishe shi don su ɗebe masa kewa har lokacin da ya warke. Idan a lokacin wasannin tashe ne, to yaran maƙwabta ne suke haɗuwa rukuni-rukuni ta la’akari da jinsi da kuma shekaru suna aiwatar da waɗannan wasanni na al’ada. Haƙiƙi ana iya bugun ƙirji da cewa, babu yaran Hausawa ’yan gida ɗaya da suke haɗuwa su kaɗai yasu-yasu su aiwatar da waɗannan wasanni na tashe. A wuraren da suke da rafi a kusa da su, za a ga waɗannan yara ’ya’yan maƙwabta tare suke zuwa wanka a rafin. Ta nan ne ake koyon yadda ake iwo, kuma ta nan ne suke koyar da ƙananansu waɗanda ba lallai sai waɗanda suka fito a gida ɗaya ba. Waɗannan wasanni na yaran maƙwabta suna koyar da su darussan rayuwa da yawa musamman da yake wasu wasannin kamar kwaikwayo ne na rayuwar da suka ga manya na aiwatarwa a al’umma.

 

4.3.2    Rakiya

Rakiya na nufin tafiya rare da mutum zuwa wani wuri don taimaka masa ko taka wa baƙo (CNHN 2006). Rakiya a tsakanin yara wani lamari ne da ke ƙara fito da abin da maƙwabtakar Hausawa ta ƙunsa. A duk lokacin da aka aiki yaro zuwa wani waje, za a ga ya nemi rakiyar yaran maƙwabtansa. Idan yaran da aka aika ƙanana ne to galibi iyayensu za su nemi ’ya’yan maƙwabta waɗanda suka fi su wayau su raka su. Wannan rakiya tana taka muhimmiyar rawa wajen ƙara danƙon zumunci a tsakaninsu. Kusan kowane ɗan Bahaushe yana da aboki ɗan maƙwabta wanda suke yi wa juna rakiya idan an aike su. Wani abin sha’awa a kan wannan rakiyar shi ne takan taimaka wa wasu iyaye wajen yin saurin kai saƙo.

 

4.3.3    Cin Abinci Tare

A yawancin lokutan da yara suke wasa a gidajen maƙwabta, idan lokacin cin abinci ya yi iyaye sukan haɗa su su ci abinci tare. Suna ƙarewa kuma za su nufi gidan wani maƙwabcin yaron su ci abinci. Haka za a yi har sai an tafi gidan kowa. A duk gidan da suka tafi, za a ga iyayen su karɓe su da fara’a. Wato babu ƙyama ko tunanin koran sauran yara su tafi gida. Abin alfahari ne ga yaro ya tafi gidansu da abokinsa maƙwabci su ci abinci tare. A wurin irin wannan cin abincin idan iyaye ba su ga wasu ’ya’yan maƙwabtansu da suka saba gani ba, sukan tambaya. Wannan ya zama kwatankwacin haɗuwa da magidanta suke yi suna cin abinci tare.

 

4.3.4    Kaciya

Kaciya ko kuidu tana nufin “yanke loɓar azzakarin yaro” (Ƙamusun Hausa 2006: 222). A al’adar Hausawa ta gargajiya, idan lokacin yi wa yara kaciya ya yi, akan sami wani gida a unguwa inda za a tara yara a kira wanzami ya yi musu kaciyar. Ibrahim (1982) da Sallau (2000) da Abdullahi (2008) duk sun tabbatar da aukuwar wanan al’adar a al’ummar Hausawa.  Bayan ’yan’uwa a cikin gida ɗaya, akan haɗa har da yaran maƙwabta wurin yin wannan kaciyar. Wannan zama da yaran maƙwabta za su yi na jinyar warkewar kaciya tana ƙara samar da zumunci da fahimtar juna a tsakaninsu. Haka kuma yakan zama musu abin tarihi musamman idan ana kirdadon shekaru ko idan ana so a san mutanen da suke warin juna. Akan ce tare da wane aka yi muna kaciya. A wancan lokacin da ake gudanar da wannan al’ada sosai, ba yadda za a yi Bahaushe ya yi wa ɗansa shi kaɗai kaciya a cikin gida. Dole sai an haɗa su da ’ya’yan dangi da na maƙwabta. 

 

4.3.5        Tanyon Aikace-aikacen

Iyaye sukan sa ’ya’yansu wasu aikace-aikace na gida ko gona ko kuma a wuraren aiwatar da sana’o’in gargajiya. Idan akwai yaran maƙwabta a kusa, za a ga tare suke aiwatar da ire-iren waɗannan ayyuka. Wato yaran maƙwabta su riƙa taya ’yan’uwansu ayyukan. A irin wannan yanayi, ba a iya bambanta ɗan gida da ɗan maƙwabci saboda irin himmar da ’ya’yan maƙwabtan suke yi a wajen aiwatar da irin waɗannan ayyukan. Daga irin tanyon ayyukan ne za a ga ’ya’yan maƙwabta sun rungumi sana’o’in gidajen maƙwabtansu.  

 

4.3.6    Yawon Salla

Yawon sallah yawo ne da yara suke yi galibi zuwa gidajen ‘yan’uwa a lokacin bukukuwan salla, suna gayar da mutane da niyyar karɓar goron salla. Yaran Hausawa a kullum ba su da abokan yawon salla kamar ’ya’yan maƙwabta. Sa’o’i sukan haɗu da juna tare da amincewar iyaye su tafi yawon salla gidajen ’yan’uwa. A ƙarshe idan aka dawo gida sai a raba abin da aka samo. Wannan al’ada tana taimakawa wajen ƙara haɗa danƙon zumuncin da ke tsakanin yara maƙwabta da ma iyayensu.

 

5.0       Cin Amanar Maƙwabtaka a Tunanin Bahaushe

Duk yadda zamantakewar maƙwabtaka ta yi wa Bahaushe daɗi, da zarar an sami matsala to wannan zama yakan yi muni. Irin wannan shi ke jawo fitintinu da rikice-rikice  iri-iri a tsakani maƙwabta. Cin amanar maƙwabtaka ita ke gurgunta ruhinta a tsakani Hausawa. Cin amanar maƙwabtaka yakan danganta da abin da ya haɗa maƙwabci da maƙwabci. Haka kuma yana iya bambanta ta la’akari da tsananin laifi ko rashin haƙuri ko kuma rashin sanin ya kamata. A wannan fasali za a jero wasu muhimman lamurra waɗanda idan sun auku, Bahaushe yakan ɗauke su cin amana na maƙwabtaka. Wasu idan aka sasanta, aka warware matsalar, dangantakar takan iya dawowa yadda take. Wani kuma alaƙar da zumuncin ba zai taɓa dawowa ba. Hasali ma dai yakan iya sa wani maƙwabcin ya bar muhallin da yake har abada. Ga wasu daga ciki.

1.         Maƙwabci ya ɗauki ɗabi’ar neman matar ko ’ya’yan maƙwabci. Da zarar wannan ya tabbata, to akan ce wannan mutum ya ci amanar maƙwabtaka.

 

2.         Maƙwabci ya aure matar maƙwabcinsa bayan sun rabu. Duk da yake a addinin akasarin Hausawa (Musulunci) ba haramun ba ne, amma Bahaushe ya ɗauke shi cin amanar maƙwabtaka idan haka ya kasance. Wanda aka aure matarsa ba zai saki jiki ya yi hulɗa da wanda ya aure ta ba. Haka kuma za a yi ta zargin wataƙila sun daɗe tare. 

3.         Mutum ya yi amfani da wata dama ta kusanci ya riƙa leƙen gidan maƙwabcinsa. An fi samun irin haka a maƙwabtakar da ke da gidajen bene a kusa. Idan har aka tabbatar da wannan, to Bahaushe na kallon wanda ya leƙi gidan maƙwabcinsa a matsayin maci amana na maƙwabtaka.

4.         Yin makwararin ruwa a gidan maƙwabci. Ga maƙwabtan da suka haɗa iyakar gida, idan ya kasance makwararin ruwan ƙazanta na wani gidan yana a gidan ɗaya maƙwabcin ne, to akan bayyana shi da cin amanar maƙwabtaka. Irin haka ya fi faruwa idan ana maƙwabtaka da mai hali. Arzikinsa zai ba shi damar ɗaga gidansa ta yadda duk ruwan da ke fitowa daga maƙwararin ruwa ya kwanta a gidan da suke maƙwabtaka.

 

5.         Ƙuntata wa maƙwabci da wata hayaniya a lokacin da bai dace ba kamar kaɗe-kaɗe ko ƙarar wani injin ko dai wani abu da zai hana maƙwabci da iyalinsa natsuwa musamman da dare.

 

6.         Saye gidan maƙwabci bisa lalurar rashi. A maimakon maƙwabci ya taimaka wa maƙwabcinsa idan ya shiga halin rashi, sai ya yi amfani da damar halin da maƙwabci ya shiga na matsin rayuwa ya saye gidansa ya haɗa da nasa. Bahaushe yana ɗaukar wannan a matsayin cin amanar maƙwabtaka.

 

7.         Hana yara wasa da ’ya’yan maƙwabci. Shi yaro ba ya da shamaki a kan abokan wasa. A duk lokacin da ya ga yaro ɗan’uwansa to ya ga abokin wasa. To idan ya kasance wasu iyayen suna hana ’ya’yansu wasa da ’ya’yan maƙwabta to ana ɗaukarsa cin amanar maƙwabtaka. Ana samun haka ne a dalilin ƙyama ko son nuna fifiko ko wani matsayi na rayuwa.

 

  1. Mutum ya yi kiwon wata dabba mai iya cuta wa maƙwabci, cin amanar maƙwabtaka ne a idon Bahaushe. Hausawa sun ɗabi’antu da kiwon ƙananan dabbobi da tsuntsaye a muhallinsu. Misalin ire-iren waɗannan dabbobi su ne awaki da tumaki da shanu da kyanwa. Haka kuma ana samun masu ajiye jakkai da dawaki saboda wasu dalilai. Su kuma tsuntsaye sun haɗa da kaji da talotalo da zabbi da sauransu. To idan ya kasance maƙwabci ya tsiri kiwon wasu dabbobi masu hatsari da tsoratar da mutane kamar birai ko kura ko wasu miyagun karnuka ko kada, to Hausawa sukan ɗauke shi cin amanar maƙwabtaka. A zahiri, ko dabbobin suna ɗaure ko a killace, maƙwabci ba ya da kwanciyar hankali na mu’amala da wannan maƙwabcin saboda tsoron illar waɗannan dabbobin.

 

9.         Babban cin amanar maƙwabtaka ne haɗa baki da miyagu kamar ɓarayi ko ’yan fashi ko wasu matsafa/masihirta a cuta wa maƙwabci. A duk lokacin da maƙwabci ya ba da damar amfani da gidansa ko gonarsa don a sami sauƙin kaiwa ga maƙwabcinsa a cuta masa ta kowace hanya, to Bahaushe yana ɗaukar hakan a matsayin cin amanar maƙwabtaka.

 

10.       Yin sanadiyyar tashin maƙwabci daga gida don ƙyashi ko baƙin rai ko wata husuma  shi ma cin amanar maƙwabtaka ne a tunanin Bahaushe.

 

6.0       Kammalawa

A wannan nazari, an yi ƙoƙarin duban abin da maƙwabtakar Bahaushe ta ƙunsa da kuma abin da ya ɗauka maƙwabtaka. Nazarin ya gano Hausawa suna ɗaukar mutanen da suke da kusanci da juna ta fuskar muhallin zama ko gona ko wurin wani kasuwanci a matsayin maƙwabta. A ɗaya ɓangaren kuma, maƙalar ta tafi a kan tunanin Hausawa na ɗaukar maƙwabtaka a matsayin kyautatawar da ke tsakanin maƙwabta da kuma kyakkyawar mu’amala da ake samu a tsakanin jinsi ko rukuni mutane daban-dabam wanda ya shafi taimakon juna da ƙoƙarin samar da yanayi na mu’amala mai kyau a tsakaninsu. Maƙalar ta bibiyi abubuwan da maƙwabta Hausawa suke gudanarwa a tsakaninsu domin tabbatar da wannan tunani. Duk da yake maƙalar ta fayyaye ƙunshiyar maƙwabtakar maza da na mata da na yara, akwai fahimtar cewa, duk sun ɗauki maƙwabtaka a matsayin wani ƙoƙari da makusantar muhalli suke yi na daɗaɗa wa juna da faranta wa juna rai da daraja mutane a kowane lokaci. Daga ƙarshe, maƙalar ta yi ƙoƙarin fito da wasu halaye ko ɗabi’u da idan maƙwabcin Bahaushe ya aiwatar da su, to akan ɗauka ya ci amanar wannan tunani na maƙwabtaka. Hakan ya tabbatar da Hausawa suna da tunanin cewa, idan aka sami maƙwabtan da ba su da fahimta ta maƙwabtakar gargajiya ta Bahaushe, to zama kawai ake yi na lalura ba maƙwabtaka ba. Ba abin mamaki ba ne tunani a kan maƙwabtaka da ma yanayin maƙwabtakar Hausawa su bambanta da na wasu ƙabilu. Sai dai shi Bahaushe ya fi ba kyautatawa da taimakon juna muhimmanci kuma ya ɗauke su a matsayin sinadaran samar da zaman lafiya da kyakkyawar rayuwa. Wannan ne yakan sa a ga wasu Hausawa suna fifita maƙwabtansu fiye da ‘yan’uwansu na jini. 

 

Manazarta

 

Abdullahi, I. S. S. (2008). ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Sakkwato: Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman Hausawa (Babu Ma]aba’a).

Alti, K. (2012). ”Wasu Dabarun Gargajiya na Kawar da Talauci a Birnin Katsina” Sakkwato: Kundin Digiri na Biyu (M. A. Hausa) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press. 

Funtua, A. I. da Gusau, S. M. et al. (2010) Al’adu da Dabi’iun Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printing and Media Concepts.

 

Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Kano: Jami’ar Bayero.

Mairukubta, H. (1999). ”Jego da Reno a Ƙasar Hausa: Tsokaci Kan Hausawa Kabi.” Sakkwato: Kundin Digiri na Biyu (M. A. Hausa) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Muhammad, M. S. (2019) Ƙuruciya a Al’adar Bahaushe. Kaduna: Isma Printing and Publishing.

Sallau, B. A. S. (2000) “Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a {asar Hausa.” Kano: Kundin digiri na biyu (M.A. Hausa) Jami’ar Bayero,

Yahaya, I. Y.  da wasu (1992) Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare Littafi na Uku. Ibadan: University   Press PLC.

Post a Comment

0 Comments