Wannan takarda tana ɗuke da nazarin Waƙar “Ilimin Zamani” Ta Mu’azu Haɗeja. An gina nazarin kan Mazahabar Sigar Adabi.
Tarken
Waƙar
“Ilimin Zamani” Ta
Mu’azu Haɗeja: Duba Zuwa Ga Mazahabar Sigar Adabi
Hafsat
Alhaji Yaya
Gabatarwa
Wannan takarda da za a gabatar za ta
yi bayani ne kan nazarinw aƙar
“Ilimin Zamani” na Mu’azu Haɗeja ta hanyar ɗora
aikin zuwa mazahabar sigar adabi. Amma kafin nan za a kawo ɗan
taƙaitaccen bayani dangane da wannan
mazahaba ta sigar Adabi.
An ƙirƙiro wannan mazahaba ne a Faransa a wajen shekarar 1960. Amma
ta tsiru ne a dalilin wani aiki da Ferdinand De Saussure (1857-1913) ya yi a
Faransa a kan nazarin harshe tun a farkon ƙarni
na 20, mai suna Lahangue La Parde (1914). A taƙaice mazahabar sigar adabi ta samo asali ne a dalilin yadda
wasu matarka suka lura da yadda aka yi amfani da wasu ra’ayoyi na nazarin
kimiyyar harshe wajen gano wasu sassa na ɓoye
masu bayar da ma’ana a cikin adabi da al’adun al’umma.
Mazahabar sigar adabi ta fara ne daga
wasu ra’ayoyin nazarin harshe da kimiyyar harsuna, kuma tana lura da wasu sassa
masu ɓoyayyar ma’ana a cikin al’adu da adabin al’umma. Wannan sassa
an danganta su don su samar da sharhi game da aikin adabi da tsarin da aka bi
aka fito da shi. Wannan mazahabar tana da wasu manufofi da aka ɗora
ta a kai, wasu daga cikin manufofin wannan mazahaba sun haɗa
da:
Ø Tana
sifantawa da feɗe tsarin da aka rubuta adabi kansa.
Ø Tana
kula da nazarin kimiyyar harshen adabi da aka ɗora
kan zubi da tsari, ba kan ƙumshiya
ba.
Ø Tana
duba yadda ake feɗe tsarin abu ta la’akari da wasu alamu.
Ø Tana
fito da tsarin ɓoye ko tubalan gina aikin adabi (ƙwarangwal) ko wasu dokoki na aikin adabi.
Ø Tana
kula da yadda ake shirya matani don a samar da jerin ma’anoni a cikinsa. d.s.
Nazarin
Waƙar
Zuwa Ga Mazahabar Sigar Adabi
Wannan mazahaba ta sigar adabi tana
magana ne kan sifantawa da feɗe tsarin da aka rubuta
adabi kansa. Don haka a nan mene ne adabin mu? Adabi shi ne waƙar “Ilimin Zamani na Mu’azu Haɗeja”.
A wannan wuri za mu feɗe tsarin da aka rubuta wannan waƙar in za mu ɗora aikin kan maganan
wannan mazahaba (sigar adabi). Idan ana magana kan tsarin adabi, wato magana
ake “kan zubi da tsari”. Zubi da tsari ta fuskar adabi ya shafi yadda aka
shirya adabin ne gaba ɗaya, za a duba carbin tunanin marubuci. Wato yana jeranta
tunaninsa ne ko akasin haka.
Zubi da tsarin waƙa a wannan wuri za a dubi tsarin waƙar ne gaba ɗaya dangane da yadda aka
shiryata. Wato za a duba carbin tunanin mawaƙin,
yana jeranta tunaninsa ko yana kwan-gaba-kwan-baya. Abubuwan da ake dubawa a ƙarƙashin tsarin waƙa rubutacciya sun haɗa
da:
a)
Shirin baitocin waƙar
b)
Yawan ɗangogin waƙar
c)
Yawan baitocin waƙar
d)
Dangantakar ɗango da ɗangon
waƙar (gangara)
e)
Dangantakar baiti da baiti (saɓi-zarce)
f)
Amsa-amon waƙar
g)
Mabuɗin waƙar
h)
Marufin waƙar
i)
Ƙulla batutuwa da
kuma
j)
Karin waƙar
Idan
muka duba waɗannan abubuwa da suka gabata a sama za mu ga cewa su ne irin
abubuwan da ake fitowa da su wajen feɗe
tsarin da aka rubuta waƙa. Mazahabar sigar
adabi tana siffanta waɗannan batutuwa a yayin feɗe
tsarin adabi. Don haka za mu ɗauki ɗaya
bayan ɗaya mu rinƙa
yin nazarin wannan waƙa ta Mu’azu Haɗeja
mai taken “Ilimin Zamani”.
A)
SHIRIN BAITOCIN WAƘA/TSARIN
WAƘA
Kamar yadda aka sani shirin baitocin
kowace waƙa ana so lalle ne
ya kasance yana ɗaya daga cikin dangogin waƙa
guda bakwai da muke da su (in dai rubutacciya ce). Dangogin waƙa su ne kamar haka:
Ø Gwauruwa
Ø ‘Yar
tagwai
Ø ‘Yar
uku
Ø ‘Yar
huɗu
Ø ‘Yar
biyar
Ø Tahamisi
Ø Tarbi’i
Waɗannan
su ne dangogin waƙa da ake so duk
wata rubutacciyar waƙa ba za ta amsa
sunanta ba, sai shirinta ko tsarinta ya kasance ɗaya
daga cikin waɗannan.
Don haka idan muka dubi wannan waƙa tamu da muke yin tarkenta kan hanyar tsarin mazahabar sigar
adabi, waƙar “Ilimin Zamani”
na Mu’azu Haɗeja za mu ga cewa lalle wannan mawaƙi ya shirya waƙar
ne a tsarin ko shirin “Gwauruwa”.
Waƙar
da za a ƙira gwauruwa waƙa ce da aka shiryata ko tsarata a tsarin waƙa mai ɗango ɗai-ɗai da babbar ƙafiya.
Saboda haka wannan waƙar “Ilimin Zamani”
tun daga farkonta har ƙarshe a wannan
tsarin aka shiryata.
B)
YAWAN ƊANGON
WAƘA
A wannan wuri ana buƙatar mai nazarin waƙa
ya tantance yawan ɗago da waƙar
ke ɗauke da su. Wato manazarci zai duba shirin kowace baiti shin
yana ɗauke da ɗango ɗai-ɗai
ne ko kuma wani ya kan fi wani?
Don haka za a iya cewa wannan waƙar mai suna “Ilimin Zamani” tana ɗauke
da ɗango ɗai-ɗai ne a kowanne baiti. Ba baitin da aka samu guda ɗaya
da ya ɗara sauran baitocin ko da guda ɗaya.
Don haka zan iya cewa wannan waƙar
da nake nazarinta tana ɗauke da ɗangwaye har guda saba’in
da bakwai (77).
C)
YAWAN BAITOCIN WAƘAR
A wannan wuri ma ana buƙatar mai nazari ya tantance yawan baitocin waƙar.
A wannan waƙa da nake nazari a kanta tana ɗauke
da baitoci har guda saba’in da bakwai (77). Ke nan yawan ɗangwaye
da baitocin sun kasance dai-dai. Me ya sa? Saboda waƙar ta kasance shirinta/tsarinta na gwauruwa ce. Ma’ana ana
samun ɗango ɗai-ɗai da baiti ɗai-ɗai,
ke nan yawan su zai zama ɗaya.
D)
DANGANTAKAR ƊANGO
DA ƊANGO/GANGARA
Wannan wurin ana magana ne kan wurin
da marubuci ko mawaƙi zai fara wata
magana a wani ɗango amma ba zai ƙarisa
ba ko ma’anarta ba za ta cika ba sai an shiga wani ɗangon.
An samu gangara a wannan waƙar
kamar a baiti na:
·
Baiti na 2
Jama’armu
ku jawo hankulanku,
Ku lura da halin zamani.
Mawaƙin ya fara magana a ɗangon
farko amma ma’anarta ba ta cika ba sai a na biyu. Gangara ke nan ko kuma mu ce
an samu dangantakar ɗango da ɗango.
·
Haka a baiti na 3. Inda mawaƙin ya ce;
Iko,
mulki, ƙarfi duka,
Na ga wanda ya ƙaddari zamani.
·
A baiti na 7 ma an samu gangara in da:
Da
tsiya da talauci duk suna,
Gun da jahilci ya yi sansani.
·
A baiti na 13
An
faɗa an sake faɗa muku
Babu Hasiya ga biɗar
Sani
·
A baiti na 15
Ga
dalilaina da ya sa na ce,
Maka mun zama bayan zamani.
·
A baiti na 25
Ɗaukaka da mutunci duk suna,
Gun sana’ar ilmin zamani.
·
A baiti na 37
“Faman
‘ya’amal misƙala zar
Rati” can a izazul kun sani.
·
A baiti na 39
Kullu
shai’in la yahafa alai-
hi, Alimun ko da ƙanƙani.
·
A baiti na 51
Sai
mai General certificate,
Sai mai Diploma mun sani
·
A baiti na 55
Cin
hanci, karɓar toshiya,
Rashawa sun ƙaura ga zamani.
·
A baiti na 64
Jama’ar
kudu sun ce sun fi ƙar-
finsa kul ya tsaya can ya boni.
·
A baiti na 65
Sai
shi koma Arewa wurin muta-
nen, da ba su da kishin zamani.
·
A baiti na 67
Sai
am mana tilas za mu ai-
kata, kome shauni zamani.
·
A baiti na 70
Zamani
ya ce a gaya muku,
Ciniki ba sauran lamuni.
·
A baiti na 74
Duk
biyun nan sai mu riƙe su ko-
wa muhalli nai zai magani.
·
A baiti na 76
Shi
Mu’azu Haɗejiya shi ya wal-
lafi, wannan “waƙar zamani”.
Idan muka duba baitoci na 2, 3, 7, 13,
15, 25, 37, 39. 51, 55, 64, 65, 67, 70, 74, 76 duk an samu dangantakar ɗango
da ɗango (gangara)> za a ga mawaƙin ya ɗauke magana amma ma’anar ba ta cika sai an shiga ɗango
na gaba.
A baitoci na 37, 39, 64, 65, 67, 74,
76. Za a ga cewar kalmomi ne ma yake fara faɗarsu
amma ba zai ƙarisa ba sai ya
shiga wani ɗangon. Ma’ana yanke su yake yi.
E)
DANGANTAKAR BAITI DA BAITI (SAƁI-ZARCE)
A wannan wuri kuwa mawaƙi kan fara wata magana cikin wani baiti, amma ba zai ƙarasa ba ko ma’anar ta ba za ta fito fili ba sai an shiga
wani baiti ko baitocin. Tabbas a wannan waƙar
mai suna “Ilimin zamani” an samu irin waɗannan
dangantaka a wurare kamar haka:
A baiti na 9 – 11 in da mawaƙin ke cewa:
-
Masu son lardinmu ya ɗaukaka,
Bisa kan juyawar zamani.
-
Kar su fara faɗar
dan-na-sani,
Da mun yi karatun zamani.
-
Allah shi zai gyara mana,
Ya fitar mu da kunyar
zamani.
A waɗannan
baitoci na 9-11 mawaƙin ya fara magana
a kan masu son lardinmu ya ɗaukaka bai ƙarisa ba ya ci gaba a baiti na gaba yana cewa kar faɗi
dan-na-sani, nan ma bai kammala ba har zuwa baiti na 11 inda ya ce “Allah shi
zai gyara mana”. ke nan a wannan baitoci an samu dangantakar baiti da baiti a
ciki.
Haka an cigaba da samun saɓi-zarce
a baiti na 15-21
-
Ga dalilaina da ya sa na ce,
Maka mun zama baya a
zamani.
-
Tun Nasara gaban ba su zo su ba,
Muka san hanyar neman
sani.
-
Sun tarar mu da halin ci gaba,
Ciniki da sarautu sun
gani.
-
Wasu kan akasi aka tad da su,
Yanzu su ne manyan zamani.
-
Sun yi ƙwazo sun yi ɗawainiya,
Bisa takidin neman sani.
-
Matuƙar ba mu tashi a
kansu ba,
Za su hau mu a wannan
zamani.
A wannan baitocin ma mawaƙi ya faro maganganu a kan nasara amma bai ƙarisa ba sai a wajen baiti na 21.
A baiti na 27-34 an samu saɓi
zarce kamar haka:
-
Ba su yin sana’a, matuƙabbarai,
Sai yawan yawo da
wuni-wuni.
-
Sai ka gan su a kowace rariya,
Sana’asu yini zagin wani.
-
Sai su je yawo sabon Gari,
Ko ka gan su a kantin
kamfani.
-
Sai yawan ihu, sai dariya,
Ba tunanin halin zamani.
-
Hanyar addini sun saki
Ba ruwansu da wannan tun
tuni.
-
Ilmin addinin ba su yi,
Ba ruwansu da ilimin
zamani.
-
Sun ɓatan ɓakatantan ba su nan,
Ba su can don wautar
zamani.
A waɗannan
baitocin da suka gabata za mu ga mawaƙin
ya fara wasu magangnu a kan jalilai marassa neman ilimi tun daga baiti na
27-34. Don haka a nan ma an samu dangantakar baiti da baiti (saɓi
zarce).
Haka a baiti na 51-53
-
Sai mai General certificate,
Sai mai Diploma mun sani.
-
Sai masu sanin ilimin Koleji,
Har a Ingila sun ƙaro sani.
-
Taimakonku da ku da sarakuna,
Shi fi ƙarfi ga ilmin zamani.
A nan ma an samu dangantakar baiti da
baiti.
Haka
a baiti na 61-63
-
Jama’a da yawa ba su farga ba,
Jalilai ya kafa sansani.
-
Ya yi Ɗanrimi yai
Shamaki,
Ya yi Kakaki yai Figini.
-
Ya yi dagatai ya naɗa
hakimai,
Ya yi Razdan yai Di’o
tuni.
A nan ma an samu dangantakar baiti da
baiti inda mawaƙi ya ce “Jalilai
ya kafa sansani, ya yi ɗan-rimi da shamaki, ya yi kakaki, ya yi dagatai da hakimai
duk a baitoci na 61-63.
A taƙaice waɗannan su ne irin wuraren da wannan mawaƙi yake faro magana daga wannan baitin zuwa wannan kafin ya
kammala ko ma’ana ta cika. Dangantakarsu kenan.
F)
AMSA-AMO
Wannan kuma na nufin irin harafin da
ke ƙarewa a ƙarshen ɗango ko ƙarshen
baitocin waƙa. Amma shi
amsa-amo ya kasu zuwa gida biyu, akwai:
Ø Amsa
amo na ciki: Shi irin wannan nau’in amsa-amo shi ne irin harafin da yake ƙarewa a ƙarshen
ɗango. Ana iya kiransa da ƙaramar
ƙafiya.
Ø Amsa-amo
na waje: Wannan kuma shi ne irin amsa-amo ko harafin da yake ƙarewa a ƙarshen
baitocin waƙa. Shi ma ana iya
kiransa da suna babbar ƙafiya.
A
bisa tsari irin na rubutacciyar waƙa,
amsa-amon ciki yana canzawa aga wannan baitin zuwa wancan baitin. Amma amsa-amo
na waje a bisa ƙa’ida ba ya
canzawa a tsarin rubutacciyar waƙa.
Don haka a matsayina na mai nazarin
wannan waƙar (Ilimin Zamani)
da nake bin hanyar mazahabar sigar adabi zan fito da tsarin ko harufan da
wannan mawaƙi ya yi amfani da
su wajen tsara wannan waƙa (ilimin zamani).
Amsa-amo
na ciki
A wannan wuri za mu dubi harrufan da
suke ƙarewa a ƙarshen ɗango tun daga na farko har zuwa na ƙarshe kamar haka:
A ɗango
na ɗaya ko kuma bari mu yi abin a jadawalance domin samu sauƙin fahimta.
Ɗangon/baiti na waƙar |
Amsa-amo na cikin (harafin) |
A ɗangon baiti na 1 |
-ya |
A ɗangon baiti na 2 |
-ku |
A ɗangon baiti na 3 |
-ka |
A ɗangon baiti na 4 |
-sa |
A ɗangon baiti na 5 |
-mi |
A ɗangon baiti na 6 |
-ni |
A ɗangon baiti na 7 |
-na |
A ɗangon baiti na 8 |
-ka |
A ɗangon baiti na 9 |
-ka |
A ɗangon baiti na 10 |
-ni |
A ɗangon baiti na 11 |
-na |
A ɗangon baiti na 12 |
-ma |
A ɗangon baiti na 13 |
-ku |
A ɗangon baiti na 14 |
-ya |
A ɗangon baiti na 15 |
-ce |
A ɗangon baiti na 16 |
-ba |
A ɗangon baiti na 17 |
-ar |
A ɗangon baiti na 18 |
-ba |
A ɗangon baiti na 19 |
-su |
A ɗangon baiti na 20 |
-ya |
A ɗangon baiti na 21 |
-ba |
A ɗangon baiti na 22 |
-su |
A ɗangon baiti na 23 |
-ke |
A ɗangon baiti na 24 |
-ne |
A ɗangon baiti na 25 |
-na |
A ɗangon baiti na 26 |
-ya |
A ɗangon baiti na 27 |
-ai |
A ɗangon baiti na 28 |
-ya |
A ɗangon baiti na 29 |
-ri |
A ɗangon baiti na 30 |
-ya |
A ɗangon baiti na 31 |
-ya |
A ɗangon baiti na 32 |
-ki |
A ɗangon baiti na 33 |
-yi |
A ɗangon baiti na 34 |
-an |
A ɗangon baiti na 35 |
-yi |
A ɗangon baiti na 36 |
-ni |
A ɗangon baiti na 37 |
-ar |
A ɗangon baiti na 38 |
-in |
A ɗangon baiti na 39 |
-ai |
A ɗangon baiti na 40 |
-on |
A ɗangon baiti na 41 |
-ji |
A ɗangon baiti na 42 |
-ni |
A ɗangon baiti na 43 |
-ta |
A ɗangon baiti na 44 |
-ta |
A ɗangon baiti na 45 |
-am |
A ɗangon baiti na 46 |
-ni |
A ɗangon baiti na 47 |
-ya |
A ɗangon baiti na 48 |
-ci |
A ɗangon baiti na 49 |
-ni |
A ɗangon baiti na 50 |
-ni |
A ɗangon baiti na 51 |
-te |
A ɗangon baiti na 52 |
-ej |
A ɗangon baiti na 53 |
-na |
A ɗangon baiti na 54 |
-au |
A ɗangon baiti na 55 |
-ya |
A ɗangon baiti na 56 |
-hu |
A ɗangon baiti na 57 |
-re |
A ɗangon baiti na 58 |
-wa |
A ɗangon baiti na 59 |
-ka |
A ɗangon baiti na 60 |
-na |
A ɗangon baiti na 61 |
-ba |
A ɗangon baiti na 62 |
-ki |
A ɗangon baiti na 63 |
-ai |
A ɗangon baiti na 64 |
-ar |
A ɗangon baiti na 65 |
-ta |
A ɗangon baiti na 66 |
-na |
A ɗangon baiti na 67 |
-ai |
A ɗangon baiti na 68 |
-ta |
A ɗangon baiti na 69 |
-ya |
A ɗangon baiti na 70 |
-ku |
A ɗangon baiti na 71 |
-ni |
A ɗangon baiti na 72 |
-ta |
A ɗangon baiti na 73 |
-ba |
A ɗangon baiti na 74 |
-ko |
A ɗangon baiti na 75 |
-na |
A ɗangon baiti na 76 |
-al |
A ɗangon baiti na 77 |
-ai |
Amsa-amo
na Waje
Dangane da wannan kuma kamar yadda
muka ambata a baya baya canzawa a tsarin rubutacciyar waƙa. A wannan waƙa
mai suna ilmin zamani na Mu’azu Haɗeja
tana ɗauka da amsa-amo na waje na harafin “ni” tun daga farko har
zuwa ƙarshenta.
G)
MABUƊIN
WAƘA
A wannan wuri manazarci, zai dubi irin
kalaman da marubuci ya fara waƙar
da su. Idan mawaƙi ya fara da
ambaton sunan ubangiji ko salati wa Annabi (S.A.W) ko yabon wani bawan Allah to
sai a ce waƙar tana da mabuɗi.
Idan ba a sami ko ɗaya daga cikin wannan ba to, sai a ce ya fara waƙar ce kai tsaya. (Ɗangambo:
2007).
Idan muka duba wannan waƙa tawa ta ilimin zamani zan iya cewa Mu’azu haɗeja
ya fara wannan waƙar ce kai tsaye ba
tare da mabuɗi ba. Za mu tabbatar da haka idan muka dubi kalmomin da
Mu’azu ya fara da su kamar haka:
-
Gishiri im babu kai ba miya,
Ilmi mai gyaran zamani.
-
Jama’armu ku kawo hankulanku,
Ku lura da halin zamani.
A nan babu wani ambaton sunan Allah ko
salati wa Annabi o nuna wani yabo d.s. Don haka ya fara waƙar ne kai tsaye.
H)
MARUFIN WAƘA
Wannan wurin kuma shi ne inda mawaƙi ya kawo ƙarshen
waƙarsa. Duk lokacin da aka ga marubuci
ya ƙare waƙarsa da ambaton sunansa, ko garinsu ko kuma shekarar da aka
rubuta waƙar ko ambaton
sunan ubangiji, to wannan waƙar
tana da marfi. (Ɗangambo: 2007).
Don haka a nan zan iya cewa wannan waƙar tana da marfi. Domin mawaƙi da ya zo baiti na 76 ya ambaci sunansa, sannan a baiti na ƙarshe kuma ya ambaci sunan Allah kamar haka:
A
baiti na 76
-
Shi Mu’azu Haɗejiya shi ya wal-
lafi, wannan “Waƙar Zamani”.
A
baiti na 77
-
Baiti saba’in da guda bakwai,
Tammat da nufin Babban
Gwani.
Don haka za mu iya cewa wannan waƙa ta Mu’azu Haɗeja
tana da marfi.
I)
ƘULLA
BATUTUWA
A wannan wuri kuma ana buƙatar mai nazari ya gano shin marubucin ya ƙulla batutuwa daki-daki ma’ana ya tsara carbin tunaninsa
daki-daki ko an samu kwan-gaba-kwan-baya.
Idan muka dubi wannan waƙa ta Mu’azu Haɗeja
za mu ga cewa lallai ya ƙulla batutuwa
daki-daki ba a samu tafiyar ƙura
ba. Domin ya tsara tunaninsa daki-daki. Ma’ana yadda ya fito da ma’anonin
baitocin sun tafi dai-dai. Ma’anar wannan baitin yana bin wancan.
Baya ga bayanin sifantawa da feɗe
tsarin da aka rubuta adabi da shi, manufa ta gaba a sigar adabi tana duba yadda
aka feɗe tsarin abu ta la’akari da wasu alamu. Kamar yadda muka faɗa
wannan mazahabar ta sigar adabi tana la’akari da yadda aka tsara wasu alamu na
cikin adabi.
Alamu a wannan wurin wata dabara ce da
mawaƙa ke bayyana wani
abu ta hanyar ba shi wata alama wadda za ta tsaya a maimakonsa.
A wannan waƙar ma mawaƙin
ya kawo wasu abubuwa a maimakon wasu kamar a baitoci kamar haak:
-
Gishirin
in babu kai ba miya,
Ilmi
mai gyaran zamani.
A
nan “Gishiri” a maimakon ilmi.
-
Yadda kaska ke tsotsan jiki,
Haka jahilci gun zamani.
A
nan “kaska” a maimakon jahilci.
-
Dubi yatsotsinka, ka tabbata,
Wani lalle ya zarce wani.
A
nan yatsa a maimakon mutum.
-
Ya yi Ɗanrimi yai
Shamaki,
Ya yi Kakai yai Figini.
-
Ya yi dagatai ya naɗa
hakimai,
Ya yi Razdan yai Di’o
tuni.
A nan Shamaki, Kakaki, Dagaci da
hakimi duk a maimakon jahilci.
A taƙaice wannan waƙar
an samu tsarin abubuwa ta la’akari da wasu alamu kamar yadda muka ambata a
sama.
Har yanzu wannan mazahaba ta sigar
adabi tana fito da tsarin ɓoye ko tubalan gina aikin
adabi (ƙwarangwal) ko wasu
dokoki na aikin adabi. A wannan wuri za mu fito da abubuwa ne guda biyu; Na
farko tsarin ɓoye da ke cikin wannan waƙar.
Na biyu kuma wasu dokoki da ke cikin wannan waƙar.
Idan muka koma baya, za a ga cewar
“Adabi” kansa wani madubi ne ko koto ne na duba yanayin rayuwar ɗan-adam
tun daga haihuwarsa zuwa mutuwarsa. Duba da wannan ma’ana za mu iya fito da
wasu ɓoyayyun abubuwa a cikin wannan waƙar da marubucin ya sako a matsayin abubuwan rayuwar yau da
kullum. Idan muka dubi wannan waƙar
za mu iya fito da wasu abubuwa na baɗini
da aka kawo a cikin waƙar. Wanda ba a iya
rabe su da harƙoƙin yau da kullum na zamantakewar al’umma. Waɗannan
ɓoyayyun abubuwan su ne kamar haka:
Ø Ilmi
Ø Iko
Ø Mulki
Ø Ƙarfi
Ø Kunya
Ø Shari’a
Ø Talauci
Ø Sutura
Ø Sana’a
Ø Kasuwanci
(ciniki)
Ø Zamba
Ø Cin
hanci
Ø Rashawa
d.s.
A
taƙaice waɗannan
abubuwa da muka zayyano ba za a iya rabe rayuwa al’umma da su. Kusan duk
halayya na zamantakewa waɗannan abubuwa su ne ake ta hulɗa
da su. Ke nan mawaƙin ya kawo ɓoyayyun
abubuwa a cikin waƙarsa.
A nan kuma za mu fito da wani ɓoyayyen
ilimi da ke ƙunshe da wannan waƙar. Mawaƙa
da marubuta Allah ya yi musu baiwa wanda kusan kashi tamanin (80%) cikin ɗari
ba su san waɗannan baiyoyin da allah ya yi musu ba. Idan muka duba yadda
mawaƙa suke kawo tsarin
gaɓoɓi na ɗangwaye da baitocin da ke cikin waƙarsu, za ka tarar cewa gaɓoɓin
suna tafiya daidai ko kusan daidai a waƙa.
Idan muka duba wannan waƙar za mu ga cewa tsarin gaɓoɓin
waƙar bai wuce 8-10. Misali:
-
Gi/shi/ri/ im/ ba/bu/ kai/ ba / mi/ya => 10
Il/mi/mai/gya/ran/za/ma/ni
=> 8
-
Sai/ya/wan/i/hu/sai/da/ri/ya => 9
Ba/tu/na/nin/halin/za/ma/ni
=> 9
Don haka za mu iya cewa ta fuskar gaɓoɓi
an tsara waƙar ne daga gaɓoɓi
guda 8-11 ba sa wuce haka. Wannan wani ɓoyayyen
tsari ne ko tubala da aka gina wannan waƙar
da shi.
ƘAFA/KARIN WAƘA
Tarin gaɓoɓi
da suke ba da takammen sauti da ake amfani da shi wajen gina baiti shi ne ake
ce wa ƙafa. Ga al’ada
kowane baiti ana gina shi da ƙafafu
biyu ko fiye.
Akwai
ƙafafu iri goma da ake amfani da su a
rubutacciyar waƙa. Ga jerin
sunayensu da alamunsu. (A.U. Tilde: 2016: ƊIƁ).
ƘAFAFUWA |
ALAMOMI |
1.
Fa-uu-lun |
Ɓ – – |
2.
Ma-faa-ii-lun |
Ɓ – – – |
3.
Ma-faa-a-la-tun |
Ɓ – Ɓ Ɓ – |
4.
Faa-i-laa-tun |
– Ɓ – – |
5.
Faa-i-lun |
– – Ɓ – |
6.
Mus-taf-i-lun |
– – Ɓ – |
7.
Faa-i-laa-tun |
– Ɓ – – |
8.
Mu-ta-fas-i-lun |
Ɓ Ɓ – Ɓ – |
9.
Maf-uu-laa-tu |
– – – Ɓ |
10. Mus-taf-i-lun |
– – Ɓ – |
Waɗannan
su ne ƙafafuwan Larabci
da muke da su waɗanda suka iya hawa tsarin rubutacciyar waƙa.
A wannan waƙa mai taken ilimin zamani na Mu’azu Haɗeja,
ƙafa ta bakwai ta ke hawa kan baitocin
kamar haka:
-
Gishiri im / babu kai ba / miya
Ilmi mai gya/ran zamani.
-
Iko, mulki / ƙarfi
duka
Na ga wanda / ya ƙaddari zamani.
Don haka wannan wani ɓoyayyen
ilimi ne da ke cikin wannan waƙar.
Dangane da karin waƙar kuma za a iya cewa “RAMAL”. Domin ƙafa ta bakwai ta ke maimaita kanta sai kuma wasu ‘yan illoli
da zahabbai da ba a rasa ba.
Sannan wannan mazahabar tana duba wasu
dokoki na musamman (codes) masu samar da aukuwar ma’ana a cikin adabi. Don haka
wannan rubutacciyar waƙar na ilimin
zamani a matsayinta na wani ɓangare na adabi tana da
wasu dokoki ko sharruɗa da ake hukunta ingancin rubutacciyar waƙa. Sharuɗa ko dokokin rubuta waƙa su ne kamar haka:
1)
Waƙa ta kasance tana
da mabuɗi da marfi.
2)
Lallai ne a samu waƙa
tana da ma’auni, ya zama yana ɗaya daga cikin ma’aunan
waƙoƙin
Larabci. Misali:
Ɗawil, Madid, Razaj, Ramal, d.s.
3)
Waƙa ta kasance tana
da amsa-amo.
4)
Shirin baitocin waƙar
ya kasance ɗaya daga cikin dangogin waƙa
guda bakwai.
5)
Ambaton jigon waƙar
tun a farko.
6)
Warwarar jigo
7)
Ambaton sunan mawaƙi
8)
Salon mawaƙi
9)
Gwanintar harshe.
Waɗannan
su ne abubuwa guda tara (9) waɗanda ake sa ran a ga sun
tabbata kafin a hukunta cewa rubutacciyar waƙa
ce. Don haka wannan mazahaba ta sigar adabi tana magana a kan kawo wasu dokoki
(codes) wajen tsara adabi.
Madogara
Tuntuɓi masu gudanarwa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.