Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Waƙar Hajiya Sa’adatu (Barmani Coge) Ta “Sai Ku Kama Sana’a Mata”

Tarken/Nazarin Waƙar Hajiya Sa’adatu (Barmani Coge). Waƙa Mai Taken “Sai Ku Kama Sana’a Mata” Duba Zuwa Ga Mazahabar Tarken Gargajiya.

Barmani Choge


Nazarin Waƙar Hajiya Sa’adatu (Barmani Coge) Ta “Sai Ku Kama Sana’a Mata”

Hafsat Muhammad

 

Gabatarwa

          Kafin na kai ga yin wannan tarken waƙar Hajiya Sa’adatu (Barmani Coge) wanda zan yi la’akari da mazahabar “Tarken Gargajiya” yana da matuƙar muhimmanci na yi sharhi ko cikakkiyar bayani dangane da mazahabar da zan ɗora aikin a kai. Domin hakan ne zai haskaka wa masu saurare sanin madosar wannan aikin ko nazari.

          Mazahabar Tarken Gargajiya: An ƙirƙiro wannan mazahaba ne tun lokacin da aka fara nazari da tarken adabin al’ummomin duniya, har ya zuwa farkon ƙarni na 19 da mazahabar sababbin matarka ta kunno kai. Wannan mazahabar (Tarken Gargajiya) an gina ta a kan wasu shiryayyun manufofi, wanda duk mai sha’awar nazari ko tarke a wannan mazahabar dole ya yi la’akari da waɗannan manufofi. Manufofin su ne kamar haka:

i)                   Duba aikin wata fasaha (adabi) a gargajiyance.

ii)                Neman bayanin manazarci da tarihinsa da kuma zamaninsa.

iii)             Kawo misali kaɗan amma babu cikakkiyar fiɗa ta aikin adabi ko fito da ainihin manufofinsa.

iv)              Bayyana ra’ayi game da aikin adabi, wato game da kyansa, ta amfani da zantukan yabo ko kushe da malamai ke darajanta shi kamar da kyau, dama-dama, ko ba kyau d.s. (Ɗangambo, 2007:7).

v)                La’akari da salo da nahawu da azanci da jigo da kyakkyawar manufa.

vi)              Ba da wasu shawarwain yadda za a bunƙasa aikin, idan akwai wata naƙasa da aka gano daga gare shi tare da la’akari da yadda aikin adabin ke zama kamar wani madubi na haskaka yanayain muhallin ɗan-adam.

vii)           Mazahabar tarken gargajiya taan ɗaukar ra’ayin mutuntakar ɗan adam, sannan tana duba fusahar adabi da muhimman kayan cikin adabi. Kuma wannan yana wakiltar saƙon da ke da nasaba da rayuwar yau da kullum ta al’umma.

viii)         Tana fito da muhimmancin aikin kansa ko ƙarfin harshen da aka rubuta aikin da shi.

A taƙaice waɗannan su ne irin manufofin da wannan mazahaba ta tarken gargajiya take magana a kai. Sannan masana sun nuna babu wata takamaimiyar hanya ko makarantar da za a ce tana kula da tarken gargajiya, amma ana kiran tarken gargajiya da tarken da ke kula da kayan cikin ko ƙunshiyar aikin adabi. Don haka, tarken gargajiya na ganin aikin fusaha kamar wani madubi mai haskaka yanayin rayuwa da muhallin da ake gudanar da ita. Kuma babu wata fitacciyar hanya ko rattaɓaɓɓiya da aka tsara kuma ake amfani da ita. Sai dai hanya ce kara-zube don bayyana ra’ayi game da ingancin adabi. (Ɗangambo, 2007:9 & Gusau, 1992:12).

          Baya ga haka, akwai wasu matakan da ake son yin amfani da su wajen tarken adabi a kan tarken gargajiya daga shi salon aiwatarwa kamar haak:

i.                   Shin harshen fayyatacce ne?

ii.                 Shin harshen ya yi daidai da yadda mai magana da masu sauraro da yanayin bikin da ake ciki?

iii.              Shin harshen mai sauƙi ne?

iv.               Shin miƙaƙƙe ne (babu harshen damo)?

v.                 Shin harshen mai zaburarwa da motsa rai ne?

Bisa ga wannan jawabi da ya gabata ya isa ya mana jagora wajen yin tarken wannan waƙa ya zuwa mazahabar tarken gargajiya.

Nazari/Tarken Waƙar “A Kama Sana’a Mata” Ta Sa’adatu Barmani Coge Duba Ga Mazahabar Tarken Gargajiya

          Kamar yadda muka ambata a baya wannan hanyar tarken gargajiya babu wata fitacciyar hanya ko rattaɓaɓɓiya da aka tsara kuma ake amfani da ita. Saboda zan fara duba wasu manufofin wannan mazahabar, sai muna danganta shi da nazarin mu. Ɗaga daga cikin manufar wannan mazahabar ta nuna cewa:

1.     Bayyana Ra’ayi Game Da Aiki Adabi; Wato game da kyansa ko muninsa, ta hanyar amfani da zantukan yabo ko kushewa da malami ke darajanta su

Saboda haka, tarken gargajiya kamar yadda aka sani babu wata hanya fitacciya wadda aka tsara kuma aka amince da ita. Kawai hanya ce wadda mutane ke amfani da ita kara zube don su bayyana ra’ayinsu game da ingancin waƙar. A taƙaice za mu iya cewa zantuttuka ne na yabo ko kushewa da ke amfani da su. Irin waɗannan zantuttuka su ne kamar haka:


 

 

-         Ta yi armashi

-         Ta ƙayatar

-         Ta burge                    Kyau mai daraja ta I

-         Ta waƙu

 

-         Ba laifi

-         Ta gamsar                  Kyau mai daraja ta II

-         Ta yi kyau

 

-         Ga ta nan dai

-         Dama-dama

-         Ɗan dama-dama         Kyau mai daraja ta III

-         Ba yabo ba fallasa


 

-         Ai sha’ani

-         Ba ta shige ni ba

-         Ba ta min ba               ba kyau

-         Ba tai kyau ba

(Ɗangambo, 2007).

 

          A matsayina na mai tarken wannan waƙa zan iya cewa wannan waƙar mai suna “A Kama Sana’a Mata” ta Hajiya Sa’adatu Barmani Coge ta ƙayatar da ni sosai ko kuma in ce ta yi armashi, ta burge ni, sannan ta waƙo sosai. Domin mawaƙiyar ta yi amfani da salon jan hankali da kuma nuna karsashi sosai a cikin waƙar, idan mutun ya fara sauraron wannan waƙar zai so ya ji ya ƙareta. Ga shi ta yi amfani da kalmomi na burgewa. A taƙaice zan iya cewa wannan waƙa ta waƙu sosai a ra’ayina.

          Don haka na yabi wannan waƙar da kalmomin yabo da ake amfani da su a kyau mai daraja ta I. Saboda haka zan iya cewa:

-         Ta yi armashi

-         Ta ƙayatar

-         Ta burge                    Kyau mai daraja ta I

-         Ta waƙu

Ni Hafsat Muhammad na bai wa wannan waƙar kyau mai daraja ta ɗaya.

2.     A wannan mazahabar (Tarken Gargajiya) ta nuna cewa duk mai son jin tarken adabi in ma waƙa ko zube ko wasan kwaikwayo rubutattu ko na baka, ana buƙatar a kawo tarihin mawaƙi/mawaƙiya ko mashiryi ko mawallafi. Don haka a matsayina na mai tarken wannan waƙar ta “A Kama Sana’a Mata” Ta Hajiya Sa’adatu Barmani Coge, yana da kyau in kawo bayanai da ke da nasaba da iliminta, hankalinta, gogayyatarta, halin rayuwarta, da kuma irin gwagwarmayarta d.s. saboda haka ga ɗan taƙaitaccen tarihinta kamar haka:

Taƙaitaccen Tarihin Hajiya Sa’adatu (Barmani Coge)

          Hajiya Sa’adatu wadda aka fi sani da Barmani Choge mai amada Funtuwa. An haife ta a wani gari da ake kira Larabar Abasawa, ƙaramar hukumar Gezawa, Jihar Kano. Zainabu shi ne sunan Uwaliya na yanka. Haihuwarta ta auku a daidai shekara ta 1984. Sunan mahaifinta Malam Abubakar, sunan Mijinta Malam Sule Nayayi.

Gado:

Uwaliya ta sami salsalar waƙa ta fuskar wanta Mamu, don haka ake yi mata kirari:

Uwaliya ƙanwar Mamu,

Kura kya ci da gashi,

Ƙuruciya da Karatun Allo:

Uwaliya ta yi karatun allo gwargwado, ta yi zurfi a ciki. Sannan ta tashi yarinya mai hazaƙa, wadda ta riƙi muƙamin zabiya a fagen waƙe-waƙen samartaka, a ko da yaushe tana tare da yara ‘yan uwanta tana yi mu su waƙa suna amsawa. Kafin Uwaliya ta yi aure ta yi kiwon shanun Kakanta Malam Sule.

Aure:

An yi wa Uwaliya aure a lokacin da take da shekara goma sha ɗaya. A ɗakin mijinta ta shiga: Jin wasu sana’o’in cikin gida na mata kamar kaɗin auduga da saƙa tufafin sawa, da sana’ar ƙuli-ƙuli. A lokaci da take waɗannan sana’o’i nata takan dinga rera waƙoƙi masu daɗi. Uwaliya ta sami amfani mai tarin yawa domin mutane na zuwa sayan ƙuli-ƙulin ko don su saurari muryarta mai daɗi da Allah ya yi mata. Daga nan kuma ta bar sana’ar ƙuli-ƙuli ta koma ga sana’ar tuyar ƙosai. Shi ma ƙosan in tana niƙansa takan rera waƙar kamar yadda ta saba.

          Bayan ‘yan waƙe-waƙen da Uwaliya ta yi na lokacin ƙuruciya da na lokacin da take sana’o’inta na cikin gida, sai ta tsiri yin waƙoƙin daɓe. Gidan Malam Shehu mijin Yarinye na unguwar Fawa a Larabar Asabawa nan ne ta fara yin waƙar daɓe a wani daɓe da aka gayyace ta a gidan. Daga nan ta sami ma su amsa mata, su ne kuwa Kande da Kaka da ‘yar Lala. A wannan lokacin Uwaliya ta sami kuɗi da zannuwa da sauran kayayyaki. Tun daga nan ne fa sai mata suka dinga gayyatar Uwaliya ta kai mata goro ga harƙoƙinsu don ta yi musu waƙa.

          To haka ne Uwaliya ta zagaɗe ta zama mashahuriyar mawaƙiya wadda kowa ke son ta yi masa kiɗa da waƙa. A wajen wannan kiɗa nata Uwaliya tana amfani ne da kiɗan ƙwarya.

Mataimakanta:

          Uwaliya tana da mataimaka kiɗan ƙwarya da amshi kamar haka:

-         Sale Nayaya – Mijinta (kiɗan ƙwarya da rawa)

-         Jummai – kiɗan ƙwarya da guɗa

-         Hasiya – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Dela – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Baƙuwa – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Ramatu – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         ‘Yar Hama – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Maimuna – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Larai – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Mai Kunu – kiɗan ƙwarya da roƙo

-         Mai Baje – kiɗan ƙwarya da roƙo

Rasuwarta:

          Uwaliya ta rasu a shekarar 2013, ta bar ‘ya’ya maza guda biyu, su ne kuwa (1) Alasan (2) Shehu, da jikoki goma sha ɗaya.

Gusau

 

          Bugu da ƙari, idan muka yi la’akari da wannan taƙaitaccen tarihin wanann mawaƙiya za mu ga ashe tu fil’azal mace ce mai son sana’a a rayuwarta. Za mu iya cewa wannan waƙa tamkar tana bai wa jama’a ne labarinta da kuma nuna musu muhimmancin sana’a a rayuwa. Don haka wannan mazahabar da ta kawo a bibiyi tarihi, hakan zai taimaka matuƙa wgaya wa mai tarken adabi domin da ma an ce wasu mawaƙa da marubutan sukan kawo abubuwan da suka faru da su a rayuwa na zahiri domin hakan zai taimaka a mai nazari wajen gano ainihin saƙon da ake son isar wa. Daga ƙarshe zan iya cewa wannan mazahabar ta dace da nazarin tarken wannan waƙar.

3.     A wannan mazahabar (tarken gargajiya) ta kawo yadda za a duba manufar adabi (jigo). Amma an kawo misali kaɗan, sannan babu cikakkiyar fiɗa ta aikin adabi ko fito da ainihin manufofin. A wannan wuri ana buƙatar mai yin tarke na adabi ya kawo ko fitar da manufar/jigo na adabin da yake nazari a kai amma ana so a kawo misalan kaɗan (ma’ana ba a buƙaci mai yin tarke/nazari ya yi cikakkiyar fiɗa ba).

Saboda haka, wannan waƙar mai taken “Ku Kama Sana’a Mata” ta Hajiya Sa’adatu Barmani Coge tana da jigon faɗakarwa kan sana’a. Idan muka duba tun daga farkon waƙar ta fito sarari tana cewa “Sai ku kama sana’a mata”. Ta yi maganganu sosai ko baitoci da dama da ke nuna cewa faɗakarwa take yi wa ‘yan uwanta mata su tashi su kama sana’a ko da a ce ƙaramar sana’a ce.

          Dalilin da ya sa na ce jigon wannan waƙar ita ce faɗakarwa shi ne, idan muka dubi wasu baitoci na cikin waƙar zai tabbatar mana da hakan. Ga kaɗan daga cikin irin hujjojina na cewa wannan waƙar jigon ta faɗakarwa; idan muka duba tun a farkon waƙar za mu ga cewa Sa’adatu ta bayyana hakan a fili inda ta ce:

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

                   Macen da ba ta sana’a aurace,

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Ka ga kenan tun a farkon waƙa ta ce wa duk wata mace da batta sana’a aurace (ma’ana jaka ce). Kenan ta fito fili ta ambaci ƙwayar jigonta a fili.

          Sannan haka abin ya rinƙa tafiya tun daga baiti na farko har zuwa ƙarshen waƙar Barmani Coga tana ta ƙoƙarin wayar da kan mata da su tashi su nemi sana’a kamar a wurare kamar haka:

Jagora:        Sai ku kama sana’a ya fi

Amshi:        Sai ku kama sana’a ya fi

Jagora:        Macen da ba ta sana’a ta bani.

 

Jagora:        Kai ku kama sana’a mata,

                   Ko dan ku huce takaicin zamani.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Haka lamarin ya kasance har zuwa baitoci na gaba kamar haka:

Jagora:        Dan Allah a kama sana’a mata,

                   Kar a raina sana’a,

                   Ayye! A yi ƙuli-ƙuli ko a yi ƙosai,

                   A yi furan madu ko ɗanwake,

                   Kai a kama sana’a ya fi,

                   Ko dan a samu abin kai wa biki.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

          Idan muka duba waɗannan baitoci da suka gabata za mu ga cewa babu wani saƙo da ake san isar wa da ya wuce faɗakarwa zuwa ga mata. Kai abin bai tsaya daga nan ba, Barmani Coge har roƙon mata take yi a cikin baitocinta don mata su tashi su kama sana’a kamar inda take cewa a cikin waƙar:

Jagora:        Ayye! Zamani ya canza mata,

                   Da kwalliya ke ɓoye,

                   Dan Allah ku kama sana’a,

                   Ayye! Lokaci ya canza mata,

                   Sai a kama sana’a mata,

                   Sai ku tashi ku nema,

                   Ai sai da kwalliya ke roho,

                   In babu kwalliya wani roho za a yi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

          Duba zuwa ga wannan mazahabar ta tarken gargajiya tana magana ne a kan kawo misali kaɗan (ma’ana babu cikakkiyar fiɗa kan saƙon adabi). Don haka ba tare da dogon surutu ko yawan misalai ba daga cikin wannan waƙar, iya misalan da muka bayar sun isa su tsaya mana a matsayin hujja na cewar jigon wannan waƙar shi ne faɗakarwa kan sana’a.

4.     Har Yanzu a wannan mazahabar (taken gargajiya) ta nuna cewa duk mai son yin tarken adabi dolensa ya yi la’akari da salo da nahawu da kuma azanci na wannan adabin da yake yin tarkensa a kai.

Idan ana maganar salo kamar yadda masana suka ce, salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa. Don haka muna iya cewa salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo. Ma’ana salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko fucui. Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma, lafazi, hanya ko tunani a maimakon wani (Ɗangambo, 2007:39).

          Dangane da wannan mazahabar, za mu yi nazarin salon waƙar Barmani Coge ta la’akari ko dangane da irin tasirin da za su haifarwa mai sauraro a cikin wannan waƙar, ta hanyar la’akari ko fita da ire-iren salo kamar haka:

Ø Miƙaƙƙen salo

Ø Salo mai armashi

Ø Ragon salo

Ø Tsoho/sabon salo

Ø Salo mai tsauri ko sarƙaƙiya               d.s.

Dangane da wannan waƙar kuma za mu iya cewa salo ne mai armashi da karsashi (salo ne da ya gamsar ta hanyar karsashi, ƙaƙale da burgewa d.s.). Za mu tabbatar da haka idan muka duba wasu baitoci kamar haka:

Jagora:        Ayye! Na tina da nisa,

                   Wannan magana ta sana’a ce,

                   Kai ni rimin tsiwa,

                   Ga mai tuwo da sunan Allah,

                   Dan Allah ki tashi ki tuƙa,

                   Ko sha biyun dare kika tuƙa a saya.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Haka zalika a wannan baitin

Jagora:        Ayye! Na tina nisa

                   Kowa ya baka dan ka faɗi ne,

                   Ba dai ya ba ka dan tsoro ba,

                   Dawo ta’ari kwana ƙwarya,

                   Allah jiƙan masa a ƙiyamu,

                   Ayye mai farin alawayyan koko,

                   Ke ki tashi ki dama,

                   Ko sha biyun dare kika dama za a sha.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

          Saboda haka, idan muka dubi wannan baitoci guda biyu na sama za mu ga cewa lallai wannan waƙar ta Barmani Coge akwai armashi da karsashi a ciki.

          Sannan za mu iya cewa a nan salon waƙe-waƙenta taa da salo na tsaka-tsaki ne. Baya ga haka a wannan wuri za mu duba irin kalmomin da ta yi amfani da su a cikin wannan waƙar.

Tsofaffin Kalmomi

          Barmani Coge ta yi amfani da tsofaffin kalmomi a wannan waƙar kamar su:

Ø bani

Ø furan-madu

Ø sakarai

Ø bankaura

Ø aurace

Ø farin-alawayyan-koko

Ø soro

Ø ƙuli-ƙuli

Ø asun-da-asun

Sannan ta yi amfani da kalmomin aro a wannan waƙar kamar su:

Ø Allah

Ø La’ilaha illallah

Ø Rasulallahi

Ø Ƙiyama

Sannan an samu azancin magana a wannan waƙar a wurare kamar haka:

          A baiti na shida:

Jagora:        Sai na ce zaman ɗako sai tulu,

                   Amma zaman ɗaka sai randa,

                   Tulu ka tashi ku koma rijiya.

          A wannan azancin ta danganta wasu mata da tulu da randa, wanda a zahiri kowa ya san tulu da randa bassa iya yin komai a kawunansu sai abin da aka kawo musu.

          Haka an samu azanci a wannan waƙar a wuri kamar haka:

Jagora:        Sai na ce biki na farar kaza,

                   Wa ya zo da angulu kai ba kallabi.

          Ma’ana duk lokacin da ake biki ko wani suna (taron mata) akan samu habaice-habaice a tsakanin mata, musamman wata ta je hannu-rabbana za a yi mata azanci kamar yadda Barmani Coge ta yi a sama.

          Haka zalika an samu habaici kamar haka a wani baiti:

Jagora:        Na faɗi na ƙara,

                   Kawo kiɗa ku-sauƙa na dokin mata,

                   Mata suna ta sana’ar nema,

                   Sakarai bankauran banza,

                   Ta sai da gulma ta sai tabarma,

                   Ta shimfiɗa ta ji daɗin tsegumi.

          Saboda an samu azanci da dama a wannan waƙar ta Hajiya Sa’adatu Barmani Coge.

5.     Har yanzu wannan mazahabar (tarken gargajiya) tana duba kayayyaki na gargajiya da aka yi amfani da su.

A wannan waƙar ta Hajiya Sa’adatu Barmani Coge ta yi amfani da abubuwan gargajiya na adabi irin su:


Ø Tulu

Ø Tabarma

Ø Kallabi

Ø Maraba

Ø Rijiya

Ø Ƙosai

Ø Furan-madu

Ø Koko

Ø Tuwo

Ø Roho

Ø Ta’ari

Ø Bankaura

Ø Dakau

Ø Soro            d.s.


6.     A wannan mazahabr ne take buƙatar mai yin tarke da ya ba da wasu shawarwarin da yake ga za a bunƙasa aikin,idan akwai wata naƙasa da ya gano, tare da la’akari da yadda aikin adabin ke zama kamar wani madubi na haskaka yanayin muhallin ɗan-adam.

A matsayina na mai tarken wannan waƙa mai suna a kama sana’a mata: Na gano wani naƙasa da wannan waƙar ta Barmani Coge. Matsalar a nan ita ce a matsayinta na mai faɗakarwa kan sana’a bai da ce ta rinƙa saka ashar a cikin faɗakarwarta domin kowa ya sani ashar ba na mutanen kirki ba ne. babu yadda za a yi ka zo yin wa’azi ko gargaɗi ko faɗakarwa ko kuma wayar da kai ka zo kana yin ashar kuma a saurare ka. Don haka ina mai bayar da shawara duk mutumin da yake son isar da wani saƙo zuwa ga wasu bai dace a ce yana ashar a ciki ba.

          An samu ashar a wannan waƙar a baiti na 9 inda take cewa:

Jagora:        Sai na ce biki na farar kaza,

                   Wa ya zo da angulu ‘yar burar uba.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Kammalawa

          A taƙaice zan iya cewa wannan waƙar ko manufar waƙar tamkar wani madubi ne na haskaka rayuwar al’umma. Domin a halin da muke ciki a yanzu ba yadda za a yi ɗan-adam ya yi rayuwa ba tare da sana’a ba.

Madogara

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa: Zaria. Amana publishers

Gusa, S.M. (1991). Mawaƙa da Makaɗan Hausa

Gusa, S.M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka


 

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

Amshi:        Sai ku kama sana’a mata.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a ya fi,

Amshi:        Sai ku kama sana’a ya fi.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a ya fi,

Amshi:        Sai ku kama sana’a ya fi.

 

Jagora:        Sai ku tashi ku nema mata,

Amshi:        Sai ku tashi ku nema mata.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Macen da ba ta sana’a ta bani.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai na ce zaman ɗaka sai tulu,

Jagora:        amma zama ɗaka sai randa,

Jagora:        Tulu ka tashi mu koma rijiya.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Kai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Ko dan ku huce takaicin zamani.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai na ce biki na farar kaza,

Jagora:        Wa ya zo da angulu ‘yar burar uba.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai na ce biki na farar kaza,

Jagora:        Wa ya zo da angulu kai ba kallabi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Dan Allah a kama sana’a mata,

Jagora:        Kar a raina sana’a,

Jagora:        Ayye ai ƙuli-ƙuli ko ai ƙosai, ai furan madi ko ɗanwake, kai a kama sana’a ya fi, ko dan a samu abin kai wa biki.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ai mu ne ƙafar kare mai yawo,

Jagora:        Mun san gida-gida wani bai san namu ba.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Kai ku kama sana’a mata,

Jagora:        Na’ina ma su abin kaiwa biki.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye ku kama sana’a, zamani ya canza mata, kai ku kama sana’a dai-dai, sai ku kama sana’a ya fi, la’ilan ha’ilallah, ayye macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        ayye na riga na gane mata,

Jagora:        Macen da ba ta sana’a ta bani.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Sai ku tashi ku nema ayye, nema yana hana ciwon zuciya.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye zamani ya canza mata,

                   Da kwalliya ke ɓaye,

                   Dan Allah ku kama sana’a,

                   Ayye lokaci ya canza mata,

                   Sai ku tashi ku nema,

                   Ai sai da kwalliya ke roho,

                   In babu kwalliya wani roho za a yi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye da kwalliya ke ƙaye,

                   In babu kwalliya wani ƙaye za a yi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Na faɗi na ƙara,

                   Kawo kiɗa ku sauƙa ma dokin mata,

                   Mata suna ta sana’ar nema,

                   Sakarai kankauran banza,

                   Ta sai da gulma ta sai tabarma,

                   Ta shimfiɗa ta ji daɗin tsegumi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye Ladi mai kaɗa ƙwarya,

                   Kin san macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye mai kiɗan ruwa ‘yar ja,

                   Ai kin san macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Wo ɗiyan mahauta rushe,

                   Kin san macen da ba ta sana’a ta bani.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Jagora:        Ayye, wo Ta’ari kwana ƙwarya,

                   Kin san macen da ba ta sana’a aura ce.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye dan ya Rasulallahi mata,

                   Kar a rena sana’a mata,

                   Kai ku kama sana’a mata,

                   Ai ƙuli-ƙuli ko ai ƙosai,

                   Ko da dakau aka samu ma a yi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye kar a rena sana’a mata,

                   Aiƙuli-ƙuli ko ai ƙosai,

                   Ko da dakau aka samu ma a yi.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye na tina na nisa,

                   Kowa ya baka dan ka faɗi ne,

                   Ba da ya ba ka dan tsoro ba,

                   Dawo ta’ari kwana ƙwarya,

                   Allah jiƙan maza a ƙiyama,

                   Ayye mai farin alawayyan koko,

                   Ke ki tashi ki dama,

                   Ko sha biyun dare ki-ka dama za a sha.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Jagora:        Ayye na tina na nisa,

                   Wannan magana ta sana’a ce,

                   Kai ni rimin tsiwa,

                   Wo Ramatu rimin tsiwa,

                   Ga mai tuwo da sunan Allah,

                   Dan Allah ki tashi ki tuƙa,

                   Ko sha biyun dare ki ka tuƙa a saya.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

 

Jagora:        Ayye ƙida na sana’a mata,

                   Macen da ba ta sana’a ta bani.

Amshi:        Lale-lale maraba da ke zinariya.

Post a Comment

0 Comments