Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).
Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 3)
Sulaiman
Salisu Muhammad
Sashen
Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami'ar
Jihar Kaduna.
Email:
sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740
TASHI DA MANYAN BAƘAƘE A RUBUTU:
Akwai abu da dama da ake fara rubuta su da
babban baƙi. Fara rubuta su da karamin baƙi a duk in da suka
zo, kuskure ne. Ana fara rubuta su babban baƙi ko a farkon jimla
ko a tsakiya ko a ƙarshe. Misali:
Sunayen Ubangiji:
Allah ba allah ba.
Arrahman
ba arrahman ba.
Almalik. ba
almalik ba.
Sunayen Mala'iku:
Jibrilu
ba jibirilu ba
Raƙibu ba
raƙibu ba
Nakiru
ba nakiru ba
Sunayen Gidan Rahama:
Aljanna
ba aljanna ba
Firdausi
ba firdausi ba
Sunayen mutane na yanka:
Muhammad
ba muhammad ba
Abubakar ba
abubakar ba
Rabi'atu ba
rabi'atu ba
Hassan ba
hassan ba
Sunayen Mutane Na Ranaku:
ɗanjuma
ba ɗanjuma ba
Asabe ba
asabe ba
Balarabe
ba balarabe ba
Sunayen Ranaku:
Juma'a
ba juma'a ba
Asabar
ba asabar ba
Lahadi
ba lahadi ba
Talata
ba talata ba
Sunayen Watanni:
Janairu
ba janairu ba
Febrairu
ba febrairu ba
Maris
ba maris ba
Afrilu
ba afrilu ba
Sunayen Garuruwa:
Zariya
ba zariya ba
Katsina
ba katsina ba
Kano
ba kano ba
Anaca
ba anaca ba
Nijar
ba nijar ba
Sunayen Unguwanni:
Hanwa ba hanwa ba
Tudun wada
ba tudun wada ba
Tarauni ba tarauni ba
Sunayen Kabilu:
Hausa
ba hausa ba
Fulani
ba fulani ba
Igbo
ba igbo ba
Yoruba
ba yoruba ba
Sunayen Sarautu:
Sarki ba
sarki ba
Galadima
ba galadima ba
Waziri
ba waziri ba
Yarima
ba yarima ba
Dallatu
ba dallatu ba
0 Comments
Rubuta tsokaci.