Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).
Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 2)
Sulaiman
Salisu Muhammad
Sashen
Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami'ar
Jihar Kaduna.
Email:
sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740
DALILIN ƘIRƘIRO RUBUTU A
DUNIYA:
DaÉ—aÉ—É—iyar hanyar sadarwa a
duniya ita ce maganar baki da baki, a tsakanin mutum biyu ko fiye.
Ita sadarwa ta baki da baki, kafin ta gudana
dole sai an hadu da mai magana da wanda ake son yi wa maganar. Idan akwai
tazara a tsakaninsu, kamar wani yana wani gari, shi kuma wancan yana wani gari,
ya zama dole É—aya daga cikinsu ya
tashi ya je ya sami dayan ya fada masa, sannan ya dawo. Ko kuma mutum ya tashi
wani ɗan aike ya faɗa masa saƙon, shi kuma ya je ya
isar da saƙon da fatar baki.
A irin wannan tsarin sadarwa akwai gajiyarwa
a cikinsa. Sannan idan abin ya haɗa da aiken ɗan saƙo ne, a nan kuma babu
sirri a maganar da za a fada. Sannan kuma akwai yiwuwar mantuwa, ko ƙarin gishiri ko
ragewa ga ɗan saƙo. To wannan a magana
ke nan, ina a ce wasu nau'o'in maganar hikima ta adabi, kamar waƙoƙi ko labarai da
sauran hanyoyin ilmantarwa.
Ire-iren waɗannan matsaloli ne suka sabbaba wa ɗan Adam ya ƙirƙiri hanyoyin rubutu.
Wannan ya ba shi damar rubuta saƙonsa, ko tunaninsa ko
wasu darussa ko dai wasu muhimman abubuwa a kan takarda da yake son adanawa, ko
aikawa daga wani wuri zuwa wani ba tare da tangarda ba, ko tauyewar abin da
yake nufi ba.
SAMUWAR RUBUTU A KASAR HAUSA:
Wadancan matsaloli da aka ambata a baya,
kowace al'umma ta duniya ta fuskance su. Wasu sun sami wayewar kai sun kirkiri
hanyoyin magance su. Sun kirkiri hanyoyin rubutu kuma sun adana su ana amfani
da su har zuwa yanzu. Akwai mutane kamar: Romawa da Chaina da Sipaniyawa da
Larabawa.
Masana harshen Hausa suna nan sun dukufa
domin gano ko Hausawa suna da nasu hanyar rubutu kafin zuwan Larabawa da Turawa
kasar Hausa.
Akwai wasu alamomi gadaddu da ke nuna cewa
Hausawa su ma akwai yunkuri da suka yi a can baya na yi wa wasu abubuwa zane.
Misali, zanen da Bahaushe ke yi a fuskarsa, da wanda yake yi a kwarya da
akushi. Ko wanda yake yi a fadojin Sarakunan gargajiya. Dukkan waÉ—annan zanuka ko
alamomi, akwai abin da suke nufi a cikin al'aldar Bahaushe. Misali zanen
kalangu na Katsinawa da na Gobirawa duk akwai abin da suke nufi.
WaÉ—annan abubuwa suna nuni da cewa Bahaushe ba a
bar shi a baya ba wajen kirkirar tasa hanyar ta magance matsalar sadarwa.
Rashin sa'ar da aka yi shi ne, magabata ba su tsaya sun inganta su ba kamar yadda
saura al'ummomin duniya suka yi ba. Larabawa da Turawa sun yi mana shigar
gaggawa, muka shantake muka ringumi nasu.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.