Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Nazarin Jumla A Nahawun Hausa (3)

 Kundin Neman Digirin Farko (B.A. Hausa) Da Aka Gabatar A Sashen Harsunan Nijeriya Tsangayar Fasaha Da Ilimin Addinin Musuluncin Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

NA

IBRAHIM HAMISU YUSUF

Ginin Jumla

BABI NA BIYU

AZUZUWAN KALMOMI  A TASKAR MASANA NAHAWU

2.0 Shimfiɗa


Aƙalla akwai fannoni guda biyar manya da a ke nazari game da nahawun  harshe (grammar). Waɗanda suka ƙunshi; Nazarin gundarin sauti (Phonetics) da  nazari akan fannin tsarin ilimin furuci (Phonology) da nazarin ginin kalma (Morphology) da nazarin ginin jumla (Syntax), sai kuma nazarin fannin ilimin ma’ana (Semantics). A fahinta ta zamani (Radford, 1981), nazarin a kan nahawun kowane harshe ba ya kammaluwa sai ya ƙunshi nazarin tsararre a kan waɗannan fannoni.

An daɗe a na gudanar da bincike da nazarce-nazarce kan nahawun Hausa, amma duk da haka a kullum ba a rasa samun waɗansu matsaloli na fahinta waɗanda kan tilasta yin sabon nazarin mai ƙyau bisa tsari na zamani. A wannan bincike zai nazarci hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, wanda ya ƙunshi, sanin azuzuwan kalmomi, da fasalinsu. Sannan a nuna yadda suke kasancewa a cikin jumla, da guraben da ya kamata kowanne ajin kalma ya zauna a cikin jumla.  Za a bayyana yadda doƙoƙin ginin jumla suke tare da gabatar da fasalin nazarin jumla, sannan a kawo yadda tsarin bishiyar li’irabin nahawu take a harshen Hausa.

Ilimin ginin jumla fannin ne da a ke bin doƙokin nahawun harshe domin amfani da azuzuwan kalmomi (word clases ) a matsayin tubalan da za a yi amfani da su a jeranta su domin a gina zance bisa ƙa’idar nahawu. A wannan fannin ne ake bayanin yadda ake sarrafa kalmomi a haɗa su da juna don su samar da jumla gamsasshiyar.

 

 

2.1 WAIWAYEN AZUZUWAN KALMOMIN NA HARSHEN HAUSA
Azuzuwan kalmomi su ne mahimman tubalan da a ke harhaɗawa ɗon gudanar da nazarin jumloli. Kusan kowanne ajin kalma ya na da nasa muhalli a fagen tsarin nazarin jumla. Wato abin nufi a nan shi ne, kowanne ajin kalma ya na cin gashin kansa ne a fannin nazarin ginin jumla.

Bisa la’aƙari da lokaci mai yawa da a ke yin nazarin kashi-kashi, a na kuma ba kowa ni gida nasa rabon na suna. Akwai ajin sunaye (Nouns) da ajin aikatau (verbs) da ajin sifa (adjectives) da ajin bayyanau (adverbs). Da makamantansu.

Masana da dama sun ba da tasu  gudunmawa wajen fito da yadda azuzuwan kalmomin suke gida-gida abin lura a nan shi ne masana suna da tsari na musamman da suke bi na ba da sunaye ga azuzuwan kalmomi. An yi wani zamani a farko inda aka rika tilastawa harsuna su bi tsarin rabe-raben kalomomi na wani harshe wanda a ka yi lokacin da harshen latin, (greek), ya gawurta hartakai shi ne ma’aunin ga sauran harsunan turai wajen raba kalmominsu. Abin nufi shi ne duk ajin kalma da latin ke da shi, to tilas ne a ce harshen Ingilishi da Faransanci da Jamusanci suna da wannan aji. Ko ba shi, sai an ƙirƙiro shi!

Rabe-raben kalmomin wannan wani tsari ne da masana ilimin kimiyyar harshe na zamani (Moden Linguistics) wannan fannin ya ba da dama ƙwarai, ya kuma karfafa gudanar da bincike mai cin gashin kai na kowane harshe. Masana sun lura cewa ta hanyar bincikar kowane harshe shi kaɗai, za a gano arzikin harshen dangane da ire-iren kalmominsa da kuma kebabben tsarinsa nahawun. Masana irin su Chomsky, sun bayar da guɗunmawa sosai wajen sake fahimtar yanayin tsarin harshe da kuma kawo hanya mafi dacewa ta aiwatar da nazarin nahawun harshe. Alal misali; Chomsky ya na nuna cewa akwai wani na bai ɗaya da yake boye a halin yanzu na tsarin nahawun harshen ɗuniya baki ɗayansu (Universal Grammar). Ya nuna cewa wata rana za a cimmma wannan tsari na bai ɗaya. Ya ce, to hanya mafi dacewa ta kaiwa ga wannan gali, ita ce ta yin nazarin zuzzurfa a kebance na tsarin nahawun kowane harshe, sannan daga baya a tace abubuwan masu kama da juna, ya ce su ne gagama-gari (Universal), waɗanda suka kasa shiga cikin wannan rukkuni na ‘yan gama-gari, to sai a jiye su a mala, har sai ilimi ya ƙaru, wanda zai bada dama a sasu a wannan ajin na ‘yan gama-gari.

Bisa la’aƙari da ajin kalmomi (Lexical Categories). Chomsky (1986:p2) ya bayyana cewa ana iya raba dukkan kalmomin harshe gida hudu bisa wata daraja mai baki biyu, wato kasancewa (+) ko rashin kasancewa (-). Ga yadda yayi rabon.

1.     suna (S) = D+S, -Ax

2.     Aikatau (A) = D+A, - Sx

 


    iii. sifa (SF)       = D+S, + Ax

1.     Harafi (H) = D.S, - Ax

 


abin nufi a nan  shi ne suna, suna ne (+S) ba shi da alaƙa da aikatau (-A).  Aikatau, aikatau ne (+A) kuma ba da alaƙa da suna (-S), sifa ta shafi suna (+S) ta kuma shafi aikatau (+A), harafi bai shafi suna ba (-S), haka kuma bai shafi aikatau ba (-A).

Bayan haka Amfani, 1996. A cikin maƙarlar daya gabata sashen harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato ya bayyana rabe-raben kalmomin Hausa, bayan haka ya bayyana rukunin mutanen farko da suka yi aikin raba kalmomin.    Abney (1987:P62) ya ƙalubalanci rabo na Chomsky, ya ce lalle akwai wasu kalmomin harshe waɗanda ba su samu shiga ba, waɗanda kuma tilas ne a sa su cikin rabon. Shawarar abney it a ce abu mafi ƙyau shi ne a ce kalmomin harshe sun kasu kasha biyu: masu yin aikin irin na nahawu a cikin jumla da waɗanda kalmomi ne kawai waɗanda an san gurabun da suke cikewa a cikin jumla. Don haka kalmomi irin su ƙwayar ma’ana mai nuna mallaƙa (possessive) ko nasaba (genetive) ko lokaci (tense) ko taƙi (aspect) da makammantansu, kalmomi ne masu yin aiki na nahawu (functional categories) a cikin jumla. Kalmomin irin su suna (noun) da aikatau (verb) da sifa (adjective) kalmomi masu gurabe na ɗindingi (non functional categories) a cikin jumla.

Bayan haka ya raba kalmomin Hausa kaman haka rukunin mutane na farko da suka yi aikin raba kalmomin Hausa gida-gida Turawa ne, kuma lalle sun yi ƙokarin a za harshen Hausa bisa tsarin Ingilishi. Yin hakan ya sa har yanzu akwai matsala  game da wasu rabon da aka yi a kalmomin harshen Hausa waɗanda basu cancanta ba. Alal aƙalla, akwai matsaloli iri uku ɗangane da matsayin rabon kalmomin a yadda yake a yanzu.

 

1.     Wasu kalmomin an basu sunan kasha wanda bai cancance su ba.

 

2.     Wasu kalmomi ba a sa su cikin kowane kashi basam.

 

3.     Wasu kalmomin har yanzu ba a yi matsaya ba a kansu.

 


Za mu bi su ɗaiɗai mu ga yanayin kowace matsala kalmomin da suna bai cancance su ba wakilin suna na gabanin aikatau, (pre-verbial-pronoun).

Galadanci, 1976. Ya na kiran wannan ƙwayar ma’ana da ɗayantau (referential). Ya nuna cewa abin nan (= kalma) da ke zuwa bayan fa’ili amma kafin aikatau a cikin jumla. Wakilin suna ne. alal misali Kalmar ta a cikin jumla Bintata ’na’ a ƙaranta jaridaa.

Babu shaƙƙa binciken irin na zamani, (Tuller 1986). Yusuf, (1991), Amfani, (1996), sun nuna cewa wanannan sai dai a kira ta da ɗiyantau koma baya (Previous Reference marker).

Lura da ƙwayar ma’ana da ke liƙe da waɗanannan sunaye kuma a kan kira

 

1.     Riga (r)

 

2.     Wando (n)

 

3.     Gidaje (n)

 


Galadanci (1976) ya na kiran wananna ƙwayar ma’ana ɗanyatau (referential). Tuller (1986) da Waɗansu masana da dama sun ba da shawara bisa ƙwaƙƙwarar hujja cewa kiran wanann kwayar ma’ana referential kurum bai wadatar ba. Sun sake mata suna wanda ya fi dacewa. Sunan shi ne “previous Reference marker” (wato ɗayantau koma baya).

Mahaɗi (link element)

Ga wasu misalai kan yi nazarinsu.

 

  • Farar mootaa

 

  • Baƙin ta’akalmii

 

  • Doogaayen gidaajee

 


Kowane misali sashe ne na jumla (phrase), kuma ya ƙunshi sifa (adjective) da suna (noun). Wani tsari na hausa shi ne a duk inda sifa da suna suka zo tare (ƙunshein ana kiransa ‘yankin suna’ koda yak e zai fi dacewa a kira shi ‘yankin sifa’), to lalle sai an tsarma -r ko -n tsakanin su. Galadanci (1976) ya na lura da –r da –n  a matsayin ƙwar ma’ana bisa la’aƙari da aiki, yace, wannan ƙwayar ma’ana, mahsɗI (link element) ce. Yusuf (1991) ya nuna cewa wannan ‘mahaɗi’ baya ɗaya daga cikin ajin kalmomi na sauran harsunan duniya (universal category). Amfani, (1996), ya yarda da maganar Yusuf (1991) ya kuma ɗora a kanta. Ya ce, a haƙiƙanin gaskiya, wannan ƙwayar ma’ana ba ‘mahaɗi’ ba ce manunin bigire (location marker) ce. Amfani (1996) ya ci gaba da bayani cewa wani tsari na Hausa shi ne a duk lokacin da sifa ta yi bayanin suna, to Hausa na da tsarin mai nuna cewa sifa ta zo kafin suna ko ta biyo shi. Akwai ƙwayar ma’ana ta musammam mai yin wannan aiki. Wannan ƙwayar ita ce Amfani ya kira su da manunin bagire (location marker). Idan sifa ta biyo bayan suna wasalin ƙarshen zai zama dogo kamar haka;

 

  • Mootaa far

 

  • Ta’akalmii baƙ

 

  • Gidaajee doogaay

 


Manunin lokaci (tense) da taƙi (aspect) masana ilimi kimiyyar harshen sun raba lokaci gida uku: shuɗadɗ’en lokaci (past) lokaci maici (present) lokaci mai zuwa (future). Akwai taƙI (aspect) wanda yake nuna cika aiki cif-cif watau (completive/perfective), ko kuma a na cikin yin shi ba a kare ba (uncompledted/continuative/imperfective). Masana nahawun Hausa sun zo da ra’ayuka mabambamta dangane da abin da Hausa ke da shi. Shin lokaci (tense) ne, kwai ko taƙI (aspect) ko harda hali (model) ko kuma ya ya abin yake?

Galadanci, (1976) ya nuna cewa lokaci (tense) kaɗai Hausa take da shi ya kuma ambaci lukuta guda takwas.

Skimmer, (1977) ya haƙiƙancecewa taki (aspect) kwai Hausa ta ke da shi. Da alama Galadanci da Skimmer ba su tsaya tsaf suka yi nazarin jumlar Hausa ba, su ga cewa lalle ɗukkana abubuwan wato lokaci da taƙi tare suke zuwa.

Yusuf (1991) da Amfani (1996) sun tabbatar da haka. Don haka suka yi matsaya cewa talle abinda ake dada shi a Hausa shi ne lokataƙ, (tense-aspect), ba tsurar lokaci (tense) ko taƙIi (aspect) kawai ba. Baya ga wananan matsayin, akwai irinsu Newman da Schuharma da Fuller waɗanda a wurare da dama sun nuna cewa abin da Hausa ta keda shi, shi ne haɗakar lokaci da taƙi da hali (tense-aspect-mood (tam)).

 

Suna da Rabe - rabensa

Suna kalma ce  ta nahawu wadda ke bayanin lafazin da ake amfani da shi wajen ambatawa kowane abu na rayuwa, mai rai ne, ko maras rai, yana motsi ko ba ya motsi, mutum ne ko dabba ko wani abu wanda ke kasantuwa a tsarin rayuwar yau da kullum. Duk a na ambata masa wannan kalma ta suna. Kusan ba wani abu da ɗan’Adam ya bar shi ba tare da ya ambata masa kalmar suna ba. Misali:

 

Mutane               Wurare      Dabbobi        Ƙwari              Sauran abubuwa

Shehu                Makaranta     Doki           Gwano                 Itace

Musa                  Zariya           Akuya         Gara                     Kogi

Citumu                Katsina         Raƙumi       Cinnaka                Ciyawa

ɗanladi                Masallaci      Giwa          Tururuwa              Ƙarya

Rabi                      Kasuwa         Zomo        Kiyashi                 Yashi



RABE – RABEN SUNA


Suna ya kasu zuwa rukunoni daban – daban na nazari, gwargwado yadda tsarin da suna ya ƙunsa.

 

1.     Sunan yanka.

2.     Suna gama - gari.

3.     Suna gagara - ƙirga.

4.     Suna tattarau.

5.     Suna harɗadɗ’e.

6.     Suna ɗan’aikatau.


Waɗannan su ne rabe - raben ajin suna, bisa la’akari da rukunin da kowanne suna ya fito. Yanzu za a ɗauke su ɗaya bayan ɗaya a yi bayanin su domin samun haske a game da su.

Sunan Yanka

Sunan yanka suna ne da al’umma suka amince da shi don su riƙa ambaton sunayen abubuwa da shi ciki har da sunayen mutane da sauran halittu. Ana amfani da sunan yanka ne wajen bambance ɗaiɗaikun halittu da abubuwa da shi ta fuskar jinsi da adadi. Sunan yanka yana iya kasancewa sunan mutane ko dabbobi ko tsuntsaye ko tsirrai ko duwatsu ko muhalli da makamantan su. Misali:

Musa

Tururuwa

Zaki

Akuya

Makaranta

Nijeriya d.s.

Suna Gama - Gari

Wannan  nau’in na suna ana amfani da shi, wajen ambaton abubuwa na tarayya. Wato ana kiran wasu sunaye da suka cancanci a haɗe su wuri guda don su samar da sunayen rukuni na tarayya wajen ambato, ba tare da an bambanta sunayen abubuwan ba zuwa ɗaiɗaikun suna. A taƙaice suna ne da al’umma suka zaɗa wajen ambata wa wasu rukunonin halittu da suka cancanci ambato a cikin adadi na tilo. Misali:

Mutum

Dabba

Tsuntsu

Ƙwaro

Littafi d.s.

A nan ba sai an ware wani daga cikin rukunin ba, an ambaci wani laƙabi da ya shafe shi, shi kaɗai ba. Wato dai ana iya kiran sa da cewa suna ne na bai-ɗaya.
 

Suna Gagara – Ƙirga

Wannan nau’in na suna, suna ne na abin da ba a iya ƙirga shi da ɗai- ɗai da ɗai-ɗai. Ire-iren waɗannan abubuwan sun haɗa da:

Madara

Nono

Yashi

Ƙasa

Gishiri

Gari.  d.s.

Abin lura a nan shi ne, kowane ɗaya daga cikin misalan da aka bayar, ba wanda zai iya ɗaukar kowane kaso ya ce zai iya ƙirga shi ɗaya bayan ɗaya don gane yawan adadinsa. Don haka ake kiran kason da suna gagara - ƙirga.

 

Suna Tattarau

Shi kuma wannan kashin na sunatattarau, yana ƙunshe da sunayen abubuwa ne waɗanda galibi ana samun su ne a cikin rukuni ɗaya. Kuma sunan kan zo a adadi mai alaƙa da jam’i. Abin nufi sunan yakan tattaro sunayen abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da jinsin tamata da na namiji a matsayin suna guda. Kuma ya haɗa da sunayen abubuwa da na halittu, kamar irin su:

Garke

Ayari

Runduna

Bataliya

Gungu  d.s

Waɗannan sunayen ana iya samun kowane jinsi a cikin kowane suna na tattarau.

 

Harɗa
ɗɗen Suna

Shi kuma wannan nau’in na harɗadɗ’en suna ana haɗa kalmomi biyu ko fiye ne, masu zaman kansu ta hanyar liƙa su da karan-ɗori ko ƙwayoyin ma’ana ta –n ko –r don su ba da sunan wuri ko wani abun amfanin yau da kullum.Misali:

Bayangida

Gidanwaya

Gidanrediyo

Bakinkogi

Tuma-ƙasa

Malam-buɗe-littafi

Cika-ciki

Da makamantrsu.

Haka kuma akwai harɗadɗ’en sunan da yake bayyana sunan wani abu ta hanyar gwama sunaye biyu da kalmar  harafi ta ɗa’ a tsakiyarsu tare da karan-ɗori. Misali:

Ƙato-da-lage

Ciki-da-alako

Rub-da-ciki

Kau-da-bara

Da makamantarsu

 

Suna ɗan’aikatau

Shi kuma wannan nau’in na suna ɗan’aikatau ya sha bamban da sauran nau’o’in sunayen da aka ambata a baya. Domin suna ɗan’aikatau ya fito ne daga kalmomin aikatau. Wato suna ne mai ɗauke da kalmar aikatau wadda aka yi wa ɗafi  ta koma suna. Misali:

 

Kalmar Aikatau Cikakka          ɗafi da Kalmar Aikatau  Kalmar Suna ɗan’aikatau

Tafiya                                        ma- +   tafiya                                  Matafiya

Noma                                         ma- +   noma                                   Manoma

Su                                              ma-  + su + -nta                                Masunta

Wannan shi ne yanayin ajin suna da rabe-rabensa a nahawun harshen Hausa.

 

Wakilin Suna

Wakilin Suna yana ɗaya daga cikin ginshiƙan rukunnan nahawun Hausa. Wakilin suna wata kalma ce da ake amfani da ita wajen tsarin ginin jumla a nahawun harshe don ta wakilci kalmar suna a muhallin da kalmar suna ta kamata ta fito, amma saboda wani sharaɗin nahawu ya zama kalmar sunan ba ta fito a wannan muhallin ba. Ma’ana, amfani ake yi da ajin kalmomin wakilin suna a madadin kalmar suna a fagen nazarin jumla. Misali:

shi maimakon Audu

Ita maimakon Binta

Su maimakon ɗalibai

Misalin wakilin suna a cikin jumla shi ne;

Musa ya a mare ta

Shi ne ya kama akuya.

Wakilin suna shi ma ya rarrabu zuwa rukunonin nazari kamar haka:

 

1.     Wakilin suna katsattse.

 

2.     Wakilin suna

 

3.     Wakilin suna tambayau.

 

4.     Wakilin suna madubi.

 


Wakilin Suna Katsattse

Wannan nau’in na wakilin suna katsattse, ya na iya cin gashin kansa a ƙa’idar rubutun nahawun harshen Hausa. Abin nufi a nan shi ne ya na iya zama shi kaɗai a matsayin kalma mai cikakken aiki, ba tare da ya haɗu da wata  kalma ta nahawu ba wajen wakiltar suna a cikin jumla. Kuma ana amfani da shi wajen fayyace sunan mutum na ɗaya da na biyu da na uku. Haka kuma ana iya nuna adadin sunan da yake wakilta, wato a san sunan tilo ne ko jam’i. A na iya sanin jinsin da sunan ya fito, wato sunan namiji ne ko tamata. Misali:

 

Mutum na ɗaya (Mai Magana)          Tilo                              Jam’i

Namiji:                                       Ni

Tamata:                                      Ni

---------------                                -----                              Mu

 

Mutum na biyu (Abokin Magana)      Tilo                              Jam’i

 

Namiji                                                    Kai

Tamata                                                   Ke

------                                                        --------                  Ku

 

Mutum na uku (wanda ake magana a kansa/Sha Magana)              Tilo                   Jam’i

Namiji               Shi
                          Su

Tamata             Ita
                            Su


Wakilin Suna Nunau

Shi wannan nau’in na wakilin suna, yana wakiltar suna ne ta hanyar nuni zuwa ga sunan da yake wakilta. Ana amfani da shi ne wajen nuna wani abu da shi, abin na kusa ne ko na nesa. Kalmomin wakilin suna nunau iri biyu ne; akwai dogo sannan akwai gajere.

Wakilin Suna Nunau Dogo

Wakilin suna nunau dogo ya na iya zama da kansa wajen wakilci. Sannan kuma yana zuwa a cikin jumla don ya wakilci suna. Kuma yana fayyace jinsi da adadi na sunan da ya wakilta. Sannan yana nuni kan wani abu da yake a kusa ko na nesa. Misali:

Kusa                            Nesa                            Jinsi

wannan                        wancan                        Namiji

wancan                       waccan                        Tamacce

waɗannan                   waɗancan                   Jam’i

 

Wakilin Suna Nunau Gajere

Wannan nau’in na gajeren wakilin suna nunau, gajeren zubi gare shi in aka kwatanta shi da dogon wakilin suna nunau. Haka kuma ba ya iya zaman kansa har sai an jingina shi da wata kalma. Dole sai ya sami abin da zai jingina da shi kafin wakilcin nasa ya inganta. Ana amfani da ƙwayoyin ma’ana na –n da –r tare da kalmomin wakilin suna nunau. Misali:

Kusa                                           Nesa

-n  nan (gidan nan)         -n  can (gidacan)

-r  nan (rigar  nan           -r  can (rigar  can)

-n nan (yaranan) -n can (yaracan)

 

Wakilin Suna Tambayau

Wannan nau’in kuma kamar yadda sunan ke nuni, ya jiɗanci yanayin tambaya ce. Duk lokacin da aka yi amfani da shi, to tabbata tambaya ce ake yi. Haka kuma shi wannan wakilin suna tambayau iri biyu ne: Akwai na gaba ɗaya (wanda ya haɗa da mutum da abubuwa) da kuma na fayyatacce abu (wanda yake rarrabe mace da namiji). Misali:

 

Gaba ɗaya

Wa? Mutum                               Su wa?

Me? Abu                                    Su me da me?

Fayyatacce

         TILO                              JAM’I

Wanene?                        Su wanene?

 

 WAKILIN SUNA MADUBI


Wakilin suna ‘madubi’, shi kuma inuwa ce ta ‘suna’ ko wakilin suna katsattse. Shi ba ya zaman kansa. Duk inda aka faxe shi, to tabbata an riga an ambaci sunan nan ko wakilin suna katsattse da ya zo a farkon jumla. Misali:

Mai Magana            Tilo       Jam’i

Namiji                   kaina
      kanmu

Tamata                  kaina
      kanmu

-------                     ------             

Abokin Magana    Tilo           Jam’i

Namiji                   kanka
         kanku

Tamata                  kanki
          kanku

---------                   --------                      

Sha Magana          Tilo            Jam’i

Namiji                   kansa
          kansu

Tamata                  kanta
          kansu

---------                   ---------                     

Kowane misali aka xauka a nan, ba zai iya zaman kansa ba. Misali:

Ni kaina

Audu kansa

Shi kansa

Binta kanta

Ita kanta

Sifa

Sifa kalma ce ta nahawu wadda takan zo gabanin suna ko bayansa, don ta fayyace suna ta fuskar launi ko tsarin jiki da ya shafi girma ko ƙanƙanta da makamantan su. Tana bayyana jinsi da adadin suna. Misali:

 

  • Binta ta sayi farar
  • Jaka faraa Binta taa sayaa.
  • Farin gida ya ƙone.
  • Gida farii ya ƙone.


A wannan misalin na (a) da yake a sama an nuna cewa, sifa takan zauna kafin kalmar suna (Sn.), tare da harafin –n ko –r  a liƙe da ita don ta nuna cewa ta zo kafin suna. Haka abin yake a misalin na (c). A gurbin misali na biyu (b) da yake a sama kuwa, sifar tana bayan suna ne, kuma babu harafi a tare da ita, watau a ƙarshenta. Maimakon haka sai wasalinta na ƙarshe ya zama dogo don ya nuna cewa ajin sifar ya biyo bayan ajin suna ne. Haka kuma abin yake a misali na (d). ƙwayoyin ma’ana na –n da –r suke nuna jinsin da ajin sifar ya kasanta. Dole ne idan ƙwayar ma’ana ta –n ta zo tare da sifa ya kasance sunan namiji ne sifar ke fayyace wa, idan kuwa ƙwayar ma’ana ta –r ta zo tare da sifa to dole ne kalmar sunan da sifar ke fayyace wa ta zamana tamata. Misali:

 

1.     a) ƙaramin gidaa gidaa ƙaramii

 


ƙaramar goonaa                     goonaa ƙarama

1.     b) kooren ganyee             ganyee kooree

 


kooriyar ciyawaa                     ciyaawaa kooriyaa

 

1.     c) doogon riimii riimii doogoo

 


dooguwar giginyaa                       giginyaa dooguwaa

Sifa ma iri-iri ce kamar haka:

 

1.     Sifa Sassauƙa

 

2.     Sifa Nanatau

 

3.     Sifa ‘Yar aikatau


Sifa Sassauƙa

Wannan nau’i na sifa an san shi da tsari ne a sauƙaƙe. Sifar ta ƙunshi saiwar kalma da ɗafa-ƙeya. Misali:

baƙi                      baƙa baƙaƙe

shuɗi                    shuɗiya        shuɗaye

dogo                      doguwa        dogaye  d.s

Idan an lura za a fahimci saiwar kowace kalma da ɗafa-ƙeyarta. A kalmar baƙi , tushen kalmar shi ne ɗaƙ’ da ɗafin wasalin ‘i’ ko na ‘a’ sunan namiji ko ‘a’, a sunan tamata ko ‘aƙe’ a jam’i. kalmar shuɗi, tushen kalmar shi ne ‘shuɗ’ da ɗafin wasalin ‘-i’, ko ‘a’ sunan namiji ko wasalin ‘-iya’, a sunan tamace ko wasalin ‘–aye’ a suna jam’i. Kalmar dogo mai tushen kalma ɗog’ da ɗafin wasalin ‘-o’, a sunan namiji ko ɗafin wasalin ‘-uwa’, a sunan tamace ko ɗafin wasalin ‘–aye’, a suna jam’i.

 

Sifa Nanatau

Nau’in wannan sifa shi ne wanda ke da tsari irin na maimaicin kalmomi. Waɗanda ba su la’akari da jinsi, ko adadi balle jam’i.  Misali:

ƙungiya-ƙungiya                tsibi-tsibi

kashi-kashi                          buhu – buhu

launi-launi                            ganga- ganga d.s

 

Sifa ‘Yar Aikatau

Ita kuma wannan sifar kalmar aikatau ke samar da ita. Wato kowace sifa ‘yar aikatau ta samo asali ne daga kalmar aikatau. Misali:

Kalmar Aikatau Ajin sifa (namiji)         Ajin sifa (tamacce)  Ajin sifa (Jam’i)

Wanke     wankakke       wankakkiya        wankakku

Gina        ginanne           ginanniya            ginannu

Rubuta    rubatacce        rubutacciya           rubutattu d.s

 

Aikatau

Aikatau shi ma ya na ɗaya daga cikin rukunan nahuwun harshen Hausa. Aikatau kalma ce da ke ƙunshe da aikin da ke aukuwa a cikin jumla. Misali:

Wanke, dafa, ji, ci, d.s

Aikatan harshen Hausa ya kasu kashi biyu kamar haka:-

 

1.     Aikatau so-karɗau

2.     Aikatau ƙi-karɗau



Aikatau So-Karɗau

Aikatau so-karɗau shi ne kalmar aikatau da suna karɗau ke biyo bayanta a cikin jumla. Aikatau so-karɗau kalmar aikatau ce da take buƙatar wani abu ya biyo bayanta a cikin jumla. Abin da take son ya biyo bayan nata shi ne kalmar suna ko kalmar wakilin suna da kan zo a ƙarshen jumla don karɗar aikin da suna aikau ya aikata a cikin jumla. Misalan kalmomin aikatau so-karɗau su ne: kaama, maari, yanka, ɗeeboo, da duk wata kalmar aikatau da suna ko wakilin suna zai iya biyo bayanta. Misalin su a cikin jumla:

Bala yaa kaamakaaza.

Kande taa maari Audu.

Rabi taa yanka naama.

Yara sun ɗeeboo ruwa

 

Aikatau Ƙi-Karɗau

Shi kuma wannan nau’in akasin aikatau so-karɗau ne. Aikatau ƙi-karɗau, shi ba ya buƙatar zuwan suna karɗau a bayansa.  Misalan kalmomin aikatau ƙi-karɗau su ne kamar haka: gudu, dahu, bugu da makamantan kalmomin aikatau waɗanda in aka faɗe su a cikin jumla basa buƙatar wata kalma ta biyo bayansu. Ga Misalin kalmomin a cikin jumla.

Audu yaa gudu.

Abincin yaa dahu.

Shinkafa taa bugu.


Bayanau

Bayanau kalma ce da ake amfani da ita cikin jumla don ta ƙara bayani kan kalmar aikatau. Saboda a san lokaci ko wuri ko yanayin da suna aikau ya aikata aikin a cikin jumla. Misali:

 

1.     Baƙii sun iso ɗaazu.

 

2.     Matasaa sunaa zaune a kan dakali.

 

3.     Malam ya a shigo aji d gaggawaa.

 

4.     Akuu yana magana a

 

5.     Hakimii ya a ziyarci ɗalibai da safe.


 

Dangane da haka kuma a iya raba bayanau zuwa gida uku ta ɗangaren nazarinsa.

 

1.     Bayanau na yanayi

 

2.     Bayanau na wuri

 

3.     Bayanau na lokaci

 


 Bayanau Lokaci:-

Shi wannan kashi yana da nasa rassa guda uku (3) kamar haka:-

 

1.     Haɗadɗ’en Bayanau

 

2.     Nanatau/ruɗayyen Bayanau

 


iii.     ƙosasshen/tsanantau Bayanau

 

 

Haɗaɗɗen Bayanau:-

 


Shi ne mai nuna lokaci na ranakun da aka gudanar da aiki a cikin jumla. Misalan kalmomin wannan nau’in na bayanau su ne: Shekaranjiya, Bana, Jibi, Bara, Yau, Ban da gobe, Baɗi, Gobe: da dai makamantan waɗannan kalmomi masu nuna lokacin ranaku da yake ƙarin bayani kan kalmomin aikatau. Misalin su a cikin jumla:

(a) Musa yaa kaama kifi jiya.

(b) Rabi taa dafa naama shekaranjiya.

 
Nanatau/ruɗanyayyen bayanau

 


Irin wannan nau’in na riɗanyayye ko bayanau na nanatau yana ɗauke ne da wasu kalmomi na bayanau da ake iya maimaita su don a samar da shi. Ire-iren waɗannan kalmomin su ne; Jiya-jiya, Yanzu-yanzu, ɗazu-ɗazu, Gobe-gobe, ƙasa-ƙasa. Misalin su a cikin jumla:

 

  • Lawal yaa tafi kasuwa ɗazu-ɗazu.

 

  • Shehu yaa maari Hauwa yanzu-yanzu.

 


Tsanantau/ƙosasshen bayanau

Shi kuma wannan kashi yana tabbatar da aukuwar aikin da aka aikata a cikin jumla. Misalin kalmominsa  su ne: ainun, sarai, ƙwarai, sosai, garau da sauran kalmomi masu aikin ƙarin bayani kan kalmar aikatau masu nuna tabbatuwar aiki a cikin jumla.

Misalin su a cikin jumla.

 

  • Hafsa taa sari ƙafarta sosai.

 

  • Abdulmalik yaa sami kuɗi ƙwarai.

 

  • Ibrahim yaa warke



Bayanau Na Yanayi.

Bayanau na yanayi ana amfani da kalmominsa ne a cikin jumla don nuna yanayin da aiki ya gudana a cikin jumla. Ire-iren kalmomin da ake amfani da su waɗanda suke ƙarin bayani kan kalmomin aikatau don nuna yanayin da aiki ya gudana a cikin jumla sun haɗa da: da Sauri, a firgice, a fusace, da gaugawa. Misalin su a cikin jumla:

 

  • Musa yaa shigo aji da sauri.

 

  • Ayuba yaa tafi makaranta a firgice.

 

  • Jafar yaa zo a fusace.

 


 

Bayanau Na Wuri

Bayanau na wuri yana nuni ne da wurin da aikin cikin jumla ya faru. Ire-iren kalmomin da ake amfani da su, a irin wannan bayanau ɗin su ne; waje, ko’ina ƙasa, sama, a kan, ciki, kusa da sauran kalmomin da suke nuni da muhallin aukuwar aiki. Misalin su a cikin jumla:

 

  • Audu yaa faɗi ƙasa.

 

  • Adamu ya shiga cikin aji

2.2 NAHAWUN  TACIYA


Nazarin ilimin harsuna abu ne Wanda tun farkon bayyanarsa yake tafe da ra’ayoyin malamai da masana, Wanda kuma a cikin ra’ayoyin nan, kowane na ganin ga yadda ya kamata a bi a yi nazarin harshe. Da farko tun wajen ƙarni na biyar kafin bayyanar Annabi Isa (A.S), Wato 5th C.B.C. |ayan nan an sami ra’ayoyin da dama daga malamai manazarta harsuna. Daga cikin su akwai ra’ayoyi daga malamai masu nazarin harsunan Girkanci da Latinanci da sauran makamantarsu. Malamai na wannan lokaci duk sun nazarci harshe ne a ta farkin  nahawun gargajiya Wanda shi nahawun gargajiya ya ta’alaka ne kan wasu dokoki ko ƙa’idoji inda suke da (mabiya ra’ayin nahawun gargajiya) kuma suna umurta jama’a a kan yadda za su furta furuci ko kalma, kuma kada ka fadi wani abu (prescriptive grammer). A bisa wannan hujjar mabiya wannan hanya kuma sun bai wa harshen rubutu (written language) duk wani mahimmanci maimakon harshen baka (spokkrn language).

Ganin wannan hanya ta nazarin harshe sai a ka sake bin sawun wasu manazarta wadanda suka fito suna sha’awa ga nazarin wasu harsuna waɗanda ba nasu ba. Hanyar da suka bi don wannan nazarin ita ce hanyar da ake kira ilimin nazarin kwatanci da bin salsalar harsuna (comparative and historical linguistics). Wannan hanya ta kara fito da wani nazarí harsuna fili don samun daukaka. A cikin wannan hanya an sami malamai da dama irinsu, Sir Willian Jone, da Rusmus Rask, da Franz Bopp, da Jacob Grimm, da makammantarsu. Waɗannan malaman sun taimaka sosai ga wannan fanni. Nazarin harshe ta kan wannan hanya ya faro tun wajen shekarar 1787 zuwa 1833. A wannan tsakanin, malamai sun wallafa littattafai da makaloli da dama ɗangane da wasu harsuna.

Ganin yadda mabiya ra’ayoyin nahawun gargajiya suka yi nazarin harshe, ta kai ma an sake samun bayyanuwar wata hanya ko wani ra’ayi Wanda a ke kira Nahawun ƙwanƙwancewa, (structural grammer). Wannan ra’ayi, ‘structuralistic’  wato ‘yan ƙwanƙwancewa, a ganinsu ya kamata a yi nazarci harshe kansa ɗungurugum, a maimakon nazarin wasu ‘yan tsirarun harsuna (Jibril, 1985:p62). Ya kara da cewa sun karfafa tunaninsu ne a cikin ƙasidu da littattafai masu yawa da suka wallafa. Bayan haka sun danganta nazarin harshe da kimiyya,  ma’ana nazarin harshe ya shafi daidai da irin ci gaban da a ka samu a halin yanzu. Abubuwan nan suka taimaka wa wannan fanni  akwai malamai irinsu; De-saussue, da Leonard Bloomfield, da Franz Boaa, da Edwan Sapir da Fries. O.G, da Zelling S. Harris, da dai makammantarsu bayan haka (Jibril, 1985:p62). Ya bayyana cewa ƙwazo da bincike da waɗannan mutane ya kai ga samun nasarar komawa kan abin da an ke furtawa a maimakon tsohuwar hanyar nan da aka fi rinjaya na a maida hankali a kan duk wani abu da a ka rubuta mahimmanci. Wannan gagarumin canjin ya auku ne a farkon ƙarni na ashirin ne (ƙ 20th C).

Hr-ila-yau  a na cikn wannan halin sai wasu malamai suka fito da wani ra’ayinsu akan nazarin harshe can kwatsam! Sai wani Ba’amerike (Bature), mai suna Noam Chomsky. Chomsky ya fito da sabon ra’ayi game da nazarin harshe,  inda ya nuna bai kamata ba a riƙa nazarin harshe ta hanyar nahawun gargajiya ko nahawun ƙwanƙwancewa ba. Wanna bayani da Chomsky ya yi cikin fagen nazarin harsuna ya samu ɗaukaka fiye da sauran malamai manazarta harsuna na wannan lokacin. Hasali ma ta kai kowa ya fito ƙokri ya ke ya kwatanta kansa da Chomsky, ko kuma ya samo wani abin kushewa daga gares hi (Chomsky). Chomsky ya bayyana ne a shekarar 1950, kuma a 1957, ya wallafa wani littafi mai suna “styntsctic structure”Wannan littafin ya kara fitowa da Chomsky fili a idon duniya musamman a wajen ɗalibai da malamai manazarta harsuna. A cikin wannan littafin ne aka samu wani sabon ra’ayi  da ya kira, “Nahawun Taciya” (Transformational Grammer).  Bayan haka bisa la’akari da irin halin ƙaƙa-ni-k-yi da nazarin harshe ya shiga a shekara 1950 .  A wannan tsakanin sai da ta kai an sami kusan shekaru ashirin babu wani canji na ku-zo-a-gani  da aka samu dangane da nazarin harshe. Malaman da suka cancanci su kawo wani sabon abu cikin nazarin ilimin harsuna, sai kuma kowanne daga cikinsu ya kasance ya na da ra’ayinsa na son rai, da zargin juna a tsakaninsu.  |ullowar  Chomsky ya sa an samu gagarumin canji Wanda a ke kira “juyin-juya-hali” a cikin a cikin nazarin ilimin harsuna, bayan haka nahawun taciya ba wani ra’ayi ba ne da Chomsky ya ƙirƙiro don ya kushe hanyoyin da a ke bi  wajen nazarin Nahawun taciya ko nahawun ƙwanƙwancewa.  Nahawun taciya hanya ce da Chomsky ya zo da shi ne don daidaita nazarin harshe ya ta bai ɗaya kuma daidai da zamani. Bayan haka Chomsky ya bayyana wasu hanyoyi da yake ganin za a samu gyra ga wasu ra’ayoyi na malamai waɗanda suka gabata, kuma waɗanda a ganinsa waɗannan hanyoyi masu rauni ne kuma kuma wasu daga cikinsu marasa makama.

Dalilan da suka ƙara ƙarfafa wa Chomsky  ƙwarin guiwa har ya fito da wanna ra’ayi, Wanda ya kira “Nahawun taciya” a na iya ganinsu  a cikin nazarce-nazarcen malamai na wannan ƙarnin da na wasu malaman da suka gabata. Daga cikin rubuce-rubucen da Zelling, S.  Harris  ya  yi, sun ƙarfafa wa Chomsky tunaninsa. Haka kuma ayyukan  Jacobson  a koda yaushe  yakan yi tunanin tsarin sauti na bai ɗaya, ko kuma na gama duniya (phonological universal). Ya  yarda cewa bambanci da ke akwai na tsarin furuci a cikin harsuna na duniya bambanci ne wanda malamai suka karkata a kan ra’ayinsu. Shi ma, De-saussue ya na cikin waɗanda suka ƙarfafa tunanin Chomsky. De–saussure kuma shi ma ya nuna cewa gina jumla ba ya cikin wani yanki na tsarin harshe kamar yadda ya bayyana kamar haka” Harhaɗa kalmomi zuwa jumloli  abu ne wanda  kowanne ɗan asali mai magana da harshe kan yi a lokaci na musamman, ba abu wanda harshe kan yi gaban ɗaya ba.” Saboda haka irin wannan rashin yarda da wasu abubuwa game da harshe da wasu malamai suka nuna, shi ya ƙara ƙarfafa tunanin Chomsky wanda ya kai shi ga fitowa da wannan ra’ayi nasa wanda ya yi wa suna da “Nahawun taciya”.

 

2.3 MATSAYIN AZUZUWAN KALMOMIACIKINJUMLAR HAUSA


A nan an dubi jumlar Hausa ne, da nufin fito da ire – irenta, don sanin yadda fasalolinta suke a fagen nazari. A nahawun harshen Hausa a na da ire-iren jumla guda huɗu ta fuskar zamantakewar azuzuwan kalmomin cikinta, waɗanda masanan zamani suka tantance su a fagen nazari. Waɗannan jumlolin sun bambanta da rabon farko da a ka sani, wato waɗanda masana suka samar da su ta fuskar yanayin zubinsu. Wato kaso uku da masanan farko suka aiwatar, kason na masanan farko da suka gudanar ya na da ire-iren jumla guda uku waɗanda suka haɗa da: sassauƙar jumla da sarƙaƙƙiya da harɗadɗ’iya. Su kuma, masanan na ilimin ginin jumlar harshen Hausa na zamani sai suka sake duba wannan rabon suka fito da ire-iren jumloli har guda huɗu kamar haka:

(i) Sassauƙar Jumla.

(ii) Jumlar Tambaya.

(iii) Jumlar Umarni.

(iv) Jumlar Korewa.

Waɗannan jumlolin su masanan zamani suka tantance don sama wa ɗalibai da manazarta ilimin ginin jumla sauƙin nazarin jumla da sassanta.Yanzu za a ɗauki kowace jumla domin a nuna yadda tsarinta yake a fagen nazari.

Sassauƙar Jumlar Hausa

Sassauƙar jumla ta ƙunshi yankuna biyu manya. Bisa ra’ayin masanan farko, sassauƙar jumlar Hausa tana da  yankin suna (YSn) da yankin aiki (YA). Amma a ra’ayoyin masanan zamani an sami bambancin ra’ayi dangane da yankin aiki. Bisa fahimtar masanan zamani suna ganin cewa yankin da masanan farko suka kira yankin aiki, sunan bai dace da shi ba, saboda yankin ya na iya kasancewa ya ɗauki wasu zmahimman azuzuwan kalmomi na daban bayan ajin kalmar aikatau. Sanin haka sai suka kira shi da yankin  abin da aka faɗi a game da suna (YAfgSn) maimakon yankin aiki (YA). Wannan batu a na iya taƙaita shi kamar haka:

J                    Suna aikau    +  Abin da aka faɗi a game da suna

Wannan yanki na abin da aka faɗi a game da suna (YAfgSn) ya ƙunshi kalmar aikatau da kalmar karɗau (Aikatau + Karɗau) sannan ana iya samun wasu azuzuwan kalmomin su fito a yankin. Ana iya samun kalmar bayanau da sifa da harafi.

Babban abin da ake son sassauƙar jumla ta ƙunsa a matsayin ginshiƙan tubalan gina ta su ne, kalmar suna aikau ta zo a farkon jumlar, sai kalmar aikatau ta fito a tsakiyar jumlar sannan kalmar suna karɗau ta zo a ƙarshen jumlar. Wannan tsarin shi zai ba da fasalin nan na S.A.K a matsayin tsarin gudanar da sassan sassauƙar jumla. Irin wannan gundarin tsarin na S.A.K shi ne ake samu a harshen Ingilishi da wasu harsunan masu ɗimbin yawa. Wannan tsarin na S.A.K. shi ake kira da S.V.O a harshen Ingilishi.

Ga Misali:

 

Hausa                                                                                                  Ingilishi

(a)    Bala     ci   abinci.                                                           (b)        John       eat     food.

Sn
Aikau  Aik   Snkaɗ                                                                     Subject noun   Verb   Object noun

 

1.     A.     K.                                                                   S.           V.       O.

 


Jumlar Hausa tana buƙatar mafayyaciya (Maf) bayyananne, wanda zai fayyace suna aikau ta fuskar jinsi da adadi. Wannan ƙwayar ma’anar ita ce, “ya” a wannan misalin na (a).

Aikatau na jumlar “ci” ya na buƙatar a fayyace shi ta fuskar lokaci da taƙi (Lokt). Ƙwayar ma’ana da ke gudanar da wannan aikin ita  ce, “a”. Ƙwayar ma’ana  “a” ana kiranta da lokataƙ (Lokt) domin tana fayyace aikatau ne dangane da lokacin da aka aikata aiki a cikin jumla da kuma kammaluwar aiki ko rashin kammaluwar aikin.Shi ya sa jumlar ta koma kamar haka:

Sassauƙar Jumlar Hausa:

 

 

  • Bala      ya      a                  ci

 


 

Sn
Aikau Maf.  Lokt       Aik      SnKarɗa

S                                 A           K

 

Ga hanyar nazarin li’irabi a zamanance. Jumlar Hausa tana ƙunshe da waɗannan azuzuwan kalmomin kamar haka:

J                                     YSn + YAfgSn

YAfgSn                              KN + YA

YA                                        Aik, YSn

KN                                        Maf, Lokat

YSn                                        Sn

Sn                                          Bala

Maf                                        ya

Lokat                                       -a

Aikatau                                    ci

Sn                                          abinci

 

 

J

 

 

YSn         YAfgSn

Sn         KN               YA

 

Maf   Lokat    Aik              Sn

 

Bala     ya        -a          ci           abinci

 

Sassauƙar jumlar Hausa tana ɗauke da ginshiƙai guda uku ne ƙwarara. Ginshiƙan su ne: Suna aikau (Sn
aik), da aikatau (Aik), sai suna karɗau (Kƙb).

 

Jumlar Korewa

Jumlar Hausa ta korewa tana ɗauke da wasu kalmomi na musamman da harshen ya tanada domin yin sharaɗi da su, kafin a gina ita wannan jumla ta amsu. Sannan da waɗannan kalmomin ne za a iya nuna irin korewar zance da aka samu a cikin jumlar. Kalmomin ana amfani da su ne wajen nuna korewar zance a cikin jumla ta hanyar bin wasu ƙa’idoji da aka gindiya na amfani da su don nuna yadda korewar ta auku. Shin korewar ta jumlar ce gaba ɗaya, ko korewar wani ɗangare ne na zance a cikin jumlar. Misalin sassan jumlar korewa shi ne:

Rabi baa ta tafi kasuwa ba.

Masana sun fito da tsarin kalmomin korewa da fasalin da ake amfani da su a cikin jumla, domin nuna irin korewar da aka samu. Ra’ayi ya bambanta a wajen bayani dangane da korewa. Masana irin su Kraft C. H. da Kirk – Greene (1973:37-40 da 61- 64) da Galadanci (1976:77- 83) da Skinner (1977:77 – 78), da Zaria (1981:82 - 84) da Bagari (1986), duk sun bayyana korewa kaɗai ba tare da sun nuna korewar yanki ce ko ta jumla baki-ɗaya ba. Yalwa (1995) da Newman (2000) da  Amfani (2006) da Muhammad (2010) da kuma Sani (2010)  da Umar (2012) duk sun yi bayani kan cewa ana samun korewa iri biyu, da ta yankin jumla da ta jumla gaba ɗaya. Masana sun yi tarayya dangane da tsarin kalmomin korewar. Ga yadda suke tare da misalan su :-

 

(i) Ba (bàà-----bá)     =   Bàà Ali ya sayaa bá.

(ii) Ba (bà-----bá)        =    Rabi bà ta tafi makaranta bá.

(iii) Ba (báá----)          =   Báá kuɗi a banki.

(iv) Ba (bâ….)                 = agwagwa bâ ta tashi sama sosai.

(v) Ba (báábù----)      =   Báábù ruwa a randa.

(vi) Ba-i (bà-i… bà)    = bài dace a hana bara bá.

(vii) Káádà/Kâr------       = Káádà ka a tafi. Ko kâr ka a tafi.

Abin lura a nan shi ne, fasalin ginin jumlar korewa yana ƙunshe da wasu mahimman kalmomi da aka tanada don amfani da su wajen nuna korewa a jumlar Hausa.

Jumlar Tambaya

Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake ginawa don a yi tambaya. A Hausa ana da jumlar tambaya  kamar haka:

(a) Yàushéé Rabi za ta tafi?

(b) Wàà Isaa ya a mààráá?

(c)  Mèè Musa ya káamaà?

Hausa tana da tsarin da take bi wajen ginin jumlar tambaya. Hanyar da Hausa take bi wajen ginin jumlar tambaya ita ce, dole ne “kalmar tambaya,” ta zo a farkon jumla. Haka kuma dole ne alamar tambaya ta zo a ƙarshen jumla. Amma ana iya samun wani tsarin da Hausa take amfani da shi a maganganun yau da kullum. Wasu daga cikin kalmomin tambaya da Hausa take amfani da su wajen ginin jumlar tambaya su ne;

(i) Iná?  = Ina Maryam ta a tafi?

(ii) Wàà?     = Wàà za a aika?

(iii) Yàushéé?  = Yàushéé za a dawo aiki?

(iv)  Ƙàƙáá?    =   Ƙàƙáá za a yi?

(v)  Yáyáá?  = Yáyáá Audu ya a faɗi jarabawa?

(vi)   Mèè?     =   Mèè Ali ya a saya?

Masanan da suka aminta da wannan tsarin sun haɗa da; Kraft C. H. da Kirk – Greene (1973) da Skinner (1977) da Zaria (1981) da Jinju (1986) da Bagari (1986) da Yalwa (1995) da Amfani (2005) Muhammad (2010) Umar (2012). Duk sun yi bayani game da wannan tsarin na jumlar tambaya.

 

Jumlar Umarni

Jumlar umarni tana ɗauke da wani tsari da ya bambanta ta da sauran jumloli da ake da su a Hausa. Jumlar umarni takan zo da kalma ɗaya rak, a matsayin jumla cikakkiya, mai ma’ana. Kuma kalmar da take zuwa da ita, ita ce kalmar aikatau (Aik).  Ga misalin jumlar umurni;

(a) Tashi!

(b) Rubuta!

Abin lura a nan shi ne jumlar umarni koyaushe takan ƙare da alamar motsin rai. Kamar  yadda aka nuna, jumlar umarni cikakkiyar jumla ce, sai dai kuma ta ƙunshi kalma ɗaya rak.

Masana irin su, Kraft da Kirk – Greene (1973) da Skinner (1977) da Zaria (1981) da Bagari (1986) da Jinju (1986) da Yalwa (1995) da Newman (2000) da Jaggar (2001) da Amfani (2006) da kuma Umar (2012) duk sun yarda da cewa wannan bayanin da aka gabatar shi ne tsarin samar da jumlar umarni a Hausa

 

2.4 NAƊEWA


A babi na biyu shimfiɗa ce ta zo a matsayin gabatarwa, bayan nan sai bincike ya yi waiwayen azuzuwan kalmomi na harshen Hausa. Inda ya bayyanansu tare da kawo su daki-daki, wanda daga bisani nahawun taciya ya biyo baya tare da ra’ayin masana ilimin taciya da nahawun harshen Hausa. Matsayin azuzuwan kalmomi a cikin jumla ta zo a gaba wanda a nan ne a ka yi bayanan gamsassahe game dajumlar Hausa. Wanda da ma nazarin shi ne hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Post a Comment

0 Comments