Dabarun koyar da Harshe

    Wannan rubutu yana ɗauke da cikakken bayani dangane da dabarun koyar da harshe.

    Dabarun koyar da Harshe
    Kabiru Abdullahi
    Muhammad Yusuf
    Farida Jafar Dango
    Farida Musa
    Samira Muhammad

    Makaranta


    GABATARWA

    Tsarin koyarwa aiki ne na hulɗa tsakanin malami da ɗalibi don a kawo canje-canje cikin abin da yara suka sani ko, suka iya ko, suka yarda da shi, malami shi ne mai buɗe hulɗa tsakaninsa da ɗalibi, watau shi ne mafarin saƙo. Malami shi ke fara yin bayani ko, gwaji ko, nuni don yaro ya gani ko, yaji ko kuma, don ya kwaikwaya. Haka kuma ɗalibi zai riƙa miƙawa malami irin nasa saƙon ta hanyar bin ummurnin malamin. Misali in malami ya ce duba nan ya duba, rubuta wannan ya rubuta, jinjina wannan ya jinjina da dai sauransu.

    Wajibine tsarin koyarwa ya shafi halin mutuntakar masu yinsa. Misali saduwar malami da ɗalibai da kuma yaro da yaro 'yan uwan juna. Saboda haka tsarin koyarwa wani abu ne mai buƙatar ƙwarewa da kuma dabarori kamar sauran sana'o'i. A nan malami na nuna ƙwarewarsa idan ya zo tsara darasinsa da kuma wajen koyarwarsa. Saboda haka, domin samun ingantacciyar koyarwa dole malami ya zauna ya yi tunanin yadda zai tafiyar da horarwarsa.

    SHIRYA DARASI

    Muhimman abubuwan da malami zai yi wajen tsara koyarwa  sune kamar haka:

    Zana jaddawalin makarantar.

    Karɓar manhaja domin amfani da ita wajen shirin mako-mako.

    Bincikar littafan da suka shafi fannin koyarwa.

    Karɓar kayan aiki da ƙirƙiro nazarin irin matallafa koyarwa da
    zai yi amfani da su.

    Shirya shirin mako-mako.     

    Shirya tsarin darasi.

    Neman wurin zama da wurin kwana idan hali ya nuna.

    Hulɗa tsakanin hukumar makarantar ga malami da mutanen gari.
    SHIRIN MAKO-MAKO

    Shirin mako-mako, tsari ne na ƙunshiya ko batutuwan da ake son koyarwa bayan wani ɗan lokaci. Haka kuma wannan ya na nuna ɓangaren manhaja da za a koyar a kowanne ɗan lokaci.

    Ana iya shirya shirin mako-mako a kan zango-zango, ko akan wata-wata ko, akan sati-sati.

    Shin mako-mako yana taimako wajen tantance irin tsarin darasi da malami ya kamata ya yi. Zai fi kyau malami ya shirya shirin mako-makonsa akan zango-zango kamar a farkon zango, wato na sati goma sha uku (13). dangane da yawan zango na makaranta.

     

    MAHIMMAN  ABUBUWAN DA SHIRIN MAKO-MAKO YA ƘUNSA

    Dangane  da mahimman abubuwan  da  shirin mako-mako ya ƙunsa kuwa, abubuwa goma ne ko tara ko kuma guda takwas a wani ƙaulin. Ga mahimman abubuwan kamar haka:

     

    Mako ƙunsa

    Darasi batu

    Ƙunshiya

    Manufa

    Matallafa koyarwa

    Aikin malami

    Aikin yara

    Aunawa

    Jawabi

    YADDA AKE SHIRYA SHIRIN MAKO-MAKO

    Shirin mako-mako ana shirya shi ne a cikin littafi ko wata takarda ta musamman. Bayanin kowanne ɗaya daga cikin abin da yaƙumsa ga shi kamar haka:

    Mako: A nan ne za'a rubuta tsarin lambobin mako tun daga na ɗaya har zuwa na ƙarshe. Haka kuma mako da darasi a shirin mako-mako duk abu guda ne, wato anan ma in darasi na ɗaya ko na biyu koma na nawa ne sai malami ya rubuta. An fi baiwa mako fifiko, a wajen shirin mako-mako na Hausa.

    Batu: A nan kuma ana nufin ire-iren batutuwan da suka fito daga manhaja da ya kamata malami ya koyar.   Misali: Tatsuniya da dai sauran makamantansu.

    Ƙunshiya: A nan abin da za a gani a ƙarƙashin wannan shi ne duk abin da batuya ƙumsa. Misali:

    a- Ma'anar tatsuniya

    b- Ire-iren tatsuniya

    c- Kayancikin tatsuniya, da daisauransu.

    Manufa: A ƙarƙashin manufa ne malami zai rubuta abin da yayi ƙudurin cimma wa. Ma’ana abubuwan da yake son yara su sani ko su ƙaru da su ko kuma su yi sharhi akan gaskiyar zance ko rashin gaskiyar zance a ƙarshen koyarwarsa na ɗan wannan lokaci.

    Matallafa Koyarwa: Kayayyaki ne da malami zai yi amfani da su wajen koyarwarsa, watau kayan koyo da koyarwa kamar irin kayan karatu da rubutu, da kayayyaki ko na’urori nagani da naji da, zanen hotuna, taswira da dai makamantansu da malami zai yi amfani da su wajen koyarwa duk anan ne zai rubutarsu.

    Aikin Malami: A nan ne malami zai rubuta ire-iren ayukkan da zai yi cikin aji a lokakcin koyarwarsa. Misali: bada bayanai da misallai, yin tambayoyi da kuma amsa tambayoyi da yin gwaje-gwaje da rubuce d.s.

    Aikin Yara: A nan malami zai rubuta irin ayyukan da yake buƙatar ɗalibai su yi a lokacin horarwarsa. Misali, amsa tambayoyin malami tambayoyi da yin zane-zane da gwaje-gwaje da rubuce-rubuce da dai makamantansu.

    Aunawa: Hanyoyi ne da malami zai bi domin gwada ɗalibansa. Wannan shi zai bi domin fahimtar an ci nasarar gane darasin ko kuma a’a.

    Jawabi: A nan nufin sharhin da malami zai yi game da wannan batu da ya koyar, wato in da malami zai ce an fahimci darasin ko kuma an sami matsala. Watau inda ya aje da kuma inda zai tashi.

    AMFANI DA KUMA MAHIMMANCIN SHIRIN MAKO-MAKO

                Amfani da kuma muhimmancin shirin mako-mako musamman a cikin koyarwa abu ne da ya fi gaban nanata. Wasu daga cikin amfani da mahimmancinsa sun haɗa da:

    Yana taimakawa malami wajen tattaunawa da kuma fahimtar matsalolin wani sashen na manhaja domin warwarewa.

    Yana taimakawa masu duba makarantu da ke zagayawa ba da shawarwari da canje-canje inda suka dace.

    Haka ma shirin mako-mako wata madogara ce ga malami da ke iya bukatar gyara da sauye-sauye duk lokacin da ake bukatar yin haka.

    Yana sa a yi aikin koyarwa cikin tsari a tsanake.

    Shirin mako-mako zai kumshi yawan Hissa da ke ga kowanne batu a cikin sati. Don haka yana nuna yawa da tsawon kowanne darasi.

     

     

    TSARIN DARASI

                Wannan wani tsararren rubutu ne da ake rubutwa a bisa waɗansu makatai domin zama jagora ga malami a lokacin da yake horarwa. Wato shi ne mataki na ƙarshe gabatar da darasi a cikin aji.. malami na shirya shi ga kowanne darasi domin gudanar da aikin koyarwa daki-daki cikin tsari.

    AMFANIN TSARIN DARASI

    Tsarin darasi jagora ne ga malami wajen gudanar da darasinsa cikin tsari kuma cikin tsanaki.

    Tsarin darasi yana taimakawa malami gabatar da darasinsa cikin sauƙi.

    Tsarin darasi tamkar tunasarwa ne ga malami a kan abubuwan da ya shirya zai koyar ga wannan darasin.

    Ya na taimakawa malami yin tsarin mataki-mataki watau, daga abin da aka sani zuwa wanda ba a sani ba (daga abubuwa masu sauki zuwa ga masu wuya).

    Tsarin darasi yana taimakawa malami ya samu sauƙin shirya darasinsa dai-dai da lokacin da aka bashi hissarsa watau dai-dai tsari dai-dai lokaci.

    Haka kuma tsarin darasi ya na taimakawa shugabannin makarantu da masu dubawa wajen ba da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin karantarwa.

    Bugu da ƙari tsarin darasi yana taimakawa ɗalibai fahimtar darasi cikin sauƙi.

    MAHIMMAN ABUBUWAN DA TSARIN DARASI YA ƘUNSA

    Mahimman abubuwa da tsarin darasi ya ƙumsa guda goma sha shida (16) ne, kamar haka:

    Sunan makaranta

    Aji

    Fanin ilmi

    Batu

    Kwanan wata

    Lokaci

    Jinsi

    Yawan yara

    Shekarun yara

    Manufar darasi

    Matallafa koyarwa

    Ilmin da ya gabata

    Gabatarwa

    Gudanarwa

    Kammalawa

    Aunawa

    BAYANI AKAN YADDA AKE ZANA TSARIN DARASI

    SUNAN MAKARANTA: Nan ne malami zai rubuta sunan makarantar da ya ke gudanar da darasinsa. Misali FCET model primary school Gusau ko, JSS Gusau da dai sauransu.

    AJI/SUNAN AJI: Anan ne malami zai rubuta sunan ajin da zai karantar. Misali: aji uku 3A ko JSS 1B da dai sauransu.

    FANNIN ILMI: Nan ne malami zai rubuta sunan fanin ilmi da yake karantarwa missali: Hausa ko, harshen Hausa da dai sauransu.

    BATU: wannan na nufin abin da malami zai koya wa yara a cikin wannan hissar. Misali sana’o’in Hausawa na gargajiya ko, almara ko, tatsuniya da dai makamantansu.

    KWANAN WATA: Nan inda malami zai rubuta kwanan watan ranar nan da zai koyar da wannan batun cikin aji. Misali 27/03/2019.

    LOKACI: A wannan wurin malami zai faɗi/rubuta tsawon lokacin wannan hissar da ta ƙunsa, watau lokacin da za yi wajen koyar da wannan darasin. Misali minti arba’in (40) ko talatin da biyar (35).

    JINSI: Nan ne malami zai faɗi irin jinsin da ajin ya kunsa. Misali, maza zalla ko, mata zalla ko kuma, maza da mata.

    YAWAN YARA: A wannan ɓangaren ne malami zai rubuta yawan ko adadinn ɗaliban da wannan aji ya ƙunsa misali yara arba’in da biyar (45) ko, talatin da biyar (35) da dai makamantansu.

    SHEKARUN YARA: wannan wuri ne malami zai rubuta shekarun yaran ajin da zai karantar. Misali ƴan aji ɗaya na furamare shekarun su shidda ne (6) da sauransu.

    MANUFAR DARASI: dangane da manufa a cikin tsarin darasi kuwa, a iya cewa keɓantattar manufa ce watau ‘Specific objective/aims’ a turance. Watau ƙudirin da ake so a cimma a ƙarshen wannan darasin. Misali malami na iya rubuta manufar darasinsa kamar haka: A ƙarshen wannan darasi ɗalibai za su iya kawo ma’anar sana’o’in Hausawa na gargajiya da ire-irensu, ko ma’anar tatsuniya da kayan cikin tatsuniya da dai sauransu.

    MATALLAFA KOYARWA: Waɗannan sune irin kayayyakin da malami zai yi amfani dasu wajen isar da saƙonsa zuwa ga ɗalibai, watau kayan da zai yi amfani da su wajen koya wa yara a cikin aji. Misali, allo, da alli da, kwalaye da, gwangwanaye da dai sauransu.

    ILMIN DA YAGABATA: Nan ne malami zai rubuta irin masaniyar da ɗalibai suke da ita game da batun da zai koyar da su ko wani abu makamancin wannan. Misali: Ɗalibai na da masaniya akan abu kaza (ma’anar tatsuniya) da dai makamantansu.

    GABATARWA: Abin nufi anan shi ne hanyoyi da malami zai bi domin jawo hankalin ɗalibai zuwa ga darasin da zai koyar. Malami na iya gabatar da darasinsa ta hanyoyin da ya ga sun dace ko sun fi dacewa wajen jawo hankali ko ra’ayin ɗalibansa. Misali: malami ya yi tambayoyi akan abin da ya koyar ga darasin da ya gabata, ko ‘yar shammata ga wani yaro cikin ajin ilmantarwa da ban dariya, ko ƴar shammata ga wani yaro cikin ajin domin a yi dariya ko, kuma malami ya gabatar da matallafa koyarwa da dai sauransu.

    GUDANARWA: Wannan bagiren ana Magana ne a kan irin matakan da malami zai bi ɗaya bayan ɗaya domin tafiyar da darasinsa, watau mataki-mataki har zuwa ƙarshen darasin. A nan ana buƙatar malami ya fara daga abu mai sauki zuwa ga wanda ba a sani ba. Haka kuma ana son malami ya yi la’akari da hanyoyin gudanarwa watau dabarun koyarwa.

    KAMMALAWA: A nan malami zai iya kammala darasinsa ta hanyar yin takaitaccen bayani akan abubuwan da ya koyar, ko fidda mahimman abubuwan da darasinsa ya ƙunsa domin a nanatasu ko kuma a yi ƙarin bayani akan su.

    AUNAWA: Nan hanyoyin da malami zai bi domin sanin ko abin da ya koyar an fahimta ko ba a fahimta ba. Misali: malami ya baiwa ɗalibai aiki ko, jinga ko, kwangila na aji gaba ɗaya, ko na wani ɗan lokaci mai tsawo domin fahimtar ko ɗalibai sun gane abin da aka koyar dasu ko ma ba su gane ba don a gyara su.

    MANUFA (AIMS AND OBJECTIVE)

    Ita ce gurace-gurace (aspirations) na irin abubuwan da ake son ɗalibai su sani ko. su iya ko, su yarda dasu a cikin wani lokaci ayyananne  (specified).

    Manufa ce ke bayyana irin sakamakon da ake nema na koyarwa. kuma nan ne ake ganin irin shedar ko an ci nasara ko ba a ci nasara ba.

    Saboda haka, ana iya cewa manufa ta kasu zuwa gida uku (3) dangane da aikin koyarwa. Watau akwai manufa ta cikin manhaja (syllabus objective), akwai kuma manufa ta cikin shirin mako-mako (scheme of work objective”), da kuma manufa ta cikin darasi wadda aka fi sani da manufar darasi (lesson plan objective). A. MANUFA TA CIKIN MANHAJA (SYLLABUS OBJECTIVE)

    Irin wannan manufa tana yin jam'i ne na ilahirin sakamakon da ake nema bayan an gama koyar da wani fanni, bayan lokaci mai tsawo. Don haka irin wannan manufa na da wuyar kamantawa kuma tana buƙatar a warwareta dalla-dalla don a sami abin kamawa, misali: a koyawa ɗalibai dabarun sadarwa da harshen Hausa, da kuma hanyoyin sarrafa harshen d.s.

    MANUFA TA CIKIN SHIRIN MAKO-MAKO (SCHEME OF WORK OBJECTIVE)

    Irin wannan manufa ita ce ta biyu a wannan tsarin. Malami zai ciro ta daga cikin manhaja ya faɗaɗaata ya kuma rarrabata dangane da aikin da zai yi na mako-mako, Misali abubawan da malami keson yara su sani ko su ƙaru da su daga batun ko batutuwan da suka fito daga cikin ƙunshiya, da dai makamantansu.

    MANUFAR DARASI (LESSON PLAN'S OBJECTIVE)

    Irin wannan manufa it ce malami ke rubutawa a cikin kowanne darasi. Ana ciro tane daga wadda aka tsara cikin shirin mako-mako, bayan an kara rairayeta an fidda ma’anarta a fili wadda kuma kowa zai iya ganinta da idanunsa cewa lallai a ƙarshen darasin yara sun kawo wani abu a fage kaza, ko sun naƙalci abubuwa kaza, ko kuma ra’ayin yara ya canza daga kaza zuwa kaza.

          Haka kuma, ita wannan manufa ta faɗa akan ɗalibai ne ba akan malami ba. Za a iya kuma karkasa manufar darasi zuwa gida uku (3) kamar haka: sani, da gwaninta da, kuma ra’ayi. Yanzu kuma ga waɗannan misallai domin kawai a ƙara fahimtar irin manufar darasin da ta kamata da kowanne batu da za a koyar. Misali.

    Sani (Cognitive Domain): Dangane da wannan malami zai iya rubuta manufar darasi dalibai na iya kawo/ ko kuma a ƙarshen wannan darasi ɗalibai na iya bada bayani akan/ ko, a ƙarshen wannan darasi ɗalibai na iya lissafa abu, kaza/ ko kuma, a ƙarshen wannan darasi ɗalibai na iya ƙarfafa abu kaza da dai sauransu,

    Gwaninta (Psychomotor Domain): A nan kuma malami na iya rubuta manufar darasinsa kamar haka: misali: A ƙarshen wannan darasi ɗalibai zasu karanata/ ko, zasu tsallaka kaza/ ko kuma a ƙarshen wannan darasi ɗalibai zasu gwada. Da dai sauransu.

    Ra’ayi (Affective Domain): A wannan ɓangaren kuma malami zai rubuta manufar darasinsa misali: kamar haka: A wannan darasi ɗalibai za su ƙi, abu kaza da kaza, ko a ƙarshen wannan darasi ɗalibai za su yarda da abu kaza da kaza ko kuma a ƙarshen wannan darasi ɗalibai za su nuna rashin yardarsu da abu kaza da kaza da dai sauransu.

    BAYANI KAN YADDA ZA A ƘIRƘIRI MATALLAFA KOYARWA (EXPLANATION ON HOW TO CREATE TEACHING AIDS)

                Kamar dai yadda bayani ya gabata a kan matallafa koyarwa cikin shirin mako-mako da kuma tsarin darasi. A nan kuma za mu yi managa ne akan yadda malami zai iya ƙirkiro matallafa koyo idan ba’a samu na anihi ba. Duk kayan da malami ke buƙata mafi yawanci zai nemi su ne a wannan wuri da yake zaune, ba lalle ne sai waɗanda aka yi ba, domin biyan wannan buƙata da kuma kaucewa tutar babu.

                Ƙwararren malami ya kamata ya yi ƙoƙarin ƙirƙiro nasa kayan matallafa koyarwa domin tsadar da ke ga mafi yawancinsu. Misali malami na iya bin waɗannan hanyoyin domin ƙirƙiro nasa kayan kamar haka:

    Gam: Domin buƙatar harhaɗa abubuwa, malami na iya yin gam, idan ya haɗa garin rogo da garin masara da ruwa, sai ayi ta jujjuyasu har su yi ɗauri da kabri, fiye da kamu. Gam ya samu. Haka kuma ana iya samun gam idan aka samo guntayen kayan roba aka hada da man fetur ana jujjuyawa da sanda har sai ya yi ɗauri sosai. Gam dai, yana da amfani wajen harhaɗa abubawa da dama. Misali takarda, da kyallaye da dai sauransu. Malami na iya amfani da jirai (Ƙaro) na itatuwa ya samar da gam.

    Kayan kwaɓe-kwaɓe: Domin gina abubuwan da malami ke son yi, malami na iya haɗa kayan kwaɓe-kwaɓe, misali: ta hanyar amfani da rogo da masara, sai a haɗa da madara da gishiri da kuma ruwa ana sa wuta sannu-sannu har sai ya yi kabri bayan ya huce sai a gina abin da ake son ginawa.

    Hanyar samun hoto: idan malami na son hoto ko zane, amma bai iya zanawa sai ya samo kyalle ko takarda mai haske da zai iya azata bisa hoton, ta haka sai a fidda hoton abun tamkar shi ne, a manna shi ga kwali a liƙa ga allo yara su gani.

    Hanyoyin samar da sauran ƙananan kayan koyo: Ana iya yin abubuwa da laka ko, katako ko, kayan roba da takardu ko, Karen ashana domin yin irinsu, dai sauransu.

    Haka kuma ana yanyanko guntayen hotuna daga cikin jaridu da kalandu domin malam ya yi wurin ajiye hotuna (photo album).

    Bugu da ƙari malami na iya samar da mota ta hanyar amfani da kwalin suga da kuma ƙwanƙwalati a zaman tayoyi da zare na ja. Wannan ga yara ai ta zama mota. Mafi yawanci, kayan da ake zubarwa ajuji, suna da amfani wajen aikin koyarwa a matsayin matallafa koywarwa.

    Har ila yau dai, ana samar da abubuwan koyo da yawa ta hanyar amfani da wuƙa da reza, zarto, da kuma almarkashi. Ta haka malami na iya yin irin su; rula da alƙalami da burushi da kansa ba tare da wahala ba.

    DABARUN KOYARWA (METHODS OF TEACHING)

                Dabarun koyarwa ko kuma ace hanyoyin koyawar su na da yawa. Haka kuma babu wata dabarar koyarwa wadda ba a gauranya ta ba. Domin ko a cikin aji ba lallai ne malami ya ɗauki dabarar ɗaya ba, ace “ita zai bi sau da ƙafa”. Misali, idan lacca watau dabarar koyarwa ta lacca yake bi wajen koyarwa to dole ne ya haɗa da allo don rubuta ko don zana wasu surori don a gani a karanta. Saboda haka tsarin koyarwa shi ne duk wata hanya da malami zai bi don ingantan koyarwarsa.

                Ire-iren dabarun koyarwa kamar yadda aka faɗa da farko suna da yawa, wasu daga cikinsu sune:

    Bincike faratis

    Wasan kwai-kwayo

    Tambaya da jawabi

    Zuwa da kai

    Waƙa da amshi

    Lacca    

    Muhawara

    Jinga d.s

    Daga cikin waɗannan za mu ɗauki guda uku (3) ne mu yi bayani a kansu kamar haka:

    Lacca (lecture method)

    Muhawara (debate/discussion method)

    Jinga (project method)

    LACCA (LECTURE METHOD)

    Wani zance ne da aka shiryawa ɗalbai, a tsara a dunƙule sa’annan azo da shi gaban ɗalibai cikin aji kuma za a shiryawa ana warwarewa daki-daki, filla-filla.

    SHARUƊƊAN DA YA KAMATA A KIYAYE WAJEN AMFANI DA HANYAR LACCA

                Sharuɗɗan da ya kamata a kiyaye wajen amfani da hanyar lacca, musamma a fannin koyarwa. Waɗannan sharuɗɗa guda uku (3) ne kamar haka:

    Dacewar saƙo: dole ne a tabbatar cewa saƙo ya dace da fahimtar ɗalibai da tunaninsu da yawan abin da suka sani da kuma yawan shekarunsu.

    Kafewar lacca: Kyakkyawan tsari misali daidaita tsarin saƙonnin daki-daki ta yadda mai yin laccar saƙonnin za su riɗa faɗo masu a zuci in ya zo warwaresu.

    Dai-daita yawan lacca da tsawon Lokaci: wato anan dole ne mai yin lacca ya daidaita darasinsa da lokacin da aka bayar, su zo daidai, ba wai lacca ta wuce lokaci ba ko kuma a ce lokacin ya yi wa laccar yawa.

    NAU’OIN LACCA

                Ire-iren lacca guda huɗu (4) ne kamar haka:

    Gundarin lacca

    Lacca tare da allo da alli

    Lacca tare da gwaje-gwaje

    Lacca ta amfani da matallafan koyarwa

    AMFANIN LACCA (ADVANTAGES)

                Kamar dai yadda bayanin masana ya nuna amfanin wannan dabarar koyawar wato lacca suna da yawa, wasu daga cikin su sun haɗa da:

    Lacca tana dunƙule da bayanai masu yawa ta miƙa wa ɗalibai cikin lokaci.

    Lacca tana tara saƙwanni mabanbanta ta yi masu sura guda.

    Hanyar koyarwa ko dabarar koyarwa ta lacca ita ce mafi dacewa wajen sharar fage a fannin da za a koyar, ko za a shiga koyarwa.

    Lacca hanya ce mafi cancanta wajen gabatar da dabarun koyarwa.

    Haka kuma lacca hanya ce ta miƙa-saƙwanni masu tsadar gaske, waɗanda babu damar ɗalibi ya karanto su wani wuri.

    AIBIN LACCA (DISADVANTAGES)

                Haƙiƙa duk abin da ke da amfani to ko, yana da nasa rashin amfani wannan haka yake ga kowanne al’amari.

                Saboda haka ita ma hanyar koyar ta lacca na da nata rashin amfanin ko aibin kamar haka:

    Lacca tana da saurin ƙosarwa in ta yi tsawo, musamman in ba a gaurayata da kowacce irin dabara ba daga cikin dabarorin koyarwa.

    Dabarar koyarwa ta lacca, babu ruwanta da banbance – banbance tsakanin ɗalibai.

    Haka kuma ita wannan hanyar koyarwa ta lacca bata damu da hulɗa tsakanin malami da ɗalibi ba, balle, tsakanin ɗalibi da ɗalibi.

    Bugu da ƙari wannan hanyar koyarwa ta lacca, bata kula da abin da ya dami ɗalibi guda ba, ko kuma sha’awarsa.

    Ƙarewa da ƙarau, ita wannan hanyar koyarwa ta lacca, ba ta sheda wa malami ko an karɓi saƙo ko ba karɓa ba.

    GYARAN FUSKAR DA ZA’A YI WA LACCA DON TAYI INGANCI

                Dangane da wannan, kamar yadda masana suka yi bayani, akwai hanyoyi biyar (5) da za a iya bi domin inganta wannan dabarar koyarwa ta lacca su ne, kamar haka:

    Ta hanyar jaddada muhimman maganganu, wato ta hanyar, nanatawa ko ɗaga murya.

    Ta hanyar misalta abubuwa ko ƙarfafasu da hannu ko da fuska ko kuma ta hanyar rubuta su akan Allo.

    Ta hanyar amfani da kayayyakin koyo misali: Amfani da abin zana hotuna da surori na gani da na ji.

    Ta hanyar tsagaitawa, watau a taɓo wurare daba-daban, sako-sako kuma ɗaki-ɗaki, filla-filla, mataki-mataki duk abin da batun da ake a lacca ya shafa.

    Hanya ta biyar kuma ta ƙarshe da za a iya inganta wannan hanyar koyarwa ta lacca, ita ce ta hanyar gauraya wannan.

    Tsakanin noman rani da na damina wane ne ya fi?

    Tsakanin al’adun turawa da na mu na huasawa na gargajiya wannne ne ya fi?

    Ire-ire waɗannan su ne misallan muhawara.

    MUHIMMANCIN MUHAWARA

                Hanyar koyarwa ko dabarar koyarwa ta muhawara ta na da amfani masu yawan gaske a wajen ɗalibai. Wasu daga cikin muhimmancin muhawara ga ɗalibai sune kamar haka:

    Muhawara tana koya wa ɗalibai faɗar gaskiya ta hanyar faɗar abubawa yadda suke.

    Wani amfani muhawara kuma ga ɗalibai shi ne: ɗalibai kan ga martabar ra’ayoyin wasu da kuma koyon abubawa ta wannan hanyar.

    Haka kuma, koyon , ladubban muhawara na sa koyon ladubban shiga mutane, wato mutum ba zai rinƙa yin katsalandan ba ga kowanne irin lamari cikin mutane wanda bai shafeshi ba.

    Muhawara tana sa ɗalibai yin tunani mai kyau da ƙoƙarin fassara abubwa kuma ta sa su gano yadda za su warware matsala d.s.

    AIBIN MUHAWARA

                Aibin muhawara suna da yawa, wasu daga cikinsu sun haɗa da:

    Muhawara tana iya yin watsi da mai kyakkyawan tunani idan ba gwanin  magana ba ne.

    Muhawara tana iya juyewa ta zama hira barkatai

    Haka kuma muhawara abu ce mai wuyar gaske ta gamsar da kowa cikin aji.

    Ta hanyar muhawara ba a iya koyon abubuwa masu yawa cikin darasi guda.

    Muhawara abu ce mai wuyar buɗewa kuma mai wuyar rufewa. Duk waɗannan da wasu ma da yawa da ba a kawo ba aibin muhawara ne.

    JINGA (PROJECT METHODS)

                Jinga, dabara ce ta koyarwa, idan aka sanya ɗalibi ya karantar da kansa da kansa, watau a rin wanna dabarar koyarwa, akan ba ɗalibi kwangila ne tare da wa’adi na ya je ya yi ayyukan koyon. Mafi yawanci jinga dabara ce ta darasi guda ɗaya tak ba kamar sauran dabarorin koyarwa ‘yan uwanta’.

                Har ila yau jinga dabara ce ta koya fanni ko wani ɓangare na fanni mai yawa. Saboda haka jinga dabara ce mai ɗaukar dogon lokaci wadda kuma kan ƙunshi duk sauran dabarun koyarwa.

    AMFANIN JINGA

    Tana karfafa aikin ɗalibi.

    Jinga ta dace da kowannen iri ɗalibi yaro ko babba, masu aiki ne a wata ma aikata ko waɗanda suke zaman kansu ne, masu jeka-ka-dawo ne ko masu kwana makaranta ne.

    Jinga tana daga cikin sahun dabarun koyarwa masu saurin sa ɗalibi faɗaɗa ilminsa da kuma saurin kama aiki.

    Jinga tana taimakawa wajen haɗa kan ɗalibai masu aiki a ƙungiya guda.

    Tana sa ɗalibi koyon abu cikin marmari da raha da kuma sanin muhimmancin abu.

    Jinga tana fito da baiwar da Allah ya ba kowanne ɗalibi a fili.

    Haka kuma jinga ta na maganin banbance-babancen ɗalibai.

    Misali: akan sha’awar ko fahimtar su, ko kuma saurin kamma aikinsu d.s. duk waɗannan muhimmancin jinga ne.

    AIBIN JINGA 

                Dangane da aibin jinga kuwa, kamar yaddar masana su ka yi bayani akwai su da dama. Wasu daga ciki su ne:

    Jinga hanya ce da kansa masu yin ta kasala, ko kuma ta masu sha’awar satar ayyukan da ba nasu ba.

    Haka kuma jinga hanya ce da bata dace da koyon sababbin tunane ba watau (concept).

    Jinga hanya ce mai wuyar gudanarwa musamman idan bambanci ya yi yawa tsakanin ɗalibai da kuma irin ayyukan da suka sa gabban su.

    MANYAN KASHA-KASHE DABARUN KOYARWA

                Dangane da wannan za a iya karkasa dabarun koyarwa dukkansu zuwwa ƙungiyar-ƙungiya har gida uku (3) kamar haka:

    Masu jaddada aikin malami: a nan aikin koyarwa yawanci yana hannun malamai ne. Muhimman salon da ake shedawa a cikin wannan ƙungiya su ne:

    Gundarin Lacca

    Lacca tare da sa bakin ɗalibai

    Lacca tare da gwaje-gwaje da aikatawa

    Nuni da gwaji da misaltawa

    Haka kuma, makarantun gaba da sakandare ne wato jami’o'i da wuraren da ya cancanta a yi amfani da waɗannan dabarun.

    Masu jaddada aikin ɗalibai: a nan ana nufin inda yawancin ayyukan sadarwa/horarwa yake hannun ɗalibai. Misali

    Gwaje-gwaje ko karance – karancen sa kai.

    Bincike ko neman samfuri

    Muhawara ko taɗi tsakanin ɗalibai

    Jinga

    Faratis

    Wasan kwaikwayo

    Masu jaddada tarayya tsakanin malami da ɗalibai: a nan kuma, aikin sadarwa/horarwa ya rabu dai-dai-wa-dai da tsakanin malami da ɗalibai. Misali:

    Sadarwa/horarwa ta hanyar kayayyakin koyoda koyarwa

    Tambaya da jawabi

    Zuwa da kai

    Waƙa da amshi

    Shifta

    YADDA AKE KOYAR DA RUBUTU TA HANYAR ZAYYANA

          Wannan hanya ita ce wadda yaro kan soma bi wajen koyon rubutu tun daga aji daya na furamare. Ana faraway ne a kasa, kafin yara su soma da alkalami. Amfani zayyana shi ne zai koyawa yara amfani da alkalami yana sa hannun yara yayi laushi saboda amfani da lakalami ta wajen rubutu.

          Kamar dai yadda bayanin masana ya nuna, ana soma zayyana ne kasa, sa’annan akan allo hhar a kai ga littafai. Dole ne malami ya rinka zagayawa ya ga cewa; rubutun da yara suke yi ya zo daidai bai daya.

    Da zarar yara sun iya zayyanawa, malami zai ci gaba dasu wajen rubuta bakake. Bayan sun iya wannan sai a koyar dasu yadda kae hada kalma, sa’annan jimla, anan za a nuna wa yara inda ya kamata a sa wakafi (,) da aya (.) da alamar tambaya (?) da alamar motsin rai (!) da sauran alamomin rubutu.

    Za a samar da su yadda ya kamata a rubuta suna, watau da babban baki a farko ko yaushe suka zo cikin jimla, kuma a sanar da dalibai cewa duk Kalmar da ta zo karshen bayani aya za a sa. In za a ci gaba a soma da babban baki. Duk wannan malami zai rubutawa yara su na bi.

    Wata hanya kuma da malami zai koyar da rubutu ita ce; ya bada labara iri-iri daga cikin labarai malami ya ce, a rubuta guda ko kuma duka. Kuma malami yana iya shirya yara su tafi ziyarar wuri kamar; kasuwa ko, masana’anta daga baya ya sa su rubuta abin da suka gano, ko kuma malami ya kawo hoto ko, taswira, su rubuta d.s.

    Wadannan matakai akan karkafa su daga aji daya har zuwa aji uku, lokacin da yara suka kai aji hudu (4) sai a ci gaba da koyar das u sakin layi da sauransu.

    YADDA AKE KOYAR DA WASAN KWAIKWAYO

    Tun da farko, ana son malami ya gabatar da darasinsa kamar yadda yake gabatar da sauran darussansa. Idan gabatarwar ta dace da wannan darasin (abin da zai koyar) shi ke nan. In ba haka ba kuwa to, ka da takaitaccen tarihi ne ya kamata ya bayar dangane da yadda yara zasu fahimci darasin. Daga nan malami zai bi waɗannan matakai kamar haka:

    Wajibi ne malami ya sanar da ɗalibai sunayen ƴan wasa da mahimmancin yin wasan. A cikin wasan nan ne malami zai iya ƙoƙarin nuna wa ɗalibai irin halayen da ƴan wasan suka nuna da muhimmancin halayen da suka nuna a cikin wasar. Misali; littafin uwar gulma da abin da ta aikata, har wayau ana son nuna wa ɗalibai muhimmancin kowanne ɗan wasa da irin matsalolin da ya fuskata da kuma yadda ya magancesu, irin nasarar da ɗan wasa ya samu da dalilin da ya sami nasarar. Misali yadda malam mai dala’ilu ya magance matarsa da ta rinjayi abinda yasso ya yi. A wani misali kuma yadda Alhaji Ruwan Ido har ya cimma burinsa a kan zaliha (cikin littafin kulɓa na Ɓarna), ko yadda malam Shehu ya ciwo kan Zainab a cikin littafin jiki magayi, ko kuma Malam Arɗo da matarsa a cikin littafin zamanin nan namu, a gama da sha’anin ƴar masu gida.

    Malami ya yi ƙoƙarin nuna wa ɗalibai irin abubwan da suka faru da abubuwan da suka yi muni da kuma irin sakamakon da aka samu. Misali: Irin abubuwa da suka faru tsakanin Mantau da Uwar gidansa a cikin littafin tabarmar kunya. Haka kuma malami ya yi ƙoƙarin nuna wa yara abinn da ya faru. Misali: tsakanin gimbiya da sarki cikin littafin dare na sha biyu.

    Har yanzu dai malami ya yi ƙoƙarin nuna wa ɗalibansa dalilin da yasa wasu ƴan wasa suka furta magana, daga nan (malami) ya bari su ɗalibai su furta nasu zantuttuka da kuma dalilin fitar furucin don nuna fahimta aikin da aka yi masu jagora, Misali; zancen da uban zaliha ke yi wa Ɗan London a cikin littafin Kulɓa na Ɓarna. Sai kuma da Haruna ya faɗa lokacin da Halima ta yi yaji, da kuma irin abin daya fito bakinsa da ya ga Hayatu a gidan mama mai saida ruwan daɗi. A nan malami na iya tambayar yara abin da Muhuti ya faɗi a ɗakin shari’a. Ma’ana anan shi ne ƙwan-ƙwance abin da ƴan wasar suka faɗa da irin muhimmancinsa akan abin da wasar ke koyarwa.

    A nan mataki na huɗu, wasu ƴan wasa idan an fitar da su dole ne a maye su da wani ko ace wasar ta gurɓata. Misali: a littafin da muka yi magana ace a fitar da Zaliha ko ƙyallu a tattauna ƙyallu ko, mantau a tabarmar kunya, dole ne idan an cire su a samu tamkar jela ga zane watau basu hana kome. Duk dai a cikin wannan matakin, bayan karanta wasar, wajibi ne ya zama a ƙarshe ɗalibai na iya fitar da manufa dangane da saƙon da marubucin ke son isarwa ga masu karanta wasar. Saboda haka idan an ƙare wasar yazan an ƙare ta yadda ɗalibai za su iya yin shari’a gwargwadon iya warsu, anan zai fi kyau ɗalibai su amayo wasu zantattuka.

    Mataki na biyar shi ne matakin ƙarshe a wajen koyar da wasan kwaikwayon. A nan ya kamata malami ya bari ɗalibai su yabi abin da ya cancanta su yaba kuma su kushe na kushewa.

    YADDA AKE KOYAR DA WAƘA DA MAHIMMAN ABUBUWAN DA YA KAMATA MALAMI YA YI AMFANI DA SU

                A nan tun da farko, muhimman abubuwan da ya kamata malami ya yi amfani da su sune kamar haka:

    Sunan mawaƙi

    Shekarar da aka yi waƙa

    Dalilin da yassa aka yi waƙar

    Shimfiɗar waƙar

    Amsa amon waƙar na ciki da na waje

    Kafiyar waƙar.

    Jigon amfani da kalmomi

    Jigon amfani da jimloli

    Salon sarrafawa

    Salon sarrafa harshe (Nahawu) watau ramzi da kari.

    Dangane da yadda ake koyar da waƙa kuwa; Tun da farko malami zai yi wa ɗalibai bayani game da waƙar da za a karantar. Misali: sunan wanda ya yi waƙar da, shekarar da aka yi waƙar da, kuma dalilin yin waƙar da dai sauransu. Bayan wannan kuma sai malami ya yi bayanin abin da ita waƙar ke magana akai a taƙaice.

    Daga wannan matakin kuma sai malami ya sa ɗalibai su karanta waƙar a bayyane ko kuma a asirce. Malami shi zai fara yin jagorancin karanta kowanne baiti: A karanta baitin kuma a hardace shi da irin abin da yake cewa. Daga nan sai a tsame wasu kalmomi da aka ga masu muhimmanci ne don yin bayani akansu. Haka kuma a yi ƙoƙarin fitar da saƙon wakar (jigo). Anan malami zai bari ne ɗalibai su yi ƙoƙarin fitar da saƙon waƙar da kansu, idan ya zamo da gyaran sai a gyara.

    Abu na gaba kuma, bayan an karanta wakar daga farko har zuwa ƙarshe sai aba ɗalibai dama su yi nazari don aga abin da suka tsinta a cikin wannan waƙar. Har wa-yau aba su damar su faɗi albarakacin bakin su. Malami kuma sai ya cigaba da jan hankalin ɗalibai da abubawan da suka sa waƙar ta shahara. Misali: siffantawa, da kamantawa, da kambamawa d.s. malami kuma ya ja hankalin ɗaliban a cikin ƙirƙirar waƙa, domin gano mai cikakkiyar basira, acikin ɗaliban, tare girmamashi da babban makin domin hankalin sauran ɗalibai, don su mai da himma acikin koyo da koyarwa.

     

    KAMMALAWA

    Tsarin koyo da koyarwa shi ne babban jigo acikin neman iliml na kowane fanni, a faɗin Duniya, domin kowace ƙasa tana da tsarin koyarwa, wanda shi ne dokar ƙasar ta aminta da shi a cikin tsarin koyarwa, duk da ana samun bambance-bambancen ra'ayi a cikin tsararrun hanyoyin koyarwa na Duniya; Duk da cewa wannan bambance-bambancen ba illa bane sai dai wani tsarin ya fi wani, amma a al'adance babu wani fanni a Duniya da ba ya amfani da tsarin koyarwa, domin samun ingantaccen ilimi da tsayayyen tunani acikin koyarwa.

     

    MANAZARWA

    Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

    Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

    Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

    Nahuche S.I.M (2008). Rubutun Lacca na Tsarin Dubarun Koyarwa (Principle and Method of Teaching). Na Kwalejin Ilimi da ke Maru, Jihar Zamfara.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.