Finafinan Hausa a Mahangar Al’umma: Gyara ko Ɓarna?

    Wannan takarda mai suna “Fina-Finan Hausa A Mahangar Al’umma: Gyara Ko  Ɓarna?” ta yi nazarin wasu finafinan Hausa tare da bayyana yadda al’umma ke kallon su ta  ɓangaren gyara da kuma  ɓarnar da suka kawo a cikin al’umma. An rubuta takardar domin fa ɗakar da al’umma dangane da irin alfanun da fina-finan suka kawo da kuma ayubban da suka haddasa a cikin al’umma baki ɗaya. An yi haka ta hanyar aron bakin al’umma aka ci musu albasa, duk da yake an yi hira da mutane masu yawa a kan irin gyaran da suke ganin fina-finan Hausa suka kawo da kuma matsalolin da suka haddasa. An gano akwai  ɗan amfani da ba a rasa ba sai dai illoli sun fi a  ƙirga. Abin da ya nuna haka shi ne, duk abin da ya zo ya raba al’umma da halinta na kirki da aka san ta da shi (tarbiyyarta) da kuma sanya ta cikin halin da ba a san ta da shi ba illa ne. Ba wannan ka ɗai ba, fina-finan har fa ɗa suke yi da addinin Bahaushe. Wasu mutane ma ganin suke yi fim bai tsinana wa al’ummar Hausawa komai ba face ci baya. Takardar ta kawo wuraren da aka samu gyara da kuma  ɓarnar da fina-finan suka tafka a al’ummar Hausawa tare da misalan da ke tabbatar da hakan. An yi haka domin iyaye su farka daga barcin da suke yi da nuna kula da ‘ya’yansu da na al’umma baki  ɗaya domin  ɗan Bahaushe na kowa ne a al’adance idan aka yi zancen tarbiyya.

    Finafinan Hausa a Mahangar Al’umma: Gyara ko Ɓarna?

    Bello Bala Usman
    Department of Nigerian Languages,
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
    08027459617

    And

    Dano Balarabe Bunza
    Department of Nigerian Languages
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
    07035141980

    Finafinan hausa

    1.0 Gabatarwa

    “Kowag gyara ya sani,

    Kuma kowaɓ ɓata ya sani

    ‘Yan Amshi: Da ɗai mutum ba shi son mai yi mai zamba”.

    (Musa Ɗanƙwairo Maradun).

     

    Allah ya jiƙan Gambo mijin Kulu mai kalangu da ya ce:

     

    “Mai gyara ba shi ɓarna,

    Sai in ba gyara shikai ba”.

     (Gambo Mai Kalangu).

     

    Sanadiyyar wayewar zamani kullum al’umma sai cigaba take samu, har da na mai ginar rijiya. Haka kuma, da yawa mutum ke son wani abu a rayuwarsa sai abin ya kasance akasin alheri a gare shi, kamar yadda wani lokaci yakan ƙi abin da shi ne alheri gare shi. Wannan takarda za ta yi tsokaci kaɗan kan fina-finan Hausa da yadda jama’a ke kallon su ta hanyar duba gyara da ɓarnar da suka haddasa a al’ummar Hausawa. A nan sai mu yi maganar raggo da ya ce an raba masa hankali, an ce ya sha hura a tafi gona. Abin nufi a nan shi ne, an aza mana nauyin waƙiltar al’umma ta fuskar faɗin ra’ayinsu kan abin da ya shafi finan-finan Hausa. Sanin kowa ne cewa al’umma taron jama’a ce daban-daban da duk wanda ya waƙilce su kan wani al’amari, sai ya yi wa wani daidai kuma ya kuskure wani. Abin da ya dace a sani shi ne, fina-finan Hausa kafafe ne da ake nuna ayyukan da al’umma ke yi masu kyau da akasi, domin a faɗakar da al’umma don su rinƙa aikata masu kyan tare da gargaɗi gare su da su guji munana. Manufarsu ita ce domin ilmantar da al’umma dangane da abubuwan da suka dace da waɗanda ba su dace da su aikata ko faɗa ba. Wannan ya yi daidai da maganar da Hausawa ke cewa “Da muguwar rawa gara ƙin tashi”. A fahimtar takardar nauyi mai girma ne aka ɗora mata. Saboda haka, za a faɗi abin da ya sauƙaƙa, waɗanda aka waƙilta su yi haƙuri da waƙilcin da aka yi musu a yau kan abin da ya shafi fina-finan Hausa dangane da gyara da ɓarnar da suka haddasa cikin al’ummar Hausawa.

     

     

    2.0 Taƙaitaccen Tarihin Fina-Finan Hausa

    An fara samar da fina-finan Hausa a shekarar1994, lokacin da wata ƙungiya mai suna Tumbin Giwa ta shirya fim mai suna ‘Turmin Danya’. A shekarar 1994 ƙungiyar ta sake shirya wani fim mai suna ‘Gimbiya Fatima’. Kamfanin Tumsy Video Club ya shirya fim mai suna ‘Rana ba ta ƙarya’ duk a shekarar 1994. A shekarar 1995 kamfanin Gidan Dabino ya shirya fim mai suna ‘In da so da Ƙauna’. Bayansa aka sami kamfanin Kwabon Masoyi ya shirya fim mai suna ‘Kwabon Masoyi’. Ƙungiyar Jigon Hausa ta shirya fim mai suna ‘Munkar’. Bayan wannan R.K. Studio sun shirya fim mai suna ‘Bakandamiyar Rikicin Duniya’. Biye da shi a shekarar 1996 ƙungiyar Yakasai Drama Association ta shirya fim mai suna ‘Kuturun Danja’. Samar da waɗannan fina-finai da waɗannan kamfunna da ƙungiyoyi suka yi ya tabbatar da samuwar fina-finan Hausa a ƙasar Hausa. Daga nan fina-finan Hausa suka ci gaba da samuwa da bunƙasa har zuwa yau.

    2.1 Mene ne Fim?

    Marubuta da dama sun bayyana abin da ake nufi da fim a cikin rubuce-rubucensu sai dai, saboda yawan da ke gare su za a ɗauki ma’ana ɗaya a wannan takarda. Ga abin da aka tsinto a takardar Haruna Alƙasim Kiyawa inda ya ce:

    ‘Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da ke ɗauke da hotunan mutane, wato hotunan maza ko mata ko maza, yara ko manya, ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ɗauka ta hanyar yin amfani da na’urar ɗauka ta musamman, tare da bai wa mutanen (kowannensu) dammar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko waninsa a wani ɗan lokaci da aka keɓe, wanda shi was an kwaikwayo yake ɗauke da wani saƙo na musamman kan nishaɗi da gargaɗi da wa’azi da soyayya da tarihi ko wanin haka, zuwa ga al’ummar duniya”

     

    A fahimtar takardar fim na nufin haɗuwar ayyuka da maganganun mutane daban-daban da amfani da wasu abubuwa marasa rai ta hanyar kwaikwayo ko ƙagawar da suka yi a cikin hoton da ake kallo ta hanyar amfani da na’urorin ɗaukar hoto da nuna shi ga jama’a, wanda ke ɗauke da wani saƙo ko saƙonni zuwa ga al’ummar da aka yi abin dominsu.

    2.2 Asalin Fina-Finan Hausa

    Kafin samuwar Fina-finan Hausa akwai majigi da ake yi a fadar sarakuna domin wayar wa jama’a kai a kan wasu shirye-shiryen gwamnati musamman kan aikin noma da sana’o’i. Biye da wannan sai aka fara samun fina-finan Indiyawa da na mutanen China (Ƙasar Sin). Ana cikin haka sai fina-finan jihar Lagos suka fara fitowa ana gudanar da su a cikin harshen Turanci. Fina-Finan Hausa ba su rasa alaƙa da waɗannan fina-finai da aka ambata. A fahimtar takardar fina-finan Hausa sun sami tushe daga wasannin kwaikwayon da ake gudanarwa na Hausa a cikin gidajen radiyo da kuma talbijin. Haka kuma littattafan Adabin Kasuwar Kano sun ƙara wa masu yin fim ƙwarin guiwar gudanar da harakar ta hanyar mayar da littafin da aka rubuta cikin fim. Lokacin da marubuta Adabin Kasuwar Kano suka fara rubuta littattafansu suka saka a kasuwa domin sayarwa, masu sha’awa na saye suna karantawa. Daga baya sai marubutan suka hango cewa, fim ya fi littafi farin jini ga jama’a masu ra’ayi ta hanyar saurin isar da saƙo. Abin da ya ƙara wa fim farin jini duk bai zarce sauƙi ta hanyar kallon da ake yi ba da hutar da mutane daga wahalar karatu kuma ga nishaɗantarwa... Ana iya saka littafi gaba ɗayansa a cikin fim ɗaya wanda da karatu ake yi, da zai ɗauki tsawon kwanuka kafin a ƙare karantawa. Yanzu kuma da ya koma a cikin faifan kallo, an rage wa masu karatu wahala, da kallon duk abin da littafi ke ɗauke da shi cikin sauƙi kuma cikin kaɗannan lokaci.

     

    3.0 Fina-Finan Hausa a Mahangar Al’umma: Gyara ko Ɓarna?

    Gano gyaran da fina-finan Hausa suka samar ga al’ummar Hausawa ba aikin mutum ɗaya ba ne domin kowa da bukin zuciyarsa, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Ma’ana, za a faɗi wani abu a matsayin gyara, wani ya hango cewa ba gyara ba ne ɓarna ce. Idan abu ya shafi ra’ayi dole a yi taka-tsantsan da shi domin akan samu saɓanin ra’ayi a kan abu ɗaya balle sun fi a ƙirga. Saboda haka, takardar ta hango waɗansu gyare-gyare da akasinsu (Gyara da ɓarna) da fina-finan Hausa suka kawo wa al’ummar Hausawa.

    3.1 Fina-Finan Hausa a Mahangar Al’umma (Gyara)

    Ba za a ce abu ba ya da amfani ga jama’a baki ɗaya ba face an san abin sosai. Wannan ya tuna min da maganar da mata ke faɗi cewa, “Komi ra’ayi ne shafin kwalli da reza”. A taƙaice, ga gyaran da aka hango da fina-finan Hausa suka kawo wa al’ummar Hausawa kamar haka:

    3.1.1 Fim Sana’a ce

    Hausawa sun ce “Sana’a sa’a”. Sana’a hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan Adam ya mallaka don buƙatun yau da kullum. Don haka ke nan sana’a wata abu ce wadda mutum ya jiɓinci yi da nufin samun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa. Sana’a abu ce wadda ta danganci tono albarkatun ƙasa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da ɗan Adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki da sauransu. Akwai sana’a iri uku: Na maza da na mata da kuma na tarayya (Ibrahim Yaro Yahaya da wasu, 2007:48). Fina-finan Hausa na daga cikin sana’o’in tarayya da ake gudanarwa a ƙasar Hausa. Ga abin da wani makaɗi ya ce:

    Jagora: Mu kama sana’a ‘yan Najeriya,

                 Zaman banza bai kyau da mu ba.

     

    ‘Yan Amshi: Mu kama sana’a ‘yan Najeriya,

                 : Zaman banza bai kyau da mu ba.

     

    Jagora: Mu kama sana’a ‘yan Najeriya,

                 Zaman banza ba namu ne ba.

                (Mammalo Shata: Waƙar Mu Kama Sana’a).

    Dangane da muhimmancin sana’a ga al’umma ba sai an nanata ba. Wanda duk ya san daɗin samu da zafin rashi, ba sai an bayyana masa muhimmancin neman zufan jikinsa ba. Bisa ga wannan a ganinmu, duk yadda sana’a take ta fi babu. Akwai rufin asiri da yawa da ake samu ta hanyar sana’a kamar yadda ake samun tonon asiri ga rashin ta. Don haka samun sana’ar yi arziki ne, rashin ta kuma matsala ce. Mutane da dama sun sami rufin asiri ta hanyar gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali sanadaiyyar sana’ar fim. Wasu kuma sun zama masu kuɗi da ake ji da su ta fannin sana’ar fim. Wannan ne ya sanya wasu jama’a daga ƙauyuka na kwarara zuwa birni domin ganin sun zama daga cikin masu taka rawa a sana’ar. A nan harakar fim sana’a ce saboda hanyar samun kuɗi ce ga ‘yan wasan. Hanyar da ake gane harakar fim sana’a ce ita ce, sayar da kaset da ake yi. Masu sayar da kaset sun sami kuɗi a matsayin riba, ina ga waɗanda suka samar da kaset ɗin (‘Yan wasan fim)?

     

    3.1.2 Samar Da Aikin Yi Ga Wasu

    Daga cikin gyaran da fina-finan Hausa suka yi akwai samar da aikin yi ga wasu jama’a da ke ra’ayin sana’ar. Samun wannan aiki ya sanya wa masu ita kariya daga kamun da ake yi wa marasa aikin yi a matsayin zauna-gari-banza. Ya dace kowa ya samu aikin da zai rinƙa samun abin gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum. Idan ba haka ba kuwa, zai faɗa cikin halin rashin gaskiya yana ji yana gani, a ƙarshe ya wulaƙanta a bainar jama’a. Misali, da mutum ya yi sata ko rikicin da ba kai ba gindi, gwamma ya je ya sami aikin yi ya tsira da mutuncinsa. Akwai waɗanda suka ƙare makarantar sakandare da kwalejojin ilmi har da digiri amma, babu aikin yi a halin yanzu. Sanin kowa ne gwamnati ba ta iya samar wa kowa da kowa aikin yi, ba saboda kasawa ba. A’a. Jama’a sun yi yawan da ya zarce gurabun aikin gwamnati. A kan haka dole kowa ya yi wa kansa tunanin bagiren da zai sami abin sanyawa a bakin salati. Samun aiki a kamfanin fim ya fi zaman banza mutum na kallo ana yi ba da shi ba. Da a yi wa mutum abin da aka yi wa Bawa Makau a garin Gummi kamar yadda Gambo mai kalangu ya faɗa, aiki ƙarƙashin kamfanin fim ya fi domin ko babu komai akwai kwanciyar hankali fiye da hanyar da Bawa Makau ke kanta a wancan lokaci. Ga abin da Gambo ya ce dangane da Bawa Makau lokacin da aka tasai kasuwar Gummi:

    Gambo: Kai ku kashe kowa ka cewa,

                 Babu guda mai kawo ceto,

                 Ko kamin Holis su amsai,

                 Na ga tarin dutci gaban Bawa.

     

    Bayan mutane sun yi masa dukar kashi har ya daina motsi, suka yi tsammanin ya mutu sai suka watse gudun a kama wani shi kaɗai a wahalar da shi. Nan take aka nemo Gambo da shi ne makaɗinsu. Nan kuma sai ya ce:

    Gambo: An ka ce a kiro Gambo mawaƙinsu,

                 Ƙila yana gane wane na,

                 Nad diba hakan ga,

                 Nac ce Naɓagarawa an nan bunsuru Bawa,

                 Bunsurun ga da kuraye ka tsoro,

                 Ga shi mutane sun kashe shi.

     

    Lokacin da aka kai Bawa ɗakin kewa tsammanin ya mutu, ga abin da Gambo ya ce:

     

    Gambo: Da nag ga mutane sun rage haka,

                 Nac ce kaicon na kaina,

                 Na ishe Makau nan garin Gumi,

                 Za ni barin Makau garin Gumi

                 Kwance mutane sun kashe shi,

                 In nat tai mi za ni cewa?

     

    Gambo na ƙare magana sai Bawa ya ɗaga kai kaɗan ya ga babu kowa kusa sai ya buɗa baki ya ce wa Gambo:

    Gambo: In don haka ɗai na kar ka damu,

                 Na lahe na ban mace ba,

                 Don kar jama’ar banza su cutan,

                 Ka rinƙa hwaɗin Allat tsare gaba,

                 Wanga karo shi mun wuce shi.

                (Gambo: Waƙar Bawa Makau).

     

    Tambayata a nan, ita ce zai yiwu a yi wa ɗan wasan fim yadda aka yi wa Bawa Makau ba tare da ya yi aiki irin nasa ba? Ke nan, sana’ar fim sana’a ce mai ba da kariya ga mai yin ta a ɓangarori da dama. Samun aikin yi ya fi zaman banza da wasu ke yi suna cutar da jama’a da kawunansu baki ɗaya. Saboda aibin da ke tattare da zaman banza shi ya sa Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa ya tsane shi a cikin wani baitin waƙarsa kamar haka:

    16. Zaman banza ba ni son ka ban son mai yin ka,

     Zama kuma ab ba ni yi da duk wani mai yin ka,

     Ga dubin kowammu mun ga dukkan aibinka,

     Muna roƙon wanda a’ Azizu ya mirɗe ka,

                Ka faɗa rami ka daina cutar jama’ammu.

    (Sambo Wali Giɗaɗawa, Waƙar Hayya fa Jama’a ku bar Zaman Banza da Roƙe-Roƙe da Barace-Barace).

     

    3.1.3 Faɗakarwa da Ilmantar da Al’umma

    Faɗakarwa hanya ce ta waye wa mutane kai kan wasu al’amurra da ake ganin suna da alfanu gare su (Usman B.B., 2008).

    A taƙaice faɗakarwa hanya ce ta ilmantar da mutane ko yi musu nasiha da tunatar da su don jan hankalinsu kan wani abu muhimmi na rayuwa (Gusau S.M., 2008).

    Haka kuma wani cewa ya yi faɗakarwa kalma ce da ke nufin jan hankali da wayar da kan jama’a a kan wani abu mai alfanu gare su (Bunza U.A., 2004).

    Kamar yadda masana suka bayyana ma’anar faɗakarwa ina da fahimtar cewa, mafi yawan fina-finan Hausa an gina su domin faɗakar da al’umma game da abubuwan rayuwa masu kyau da marasa kyau domin su aikata masu kyau tare da daina aikata marasa kyau. Duk da haka wani lokaci wajen neman a yi gyara sai ɓarnar da ba zato ba tsammani ta shigo. Yana yiwuwa wanda ke faɗakarwar ma bai tsira daga abin da yake faɗakarwa a kai ba. Misali idan aka sami wani ko wasu daga cikin ‘yan wasa ya aikata wani abu da bai dace ba, akwai wani mutum da aka tanada domin ya faɗakar dangane da abin da aka aikata da ba daidai ba. Hakan na kasancewa malami ko kuma duk wanda aka aza wa wannan nauyin yin faɗakarwar.

    Fim hanya ce ta faɗakar da al’umma, wato ana amfani da fim domin ilmantar da mutane a kan wani abu da ya shige musu duhu ko kuma wani abu da ake so su yi ko su ɗauka. Alal misali idan gwamnati na son ta faɗakar da jama’a a kan muhimmancin ilmi za ta sa a shirya fim ɗin da wani ya shiga makaranta kuma ya sami aiki bayan ƙarewarsa har ya zama wani babba a cikin al’umma. Wannan zai sanya mutane su kwaikwayi wannan mutum domin su ma su sami aiki idan suka ƙare karatunsu. Akwai fina-finan da aka shirya domin ilmantarwa da suka haɗa da ‘Jahilci Ya Fi Hauka Wuyar Magani’ da ‘Zato’ da ke ilmantarwa a kan zarge-zarge da ke faruwa a ƙauyuka musamman a kan matsalar maita da sauransu. Maƙasudin shirya fim shi ne domin wayar da kai ko kuma maganin wata matsala da ke tattare da al’umma wato, matsalar da ke damuwar al’umma. Ta hanyar fim ake nuna wa jama’a wata matsala mai wuyar warwarewa kuma a warware ta ko a magance ta, domin nuna wa jama’a hanyar da za su kuɓuta duk lokacin da suka ci karo da irin wannan matsala. Haka kuma ana shirya fim a kan kowace matsala ta rayuwa domin warware ta ko magance ta. Idan aka sami yin haka, faɗakarwa ta samu tare da ilmantar da jama’a dangane da matsaloli da hanyoyin magance su.

    3.1.4 Samar da Nishaɗi

    Nishaɗi yanayi ne da mutum ke shiga yana tattare da farin ciki da kuma rage damuwar da yake tare da ita. Lokacin da mutum ke cikin nishaɗi yakan nuna annashawa (Farin ciki) ta hanyar sake fuska da dariya ga abin da ya dace a yi su a kansa. Duk lokacin da mutum ke cikin nishaɗi ya manta da damuwar da yake cikinta har sai nishaɗin ya kau. Mutum ba zai kasance cikin nishaɗi da damuwa lokaci ɗaya ba domin abubuwa ne guda biyu da ba su haɗuwa a lokaci ɗaya. Duk lokacin da ɗaya ya zo dole ɗaya ya gusa. Fim na gyara rayuwar ma’abuci kallon sa ya sami nishaɗi, damuwar da yake fama da ita ta tafi tamkar ba ya tare da damuwar. Dalili a nan shi ne, fim abokin hira ne ga mai kallon sa musamman idan wanda yake ra’ayi ne sosai a rayuwa. Misali, duk lokacin da rayuwar mai shan sigari ta gurɓata, yakan sami natsuwa idan ya busa tabar. A taƙaice, fim na rage wa masu kallon sa damuwar rayuwar da suke tare da ita na ɗan wani lokaci. Wannan ya nuna fim wata garkuwa ce ga damuwar da jama’a ke ciki lokacin da suke kallo.

    3.1.5 Ƙulla Zumunta

    Zumunta na nufin kyakkyawar dangantaka tsakanin mutane ko ta jini ko aure ko kuma ta abokantaka. Fim na ƙulla zumunta tsakanin mutane da yawa da suka haɗa da masu wasar fim da kuma ‘yan kallo baki ɗaya. Hausawa sun ce “Zumunta a ƙafa take”. A halin yanzu zumunta ta shiga dukkan hanyoyin sadarwa da ake amfani da su. Soyayya na haddasa zumunta kuma ba tare da soyayya ba, zumunta ba ta samuwa. Zumunta na taimakawa a sami fahimtar juna kuma, danƙon zumunci ya ƙara ƙarfi. An sami auratayya tsakanin masu gudanar da sana’ar fim da dama a lunguna da saƙon Nijeriya. Haka kuma, ana haɗa zumunta tsakanin ‘yan fim na jihohi daban-daban da sauran jama’a masu kallonsu da sha’awar abubuwan da suke gudanarwa. A sandiyyar ziyartar juna da ‘yan wasan fim ke gudanarwa tsakaninsu, zumunta mai yawa na ƙulluwa tsakanin mafi yawan maza da mata.

    3.1.6 Fim Taskar Tarihi Da Al’adun Hausawa Ce

    Kalmar tarihi ba kalma ce mai rikitarwa ba ta fuskar ma’ana. Kalma ce da ke ɗauke da tsayayyiyar ma’ana da ke da sauƙin fahimta. A cikin Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ta Kano (2006), an ba da ma’anar kalmar gida biyu. Ma’anar farko cewa aka yi, tarihi na nufin labarin abubuwan da suka wuce. Ma’ana ta biyu cewa aka yi, fannin ilimi ne na al’amurran da suka faru a zamanin da ya wuce. Kalmar tarihi da wannan takarda ke ƙoƙarin bayani ba ta wuce waɗannan ma’anoni biyu da aka ambata ba, saboda labarin abubuwan da suka wuce ne takardar za ta kawo. Babu kokwanto ana samun labarin abubuwan da suka shuɗe a cikin fina-finan Hausa musamman hotunan da idan aka kalle su wata rana za a tuna baya sosai. Haka kuma, ta duban waɗannan hotuna ake tsintar wasu al’adun Hausawa da aka taskace cikin fim lokacin da aka yi shi. Za a ga tufafi da wuraren zama na al’ada da bukukuwan al’ada na Hausawa da sauransu.

    3.1.7 Bunƙasa Kamfani

    Fim da ya tsaru na jan hankalin masu kallo ta hanyar yin tururuwa zuwa saye. Idan kamfani ya fito da fim da ya tsaru ba shakka yana samar wa kamfani da kuɗin shiga tare da cicciɓa sunan kamfanin ta hanyar fitowa da shi a idon duniya. Wannan ya sanya masu kallon fim na muhawara kan wani fim ya fi wani fim tsaruwa. Abin da ke warware matsala shi ne, kasuwar da fim ɗin ya samar wa kamfani. Duk mai kallon fim ya san haka kamar yadda ɗan kasuwa ya san da haja mai kyau na kira wa mai ita masaya. Kuɗin shiga muhimmi ne ga kowace masana’anta. Idan kamfani ba ya samun kuɗin da ke isarsa gudanar da kasuwancinsa to ya kusa rugujewa. Idan kuma yana samun kuɗin shiga sosai, wannan zai taimaka ga ɗorewarsa na tsawon lokaci. Kamfanin ba ya rayuwa sai da kuɗin shiga. Rashin kasuwa ga abin da kamfani ke samarwa na sanya rage ma’aikatan kamfani, rashin ma’aikata ga kamfani na sanadiyyar rugujewarsa baki ɗaya. Babu kamfanin da zai rayu matuƙar ba a sayen kayan da yake yi. Idan aka ce kamfani na tashe, yana samun ciniki ke nan, idan kuma aka ce kamfani ya yi sanyi, ana nufin babu ciniki, ya kama hanyar rugujewa.

    3.2 Ɓarnar Da Fina-Finan Hausa Suka Haifar A Mahangar Al’umma

    Bayan gyaran da aka ambata na fina-finan Hausa sun tafka ɓarna mai yawan gaske da ba a san yawanta ba a cikin al’umma. Wannan ne dalilin da ya sanya Hausawa faɗar “Gyara bai yi kamar ɓarna ba”. Abin da Bahaushe ke nufi shi ne, gyara alheri ne ga kowa kuma, kowa na sonsa. Ita kuma ɓarna sharri ce da kowa bai son haɗuwa da ita. A taƙaice, ga ɓarnace-ɓarnacen da fina-finan Hausa suka haddasa ga al’ummar Hausawa da takardar ta hango kamar haka:

    3.2.1 Taho-Mu-Gama Da Karantarwar Addinin Musulunci

    Idan ba duka ba kashi casa’in da tara na masu gudanar da fina-finan Hausa Hausawa ne kuma Musulmai kuma, suna da ilmi gwargwado. Hasali ma, wasu daga cikinsu malamai ne. Za a tarar sun karanci Alƙur’ani da littattafan addini sosai wanda sai dai su faɗi hukunci ba a faɗa musu ba. Wanda yake haka, babu zancen rashin sani tattare da shi sai dai, a kira shi ‘Malam ga sani ga ratse’. Wasu sun yi firamare, wasu sakandare, wasu har manyan makarantu sun leƙa domin neman ilmi. Wanda yake haka kuwa, sai dai a ce ya gani ya kau da ido ko kuma, ya sani ya ratse. A taƙaice, ‘yan fim ba jahilai ba ne domin duk abin da suke yi sun san hukuncinsa. Da ayoyi da hadisai da sauran littattafan addini sun san su domin sun karanta ko kuma an karanta sun ji. Abin da kaɗai za a ce dangane da hakan shi ne, akwai kwaɗayin abin duniya da fifita rayuwar yau a kan ta gobe da wulaƙanta mahaifa da dangi kamar yadda fim ɗin ‘Mahaifiyrmu’ ya nuna. Duk wanda ya kasance haka kuwa, shaiɗan ya sami aboki. Saboda haka, mutum ya san abu ya ba shi baya ta hanyar ƙin amfani da shi saɓawa da yin watsi da shi ne. A fahimtar takardar kwaɗayin abin duniya ya yi sanadiyyar wannan saɓawa. Shi kuma kwaɗayi Hausawa sun ambaci haɗarin da ke tattare da shi in da suka ce “Kwaɗayi mabuɗin wahala”. Wannan ya yi daidai da maganar da Gambo mai Kalangu ya faɗa a cikin waƙarsa kamar haka:

    Gambo: Kiɗin ga ba bisa jahilci nikai ba,

                 Don kwas san Ƙur’ani irina ,

                 Duniyag ga uban wa za shi tsoro?

     

    A cikin maganar da Gambo ya yi babu rashin ilmi balle a ce bai san hukuncin aikin da yake yi ba. Abin da ke akwai kawai shi ne kwaɗayin abin duniya. Idan aka duba sosai akwai waɗanda suka zarce Gambo da ilmi a cikin ‘yan wasan fim amma, suka shiga ana fafatawa da su a cikin wasannin kwaikwayon zamani.

    3.2.2 Ruguza Tarbiyya

    Tarbiyya na nufin muhimman halaye na nagarta, ko kuma kyawawan ɗabi’u da halaye, waɗanda Hausawa suka fi ƙarfafawa, ana gane su ta fuskar mu’amala, da yin ladabi da biyayya, da kunya da kara, da zumunci, da riƙon addini, da kuma sana’a, da tsare mutunci, da haƙuri da juriya da jarunta (Alhassan da wasu, 1982:25). A wani wuri cewa aka yi tarbiyya na nufin koyar da hali nagari, (Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano, 2006:428).

    ‘Yan fim na yin fina-finansu domin gina tarbiyya ba ruguza ta ba. Wurin da matsala take shi ne, kowa da bukin zuciyarsa, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Ma’ana, dabarar da ‘yan fim suka bi domin magance aikata wata matsala ita wasu ke amfani da ita domin cutar da al’umma, kamar yaudarar da ake yi wa ‘yan mata ana lalata da su. ‘Yan fim na yi ne domin faɗakar da al’umma kan halayen wasu da ba na kirki ba domin a guje su. Wani kuma idan ya ga haka, ya sami guzuri da dabarar da zai ci gaba da lalata ‘ya’yan al’umma. Mafi yawan fina-finan Hausa akwai ruguza tarbiyyar al’umma a cikinsu ko da an sami gyara a ciki. Akwai rashin ladabi da biyayya ga na gaba. Idan aka dubi wasu fina-finai za a ga rashin ɗa’a a cikinsu. Misali a cikin fim na ‘Mahaifiyarmu’ da na ‘Kishiyar Gida’ akwai wulaƙanta iyaye da rashin ladabi da biyayya. Wanda ya kalle su ya ga haka, wanda bai kalla ba kuma, idan aka ba shi labarin abubuwan da suka faru zai yi mamaki ya ce wulaƙanta iyaye da ƙin yi musu ladabi ba halin Hausawa ba ne. Mai yiwuwa Hausawa sun ara ne daga wasu al’ummu na daban.

    Tarbiyya fage ne mai faɗi na rayuwar Hausawa da ya shafi kula da abin da aka haifa daga ranar da ya zo duniya har zuwa kabarinsa. Da yawa ɗabi’un da aka san Hausawa da su na ƙwarai fina-finan Hausa sun yi watsi da su gefe ɗaya, suka maye da halaye marasa kyau. Akwai lalata ‘yan mata da shaye-shaye inda aka nuna a cikin wani fim mai suna Jamila, aka nuna suruki ya yi wa surukarsa fyaɗe. Wannan ɓangare ya ƙunshi kowace mummunar ɗabi’ar da fim ya kawo wa al’ummar Hausawa. Wannan ya sanya Kyaftin Umaru Ɗa Suru faɗar wani abu kamar haka a cikin waƙara mai suna “Jiya Da Yau”:

                                                     Mutumin yau bai da kunya,

                                         Da ido ƙulai na ƙarya,

                                         Suruki bai kauce hanya,

                                         Wai don suruki ya ɓuya,

                                                                            Mata sun daina huni.

     

     

    12. Ɗan da bai kunna taba,

          Abada bai buɗa kwalba,

          Disko ba a san shi da ba,

          In ba sallah ta zo ba,

                Kiɗa ganga sai ga rani.

     

    93. Turawa kar su ja ka,

                                                                       Ka bi nasu ka ya da naka,

                                                                       Ya zan wauta gare ka,

                                                                       Al’adun kakanninka,

                                                                Ka riƙe su su zan ma’auni.

    A baitin farko da aka kawo a sama marubuci waƙar na nuna yadda tarbiyyar al’ummar yau ta bambanta da ta jiya a inda ya nuna cewa, mutumin yau ba ya da kunya. Abin da yake nufi a nan su haɗa ido saboda girmamawa. Haka a da da wuyan gaske ka sami mutum maƙaryaci. Ana gudun waɗannan miyagun halaye don illar da suke tattare da ita. Haka kuma a zamanin da, kowace mace na sanya lulluɓi domin suturce jikinta baki ɗaya domin sanin fitinar da ke tattare da sakin jiki ga mata. A zamanin yau kuma sai ga shi an wayi gari halayen mutane ya jirkita, abin da ake ƙyamar aikatawa a da, shi ne ya koma ƙawa ga mutane.

    A baiti na 12 da ke sama kuma marubucin ya bayyana cewa, mawuyacin abu ne ka sami mai shan taba sigari ko shan giya ko kaɗe-kaɗe da raye-rayen da ba su da asali ga al’ada. A taƙaice, duk abin da mutumin da ke aikatawa za a taras al’adar al’ummar wurin ta aminta da shi ba kamar mutanen wannan zamani ba. Marubutan na da ra’ayin ba komai ya kawo wannan ba sai baƙin al’ummu da suka shigo cikin Hausawa suka ruɗe su ta hanyar yaudarar nuna musu halayen zamani abin riƙawa ne, domin ba a wayewa sai da aikata su. Wannan ya sanya aka kawo shawara a matsayin mafita ga al’ummar Hausawa cewa, kar waɗannan mutane su janye ra’ayinmu har mu yi watsi da al’adunmu don ganin nasu. Ya ƙara da cewa ba mutumin da zai yi haka sai wawa. A fahimtarsa, ya fi dacewa mutum ya riƙe al’adun kakaninsa su kasance jagora gare shi, ba ya yi watsi da nasa ya rungumi na wasu ba. Idan aka dubi halin da samari da ‘yan mata ke ciki a wannan zamani na wayewar kai, babu shakka an tabbatar da akwai babbar matsala dangane da tarbiyyar mutanen zamani, yara da manya, kuma maza da mata. Kyaftin ya faɗi gaskiya a cikin baitocin da ke sama domin, babu abin da ya kawo lalacewar tarbiyyar matasa da ya kai fina-finan da suka shigo cikin al’umma barkatai. Asalin waɗanda suka kawo fina-finan kuma, Turawa ne.

    3.2.2.1 Raunana Al’adun Hausawa

    A nan al’adun Hausawa sun haɗa da na aure da haihuwa da mutuwa. A bukukuwan duka akwai wuraren da aka ruguza al’adar yin ta ba tare da gano hakan ba. Maimakon zama gidan iyayen mata ko danginta lokacin da aka ɗaura aure, sai ‘yan mata da samari su shiga daji cikin duwatsu da labaye domin yin picnic. A wurin ake lalata mafi yawan ‘yan mata ta hanyar koya musu lalatar amfani da maza. Akan sami maciji ya ciji ko a sami haɗari lokacin zuwa ko dawowa daga wurin taron picnic ɗin. Maimakon a tsaya gida cikin gari a yi kaɗe-kaɗe da raye-rayen murnar da ake ciki, sai aka raya al’adun wasu da ƙoƙarin daƙushe na kai. Akan sami haka a cikin waɗansu fina-finan Hausa a lokacin bikin aure. Haka kuma, akan yi watsi da al’adun gargajiyar Bahaushe a wuraren bikin suna idan ya samu. Ga al’adar Hausawa idan matar ɗan uwa ta haihu ko ba ya da abin lalura su ke tsayi kai da ƙafa su yi gwargwado domin rufa wa juna asiri. Akwai fim da aka yi wa wani haihuwa aka tara maza da mata ana kaɗe-kaɗe da raye-raye, sai mijin ya fito yana kuka ana tambayar me yake yi wa kuka? Da ƙyar ya faɗi cewa ga yaron ya zo lokacin da ba ya da kuɗin saya masa madara a ba shi. Nan take sai wata mata ta ce masa ai babu buƙatar sayen madara domin nonon uwa ya fi madarar amfani ga yaron da aka haifa masa. Fim ɗin na nuna muhimmancin nonon uwa ga jinjiri amma a idon ‘yan kallo mijin na kukan rashi tare da nuna wa al’umma kasawar ‘yan uwansa ta hanyar rashin taimaka masa. Haka kuma, taron da aka yi na bikin sunan ya nuna ba bikin sunan Hausawa ba ne, na wata ƙabila ne. A ɓangaren mutuwa kuwa, akan yi watsi da al’adar gida da kuma rungumar ta wasu mutane da ba Hausawa ba. A al’adance, duk gidan da aka yi rasuwa za a ɗauki tsawon kwana uku ana zaman makoki. Haka kuma duk yadda rashin jituwa ya kai tsakani, wani bai ganewa a wurin zaman makoki. Tare da haka an sami faɗa tsakanin ‘yan uwa har sai da aka raba su a wurin karɓar gaisuwar mahaifiyarsu da ta rasu. An yi haka a cikin fim ɗin ‘Mahaifiyarmu’. Yin faɗa a wurin bikin farin ciki ya saɓa wa al’adar Bahaushe balle a wurin zaman makoki.

    3.2.2.2 Fitar Tsiraici Da Aron Al’adun Wasu

    Hausawa na da kamala ta ɓangaren tufafinsu domin al’ada ba ta bar su sagaga ta hanyar sanya tufafin da suka ga dama ba. Abin kunya ne ga ‘ya’yan Hausawa a ga sun yi fita irin ta wata al’umma. Wannan ya sanya aka ƙyamaci ‘yan gaye masu sanya tufafin Turawa irin ƙaramar tagguwa (Shirt) da wando da takalma masu tsawo da ake kira ‘Higher Hils’. Saboda saɓa wa al’ada ta fannin tufafi da samari ke yi a wancan lokaci, har waƙa ake yi wa mai wannan irin fita ana cewa:

    Ɗan gaye mugun bawa,

    Ya share gidansu da falingo”.

     

    Idan aka dubi yara ‘yammata na cikin fim da irin fitar da suke yi sai a ce Allah ya sauƙaƙe. Sun yi sanadiyyar ‘ya’yan Hausawa mata na kwaikwayon tufafin da suke sanyawa a cikin fina-finansu. Suna amfani da tufafi masu matse musu jiki tare da bayyanar da al’aura a fili. Haka kuma suna yin ɗunki iri-iri masu bayyana siffar jikinsu. Daga cikin waɗannan ɗunkuna akwai ‘sakaɗa hannunka masoyi’ da ‘show me your back’ da ‘half sunna’ don tsananin izgili ga addini da sauran kalar ɗunkuna daban-daban da ba sai an ambaci sunayensu duka ba domin, mai karatun wannan bayani ya ɗara waɗanda suka rubuta shi sanin waɗannan abubuwa. Haka kuma suna sanya tufafi masu raga da ke bayyana al’aura, waɗanda ba ɗabi’un Hausawa ba ne. Idan aka sami waƙar sarkin Taushin Katsina ta ‘Festac ‘77’ za a ji yadda ya sifanta Bahaushe ta fannin tufafinsa. Wannan ya saɓa wa al’ada ƙwarai ba kaɗan ba. Mutanen zamani ba su da tunanin gano illar wannan abu domin, ra’ayin da suke da na ganin wayewa ne su yi watsi da al’adunsu tare da muhimmantar da na wasu al’ummu a kan nasu.

    3.2.3 Wulaƙanta/Tozarta Igiyar Aure

     Ɗaukar wani abu mai muhimmanci ba bakin komai ba ake nufi da wulaƙantarwa. A cikin fim akan sami matar aure ta nuna ba ta da aure don neman ha ɗa soyayya da wani. Haka kuma akan sami wasu daga cikin maza masu aikata irin wannan ta’asa. Igiyar aure ba abin wasa ba ce. Abin da takardar ta hango dangane da wulaƙanta igiyar aure shi ne mijin aure ya nemi matar aure da lalata ko matar aure ta nemi wani namiji da lalatar. Tunanin ‘yan fim a duk wurin da aka nuna haka shi ne su faɗakar tare da nuna wa al’umma rashin kyawon abin domin a guje shi.

    Su kuma masu kallo ko yaushe suna kallon ‘yan fim lalatacci ne, bara- gurbi da ba su da aiki sai lalata al’umma ta hanyar nuna musu yadda ake saɓon Allah da nufin a ji daɗin rayuwa. Haka ya sanya Wasila ta janyo wani kwarto a gidanta har aka nuna ta kwanta da shi, mijin kuwa ya yi waƙar ‘Wasila Kin Ci Amanata’ don nuna jin zafin abin da ta yi mishi. Fim ɗin ‘Wasila’ sananne ne kuma fitacce a zamaninsa domin har ƙananan yara ana ji suna cewa, “Wasila Kin Ci Amanata” Wato, maganar da mijinta ke yi a cikin waƙa bayan ya kama ta tare da kwarton. A ɓangaren mata kuma, An kalli wani fim a cikin ‘YouTube’ da wani ya kawo wata kwartanya cikin gidansa sanadiyyar tafiyar da matarsa ta yi ganin gida. Yana cikin ɗaki da matar banzar sai ga matarsa ta dawo gida domin tafiyar ba ta yiwu ba. Mijin ya yi amfani da dabaru daban-daban ta yadda kwartanyar za ta fita ba tare da matarsa ta gano sirrin ba. A  ƙarshe ya samar wa matar hoda ta shafa a fuskarta, ta fito a sifar dodanni ta biyo bayan matar mutumin tana bu ɗar ido tamkar fatalwa, matar na kallo har ta bar gidan. Matar na kuwwa mijin ya zo ya ga abin da ta gani, ya zo ya ce bai ga komi ba.

    Wannan ya sanya an sami matan aure da ke hulɗa da wasu mazan banza sanadiyyar koyi da abin da kwartayen suka aikata. Matar aure ta yi hul ɗa da wani mutum ta hanyar kwartanci wulaƙantar da igiyar aure ne kuma, yana dalilin a saki mata ta koma gidansu. Ba wannan ka ɗai ba, takan iya rasa miji har abada ba tare da ta sami mai auren ta ba sanadiyyar wannan wula ƙantar da igiyar aure da ta yi.

    3.2.4 Shaye-Shaye

    Shaƙa ko sha ko haɗiyar wani abu da niyyar a fita hayyacin da ake ciki a yi maye don biyan wata buƙata shi ne shaye-shaye. Mafi yawa daga cikin al’umma sun sami kansu cikin wannan halin shaye-shaye saboda wasu dalilai. Ba ana so a ce masu gudanar da harakar fim mashaya ba ne, sai dai an ga biri ya yi kama da mutum a wasu wurare. A cikin fim wani aiki ba ya yiwuwa sai an gusar da hankali. A taƙaice akwai wurin da aka nuna wani ɗan fim ya yi wa surukarsa fyaɗe sanadiyyar shan da ya yi. Idan an dubi fim ɗin ‘Ƙara’i’ za a ga haka. An nuna ana shan kodin da ƙwaya domin, wani aiki ba na hankali ba ne. Saboda haka ne aka zaɓi a sha a nakkasa, a yi abin da aka ga dama. Irin waɗannan ayyuka ba su yiwuwa sai an gusar da hankali. Ba sai an zurfafa kan shaye-shaye ba domin an san illarsa kamar yadda Kyaftin Umaru Ɗa Suru ya yi bayani a cikin baitocin waƙarsa da aka kawo misali a ɓangaren lalata tarbiyyar al’umma musamman matasa.

    ‘Yan fim na wa ɗannan abubuwa ba tare da sun san ana koyi da su ba sai dai, fim makaranta ce da kowane  ɗalibi na samun daidai gwargwadon ilmi daga malamin da ke karantar da shi. Masu aiwatar da fim ba su san da duk abubuwan da suke aikatawa ana kwaikwayon sa daga gare su ba. Wani abu da ya kamata a sani shi ne, yaro na koyon abu ba tare da sanin amfani ko illarsa ba. Idan ya koye shi yana yaro zai ci gaba da aikata shi har lokacin da abin ya zama jiki a gare shi. Haka kuma lokacin da yana kallon abin bai iya gano illar da ke tattare da shi. Wannan ya nuna cewa, yi wa yaro tarbiyya tun yana  ƙarami shi ya fi kamar maganar Hausawa da suka ce “Geza tun tana  ɗanya ake tan ƙwara ta”. Da zarar abin ya zame masa jiki ko ya girma hankalinsa ya kawo ya gane cewa abin ba mai kyau ba ne, jiki ya saba don haka da wuyar gaske a daina. Irin wannan ne ke faruwa ga shaye-shaye da masu yin sa. Don haka, shi ya sa Bahaushe ya yi wata karin magana mai cewa “Sabo turken wawa”.

    3.2.5 Tilasta Wa ‘Ya’ya Neman Maza

    Idan dai Bahaushe ake magana da wuya a sami mahaifi ya nuna wa ‘yarsa ta je ta nemi maza don wata buƙatar da yake da ita ta kuɗi amma, sai ga shi a cikin fim ɗin Ƙara’i an nuna wani Malam Musa ya nemi wata ‘yarsa budurwa ta ba shi kuɗi. Yarinyar kuwa budurwa ce son kowa ƙin wanda ya rasa. Ta mayar da tambaya ga baban cewa, ina za ta samo kuɗi? Kai tsaye ya kayar da baki ya ce mata ‘Ga samari nan a gari? Za a sami wannan a cikin fim mai suna ‘Babban Yaro’. In tambaye ku, kun aminta da ‘yar cikinsa ce? Idan amsarku e, to ina ganin ba Bahaushe ba ne, sai dai yana zaune cikin Hausawa kawai. Ba a rasa masu tsawatawa a cikin fim kan irin wannan muguwar ɗabi’a sai dai mafi yawan mutane a cikin al’umma ba su da sanke ga abin da ya shafi mata. Dalili a nan shi ne, duk wurin da mace ke tare da namiji, Shaiɗan na nan zaman na uku kuma, aikinsa bai zarce a aikata abin da Allah ya hana ba.

    3.2.6 Yaudara/Zalunci Da Kwaɗayi Da Sagarci Da Ƙulla Fasadi

    Akan sami wasu mayaudara su yaudari abokan wasarsu a cikin fim. Misali, an sami wani bakanike mai suna Ɗan Auta a cikin fim mai suna ‘Babban Yaro’ da mani mutum (Basakkwace) ya kai wa gyaran mota ya cuce shi don ganin gara (baƙauye) ne. A nan, akwai rashin amana kamar yadda Annabi ya ce duk wanda aka amince da shi ya yi yaudara munafukin Allah ne. Wannan ɗabi’a na nan cikin kanikawa face kaɗan da Allah ya tsare. Aikin ‘yan fim su faɗakar amma, ana koyon miyagun ɗabi’u masu yawa daga cikin abubuwan da suke yi. Abin da ya dace a sani a nan shi ne, kallon fim da wasu ke yi ba domin rage dare da sha’awa ba ne. Suna yi ne domin koyon dabarun yaudarar al’umma kamar yadda suka ga an yi a cikin fin ɗin da suka kalla. Masu yin fim na yi domin nuna rashin kyau kar a yi. Shi kuma macuci ya fi son ya ga yadda ake cuta domin ta zama karantarwa gare shi.

    Kwaɗayi ruwan dare ne game duniya musamman ga wanda ba ya iya nemo wa kansa abin buƙata ta hanyar halal. Misali akwai kwaɗayi ga ‘yan mata a kan nuna ba su auren talaka sai mai hali. Kun sani da yawa ake gudun gara a faɗa zago. A fim ɗin Babban Yaro har yanzu an sami wata yarinya ta tsaya kai da fata ba ta son talaka sai mai mota. An san ana aron mota a yaudari ‘yan mata ba. An yi haka ba iyaka. An ari riga an yi yaudara balle an sami mutum makwaɗaici? A irin wannan da yawa ake yaudarar mace mai kwaɗayi ta hanyar ba ta abin da take buƙata ba da niyyar auren ta ba sai don a lalata ta. An sha ganin irin wannan a fili ba sai a cikin fim ba.

    Sagarci na ɗaukar ma’anar lalaci sanadiyyar jin daɗi a ƙarƙashin wani mutum. Waɗanda suka fi sagarci cikin al’umma su ne waɗanda kakanni suka riƙa. Shi ya sanya ana cewa jika wanda ya fi ɗan ciki daɗi. An sami irin wannan sagarci a cikin wani fim inda Ɗan’auta ke ƙyamar ɗumame (kwanannen tuwo) sai dai kakarsa ta ba shi kuɗi (naira hamsin ko ɗari) ya sayi shayi. Wannan ƙyamar ɗumamen tuwo da ya yi shi ake kira sagarci kuma, akwai fifita abincin baƙi a kan na gargajiyar Hausawa. Wannan na nan cikin fim ɗin Babban Yaro. A nan, kakar ta yi sanadiyyar sagarcewar jikanta domin idan ba ta nan wa zai rinƙa ba shi kuɗin shan shayi? Don gudun irin wannan ya dace duk wanda ke da halin riƙon ‘ya’yansa ya riƙe kar ya bar su a wurin kaka kowane.

    Babu abin da ya kai haɗe mata da maza wuri ɗaya zama fasadi. Babu mai cewa a yi masa bayanin yadda haɗe maza da mata wuri ɗaya ya zama fasadi domin zancen Allah ya gabata. Haka kuma, duk haɗuwar mata da maza da ba ta addini ba, kuma ba da iznin addini ba fasadi ne. Bayan wannan ana sane da cigaban mai ginar rijiya da zamani ya kawo na haɗuwar mata da maza a wuri ɗaya. An haɗa mata da maza a wuri ɗaya cikin fim ɗin ‘Babban Yaro’ wurin da aka bayyana haɗuwar mata da maza wuri ɗaya fitina ce, lokacin da wani wanzami na yi wa wani mutum aski, saboda ɗaukar hankalinsa da matan suka yi, ya haddasa ya yanke wa mutumin kunne wajen kallon mata lokacin da yake yin aski. Saboda kallo kaɗai ya sanya an yanke kunnen wani ina ga haɗuwar jiki? Kuma muna da labarin da Annabin rahama ya ba mu cewa, da za a kai jijiyar namiji a bangon gabas, a kai ta mace a bangon yamma, da sun yi ƙoƙarin haɗuwa saboda ƙaunar da ke tsakaninsu. Waƙe-waƙen da ke gudana cikin fina-finai tsakanin mata da maza ƙulla fasadi ne idan aka yi la’akari da maganar Annabi da ke sama dangane da jiyojin namiji da mace da ke gabas da yamma, balle ga su wuri ɗaya?

     

    3.3 Bayyanar Da Kishin Hauka

    Hausawa sun ce “Kishi kumallon mata’’. Ma’ana, rashin lafiya ne gare su don haka matuƙar suna da abokiyar zama sai rashin lafiyar ya bayyana gare su. Mata na nuna kishi tsakaninsu tamkar maƙiya juna ta hanyar nuna ƙiyayya. Akan samu wasu mata har wurin boka suke zuwa domin hallakar da abokan zama da ‘ya’yansu baki ɗaya. Takardar na ganin kishi rashin lafiya ne da ke cikin ƙirjin kowane mutum. A cikin fim mai suna ‘Kishiyar Gida’ an samu wata mata mai tsananin kishin hauka da ta yi tattaki zuwa gidan wadda mijinta ke nema aure. Da isar ta gidan ta haɗu da wadda mijinta ke nema aure. Ta yi tambaya ko gidan ne, aka ce mata nan ne. Ba ta fara da komai ba sai marin wadda mijinta ke nema aure. Mahaifiyar wadda ake nema aure ta tambayi matar, me aka yi mata har ta zo tana yi musu hargagi a cikin gida? Sai ta ce “Abin da na yi ba hargagi ba ne, sunansa gargaɗi”. A taƙaice har da zagin matar ta yi a kan tambayar da ta yi mata.

    A wata fitowa kuma, ta haɗu da mijinta na tare da wadda yake nema aure kuma ta tayar da rikici. Ana nan sai ga wata mata ta zo ta tambayi abin da ya faru. Mijin ya yi mata bayani, ta koma kan matar tana ba ta haƙuri da sauran jawabai masu amfani sai matar ta ce wa tsohuwar “Mama ba zan ji huɗubarki ba idan dai a`kan kishiya ne. Ba zan aminta kowace mata ta zo gidana ta raba ni da mijina ba”. A nan ma har zagin tsohuwar ta yi in da ta ce “Mama, zan zagi uwarki idan kika ƙara yi min magana”. Bayan tsohuwar ta wuce, har dambe ta soma yi da wadda mijinta ke nema aure. Mijin ya ce wa wadda yake nema aure ta je ta shiga mota su wuce, matar ta je ta hana matar shiga motar, tana zagin ta tana faɗin “Ba za ta shiga motar ba tun da ba ubanta ya saya ba”. Idan ba hauka ba me ya kai ta gidan matar da mijinta ke nema aure?

    An kuma sami wata mata da ta tarar da wadda mijinta ke nema da aure a kan hanya ta gwada kishin hauka, inda ta zo ta tarar wadda mijinta ke nema aure tana sayar da ɗanwake. Da ta zo nan ba ta bar wurin ba sai da ta yi faɗa da matar. Tana cikin faɗa da matar da kuma zubar mata da sana’a a ƙasa, sai mijinta mai suna Mukhtar ya zo ya tarar tana abubuwan da ba su dace ba. A ƙarshe sai da mijin ya mare ta cikin jama’a a gaban wadda ta yi faɗa da ita. A nan mai ɗanwaken ta tambayi Mukhtar yana son ta? Ya amsa mata da e. Ta ce to, tana son a ɗaura musu aure a yau. Mukhtar ya tambaye ta cewa shi kaɗai take so? Ta ce i. Ya ce ta kwantar da hankalinta za a ɗaura musu aure a yau ɗin. Duk abin da ke gudana a gaban matar da ta zo faɗa da wadda mijinta ke nema kuma, ba ta hana ba. Wannan ne ya sa takardar ta yi wa wannan kishi suna kishin hauka.

    4.0 Sakamakon Bincike

    Wannan bincike da aka yi ɗan tsokaci a kansa an gano cewa, finan-finan Hausa na da amfani da kuma matsalolin da suka kawo wa al’ummar Hausawa. An gano daga cikin amfanin da ake samu da fim ke kawowa sun haɗa da kasancewarsa sana’a da samar wa jama’a aikin yi da faɗakarwa da ilmantarwa da samar da nishaɗi da ƙulla zumunta da taskace wasu daga cikin al’adu da tarihi da kuma bunƙasa kamfunnan fim. A ɗayan ɓangaren kuma, an gano cewa fim na tattare da matsaloli masu yawan gaske da ya kawo wa al’ummar Hausawa. Matsalolin finan-finan Hausa sun haɗa da yin taho-mu-gama da karantarwar addinin Musulunci da ruguza tarbiyya da ruguza al’adun Hausawa da sabbabar da fitar tsiraici da wulaƙanta igiyar aure da shaye-shaye ga al’umma da haddasa lalaci ga ‘ya’yan Hausawa musamman mata inda aka sami yaudara da yawan kwaɗayi da sagarci da ƙulla fasadi da kuma aikata kishin da ba a san Hausawa da shi ba.

    5.0 Shawarwari

    Shawara ga masu sana’ar fim ita ce su tsayar da ƙafa domin yin la’akari da saƙon da suke aikawa ga jama’a kuma, su kula da ɓangaren da al’umma ke kallon kasawarsu a ciki. Ya dace su sami masu ba su shawararwari da duba musu fina-finansu kafin a saka su kasuwa. Su nemi shawarwari ga malumman addini da masana sana’ar fim tare da yin la’akari da ‘yan wasan da za su zaɓa don gudanar da aikinsu. Bayan haka, su rinƙa duban matsalar da ke tare ga kowane saƙo da suke son isarwa ga al’umma. Kar su yi abin da ke kawo rabuwar kawunan al’ummar Hausawa da na masu addini.

    6.0 Kammalawa

    Wannan takarda ta tattauna abubuwa iri biyar a cikinta da suka haɗa da gabatarwa da taƙaitaccen tarihin fim da ma’anar fim da asalinsa da maudu’in takardar wato, fina-finan Hausa a mahangar al’umma da aka yi tsokaci kan amfani da kuma matsalolin fim ga rayuwar Hausawa (Gyara da ɓarna). Fatarmu ita ce a inganta sana’ar fim ta hanyar neman shawarwari ga masana tare da tace shi kafin a saka kasuwa.

     

    Manazarta

    Tuntuɓi masu takarda (lambobin wayoyinsu na sama).

     

    Mutanen da aka yi hira da su

    Suna

    Sana’a/Aiki

    Ƙiyasin Shekaru

    A’ishatu Muhammad

    Ɗalibta

    16

    Abdullahi Sani

    Ɗalibta

    36

    Abdullahi Sarkin Gulbi

    Aikin Gwamnati

    50

    Abu-Ubaida Sani

    Aikin Gwamnati

    27

    Alhaji Na’allah Muhammad

    Aikin Gwamnati

    60

    Altine Muhammad

    Aikin Gwamnati

    61

    Aminu Ango

    Aikin Gwamnati

    50

    Asma’u Alhaji Isah

    -

    34

    Bello Muhammad

    Aikin Gwamnati

    42

    Danladi Dammu

    Aikin Gwamnati

    62

    Dansule Bahago

    Aikin Gwamnati

    70

    Faruku Jingi

    Aikin Gwamnati

    40

    Fatima Usman

    Ɗalibta

    12

    Hadiza Aliyu

    -

    43

    Halima Ahmad

    Aikin Gwamnati

    40

    Ibrahim Umar

    Aikin Gwamnati

    35

    Jamila Usman

    Ɗalibta

    24

    Khalid Muhammad

    Aikin Gwamnati

    35

    Kware Na’amada Tela

    Aikin Gwamnati

    58

    Malam Jaɓɓi Bunza

    Aikin Gwamnati

    40

    Muhamman Ɗangoggo

    Aikin Gwamnati

    60

    Musa Shehu

    Aikin Gwamnati

    40

    Namata Naizagu

    Noma

    61

    Rabi’u Aliyu Rambo

    Aikin Gwamnati

    50

    Shekare Tanimu

    Aikin Gwamnati

    40

    Umar Aliyu Bunza

    Aikin Gwamnati

    46

    Umar Shehu

    Aikin Gwamnati

    43

    Zainab Muhammad

    Ɗalibta

    20

     

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.