Sau da dama akan samu dangantaka tsakanin al’ada da adabin Bahaushe. Irin wannan dangantaka ce za a tarar yayin da aka nazarci waƙar Bahaushen Girka ta Sulaiman A. Tijjani. Dalili kuwa shi ne, a cikin waƙar ya zayyano al’amuran da suka shafi al’adar girka daki-daki. Wannan takardar ta mayar da hankali wajen nazarin waƙar domin fito da muhimman kalmomi da Sulaiman Tijjani ya yi amfani da su da ke da alaƙa da al’adar bori da girka. An bi manyan hanyoyi guda biyu domin gudanar da wannan bincike. Hanya ta farko ta shafi nazarce-nazarcen ayyukan da suka gabata masu dangantaka da binciken. Bayan haka kuma, an yi ziyarar gani-da-ido zuwa wuraren da ake gudanar da bori domin samun ingantattun bayanai daga tushe. Sakamakon binciken na nuna cewa, mawaƙin ya yi ƙoƙari wajen samar da bayanai masu inganci game da al’adar girka. Dangane da hakan ne takardar ke ba da shawarar cewa, a ba da ƙaimi wajen nazartar ire-iren waɗannan waƙoƙi da ke ƙunshe da al’adun Hausawa.
Muhamman Kalmomi: Bori; Girka; Bahaushen Girka; Waƙa; Al’ada
Bori Da Girka A Bahaushen Tunani:
Duba Cikin Waƙar
Bahaushen Girka Ta Sulaiman A. Tijjani
YUNUSA IBRAHIM ADAMU
Center for Hausa Studies
Usmanu Danfodiyo University,
Sokoto
08037593085
Gabatarwa
Adabi wani lamari ne mai
matuƙar muhimmanci a wajen kowacce al’aumma. Sai dai manazarta Adabi suna
amfani da kalmomi biyu wajen bayyana rayuwar Bahaushe ta asali. Kalmar ‘adabi’
ta fi shahara a bakin manazarta ko masu ilimi. (Ɗangambo, 1982:3) Ita kuwa
Kalmar ‘al’ada ta fi zama a bakin mutanen gari da kuma masana addini. (Bunza,2001) Amma duk da cewa manazarta
suna kallon Kalmar a matsayin ‘adabi’, a iya cewa idan ka ambaci adabi dole sai
ka fassara wa mutanen gari abin da ake nufi da kalmar. Domin an yi ittifaƙin
cewa adabi yana da rassa biyu, wato na baka da rubutacce. (Umar, M.B 1982)
Ita kuwa Kalmar ‘al’ada’
ita ma ararriya ce daga harshen Larabci, wacce ita a gangariyar Hausa ake cewa
‘gargajiya’. Sai dai yarda da addinin musulunci ne ya sa, Bahaushe ya maye
gurbin kalmar gargajiya da ta al’ada. Sakamakon yadda duk wani lamari da
Bahaushe yake son ya kauce masa sabo da tasirin addinin musulunci. Hakan ya sa
da wuya ka ji an ambaci kalmar gargajiya, sai dai a ce al’ada. Dan haka al’ada
ita ce hanyar rayuwar kowacce al’umma. Ita ce hanya ɗaya tilo ta rayuwar
kowanne mutum tun daga haihuwarsa da balagarsa da girmansa da Aurensa da kuma
mutuwarsa (Yahaya, I.Y.
1978).
Manufar
Bincike
Manufar wannan bincike
shi ne wayar da kan Manazarta game da lamarin Bori da kuma Girka. A irin wannan
manufa ne, za a ga yadda za a samar da wani bayani mai ɗauke da yadda tsarin
Bori yake faraway. Kafin mutum ya zama cikakken Ɗan Bori, har wani yanayi ya sa
a yi masa girka. Wata Manufar kuma ita ce samar da abin karantawa ga Ɗalibai da
masu sha’awar Nazarin harshen Hausa. Da nufin inganta ɓangaren Adabin Bahaushe
da kuma Al’adunsa. Haka kuma yana daga cikin Manufar wannan bicike yin hannunka
mai sanda domin a san yadda lamuran suke, sannan a rairaye tsakuwa daga cikin
tsakin. Wato a ɗauki masu amfani da adana Tarihi, kuma a watsar da Baragurbin.
Dabarun
Bincike
Bahaushe ya yi gaskiya da
ya ce “Kowanne bakin wuta, da nasa hayaƙi” Kamar kowanne bincike ita ma wannan
takarda ta yi amfani da irin nata dabarun domin ganin kwalliya ta biya kuɗin
Sabulu. Da farko dai an kunna nutso a cikin waƙar ‘Bahaushen Girka’ wacce
Sulaiman Ahmad Tijjani ya rera. Sai da aka tabbatar an fitar da tsoka daga
ƙashi kafin ma fara wannan aikin. Sai kuma duba manya da ƙananan kundayen
bincike masu alaƙa ta kusa da wannan aikin. An sake duba manyan litattafan adabi
da al’ada dan wannan bincike ya samu nasara. Sannan an je ƙafa ya ƙafa wajen da
ake aiwatar da lamuran bori da girka, dan zama ganau ba jiyau ba. A ƙarshe kuma
an tattauna da ƙwararru a harkar bori da girka da bayar da magungunan
gargajiya, duk dan wannan aikin ya yi nasara.
Taƙaitaccen
Tarihin Sulaiman Ahmad Tijjani (Farfesan Waƙa)
A wata hira da Sulaiman
Ahmad Tijjani ya yi a cikin shirin ‘Hikima Taguwa’ na gidan Rediyon Garkuwa Fm.
Dake birnin Sakkwato. Ya bayyana cewa an haife shi a ƙauyen Paki dake yankin ƙaramar
hukumar Ikara ta jihar Kaduna. A ranar 2 ga watan Fabaraiyun, 1985. Yanzu haka
yana da shekaru 36. Ya yi karatun Firamare a makarantar Paki Central Primary
School, ya kuma yi ƙarama da babbar Sakandare a Sakandaren Paki da ake kira da
GSS, Paki. A inda ya kamala a shekarar 2010. Ya ce “ A gidanmu muna da wata
al’ada ta idan Yaro ya kammala karatun Firamare, akan zaunar da shi a gida da
nufin koyar da shi ilimin addinin Islama. Tun daga kan karatun Allo na Alƙur’ani
mai tsarki, da kuma litattafan koyon tsarki da koyon Tsarki da Alwala da kuma
Sallah”. Bayan ya gama irin waɗancan litattafai, sai ya wuce GSS, Paki kamar
yadda aka faɗa a baya.
Sulaiman, ya fara waƙa ne
tun yana Yaro ƙarami, mutum ne mai son yawan yin rubutu na zube da ‘yan waƙoƙi.
Sai dai abin da zai iya tunawa shi ne, a shekarar 2011 ne ya tsunduma a harkar
waƙa sosai da sosai. A lokacin ne ya fara zuwa Sitidiyo domin buga waƙa. Wannan
a taƙaice Kenan.
Bayan an ji ta bakin
masana game da adabi da kuma al’ada, abu na gaba a cikin wannan maƙala za a
duba yadda Bahaushe yake kallon Bori da Girka, da yadda aka yi baje-kolin
al’adu a cikin Waƙar ‘Bahaushen girka’ wacce Mawaƙi Sulaiman A. Tijjani da aka
fi sani da Farfesan waƙa ya wallafa.
Bori
Wata hanya ce ta bautar
Iskoki, kamar yadda Musulmai ke bautar Allah (SWT) da nufin neman biyan buƙata.
(Bunza 1990) Haka kuma Bori wata daɗaɗɗiyar al’ada ce da ake yi a ƙasar Hausa
tun kafin zuwan addinin Musulunci. Hanya ce da ake bi wajen bautar iskoki a
matsayin addini. Domin nema da samun dukkan buƙatu daga Aljanu ko Iskoki. Masu
riƙo da wannan al’ada ta Bori, sun yarda kuma sun amince cewa bautar irin waɗannan
Iskoki ita ce hanyar samun duk wani magani ga marasa lafiya ko masu lalura.
(Uba 2006:304)
Sai dai sharuɗan dake cikin wannan addini na
Bori shi ne, dole ne sai ka kasance kana da Iskoki da suke a kan ka ko kan ki,
kafin ka zamo ƊanBori. Idan kuma kana da sha’awar ka shiga wannan addini kuma
baka da irin waɗancan Iskoki, sai ka zauna da manyan Sarakunan Bori da manyan
Bokaye a girka ka, kafin ka samu shiga cikin irin wannan addini.
Haka kuma Bunza, (2006:25) Ya raba Bori ya zuwa kashi huɗu
kamar haka:
1.
Borin Fage
2.
Borin magani
3.
Borin giri
4.
Borin girka
A nan, wanna maƙala za ta
fi mayar da hankali ne ga ‘Borin girka’ wanda a kan sa ne Sulaiman Ahmad
Tijjani da aka fi sani da Farfesan waƙa ya gina waƙarsa ta ‘Bahaushen girka’
Girka
Wannan na nufin kafe wani
abu ko ɗora wani abu a kan wani da nufin a zaunar da wannan abin a kan wani. Za
a iya tabbatar da wannan ma’ana idan aka dubi Kalmar ‘Girki’. Kowa ya san cewa
idan aka ce “Furera tana yin girki”. Abin da mutum zai sa ran ya gani shi ne,
ya ga an ɗora tukunya a kan murhu ana dafa abinci. Waccan ɗora tukunyar da ake
yi a kan murhu, ita ce girkawar. Amma a harshen Bori idan aka ce ‘girka’ ana
nufin zaunar da wasu gungun Aljanu ko Iskoki a kan wani Bil’adama da nufin su
saba da shi su riƙa yi masa hidima, ta fuskar bayar da magungunan dukkan
cututtuka. Sannan girka na daga cikin lamura masu wahalar aiwatarwa a cikin
aikin Bori, domin sai an tanadi kayayyakin da za a yi amfani da su a wannan
aiki na girka. Hakan ta sa ba a iya yin girka a lokaci guda. Kuma dole sai an
yi tarayya da juna, wato mutum guda ba zai iya aiwatar da girka shi kaɗai ba.
Bahaushen
Girka
Waƙar Bahaushen girka, waƙa
ce da a cikinta mawaƙin ya zayyano ma’anar Bori da kuma Ɗan Bori. Da irin
zurga-zurgar da ake yi kafin a zama ƊanBori. Har ya kwatanta shi da ‘Hurtumin
Sa’ wato irin artabun da ake yi da gawurtattun Shanu. Da irin yadda suke
dalalar da yawu mai yauƙi da kumfa kamar dai yadda Sa mai asurka yake yi. A
gaba kuma ya ambace shi da irin Amalen Raƙuma, da irin tsallen da Amalen Raƙuma
yake yi a dokar daji, ko a duk lokacin da wani abu ya taso, haka ƊanBori yake
yi, a lokacin da ake yi masa girka.
An rera wannan waƙa ne
domin zayyano lamarin Bori da kuma yadda idan lamura sun gawurta ake tashi daga
ƊanBori gama-gari a koma ‘girkakken ƊanBori. Kamar yadda mawaƙin ya faɗa tun a
farkon buɗe waƙar kamar haka:
Jagora: Yin baitukan
Bahaushen girka, na san muna da turka-turka
Farfesan Waƙa nai waƙa na bankaɗo Bahaushen
girka
Har na aza shi bisa misalign nan na hurtumi na
Sa da asurka
Amshi: Bauri da Bori ware
bare baubauniya rawarsu ta dauri
Na bankaɗo Bahaushen girka
Amshi: Bauri da Bori ware
bare baubauniya rawarsu ta dauri
Ya bankaɗo Bahaushen girka
Jagora: Yin baitukan
Bahaushen girka na san muna da turka-turka
Farfesan waƙa nai waƙa na bankaɗo Bahaushen
girka
Har
na aza shi bisa misalin nan na hurtumi na Sa da asurka.
Tun a amshin waƙar Mawaƙin
ya bayyana ma’anar Bori da cewa wani lamari ne da ya kangare ko kuma wani ya
tashi daga asalin siffar da aka san shi. Wato ya koma wata siffar. Kamar a ce
ka tauna Gyaɗa Bori, kana tsammani da ka tauna za ka ji garɗi a baki, amma sai
ka ji ta sauya daga garɗin ta koma wani yanayi na da ban. Sai kuma ya ambaci
‘Baubauniya’ wato wata rawa da masu Bori ke yi, kafin ajanun su iso garesu. Sai
kuma a ɗango na gaba ya shiga cikin waƙar da bayyanar da al’adun dake cikin
addinin Bori da kuma yadda ake yin aikin girka, kamar haka:
Jagora: Ɗirkaniyar kiran ‘yan kogo
wane mutum ya rushe girka,
In an yi katarin haɗa komai sai ran shigar su
wa Dokin ka,
Mai Kacakaura ga su garaya sautin a gane taken
iska,
Gaɗa Ira’izai an ca-cum ga
Julkukuwa mutanen girka,
Amshi: Bauri da Bori ware
bare baubauniya rawarsu ta dauri
Ya bankaɗo Bahaushen girka
A ɗangon da ke sama
Sulaiman A. Tijjani ya yi baje-kolin al’adun Bahaushe ta fuskar Bori da yadda
ake yin girka. A inda yake gani wani babban al’amari ne, da Hausawa ke yi tun
iyaye da Kakanni, wanda yake ganin zai yi wuya rana ɗaya a tsawatar, ko a hana
aiwatar da Bori ko lamarin girka.
A bisa al’ada Garaya da
Goge aka fi sani da kayan kiɗan ‘Yanbori. Kayan kiɗa ne da kowa ya san ake
amfani da su wajen kaɗa taken iskokin da ake son su zo dan su hau kan mutum.
Ita garaya, abin kiɗa ne da ake yi da karamin Ƙoƙo da sanda da izga ko tsirkiya
ake kaɗawa da ‘ya’yan wuri. Ana samar da dukkan sautin da ake bukakata. Sai
kuma ‘Caki’ shi kuma butar duma ce ake fafewa, idan ya bushe sai a rarake
cikinsa akan zuba ‘ya’yan tafasa ko na Zogale busassu. Sai a toshe bakin ta
yadda ‘ya’yan ba za su zubo ba. Da shi ake girgizawa, ana bugawa a ɗaya hannun
da aka sa ‘ya’yan wuri a jiki duk dan ya bayar da sautin da ake buƙata.
Bayan waɗannan bayanai da
suka gabata, a yanzu wannan muƙala za ta kunna nutso a cikin wannan waƙa ta
Bahaushen girka, domin yin taza da tsifa, wajen ganin an zaƙulo al’adun
Bahaushe a ciki.
5.
Jagora:
Yin baitukan Bahaushen girka na san muna da turka-turka
Amshi:
Bauri da Bori ware bare
6.
Jagora:
Domin aza shi nan ga misali na Hurtumi na Sa da asurka,
Amshi: Ya
bankaɗo Bahaushen girka,
7.
Jagora:
Ranar shiga da rana ta fita bishiyar Kuka a nan zai wanka,
Amshi:
Baubauniya rawarsu ta dauri
8.
Jagora: Mutantani su hau bisa Dokinsu sai
mu ce Bahaushen girka.
Tun
a ɗango na biyar da na shida da bakwai da kuma na takwas, Mawaƙin ya fara
zayyano yadda ake girka kafin a zama cikakken Ɗanbori. Wato irin faɗi-tashin da
ake yi kafin a kai ga nasara. Kamar yadda ya ambaci girka da kalmar
turka-turka. Wato akan sha wahala sosai kafin a kai ga girka mutum ya zama ɗanBori.
Sai
a ɗango na bakwai ya yi bayanin inda ake yin girka. Wato ƙarƙashin bishiyar
Kuka, wanda bisa al’ada ba dole sai kuka ba, akwai bishiyoyi da yawa a ƙasar
Hausa, da Bahaushe ya yi imanin cewa ana samun iskoki ko mutanen ɓoye a
jikinsu. Irin waɗannan bishiyoyi sun haɗa da Tsamiya da Kuka da Tumfafiya da
Marke da Zuwo da Kargo da Sabara da Danya da sauransu. Sai kuma ya ambaci ranar
shiga da kuma ranar fita. A Bahaushiyar al’ada, akan shirya ranar da za a girka
Ɗanbori ne, wato akan sanya wata rana da ake ganin cewa ita ce wacce ta fi
dacewa da a kira waɗannan iskoki. Domin sun yarda cewa, idan aka sa wata ranar
da ba ta zuwan iskoki ba, lallai in za akwana ana kaɗa garaya ko goge, ba za su
zo ba. Dan haka a wasu lokutan akan sa ranar Lahadi ko Talata ne, su kasance
ranar shiga. Wato ranar da za a fara wannan aiki na girka. Ya danganta da yadda
aka tattauna da sarakunan Bori, ko manyan Bokaye. Domin sa irin wannan rana.
Sannan wajibi ne a aike da goron gayyata ga mutane masu irin wannan sana’a ta Bori
na kusa da na nesa, da nufin su hallara a wannan waje. Domin an ce “Kowanne
bakin wuta da nasa hayaƙi”. Wato kowa da irin gudun muwar da zai bayar wajen
ganin wannan aiki na girka ya kai ga nasara. A lokuta akan sa kwana Bakwai ne
ko fiye da haka. Ya danganta da yadda iskokin suka bayar da haɗin kai, wajen
zuwan su da wuri.
A ɗango na takwas kuma sai mawaƙin ya yi magana
a kan yadda iskokin suke zuwa su hau kan mutum, a inda ya ambace su da
‘mutantani’. A al’adar Bahaushe, da zarar an fara kaɗa taken iska, duk inda ta
ke, za ta zo ta hau kan wanda ake nufin girkawa ne. Wani lokacin sai an yi da
gaske, sannan wata iskar za ta zo. Sukan ce ƙila an ɓata musu rai ne ya sa suka
ƙi zuwa. Ko kuma ba a gama yin yarjejeniya da su ba ne. Wasu kuma salin-alin
sukan zo su hau kan wanda ake so su hau.
9.
Jagora:
Ga tsagwaron tsumi tsumin tsanbauri, kayan shirin Bahaushen Girka,
Amshi: Bauri da
Bori ware bare
10.
Jagora: ‘Ya’yan wuri a nemo warki ranar bikin
ga ba a kuka,
Amshi: Ya
bankaɗo Bahaushen girka,
11.
Jagora: A Hausa nan ake al’ada girka kama ɗaukar
jinka,
Amshi:
Baubauniya rawarsu ta dauri,
12.
Jagora: Zobba da hannuwa da ƙafafu domin a
samu yardarm iska.
A ɗangwaye na tara da
goma da shaɗaya da kuma shabiyu, Malam Sulaiman Farfesan waƙa, ya yi ƙoƙarin
fayyace wasu muhimman al’adun da ake yi a lokacin yin girka. Da farko ya yi
Magana a kan wani tsumi da ake amfani da shi. Dole ne kafin a girka mutum ya
zama Ɗanbori, sai an yi masa wani tsumi, a inda ake samun sabuwar ‘kwatarniya’
a cika ta da ruwa, sai a bazama cikin daji a sassako wasu itatuwa da saiwoyi da
ganyayyaki, wasu lokutan ma har da kitsen wata dabbar ko fatar wasu namun daji.
Bayan an gama haɗawa sai a zuba a cikin wannan kwatarniya a rufe, sai sun samu
kamar mako uku, wato sun gama tsumama, sai ranar da za a fara bikin girka, za a
ɗauko wannan kwatarniya a sanya ta a tsakiyar fili, a nan za a yi wa wanda za a
girka wanka da wancan ruwan magani. A kuma ba shi ruwan ya sha. Haka za a riƙa
yi har bayan kwanakin da sarakuanan Bori suka yanke za a gama aikin girka.
Sai kuma mawaƙin ya ci
gaba da baje kolin al ’adun girka, da zayyano irin kayayyakin da ake buƙata ranar
bikin girka. A nan ya ambaci za a samo ‘ya’yan wuri da warki. ‘Ya’yan wuri wasu
fararen abubuwa ne da ake yin ɗamara da su a ka ko a ƙugu da nufin kiran iskoki
ko kuma barazana ga wanda bai san dawan garin ba. Shi kuwa warki, fatar naman
dawa ce ake jemewa, a tsunduma ta a cikin ruwan shuni ko Baba, da nufin ta
sauya kala, sai a yi mata maɗaurai a sama da ƙasa, ana ɗaura warki a ƙugu ne,
ta yadda duk wanda ya gani zai san cewa akwai wata alama ta jarumta a tattare
da wanda ya ɗaura. Sai ka ga ya zauna cif a jikin mutum, hakan ya sa Hausawa ke
yin Karin Magana da cewa “Warki nake dai-dai da ƙugun kowa”.
A ɗango na shaɗaya kuwa
sai mawaƙin ya yi yabo ga harshen Hausa Da yadda yake ganin a nan kusa yana
wahala a samu wani harshe da zai iya jayayya da harshen Hausa ta fuskar al’adu.
Inda yake nuna lallai harshen ba kanwar lasa ba ne, ta fuskar inganta
al’adunsa. Sai kuma ya nuna irin wahalar da ake sha kafin a gama aikin girka.
Har ya kwatanta aikin da Karin maganar Bahaushe da yake cewa “Hannu ɗay aba ya ɗaukar
jinka”. A nan yana nufin girka wani babban aiki ne, da mutum ɗaya ba zai iya
yinsa ba. Dole sai an haɗa hannu da ƙarfe, kafin a kai ga nasara.
A ɗango na sha biyu, mawaƙin
ya ambaci wasu ƙarin kayayyakin da bisa al’ada ake amfani da su, wajen aiwatar
da aikin girka. Irin wannan kayayyaki sun haɗa da ‘zobe’ ko ‘zobba’, wato ƙawanyar
da ake sa wa a hannu, su ne wanda za a girka, zai sanya su a ƙafafu da hannaye,
duk da nufin idan iskokin sun iso gare shi su yarda kuma su amince su hau kan
wanda ake son a girka.
13.
Jagora: Sandar dargaza da ‘yar bulala ɗamara
tamau abin ba shakka,
Amshi:
Bauri da Bori ware bare,
14.
Jagora: Kai har baƙin zane ga ƙunshi ƙafa da
hannu hanyar boka,
Amshi: Ya
bankaɗo Bahaushen girka,
15.
Jagora: An gabza tozali a idanu alami da goro
leɓɓa toka,
Amshi:
Baubauniya rawarsu ta dauri,
16.
Jagora: Da
turaren wutar kiran ƙwanƙwamai Dogo da Inna na ta jiranka.
A ɗangwayen dake sama,
wato na sha uku da sha huɗu da sha biyar da kuma sha shidda, Farfesan waƙa, ya ci
gaba da zayyano kayayyakin da ake buƙata ne, wajen aiwatar da wannan aiki na
girka. A inda ya ambaci ‘Sandar dargaza da ‘yar bulala, waɗannan suna daga
cikin irin kayan da ake buƙata, wato ita sandar da ita ce ake wulwulawa, wato a
yi ta wurga ta sama, ana cafewa, idan ana yin rawa da juyi, lokacin da ake
kiran iskar da ake so ta zo. Akan yi mata kwalliya da fatoci su yi beza a jiki,
kuma a yi mata ƙunshi kala-kala, yadda za ta bayar da sha’awa. Ita kuma bulalar
akan rataya ta ne a jikin ɗamarar kayan da aka sa na girka. An fi amfani da
wannan sanda da bulala, idan za a hau iska mai suna ‘Babule’, Za a ga yadda
wanda za a a girka ɗin yakan sa kayan ɗamara kamar na sojoji, a tsuke ƙugu, a
sanya ƙwamemen takalmi, a sa hula irin ta Soja, kamar dai Sojan gaske. Haka zai
yi ta rawa yana ƙamewa, yana sara wa mutane, kuma yakan yi amfani da kalanzir
yana fesa wa sama wuta na tashi, shi kuma mai garaya, ko mai goge yana ta yi
masa kirari. Abin sai wanda ya gani.
A ɗango na sha huɗu kuwa,
ya ɗauko salon yadda idan iskokin sun fara zuwa ne, akan samu baƙin zane gwado (na saƙi) ko kuma fari a rufe wanda za a
girka a ciki. Haka zai yi ta murƙususu, duk zafin da ake yi haka zai kwanta a
cikin wannan zane, ana ta gayyato masa iskoki daban-daban. Ya ci gaba da bayyana
yadda Hausawa suka yarda cewa idan aka yi irin waɗannan abubuwa ne kawai
iskokin za su zo. Tun farko akan yi ƙunshi, a hannu da ƙafafu, a sanya tozali a
idanu ya ri raɗau. A kuma tauna goro, leɓɓa su ja wur! Duk da nufin iskokin su
lamince wa wanda ake son a yi wa girka. Sai kuma a kunna wasu irin turarukan
wuta, masu wani irin ƙamshi mai tayar da hankali, wanda a Bahaushiyar al’ada
ake ganin da su ne ake kiran iskokin.
17.
Jagora:
Ɗirkaniyar kiran ‘yankogo wane mutum ya rushe girka,
Amshi:
Bauri da Bori ware bare,
18.
Jagora: In an yi katarin haɗa komai sai ran
shigar su wa Dokin ka,
Amshi: Ya
bankaɗo Bahaushen girka
19.
Jagora: Mai kacakaura ga su Garaya sautin a
gane taken Iska,
Amshi: Baubauniya
rawarsu ta dauri,
20. Jagora: Gaɗa Ira’izai an ca-cum ga Julkukuwa
mutanen girka.
A ɗangwaye na 17 da 18 19
da kuma 20, Mawaƙin ya yi wani jawabi ne da nufin yana da matuƙar wahala, irin
yadda tunanin Bahaushe ya ginu a kan Bori da girka, wani ko wasu da rana tsaka,
su ce za su iya hana wannan addini na Bori. Kasancewar daɗaɗɗiyar al’ada ce tun
kafin zuwan musulunci ƙasar Hausa. Shi yasa yake ganin ba abu ne mai sauƙi ba a
iya kawo ƙarshen wannan al’ada ta Bori da girka ba a nan kusa. Sai kuma ya ci
gaba da cewa, idan duk an gama harhaɗa waɗannan kayayyaki da aka ambata a baya,
sai kuma a sa ranar da za a gayyato waɗannan iskoki da za su zo su hau kan
wanda ake son a girka.
21.
Jagora: Kafin zama
Bahaushen girka kwana bakwai ake bisa girka,
Amshi:
Bauri da Bori ware bare,
22.
Jagora: An sha wuyar dare da ta rana an sha
tsumi na baurin girka.
Amshi: Ya
bankaɗo Bahaushen girka.
23.
Jagora : Bishiya ta goruba ko tsamiya a gurin
da za wanke girka,
Amshi:
Baubauniya rawarsu ta dauri,
Jagora: Wankan fita fita daga girka daɗa ya
zamo Bahaushen girka
A ɗangwayen sama kuma
Mawaƙin yana ƙoƙarin rufe waƙarsa da bayanin abubuwan da suke faruwa, idan an
kamala aikin girka. Kamar yadda y ace ‘an sha wuyar dare da ta rana, a nan yana
nufin yawan kwanakin da ake kwashewa kafin a kammmala wannan aiki kamar yadda
aka yi bayani a baya. A ƙarshe kuma ya bayyana cewa bayan duk an gama irin
wannan aiki na girka, shikenan mutum ya zama Bahaushen girka. wato ya zama
cikakken ɗanBori, ko kuma wani ƙasurgumin boka, da ake ji da shi a yankinsu.
Domin a yanzu yana da alaƙa da iskoki da yawa, da za su riƙa yi masa hidima. Suna
kafa masa wasu sharuɗɗa da dokoki da zai riƙa bi. Za ka samu wani a ce kar ya
sake cin nama sai kifi ko kar ya sake yin wanka, ko kuma ya yanka dabba iri
kaza kamar baƙin Ɗan akuya ko baƙar Kaza, ko dai wani lamari da yake da alaƙa
da bayar da magani. Su kuma waɗannan iskoki, sai yu yi ta biya masa buƙatu.
Kammalawa
Abin lura a wannan ‘yar
muƙala shi ne, an
fito da irin al’adun da ke cikin aikin bori da girka. An yi hakan ne ta amfani
da waƙar ‘Bahaushen girka’ wacce ta zamo kanwa uwar gami wajen zaƙulo irin waɗannan
al’adu. Haka kuma kayayyakin da ake yin girka, kamar yadda mawaƙin ya bayyana,
sun taimaka ainun wajen samar da wannan takarada. Sai dai za a iya ganin sauye-sauye
ko bambancin wasu al’adu a cikin wannan aiki. Ƙila hakan ya samo asali ne da
yadda ƙasar Hausa ke da yawa. Kamar yadda ake samun kare-karen harshe daga waje
zuwa waje, haka nan dole a samu bambancin al’adu. Kuma an kawo su ne ta yadda
mawaƙin Bahaushen girka, wato Malam Sulaiman Ahmad Tijjani, mai laƙabin
Farfesan waƙa ya zayyano a cikin waƙarsa.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
Rataye
S/N |
Kalma |
Ma’anar
Kalmar |
1. |
Girka |
Girka
mutum ya zama ƊanBori |
2. |
Baubauniya |
Rawar
da ‘YanBori ke yi/ faɗuwa da ake yi |
3. |
Turjiya |
Dagiya ka ƙin
yin abu |
4. |
Turka-turka |
Gwagwarmayar
ana tura ka kana turjewa |
5. |
Doki |
Waanda
ake so Aljanu su hau kansa |
6. |
Tsagwaro |
Abu
da yawa |
7. |
Tsambauri |
Tsananin
bauri |
8. |
Tsumi |
Jiƙaƙƙen
sassaƙe-sassaƙe da saiwoyi |
9. |
‘Ya’yan
wuri |
Hular ijiya |
10. |
Warki |
Wani bante ne na
fata mai maɗaurai da ake ɗaurawa ƙugu |
11. |
Jinka |
Ɗanboto |
12. |
Sandar
dargaza |
Wata sanda da
‘YnBori ke amfani da ita |
13. |
Kacakaura |
Wani abin kaɗawa
mai fitar da sauti |
14. |
Hurtumi |
Ƙasurgumin namijin
Sa mai tsananin faɗa |
15. |
Asirka |
Hujin hancin da
ake yi wa shanun huɗa |
16. |
Ɗirkaniya |
Wani aikin da ya
fi ƙarfin ka, amma k adage sai ka yi |
17. |
Gaɗa |
Wasan dandali na
‘yammata |
18. |
Ca-cum |
Taruwar abu da
yawa |
19. |
Tukku |
Kaza ko Zakaran
da yake da wani tudun gashi a kan sa |
20. |
Ɓurgu |
Namijin gafiya
da ya gawurta |
21. |
Ƙwanƙwabilo |
Babban birnin
Aljanu |
22. |
Dogo |
Sunan Aljani |
23. |
Inna |
Sunan uwar
Aljanu |
24. |
Jilkukuwa |
Sunan wata
Aljana |
25. |
Ƙwanƙwamai |
Jam’in sunan
Aljanu |
26. |
Iska |
Sunan Aljana |
27. |
Ira’izai |
Sunan Aljanu |
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.